A yau za mu koyi yadda ake miyar ƙoda; Miyar ƙoda miya ce da ake iya cin shinkafa, taliya, da makamantansu. Ƙoda na da matuƙar amfani a jikin mutum.
Abubuwan da ake buƙata
- Ƙoda
- Mai
- Maggi
- Gishiri
- Curry
- Attaruhu da tattasai
- Albasa
Yadda ake haɗawa
- A zuba mai a tukunya kaɗan a saka albasa.
- A wanke ƙodar a zuba, sai a ɗan bar ta, ta yi ‘yan mintuna ruwanta su fito, sai a zuba maggi, curry.
- Idan ya tafaso sai a zuba yankakken karas da aka gyara, a bar shi ya dahu sai a sauke.
Domin sanin Yadda Ake Kunun Aya danna nan