Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙanzo - Tana nufin ragowar abincin da ke maƙalewa a cikin tukunya idan an gama girki.
Misali; Idan an gama tuwo, za mu kwashi ƙanzo don mu shanya.
ENG; Scraps of food stuck to the pot (A turance tana nufin ƙanzo)
Ƙanƙamo - Tana nufin mutum mai rowa, wanda baya son yin kyauta.
Misali; Wannan mutumin ƙanƙamo ne, baya son taimakon kowa da kuɗinsa.
ENG; Stingy (A turance tana nufin ƙanƙamo.)
Ƙanƙance - Tana nufin raguwa ko komawa ƙarami.
Misali; Idonsa ya ƙanƙance saboda ciwon da yake yi.
ENG; Become small (A turance tana nufin ƙanƙance.)
Ƙanƙani - Tana nufin abu ƙarami ko mara girma.
Misali; Na sayi ƙanƙanin littafi domin yara su riƙa karantawa.
ENG; Small (A turance tana nufin ƙanƙani.)
Ƙanƙara - Tana nufin ruwa da ya daskare sakamakon tsananin sanyi.
Misali; A lokacin sanyi, ana iya ganin ƙanƙara a saman ruwa.
ENG; Ice (A turance tana nufin ƙanƙara)
Ƙara - Tana nufin yin koke ko bayyana rashin jin daɗi game da wani abu don neman ɗaukan mataki.
Misali; Ya je ofishin shugaban makaranta domin ya kai ƙara kan rashin adalcin da aka yi masa.
ENG; Complain (A turance tana nufin ƙara.)
Ƙara - Tana nufin maimaita wani abu ko yin sa sau biyu ko fiye.
Misali; Malam ya ce a ƙara karanta darasin domin a fahimce shi sosai.
ENG; Repeat (A turance tana nufin ƙara)
Ƙaraji - Tana nufin ihu ko kuka mai ƙarfi saboda ciwo ko wahala.
Misali; Yaron ya yi ƙaraji lokacin da ya faɗi ya ji rauni.
ENG; Crying out in pain (A turance tana nufin ƙaraji)
Ƙarambau - Tana nufin cutar fata da ke sa ƙuraje ƙanana masu ruwa su fito a jiki, musamman ga yara.
Misali; Yaron ya kamu da ƙarambau, don haka ba ya zuwa makaranta har sai ya warke.
ENG; Chickenpox (A turance tana nufin ƙarambau)
Ƙaranci - Tana nufin rashin isa ko rashin wadata ko rashin kai wa wani adadi.
Misali; Akwai ƙarancin abinci a kasuwa saboda ana fama da fari.
ENG; Shortage (A turance tana nufin ƙaranci)