Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ulcerated Wound - A turance tana nufin gyambo.
Misali; Ai gyambon da ke ƙafarsa ya daɗe sosai.
HAU; Gyambo (Tana nufin ciwon da ba ya warkewa ko kuma ya daɗe bai warke ba)
Uncle - A turance tana nufin kawu.
Misali; A cikin mutanen da suka zo har da Kawu, shi ne ma ya jagoranci tafiyar.
HAU; Kawu (Tana nufin wa ko ƙanin mahaifi ko mahaifiya)
Uncompleted Building - A turance tana nufin kango.
Misali; Har yanzu ginin kango ne ba a ƙarasa ba.
HAU; Kango (Tana nufin ginin da ba a kammala ba)
Understand - A turance tana nufin fahimta.
Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske.
HAU; Fahimta (Tana nufin ganewa)
Kishiyarta; Rashin Fahimta
Understand - A turance tana nufin gane.
Misali; Ina fatan kun gane abinda nake nufi?
HAU; Gane (Tana nufin fahimta)
Kishiyarta; Rashin Ganewa
Ungrateful - A turance tana nufin butulu
Misali; Cindo butulu ne saboda ya butulcewa maigidansa a kasuwa.
HAU; Butulu (Tana nufin wanda yake manta alkahairin da aka yi masa)
Union - Tarayya, Gamayya, Ƙungiya
United Labour Congress (ULC) - Gamayyar Ƙungiyoyin Ƙwadago
United Nations (UN) - Majilisar Ɗinkin Duniya
United Nations Development Program (UNDP) - Shirin Bunƙasa Ƙasashe Na Majilisan Ɗinkin Duniya