Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Fa’ida - Tana nufin amfanin abu. Misali; Zumunci yana da fa'ida don yana sa albarka a rayuwa. ENG; Usefulness (A turance tana nufin fa'ida) Kishiyarta; Rashin Fa'ida
Fabrairu - Wata ne na biyu a shekara.  Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar. ENG; February(A turance yana nufin wata na biyu a shekara)
Facaka - Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba. Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi. ENG; Squandering (A turance tana nufin facaka)
Face - Tana nufin sai dai. Misali; Babu wanda zai makara face ya kasance mai saɓa alƙawari. ENG; Except (A turance tana nufin face)
Face - A turance tana nufin fuska. Misali; Ta mare shi a fuska hakan ya janyo suka fara faɗa. HAU; Fuska (Tana nufin sashen jiki mai ƙunshe da ido da hanci da baki)
Faci - Tana nufin sacewar taya. Misali; Tayar keken ta yi faci sai an an gyaro. ENG; Patch (A turance tana nufin faci)  
Facial Markings - A turance tana nufin jarfa. Misali; Jarfa, gadon gidansu ne. HAU; Jarfa (Tana nufin tsagun fuska)
Fade - A turance tana nufin koɗe.  Misali; Atamfar ta koɗe saboda ta sha wanki a kai a kai. HAU; Koɗe (Tana nufin canja yanayi ko launi musamman sakamakon jin jiki)
Fade - A turance tana nufin ƙoƙe. Misali: Launin zanen ya ƙoƙe saboda yawan wankewa da take yi. HAU: Ƙoƙe (Tana nufin dusashewa ko raguwar launi)
Faffaɗar Jami’ar Najeriya - National Open University Of Nigeria (NOUN)
1 2 3 19