Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙalau - Tana nufin sosai ko matuƙa. Misali; Shanyin ya yi sanyi ƙalau sai an sake dafa shi. ENG; Very (A turance tana nufin ƙalau.)
Ƙam-ƙam - Tana nufin riƙe abu da ƙarfi. Misali; Ya kamata mu riƙe addini ƙam-ƙam domin inganta rayuwarmu. ENG; Tightly (A turance tana nufin ƙam-ƙam)
Ƙamfa - Tana nufin rashin wani abu ko ƙarancinsa. Misali; An samu ƙamfar ruwa a ƙauyen saboda rashin zuwan ruwan sama. ENG; Lack/Shortage (A turance tana nufin ƙamfa)
Ƙamshi - Tana nufin shaƙar daddaɗar iska. Misali; Furen nan yana da ƙamshi mai daɗi. ENG; Fragrant (A turance tana nufin ƙamshi)
Ƙamusu - Tana nufin littafin da ke ƙunshe da rubutattun kalmomi da ma'anarsu. Misali; Dalibi ya duba ƙamus domin ya fahimci ma’anar kalmar. ENG; Dictionary (A turance tana nufin ƙamusu)
Ƙandare - Tana nufin bushewa ko zama babu ruwa. Misali; Rijiyar ta ƙandare saboda tsananin zafi. ENG; Become dry (A turance tana nufin ƙandare)
Ƙandas - Tana nufin abu mara maiƙo ko wanda man sa ya ƙare. Misali; Miyar nan ta yi ƙandas saboda babu mai sosai a ciki. ENG; Lacking oil (A turance tana nufin ƙandas)
Ƙani - Tana nufin ɗan’uwa namiji wanda yake bin wasu ma'ana yayye. Misali; Ƙanina yana makaranta tare da abokansa. ENG; Younger brother (A turance tana nufin ƙani)
Ƙanjame - Tana nufin ramewa ko sirancewa. Misali; Ya ƙanjame sosai bayan doguwar jinyar da ya yi. ENG; Become thin (A turance tana nufin ƙanjame)
Ƙanwa - Tana nufin ‘yar’uwa mace wadda take da yayye. Misali; Ƙanwata tana makarantar firamare. ENG; Younger sister (A turance tana nufin ƙanwa.)
1 324 325 326 327 328 337