Toshewar Magudanar Jini Da Shanyewar Ɓarin Jiki

1
81

Ranar 29th ga kowanne wata na October rana ce da  hukumomin lafiya na duniya suka ware domin tunasarwa tare da wayar da kan al’umma game da larurar toshewa gami da fashewar magudanan jini wato CEREBROVASCULAR DX ko kuwa ince “STROKE” yaren da kuka fi ganewa! wanda sanadiyyar hakan ke haifar da shanyewar ɓarin jiki wato PARALYSIS tare da mutuwa.

Akalla Sama Da Mutum Milyan 77 Na Fama Da Ita Ta yadda:
  • Tafiya sai andawo ana koyama mutum ya zai yi.
  • Abinci koda ansawa mutum  abaki zaike suɓutowa yana ci yana zubarwa kasa, don baya iya rufe  bakin.
  • Fitsari ko bayan gida saidake aikin cirema wando tare da daurama, kashi ko saide a wanke ma,
  • Magana sai an yi zaman koyawa mutum, domin in kayi ma ba fita take agane ba, sai ahankali masu zama dakai kadai ke iya  fara gane maganarka domin komawa take kamar me magana da hanci,
  • Stroke na iya sa ganin mutum a bangaren idanu ɗaya ya tafi. Haka shan ruwa na wahala mutum yaita ƙwarewa
  • Yana Haddasa matsanancin ciwon kai wanda tunda mahaifiyarsa mutum ta haifesa zaice bai taɓa jin wani abu me tsanani irin sa ba a duniya,, domin kamar kan zai bindiga ya tarwatse haka zaice saiyasa wasu ke suma.
  • Yana iya sa ka’ida jima’i shikenan kuma saide a lahira in ana yi,
  • Yana haifar da cutar mantuwa
  • Yana haddasa cutar damuwa da baƙinciki,
  • Gadar da tsanar kai, domin yana maida mutum  yadda shi kansa inya kalli kansa a madubi bazai so ya ƙara ba ganin yadda gefen fuskarsa ɗaya ya zazzaɓo ya kwafo, bakinsa ya muskuce ko muguɗe tare da sa dalalar miyau domin bakin bazai iya rufuwa,
  • Yana sa tafiya dole saide da sanda a kaikaice tare da jan ƙafa,sannan ba sauri.
  • Yana haddasa bugun zuciya
  • Yana kashe mutumin cikin kankanin lokaci sai tarihi…

Stroke matsala ce babba me hatsarin gaske. Domin Inta faru to fa koda ka haure duk da waɗancan illolin galibi mutum bazai wuce shekaru 5 zuwa 8 ba araye zai mutu dalilin complication, baya ga akalla sai anhadawa mutum magani wajen kala 5 nasha dole-dole kullum inba haka ba bama shekara 5 ba wani ko sati 1 bazai ƙara ba zai mutu

Idan kanason sanin Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki Shiga nan

Allah su karanta wannan Rubutun  nawa na Hausa baki ɗayan mu  kaf zamu iya wayar gari da wannan matsalar harni. Duk tana bibiyar mu shiyasa ake son wayar dakai karki dauka sai wasu mutane daban, kuma gaba zakuji me yasa nace duk muna cikin hatsarin. 

Anyi ittifaki dukkan mutum 1 cikin 4 zai haɗu da strokes,ma’ana duk inda mutum 4 suka taru Toh ka ɗauka ɗaya zai gamu da ita.

Abin tsoro ne, matsala ce da  akalla sai  manyanta amma ayanzu anfara samunta cikin matasa abinda da ake ga sai ka kai  shekaru 50 baya a duniya, saide yanzu yan shekara 20 ma anfara samun CASES na stroke.

Manyan Alamu Hudu  Na  Strokes Da Za’ayi An Kare hakkin F. A. S. T

F: [Face]  Wato da anga alamun jirkicewa ko saukowa ɓari guda na fuskar mutum, ko baki ya karkace…

A: [Arms]  Wato idan kaga kuma mutum ya kasa ɗaga hannunsa,ko kuwa in anɗaga hannun yana dawowa ya faɗo batare da mutum ya iya ƙoƙarin rike hannun ɗage a iska ba, wato weakness…

S: [SPEECH]  Aka ji magana ta canza, murya ba’a gane me yake faɗi, wato bakin ya fara karewa…

T: [TIME] To ai amfani da lokacin maza-maza a ɗauko mutumin da alamu ukun can na sama (F.A.S) suka bayyana zuwa asibiti da gaggawa. alamune ya sami stroke.

Mu sani duk jinkiri ɗaya ƙarin dagulewar al’amura ne ga wanda matsalar ta samu, haka gwargwadon saurin kaisa ga likita gwargwadon samun saukin taƙaituwar abubuwan da zasu gagaresane wato waɗancan illolin dana lissafo stroke na sawa.

Don haka sashin da abun ya faru irin aikin da wannan sashin ke yi za’a ga mutum na fuskantar matsala,domin ƙwaƙwalwa mutum ko ina aikinsa daban.

Waɗannan Sune Rukunan Mutanan Dake Cikin Hatsari Samun Stroke Y7

(1) Mutane masu ɗauke da hawan jinin da basa bashi kulawa data dace, musamman ace dama basa waiwayarsa ko kiyaye komi jira ake har sai randa mutum yaje asibiti akace jinin sa ya hau sannanne zai sha magani. Ka kuka da kanka domin hawan jini lalata ma magudanar jini yake saboda karfin pressure. 

(2)  Mutane masu dauke da ciwon suga, dole ku lura kubi likitocin ku sau da ƙafa,ciwon sugar koda ana shan magani fa sai ankara da lura domin shi aka ran kansa dama kara cushe magudanar jinin tare da lalata ciwon keyi. 

