Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Quantity Surveyors Registration Board Of Nigeria (QSRBN) - Hukumar Maƙiyasta Kayan Gini Ta Najeriya
Quarrel - A turance tana nufin faɗa. Misali; Ɗaliban faɗa suke bayan an tashi daga makaranta. HAU;Faɗa (Tana nufin ɗaga murya da faɗin maganaganu marasa daɗi saboda ɓacin rai)
Quarter of yard -

A turance tana nufin kwata.

Misali: Ta sayi kwata na yadi domin ɗinka gyale.

HAU; Kwata (Tana nufin rubu’in yadi ko wani ɓangare ɗaya cikin huɗu na awo)

Quick Action/ Haste - A turance tana nufin garaje. Misali; Indo tana da garaje, shi yasa ta zubar da niƙan. HAU; Garaje (Tana nufin hanzari ko sauri ko zafin nama)
Quick-Tempered - A turance tana nufin ƙufula. Misali; Ƙufula ya yi har ta kai ga ya mare shi. HAU; Ƙufula (Tana nufin saurin fushi)
Quiver -

A turance tana nufin kwari.

Misali; Maharbin ya ɗauki kwari cike da kibiyoyi.

HAU; Kwari (Tana nufin akwati ko jakar da ake ɗaukar kibiyoyi a ciki lokacin harbin kibiya)