Hadisai da dama sun zo kan bayanin siffofin wutiri kamar haka
1- Wutiri da Raka’a Ɗaya:
Manzon Allah (S. A. W.) ya ce: “Sallar dare raka’a biyu- biyu ce, idan ɗayanku ya ji tsoron fitowar alfiji, ya sallaci raka’a ɗaya ta zama wutiri ga abin da ya sallata” kuma ya ce ” wutiri raka’a ɗaya ne a ƙarshen dare” (Muslim 752).
2- Wutiri da Raka’a Uku:
A yi raka’a biyu a yi sallama, sannan a yi wutiri a yi sallama. Wannan ya inganta a hadisan Sayyada Aisha, Ibn Abbas, da Ubayyu Ibn Ka’ab (RA) kuma ya inganta cewa Manzon Allah (S.A.W.) yana karanta sabbi isma Rabbikal A’ala raka’ar farko, ƙulyaa ayyuhal kafirun a raka’a ta biyu sannan ƙulhuwallahu a raka’ar wutiri. (Bukhari 991, Malik 1/125) Tahawi 1/285). Amma karanta ƙulhuwallahu da falaƙi da Nasi wannan ya zo a Hadisi mai rauni.
A yi raka’a ukun a jere ba tare da an yi zaman tahiya ba sai a raka’a ta uku. (Bukhari 1147, Muslim 783)
3- Wutiri da Raka’a Biyar:
Ana so ga wanda zai yi wutiri da raka’a biyar ya yi su a jare kada ya yi zaman tahiya sai a raka’a ta biyar. Wannan ya inganta a Hadisin Aisha (RA) wanda Muslim ya ruwoito.
4- Wutiri da Raka’a bakwai ko Raka’a tara:
Ana so ga wanda zai yi irin wannan wutiri, ya yi su a jere kada ya zauna sai a raka’a ta shida ko ta takwas, sannan ya tashi ya kawo raka’a ta bakwai ko ta tara sannan ya yi sallama. Wannan ya zo a Hadisin. (Muslim 746, Abu Dawud 1328 da Nasa’I 2/199).
Danna nan don karanata Rafkanuwa a Sallar nafila
Edita:@rumasau-kallamu