(3)  Mutanen da nauyinsu ya wuce ka’ida wato overweight wato BMI dinsu ya zana tsakanin 24-29.

(4) Mutane masu teɓa wato ƙiba (obese), wanda BMI dinsu yakai ko yama ketare 30. 

(5)  Mutanen da basa iya motsa jiki akalla na minti 15 sau 4 a sati. Komi sirantakarsu kuwa.

(6) Masu yawan ci,ko wanda zama ɗaya suke share abinci me tarin yawa

(7)  Mutanen dake shan taba sigari da kuma masu zama a inda ake shanta a warin hayaƙin na zuwa musu suna shaƙa.

(8)  Mutanen dake da kitse fiye da kima wato HIGH CHOLESTEROL ajika,anan basai me ƙiba ba, har sirara akwai wanda suke da bad cholesterol level, gwaji ne kurum zai tantance. saboda cin junk foods kuna bakar fata amma baku da abinci sai na turawa su  da lemukan kwalba dana roba, gami da jan nama akaikai kamar zaki,ko zakanya… Toh mutum yai hankali da kanaa

(9)  Masu larurar minshari,irin wanda har dauke wa numfashi su keyi a bacci yana dawowa. 

(10) Mutane masu cuttukan zuciya iri-iri dake shan magani

(11)  Kasancewar a family dinku antaɓa samun me matsalar stroke, paralysis din ko kuwa mahaifi,ko kuma tarin heart attack ko heart failure a family.

(12)  Kasancewar ka baƙar fata ɗan africa… mun fi kowa hatsarinsa fiye da sauran al’umma yankuna duniya,kar ace bakar fata ki kalli kanki  ke wai fair complexion ko bafulatana ki dauka banda ke a’a bakar fata africa baki daya tunda ba tsatson turawa kika fito ko larabawa ba. 

(13)  Kamuwa da cutar corona

(14)  Inya kasancewar shekaru sunja mutum yaba 55yrs baya musamman inda hawan jini hakan karin kusancinsa ga matsalar ne.

(15)  Kasancewar ka namiji domin yafi faruwa a maza fiye da mata saboda namiji baida estrogen ajika, baida nonuwa,baida mahaifa,baida kwayyen Ovary baya kuma daukar ciki, amma fa baya nuna Mata ba zasu hadu dashi ba, musamman in suna da ciwon sugar ko hawan jini suna cikin gagarumi hatsari

(16) Amfani da magungunan bada tazara haihuwa masu kunshe da estrogen wato musamman combination pills nasha.

Bayin Allah Inkuka duba haƙiƙa zakuga kusan kowa na cikin hatsari wannan matsala don haka cewa 1 cikin 4 ka. Iya haduwa da ita,in bamui wani abu ba hatsarin zai dawo 1 cikin 3, harma ya dawo 2 cikin 4.

Matakin  Dauka Domin Kariya

Akwai hatsarurrukan (risk factors) wanda a zahiri ba abinda zamu iya yi akansu saide mubarwa Allah ikonsa domin bazamu iya canza su ba kamar:-

Kasancewa namiji,kasancewa baƙar fata,shekaru,da kuma tarihin matsalar a dangi,wannan ba abunda zamu iya yi akai saide fatan Allah yai mana da sauki.

Domin sanin abubuwan da suka Halatta Game da Mai Jinin Haila da na Biƙi Tare da Mazajensu Shiga nan

Toh kuma kwai wanda zamu iya yin wani abu akansu wato mu kiyaye kanmu, kamar:
  • Sanya ido tare da shan maganin hawan jini kullum batare da ɗaga kafa ballantana wasa ba, domin so ake ya dena tashi bawai ka jira ya tashi kasha magani ba, sannan da yawa yana tashin yai mugun hawa baku sani ba koda kuwa cikin bacci jini na hawa, kuma babu alamun da zaka ji na ya hau.
  • Maddin an lura da hawan jini ankarɓi larura yadda tazo mutum ya huta,iya kaci aita shan magani batare da wasa ba, za’a rayu lafiya,sannan ya zamto ana kiyaye abincin da likita ya hana ci. Ina shawartar duk me hawan jini yai kokari ya mallaki abin gwajin yake dubawa kullum a gida. 
  • Masu ciwon sugar suma su kiyayi wasa da magani,su sanya ido sosai,su kuma kiyaye abin ci da sha.Sannan suyi kokari su mallaki Glucometer suke duba sugar dinsu a gida akai akai
  • Masu cutar minshari kuma kuke amfani da ventilation mask tare da zuwa ku nemi shawarwarin likita domin ku dama ahaka ma numfashinku ɗaukewa yake.
  • Arika motsa jiki, wasu kuna ganin kamar likita baisan wahalar ba: kungani duk irin busy dina komi dare saina ware away a 2 na motsa jiki ranar Lahadi kurum ne bana yi.ballantana kai don haka ba uzuri,shyasa muma likitoci bama uzuri kan wannan.
  • In angano mace na da hatsarin samun stroke a canza mata Maganin family planning daidai da ita

Daɗe sauran abubuwan da suka kamata, don haka a lura dakai.Babu me son ya zamewa ƴan uwansa kaya, domin tun ana ma saboda Allah tofa za agaji dakai inda daga sannan kunci zai fara bai baye mutum, haka na faruwa mutum zai iya kuma samun second stroke kila shikenan sai mutuwa.

Domin karanta bayani akan Larurar  Gaggartowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty) Danna nan

labarin da ya wuceLikita Ina Neman Taimako Haɗe Da Shawara Game Da Matsalar Ƙanƙantar Azzakari [Micro Penies]
Labarin na GabaLarurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za a Magance

SHARHI ƊAYA