Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙarangiya - Tana nufin wata irin ciyawa mai ƙaya da ke manne wa tufafi ko fata. Misali; Yara sun guji shiga cikin ƙarangiya saboda suna tsoron kar ta manne musu. ENG; Grass with prickly burrs (A turance tana nufin ƙarangiya.)
Ƙararrawa -

Tana nufin wani abu na ƙarfe da ake bugawa mai ƙara, wanda ake amfani da shi wajen sanarwa ko faɗakarwa.

Misali; An buga ƙararrawa domin ɗalibai su shiga aji.

ENG; Bell (A turance tana nufin ƙararrawa)

Ƙarasa -

Tana nufin kammala wani abu ko kaiwa ƙarshe.

Misali; Na ƙarasa aikin gida kafin dare ya yi.

ENG; Finish (A turance tana nufin ƙarasa)

Ƙare - Tana nufin kammala wani abu gaba ɗaya ko gamawa da shi. Misali; Ta ƙare karatun littafin cikin kwana biyu. ENG; Complete (A turance tana nufin ƙare)
Ƙarfafa - Tana nufin maganganun da ke ba da ƙwarin gwuiwa ga wanda ake yi wa su. Misali; Malamin yana ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa don su riƙa yin karatu sosai. ENG; Strengthen (A turance tana nufin ƙarfafa)
Ƙarfamfana - Tana nufin datti ko ƙura da ke taruwa a cikin aljihu. Misali: Ya wanke ƙarfamfana da ke cikin aljihunsa kafin ya sa rigar. ENG: Dirt inside pocket (A turance tana nufin ƙarfamfana)
Ƙarfe - Tana nufin wani irin abu mai ƙarfi da ake amfani da shi wajen ƙera kayayyaki kamar ƙofa, mota, ko cokali da sauransu. Misali: Ma’aikacin ya sa ƙofar ƙarfe a shagon. ENG: Metal (A turance tana nufin ƙarfe)
Ƙarfi - Tana nufin kuzarin da mutum yake da shi ko ikon aikata aiki. Misali: Ma'aikatan na buƙatar ƙarfi domin ɗaga kaya masu nauyi.. ENG: Strength (A turance tana nufin ƙarfi).
Ƙari - Tana nufin ƙara wani abu fiye da yadda yake a da. Misali: Farashin kaya ya ƙaru a wannan watan. ENG: Increase (A turance tana nufin ƙari ko ƙaruwa).
Ƙari - Tana nufin dafin  ƙudan zuma, maciji ko kunama da ke jawo zugi ko kumburi. Misali: An cire masa ƙari bayan kunama ta harbe shi. ENG: Sting of bee (A turance tana nufin ƙari).
1 326 327 328 329 330 337