A yau za mu koyi yadda ake masar dankalin Turawa.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Dankalin Turawa
- Attarugu
- Albasa
- Ƙwai
- Gishiri da magi
- Kori
Yadda Ake Haɗawa
- A fere dankali, sai a ɗora shi a wuta, ya nuna ya yi luguf sosai.
- Sannan sai a ɗauko roba ko kwano mai zurfi a zuba a ciki.
- A ɗebo ƙwai mai ɗan dama a fasa a kan dankalin.
- Sai a samu ludayi a dama dankalin da ƙwan, har sai sun haɗu sosai.
- Sai a debo albasa da attarugu a jajjaga, su sannan a zuba a kan haɗin dankalin da magi da gishiri da kori daidai kayan ɗanɗano,
- Kuma a sake dama haɗin domin kayan hadin su shiga dankalin sosai.
- A ɗauko tanda a dora a kan wuta, a zuba man gyada a kowane gida sannan a ɗebo ƙullun dankalin a zuba a kowane gidan tandar.
- Sai a ɗan ba shi mintuna, domin dahuwar cikin masar, idan gefe ɗaya ya yi, sai a sake juya wainar zuwa dayan gefen har sai ta nuna kafin a sauke daga wuta.
Domin sanin Yadda Ake Lemon Ardeb danna nan.