Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Nail - A turance tana nufin ƙusa. Misali: Kafintan ya buga ƙusa a jikin bencin da ya karye. HAU: Ƙusa (Tana nufin wani nau'in ƙarfe mai tsini daga ƙarshensa wanda ake amfan da shi wajen haɗe katako ko a buga a bango don rataye abu)
Naked State - A turance tana nufin gaya. Misali; Ta dama min fura gaya, ba nono bare suga. HAU; Gaya (Tana nufin tsura ko tsirara)
Nape of the neck - A turance tana nufin ƙeya. Misali: Mutumin ya ji ciwo a ƙeya bayan ɗaukar kaya masu nauyi. HAU: Ƙeya (Tana nufin bayan wuya, wato sashen da ke tsakanin kai da kafaɗa)
Nation - A turance tana nufin al'umma. Misali; Al'ummar Hausawa na da ɗimbin tarihi. HAU; Al'umma (Tana nufin mutane ko jama'ar wani yanki)
National Root Crops Research Institute (NRCRI) - Cibiyar Nazarin Amfanin Gona Mabunƙusa-ƙasa Ta Najeriya
National Transport Commission (NTC) - Hukumar Sufuri Ta Ƙasa
National Aeronautics & Space Administration (NASA) - Hukumar Binciken Sararin Samaniya
National Agency for Food & Drugs Administration & Control (NAFDAC) - Hukumar Ingancin Abinci Da Magunguna ta Ƙasa
National Agency for Prohibition of Trafficking in Persons (NAPTIP) - Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa
National Agency for Science & Engineering Infrastructure (NASENI) - Hukumar Kimiyya da Ƙirƙirar Ababen More Rayuwa Ta Ƙasa
1 2 3 31