Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙaba - Tana nufin ciwon da mutum yake ji a sassa daban-daban na jiki musamman a ciki. Misali; An yi masa aikin ƙaba satin da ya gabata. ENG: Pain felt in various parts of the body (A turance tana nufin ƙaba)
Ƙabila -

Tana nufin rukunin mutane masu asali, al’ada da harshe iri ɗaya.

Misali; Hausa wata babbar ƙabila ce a Najeriya.

ENG; Tribe (A turance tana nufin ƙabila).

Ƙadandoniya -

Tana nufin wani ƙwaro mai ƙafafu da yawa.

Misali: Yara sun ga ƙadandoniya a bayan gida.

ENG: Large millipede (A turance tana nufin ƙadandoniya).

Ƙadangare -

Tana nufin dabba mai rarrafe da ake yawan gani a bango ko ƙasa.

Misali: Ƙadangare ya hau bangon ɗaki.

ENG: Lizard (A turance tana nufin ƙadangare).

Ƙaddara -

Tana nufin abin da Allah ya riga ya tsara ko ya hukunta zai faru.

Misali: Komai yana faruwa ne bisa ƙaddarar Allah.

ENG: Predestine (A turance tana nufin ƙaddara)

Ƙafa -

Tana nufin sashen jikin mutum ko dabba da ake amfani da shi wajen tafiya.

Misali: Ya ji ciwo a ƙafarsa sakamakon faɗuwa da ya yi a filin ƙwallo.

ENG: Leg / Foot (A turance tana nufin ƙafa).

Ƙafe -

Tana nufin abu ya bushe, babu ruwa ko danshi a ciki.

Misali: Kogin ya ƙafe tun bayan da damina ta wuce.

ENG: Dry (A turance tana nufin ƙafe).

Ƙaga -

Tana nufin ƙirƙirar wani sabon abu wanda ba a taɓa yin irinsa ba.

Misali; Masanin ya bayyana sabuwar na'urar da ya ƙaga.

ENG; Invent (A turance tana nufin ƙaga).

Ƙagauta -

Tana nufin jin gaggawa ko tsananin son yin wani abu.

Misali: Yaron ya ƙagauta ya je makaranta yau.

ENG: Be eager (A turance tana nufin ƙagauta).

Ƙage -

Tana nufin jiki ko wani sashen jiki ya yi tauri ko ya daskare na ɗan lokaci, yawanci saboda tsoro, sanyi ko jin zafi.

Misali; Wuyansa ya ƙage bayan ya yi tsalle ya faɗo daga sama.

ENG: Become temporarily stiff (A turance tana nufin ƙage).

1 2 3 17