Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ɗazu - Tana nufin lokacin da be daɗe da wucewa ba.
Misali; Ɗazu na dawo daga gidan bikin.
ENG; A moment ago (A turance tana nufin ɗazu)
Kishiyarsa; Yanzu
Ɗaɗɗoya - Tana nufin wani ganye mai ƙamshi wanda ake magani da shi.
Misali; An yi amfani da ganyen ɗaɗɗoya wajen haɗa maganin.
ENG; A fragrant herb (A turance tana nufin ɗaɗɗoya)
Ɗigil - Tana nufin ɗan gajere ko ƙanƙani.
Misali; Na ga wani ɗan ɗigil a kasuwa yau.
ENG; Very Short (A turance tana nufin ɗigil)
Ɗimbi - Tana nufin da yawa.
Misali; Muna miƙa godiya mai ɗimbin yawa ga waɗanda suka samu damar zuwa taron buɗe kamfaninmu.
ENG; Superabundance (A turance tana nufin ɗimbi)
Ɗingishi - Tana nufin yin tafiya ba daidai ba, ana yi ana dakatawa saboda dalilin ciwo a ƙafa ko wani abu daban.
Msali; Ɗingishi take yi saboda marurun da ya fito a ƙafarta.
ENG; Limping (A turance tana nufin ɗingishi)
Ɗoyi - Tana nufin tsananin wari.
Misali; Kwatar ɗoyi take tun safe da aka kwashe.
ENG; Stench (A turance tana nufin ɗoyi)
Ƙaba - Tana nufin ciwon da mutum yake ji a sassa daban-daban na jiki musamman a ciki.
Misali; An yi masa aikin ƙaba satin da ya gabata.
ENG: Pain felt in various parts of the body (A turance tana nufin ƙaba)
Ƙabila -
Tana nufin rukunin mutane masu asali, al’ada da harshe iri ɗaya.
Misali; Hausa wata babbar ƙabila ce a Najeriya.
ENG; Tribe (A turance tana nufin ƙabila).
Ƙadandoniya -
Tana nufin wani ƙwaro mai ƙafafu da yawa.
Misali: Yara sun ga ƙadandoniya a bayan gida.
ENG: Large millipede (A turance tana nufin ƙadandoniya).
Ƙadangare -
Tana nufin dabba mai rarrafe da ake yawan gani a bango ko ƙasa.
Misali: Ƙadangare ya hau bangon ɗaki.
ENG: Lizard (A turance tana nufin ƙadangare).