Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tana nufin sashen jikin mutum ko dabba da ake amfani da shi wajen tafiya.
Misali: Ya ji ciwo a ƙafarsa sakamakon faɗuwa da ya yi a filin ƙwallo.
ENG: Leg / Foot (A turance tana nufin ƙafa).
Tana nufin abu ya bushe, babu ruwa ko danshi a ciki.
Misali: Kogin ya ƙafe tun bayan da damina ta wuce.
ENG: Dry (A turance tana nufin ƙafe).
Tana nufin ƙirƙirar wani sabon abu wanda ba a taɓa yin irinsa ba.
Misali; Masanin ya bayyana sabuwar na'urar da ya ƙaga.
ENG; Invent (A turance tana nufin ƙaga).
Tana nufin jin gaggawa ko tsananin son yin wani abu.
Misali: Yaron ya ƙagauta ya je makaranta yau.
ENG: Be eager (A turance tana nufin ƙagauta).
Tana nufin jiki ko wani sashen jiki ya yi tauri ko ya daskare na ɗan lokaci, yawanci saboda tsoro, sanyi ko jin zafi.
Misali; Wuyansa ya ƙage bayan ya yi tsalle ya faɗo daga sama.
ENG: Become temporarily stiff (A turance tana nufin ƙage).
Tana nufin zargin mutum da wani abu da be aikata ba ko ba tare da hujja ba.
Misali: An yi masa ƙagen ya saci kuɗi.
ENG: False accusation (A turance tana nufin ƙage)
Tana nufin wani abu mai ƙarfi da ke fitowa a kan dabba kamar shanu, awaki ko tumaki.
Misali: Shanu suna da ƙaho a kansu.
ENG: Horn (A turance tana nufin ƙaho)
Tana nufin wani abu mai kaifi da ke fitowa a ƙafar dabba (musamman zakara ko wasu tsuntsaye) da suke amfani da shi wajen kare kai ko faɗa.
Misali; Zakara yana amfani da ƙaiminsa wajen faɗa.
ENG; Spur (A turance tana nufin ƙaimi)
Tana nufin jin son sosa wani guri ko sashen jiki.
Misali: Yana jin ƙaiƙayi a hannunsa bayan sauro ya cije shi.
ENG: Itching (A turance tana nufin ƙaiƙayi)