Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana tsuntsuwa Talipaku da Kurciya suka yi sheƙa a bishiya ɗaya. Da lokacin saka ƙwan da suka ɗauka ya zo, sai suka haɗa ƙwansu a wuri ɗaya. Bayan sun gama kwanci, sai suka ƙyanƙyashe ƙwayayensu, suka sami ’ya’yansu guda biyu.
Suna nan a haka, kullum sai su fita neman abincin’yan tsakinsu. Kansu ya haɗu, komai na tafiya rumui-rumui. To ashe ita Talipaku ba ta jin daɗi da bakin ’yarta ya yi tsawo fiye da na’yar Kurciya, wadda ba wani abu da ya dami ’yarta, kyakkyawar gaske. Duk lokacin da za su fita neman abincin ’ya’yansu, sai a karɓi renon’yar Kurciya, amma a bar ’yar Talipaku a sama cikin sheƙa.
Shi ke nan sai wata rana Talipaku ta yanke shawarar sace ’yar Kurciya ta gudu da ita. Wata rana suna wurin neman abinci, sai Talipaku ta sulale, ta je ta sace ’yar Kurciya ta gudu da ita. Da Kurciya ta ɗaga kai ba ta ga Talipaku ba, kuma suna daf da tafiya gida, kuma ta nemi ƙawarta har ta gaji, sai ta dawo gida ita kaɗai.
Da ta shiga sheƙa, sai ta ga ba ’yarta, sai ɗiyar Talipaku. Sai ta fita ta kama cigiya. Sai
aka ce mata ai an ga Talipaku ta ɗauki ’yar Kurciya sun yi yamma. Da jin haka sai Kurciya ta koma sheƙarsu ta ɗauki ’yar Talipaku ta fito fur ta kama waƙa tana cewa:
“Talipaku, Talipaku,
Don bambancin ’ya’ya,
Nawa a gabanki,
Naki a bayana,
Kika ɗauki mai kyau,
Kika bar mummuna.
Garinmu, garinmu,
Garinmu da Sarki,
Mai yawa in kin je,
Sai idonki ya ɓata,
Mu je mu, mu je mu.”
Haka dai ta dinga yin wannan waƙa, tana tafiya tana ci gaba da bincike har ta haɗu da wasu manoma. Sai ta gaishe su, suka amsa, sai ta tambaye su ko sun ga Talipaku ta wuce? Sai suka ce: “E, tun ɗazu ta wuce.” Kurciya ta ɗauki ’yar Talipaku tana waƙa ta ci gaba da tafiya ta je wajen masu kiwo, sai ta tambaye su ko sun ga Talipaku? Sai suka ce: “E, ba ta daɗe da barin wurin nan ba.”
Haka dai Kurciya ta ci gaba da tafiya tana waƙa, tana tambaya. Ita kuwa Talipaku tuni har ta isa garin Sarkin tsuntsaye ta tambayi hanyar gidan Sarkin. Aka kai ta gidan Sarkin tsuntsaye. Sunan Sarkin Miki. Da ta je gaban Sarkin, sai Sarkin ya tambayi Talipaku ko me ke tafe da ita?
Sai tace ta zo ne ita da ’yarta a ba su wuri a garin domin ta zauna. Da Miki ya ji haka, sai ya ce: “To ai ’yar da kika zo da ita ba ta yi kama da ke ba. Ba ’yarki ba ce. Ina kika samo ta?” Ita kuwa Kurciya tuni ta haɗu da wasu mutane a jeji ta tambaye su ko sun ga Talipaku?
Sai suka gaya mata cewa yanzu ta tambaye su hanyar gidan Sarkin tsuntsaye. Sai suka nuna wa Kurciya hanyar, suka ce ta yi sauri ko ta same ta a gidan Sarkin tsuntsaye. Nan take ta kama hanyar zuwa gidan Sarkin tsuntsaye. Tana zuwa gidan, sai ta tarar ana tambayar Talipaku a inda ta samo’yar da ba ita ta haifa ba.
Sai Kurciya ta fara rera waƙa ta faɗi a gaban Sarkin tsuntsaye ta yi gaisuwa, ta kuma yi wa Sarki bayani a kan yadda suka yi da Talipaku. Sai Sarkin ya sa aka ƙwace ’yar Kurciya, aka ba ta ’yarta. Ita ma Talipaku aka ba ta ’yarta. Sarkin tsuntsaye ya ja kunnen Talipaku da kada ta kuskura ta sake satar ’yar wani tsuntsu.
Idan kuma aka sake kawo ƙararta, to za a kashe ta. Sai aka sallame su. Kurciya ta ɗauki ’yarta. Ta yi godiya ta tafi. Ita kumaTalipaku ta tafi da ’yarta. Ƙurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Maciyi amana ba shi da mabuya a duniya.
- Baƙin ciki da abin da Allah ya yi wa wani ba zai ƙara komai ba sai faɗawa cikin wahala.
- Maci amana yana tare da jin kunya.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Yarima Da Labbi
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu










