Meyasa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Yana Fitowa  Kafin Ko Bayan Sanin Period Din Su?

0
49

Akwai Matsala Ne Tattare Da Hakan?

  • Normally mafi yawan mata suna samun fitowar farin ruwa a gabansu throughout menstrual cycle dinsu.
  • Akalla mata dayawa suna ganin farin ruwa mai kauri ko salala, mara launi yana fito musu a kowace rana, adadin daya kai kimanin cikin cokalin shayi. Launin ruwan yana iya sauyawa daga farin madara, zuwa farin ruwa, ko kuma baki baki (brown).
  • Banbancin launin ruwan ko kaurin sa yana da allaqa ne da hormonal changes na jikin ta a lokacin da yake fitowa.
  • Wannan fitan farin ruwa da mace take gani ta gaban ta kafin period dinta normal ne, babu matsala tattare da hakan. Process ne da ake kira “Leukorrhea” Wani lokacin yana iya kasance wa yellow
  • Hakan yana faruwa ne sbd yawan hormones “progesterone” dayake taruwa ajikin ta. A wannan gaban ana kiran yanayin da “luteal phase”
  • Wannan hormones kamar su”progesterone” “oestrogen” “androgen” etc sauyin yanayin sune ajikin ta shike sawa tayi ta ganin “vaginal discharge” yana fito mata.
  • Idan “estrogen” ne sukayi yawa ajikin ta a lokacin sai ruwan ya kasance fari fari, mai yauki kuma ruwa ruwa.
  • Idan kuma “progesterone” ne sukayi yawa ajikin ta sai ruwan ya kasance farin madara kuma mai kauri kauri.
  • Koma ya launin ruwan ya kasance, fari ne, ruwa ruwa ne, madara madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin baya wari ko ƙarni, gaban mace baya zafi, ƙaiƙayi ko radadi, to wannan normal ne.
  • Aikin sa (ruwan) shine yayi flushing duk wani dattin vagina, wasu harmful germs, da kuma ya sa vagina ta zama moist all the time.Hakan yana nuna alamar the vagina and the reproductive system is healthy and functional.
Wane Lokotan Ne Zaki Tsammanci Ganin Farin Ruwa A Gabanki Idan Kingani  Ba Damuwa Bane
  • Normally mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan yankewar period dinsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danqo yakan sake bullowa wanda zayyi kamar kwana 4 zuwa 5 kafin ovulation, alama shi ta eggs sun fara developing. ana kiran shi da “follicular phase” that means a lokacin ne “eggs” (for ovulation) suke kokarin girma.
  • Idan kuma lokacin ovulation yayi, ruwan se ya canza daga mai danƙo zuwa fari mai  yauƙi kuma mara kauri (salala) haka a wannan lokacin yana kara yawa sosai fiye da na kullum a da. Shi kuma ana kiran shi “egg white”.Aikin sa shine ya taimaka wajen santsin sperm a vagina da cervix domin ya samu damar isowa kwai da yake jiransa for ovulation.
  • Sannan mata dayawa suna amfani da ganin wannan ruwan a matsayin alama ta ovulation dinsu, hakan yana taimaka musu wajen samun ciki da wuri ko kuma kaura cewa yin cikin. Wannan process din shi ake kira da “natural family planning” ko “fertility awareness method”.

1. Idan ruwa ruwan ya kasance mara kauri (salala) to ana kyautata zaton shine “fertile” (i.e ciki zai iya shiga kenan in ƙwan ya samu sperm). Saboda a lokacin kwan zai sauka zaman jira.

2. Idan kuma ruwa ruwan ya kasance fari mai kauri to shi kuma shine “infertile” (wanda ko an sadu ciki bazai shiga ba) saboda ƙwan har ya riƙa, karfin sa ya kare, yanzu sedai ya harziƙa, sa facewa.

  • To irin wannan ruwa ruwan mai kauri zaki cigaba da gani daga bayan ovulation har zuwa wani period din.
  • Daga bayan ovulation din zuwa wani period din, yawan fitowar ruwan zai na raguwa a hankali, yana zamowa mai kauri kuma mai danƙo again, wani lokaci har zaki iya jinsa kamar wata gum ko glue.
  • On average dai, yana kaiwa irin kwana 11 zuwa 14. That is tsakanin ovulation dinki zuwa wani period dinki kenan.
  • Wasu lokuta kina iya ganinsa yellow haka kafin period dinkin.
  • Idan mace taga wani irin brown discharge a bayan period dinta kuma, bayan jinin ya dauke, se ta sake ganin wani baki baki haka brown ya zo mata, to shi din yana kasance wa tsohuwan jini ne daya daskare bai samu damar fitowa ba last time. shine yanzu yake kamo hanya.
  • Idan kuma brown discharge din kafin period ne fa? Ko kuma taga jinin Dan digo digo haka a lokacin da take tsammanin period dinta, to shi kuma yana iya kasance wa sign ne na “implantation” daga farko farkon pregnancy. maza sai kiyi kokari kije pregnancy test domin a tabbatar da hakan ko akasin hakan. (In kin samu congratulations)
Sako Daga Asibitin Kwararru Na Jami’ar Legas (LUTH). Ga Wadanda Suke Shekaru 18 Ko Sama. Wadanda Suka Balaga.

Kafin nan yana dakyau ku shiga nan ku karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki

Ya kamata ka bar matar ka ta san wannan, wannan jan hankali ne daga masu kiwan lafiya, (LUTH) zuwa ga duka mata, kama da yara, ƴan mata: wannan shine ciwon daji na gaban ‘ya mace. A gujewa  wanke gaba da sabulu, a wanke kawai ba ruwa kawai akwai wani sabulu mai hatsarin gaske wanda ke jawo ciwon daji na gaban ‘ya mace, akwai rahotanni da yawa a asibitoci a ko ina. Akwai bukatar mu sanar da sauran yan uwa da abokan arziki.

Yan mata 56 ne suka mutu saboda amfani da whisper, a kiyaye.

Kada ayi amfani da Kunzugu (pad) daya a rana a lokacin al’ada, saboda akwai wasu sinadarai wadanda ke maida ruwa zuwa wani sinadari (Gel), yana kawo ciwon daji a mara da mahaifa. dan haka sai ayi amfani da Kunzugu na a’uduga, idan za’ayi amfani dana zamani sai a canza shi duk bayan awanni 5 a rana akalla. Idan ya dade jinin yana komawa kore sai hunhunar da yayi ya shiga cikin jiki da mahaifa. 

Kada aji kunyar yaɗa wannan ga ƴan mata da maza domin su ma su tura ma kannen su.

Buri:

A kawar da ciwon daji na mama ki sabar da dan ki wanke rigar mama kullum,Kauce ma bakar rigar mama a lokacin zafi,kada a sanya rigar mama lokacin bacci,kada a sanya wata rigar kasa da rigar mama a lokutta da yawa,ki kulle kirjin ki a koda yaushe in kina cikin rana. 

ayi amfani da turaren hana wanri ba wanda zai hana zufa ba.

Domin karanta bayani game da Malaria Danna nan

labarin da ya wuceMalaria
Labarin na GabaLikita Ina Neman Taimako Haɗe Da Shawara Game Da Matsalar Ƙanƙantar Azzakari [Micro Penies]