Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙarko - Tana nufin ƙarfin ko juriya ko daɗewa.
Misali: Wannan kujera tana da ƙarko sosai saboda an yi ta da katako mai kyau.
ENG: Durability (A turance tana nufin ƙarko).
Ƙarni - Tana nufin shekaru ɗari.
Misali: Wannan gini ya wanzu tun ƙarni da ya gabata.
ENG: Century (A turance tana nufin ƙarni).
Ƙaro - Tana nufin wani abu mai ɗanko da ke fitowa a jikin bishiya.
Misali: Ana amfani da ƙaro wajen yin tawadar da ake rubutu.
ENG: Gum (A turance tana nufin ƙaro).
Ƙarshe - Tana nufin kankat wato daga nan ba ƙari ko cigaba.
Misali: Fim ɗin da muke gani ya zo ƙarshe.
ENG: End (A turance tana nufin ƙarshe).
Ƙaru - Tana nufin ƙaruwa ko ƙara yawa.
Misali: Yawan ɗalibai ya ƙaru a makarantar wannan shekara.
ENG: Increase (A turance tana nufin ƙaru).
Ƙarya - Tana nufin faɗin magana wadda ba gaskiya ba.
Misali: Ya faɗi ƙarya domin ya gujewa hukunci.
ENG: Lie (A turance tana nufin ƙarya).
Ƙaryata - Tana nufin ƙin amincewa da wani abu ko musanta shi.
Misali: An zarge shi da laifi amma ya ƙaryata hakan.
ENG: Deny (A turance tana nufin ƙaryata).
Ƙarzuwa - Tana nufin cutar fata da ƙazanta ke haifarwa, inda ƙananan ƙuraje ke fitowa a sassan jiki.
Misali: Ƙarzuwa na iya yaɗuwa cikin sauri idan ba a kula da tsafta ba.
ENG: Scabies (A turance tana nufin ƙurajen fata masu ƙaiƙayi)
Ƙarƙashi - Tana nufin abin da yake ƙasa.
Misali: Katin ya faɗi a ƙarƙashin tebur.
ENG: Underneath (A turance tana nufin ƙarƙashi).
Ƙasa - Tana nufin duniyar da muke rayuwa a kanta.
Misali: Allah ya yi halittu masu yawa a doron ƙasa.
ENG: Earth (A turance tana nufin ƙasa).