Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

0
4

Hanyoyin Tabbatar Da Adalci – Majaddid shaihuna Usman ɗan Fodiyo Allah ya ƙara rahama a gare shi; ya rubuta littafi mai suna; “Usulul adli liwalatil umuri wa ahlil fadli” – wato Ginshiƙan kafuwar adalci domin shugabanni da manyan mutane.

A cikin wannan littafi, ya yi bayanin hanyoyi goma waɗanda in dai shugabanni daga sama har ƙasa za su yi bi su; babu makawa za su kasance masu adalci a shugabancinsu.

A taƙaice ga waɗannan ginshiƙai na hanyoyin tabbatar da adalci;

Tushe Na Ɗaya

Shugaba ya san matsayi da darajar shugabanci da yake yi. Ya sani cewa shugabanci ni’ima ce babba; wacce in ya yi gaskiya da adalci za ta kai shi ga samun ni’ima madawwamiya a lahira da kyakkyawan suna a duniya. Idan kuwa aka samu akasi to zai gamu da matsananciyar azaba a duniya da lahira; saboda haka kada ya yi wasarere da shugabanci ya riƙe shi ƙam ƙam ya yi da gaske ba wasa.

Tushe Na Biyu

Lallai ne shugaba ya ja malamai masu tsoron Allah da aiki da iliminsu masu son alhairi ga al’umma masu faɗar gaskiya marasa tsoro marasa kwaɗayi, ya ja su a jikinsa ya rinƙa neman shawarwarinsu da fatawa akan al’amuran shugabancinsa; ya kuma rinƙa amfani da shawarwari da nasihohi da suke yi masa.

Haka kuma ya nemi masana ƙwararru a kowane fanni na rayuwa kamar manyan ‘yan kasuwa; tsofaffin shugabanni, da ma’aikata na kowane ɓangare dattawan gari har ma da matasa maza da mata masu tsoron Allah da kishin ƙasa domin ya amfana da iliminsu da ƙwarewarsu a fannonin rayuwa da sauransu.

Tushe Na Uku

Kasancewarka mai gaskiya da riƙon amana da adalci ba zai kuɓutar da kai ba a wurin Allah; sai ka tabbatar mai ma’aikatanka da jami’an gwamnatinka suna da hali irin naka. Amma idan kana ganin ɓarna ka yi shiru; to haƙiƙa sai ka ba da amsa akan wannan ɓarnar; kuma sai an tuhume ka akan duk ɓarnar da akayi kana sane ka yi shiru ayi maka azaba a kanta ranar ƙiyama.

Tushe Na Huɗu

Lallai ne shugaba ya kasance mai yawan haƙuri; afuwa da kau da kai ya guji saurin fushi da yanke hukunci cikin ɓacin rai.

Tushe Na Biyar

A duk lokacin da za ka ɗauki wani matakai ko yanke hukunci ko shawara ko sanya hannu akan wani ƙudiri; waɗanda suke ƙarƙashinka ka ɗauki kanka a matsayin ɗaya daga cikin talakawa duk abinda ba za ka so a yi maka ba to kada ka yi wa waninka, duk abinda za ka so ayi maka to ka zartar da shi.

Tushe Na Shida

Kada ka wulaƙanta talaka da sauran mutane masu kawo buƙatunsu gare ka da koke – kokensu; saboda babban amfanin shugabanci shine sharewa mabiya hawayensu da sauran buƙatunsu da yin abinda ya kamata akansu.

Tushe Na Bakwai

Ka yi rayuwa matsakaiciya tare d tsantseni da wadatar zuci kada ka sabawa kanka da zurfafawa da al’mubazzaranci; a wajen jin daɗi da kece raini wannan zai sa ka mance da wahalhalun da talakawa suke ciki zuciyar ka ta bushe; in suna kuka ka rinƙa jin kamar kukan daɗi suke yi. Kana sheƙa dariya abinka.

Tushe Na Takwas

Dukannin abinda zai yiwu cikin sauƙi da lumana, kada ka bi hanyar tsanani ne da tursasawa wajen tabbatar da shi. Ana amfani da tsanani kawai a lokacin da sauƙi ba zai yi amfani ba.

Tushe Na Tara

A kowane lokaci ka rinƙa tunanin mutuwarka da kwanciyar ƙabari da tashin alƙiyama da musiba da azabobin da suke cikinta; da kuma ni’ima da rahamar da Allah ya tanada ga masu binsa. Ka rinƙa tunanin shin kai a wane ɓangare za ka kasance idan Allah ya tashi alƙiyama.

Tushe Na Goma

Ka sanya tsarin shugabanci na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance madubinka, ma’aunin shugabancinka ka rinƙa kwaikwayonsa gwargwadon ikonka.

Bayan waɗannan tuwassa goma waɗanda Shaihu Usman ɗan Fodiyo; ya ambata ya kuma ce imamul Gazzali ne ya faɗe su a cikin wani littafinsa.

Domin karanta cikakken bayani a kan Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari danna nan

Domin karanta cikakken bayani a kan Raka’a Biyu Kafin Magariba danna nan

labarin da ya wuceYadda Sakamakon Zalunci Yake
Labarin na GabaHalaye Da Siffofin Shugaba Nagari