Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.
A yau za mu koyar da yadda ake Mini Pizza; ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.
Abubuwan Buƙata:
- Biredi
- Tomato sauce
- Yankakkiyar albasa
- Yankakken Tumatur
- Koren tattasai yankakke
Yadda Ake Haɗawa
- A ɗauko biredi sai a yanka zuwa ƙawanya (round shape).
- Sai a shafa “tomato sauce”, a yaryaɗa albasa, tumatir da koren tattasai.
- A goga mozzarella cheese a saman haɗin biredi.
- Cikin oven mai zafi, sai a saka haɗin biredin har sai mozarella cheese ya fara narkewa.
- A ci lafiya.
Domin koyon Yadda Ake Grilled Cheese And Corn Sandwich danna wannan koren rubutun.