Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ear - A turance tana nufin kunne.
Misali; Yara na yawan yin ciwon kunne musamman lokacin sanyi.
HAU; Kunne (Tana nufin gaɓar da ake ji da ita)
Economic Financial Crime Commission (EFCC) - Hukumar hana ta'adin tattalin arziki
Eczema - A turance tana nufin kirci.
Misali; Abin da yasa almajirai suke yin kirci shi ne rashin wanka.
HAU; Kirci (Tana nufin wasu ƙuraje masu matuƙar ƙaiƙayi da ke fitowa a fata sakamakon rashin tsabta)
Education Trust Funds (ETF) - Asusun Tallafawa llimi
Egg Shell - A turance tana nufin kamɓori.
Misali; Ana haɗa hoda wacce mata ke shafawa da kamɓori.
HAU; Kamɓori (Tana nufin ɓawo ko kwanson ƙwai)
Either/Or - A turance tana nufin imma.
Misali; Ka zaɓi ɗaya, imma makarantar kwana ko ta je-ka-ka-dawo.
HAU; Imma (Tana nufin ko)
Electric Fan - A turance tana nufin fanka.
Misali; An kunna fanka a ɗakin saboda yau ana zafi.
HAU: Fanka (Tana nufin na'urar da ke ba da iska)
Elephant - A turance tana nufin giwa.
Misali; Giwa tana da manyan kunnuwa masu faɗi.
HAU; Giwa (Tana nufin wata dabbar daji mai girma, ita ce mafi gima a cikin dabbobin da suke doron ƙasa)
Emir’s Bodyguard - A turance tana nufin dogari.
Misali; Tanimu dogari ne a masarautar Kano.
HAU; Dogari (Tana nufin masu ba wa sarki tsaro)
Empty container - A turance tana nufin fanko.
Misali; Gwangwanin fanko ne.
HAU; Fanko (Tana nufin babu komai)