Tag: yadda ake

  • Tatsuniyar Awa Da Dawi

    Tatsuniyar Awa Da Dawi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Awa da Dawi suna kiwo a daji, sai wani abu ya tsoratar da su. Kowa ya kama gabansa domin neman tsira. Suka ɓace wa juna. Da Dawi ya nemi ƙanwarsa bai gan ta ba, sai ya kama hanya ya tafi. Ita kuma ta nemi hanya ta rasa. Ta riga ta ɓata a dajin nan.

    Sai tafiya take ta yi, ba ta san inda za ta ba, har dare ya yi. Da ta gaji, kuma ga dare ya yi, sai ta sami gindin wata bishiya ta kwanta, har gari ya waye. Da sassafe tana kwance sai wata tsohuwa da ta yi sammakon neman ganyen miya ta tarar da ita. Da tsohuwar nan ta ga Awa a kwance sai ta tashe ta daga barci, tace da ita: “Ke yarinya me ya kawo ki nan?”

    Sai Awa ta kwashe labarin yadda suka yi da ɗan’uwanta ta gayawa tsohuwa. Sai tausayinta ya kama tsohuwa, ta dubi Awa tace da ita: “To idan kin yarda ki zo mu tafi da ke gidana.” Nan take Awa ta yarda suka tafi gidan tsohuwa, ta ba ta masauki da abinci. Awa ta ci abinci ta ƙoshi, ta yi wanka ta zauna.

    Da tsohuwa ta kalli Awa, sai ta ga yarinya ta ƙara kyau. Dama yunwa da dauɗa da gajiya da tsoro ne suka ɓoye kyaunta. Sai tsohuwa ta yanke shawarar kai wa Sarkin garin labarin Awa ko zai so ta. Nan da nan ta isa gidan Sarki, ta same shi a fada, ta durƙusa ta yi gaisuwa ta ce: “Ranka ya daɗe, na zo maka da wani albishir idan kana da buƙata.”

    Sarki ya ce: “Albishir na mene ne?” Sai tsohuwa ta ce wa Sarki “Ina da wata kyakkyawar yarinya wadda za ta dace da kai idan za ka yarda ka aure ta.” Sarki na jin haka sai ya ce: “A kawo ta in gan ta.” Da tsohuwa ta ji haka, sai ta je gida ta gaya wa Awa, kuma suka tafi fada tare.

    Da Sarki ya ga Awa sai ya ce zai aure ta. Ba jimawa aka ɗaura musu aure da Sarki, ta tare a gidansa. Bayan wasu ’yan shekaru, sai Awa ta haifi ɗanta aka raɗa masa sunan yayanta wanda ya ɓata, watau Dawi. Ana nan sai Sarki yace kada a riƙa katse ƙashin ɗansa da ƙara domin zai ji masa ciwo, sai dai da hantar sa.

    Haka kuma ake yi. Kullum da safe sai a yanka shanu, a yanke hantar da huhun a ba Awa ta riƙa share wa yaron ƙashi da su. Wata rana sai Awa ta gaya wa Sarki tana so ta ziyarci iyayenta. Sai ya tambayi sunan garinsu, ta faɗa. Sarki ya sa cigiyar wanda ya san garin. Aka yi sa’a, aka samu.

    Sai aka haɗa shi da matar Sarki da doki ya kai ta garinsu. Kafin su tafi sai aka yanka shanu aka zuba mata hanta da huhu a cikin ƙwarya don katse ƙashin ɗan Sarki, aka kawo kayan tsaraba masu yawa aka ba ta. Da Awa da ɗan rakiyarta suka kama hanya, har Allah ya kai su garin lafiya, murna ta kama ta. Sai ta doshi gidan iyayenta, ta shiga.

    Mutanen gidan suka yi murnar ’yarsu ta dawo. Bayan sun huta, sai ta ba su labarin abin da ya faru har zuwa aurenta da Sarkin garin da suke. Iyayenta da sauran danginta suka yi ta murna. Awa ta kawo kayan tsaraba ta ba iyayenta da sauran’yan’uwanta. Suna zaune ana hira sai ɗanta ya yi ƙashi, sai nan da nan ta zaro hanta za ta katse ƙashin yaron da ita.

    Da uwar ta gani sai ta ce: “Me za ki yi da wannan hanta?” Sai Awa ta ce: “Ai da hanta ake katse ƙashin ɗan Sarki, ba a katse masa da ƙara; mahaifinsa ya hana.” Mamaki ya kama mahaifiyar Awa da ta ji wannan batu. Sai ta shiga tunanin cewa ga abin da mutum ba zai iya samu ya ci kullum ba ya zama abin katse ƙashin jikanta.

    Daga nan sai ta shiga ƙulla yadda za ta kwashe hantar ta cinye. Shi ke nan sai uwar ta kira Awa ta ce mata: “Ɗauki gora ki je ki ɗebo mana ruwa a rafi.” Saboda halinta na bin iyaye, sai kawai tace: “To, amma ki kular mini da yaron nan don ba zan je rafi da shi
    ba.” Sai kakar yaron ta ce: “To, zan lura da shi.”

    Da ta ga lallai Awa ta tafi ɗaukar ruwa rafi, sai ta kwashe hantar katse wa ɗan Sarki
    ƙashin da ta zo da ita gaba ɗaya, ta gasa ta cinye. Da yaron ya yi ƙashi kafin Awa ta dawo daga rafi, sai uwar ta ɗauki ƙara ta katse masa da shi.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Tsautsayi ba a sa maka rana.
    • Mai mugun hali tun a duniya sai ya ɗanɗana kuɗarsa.
    • Aikin da ba a yi shi da kyakkyawar niyya ba ƙarshensa nadama.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Maye Da ’Ya’yansa

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Maye Da ’Ya’yansa

    Tatsuniyar Maye Da ’Ya’yansa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani mutum a wani gari da ke gabas da garin nan. Yana da mace ɗaya da ’ya’ya biyu mata. Da suka isa aure Allah ya ba su masoya, aka yi musu aure aka kai kowacce ɗakinta. Bayan ’yan shekaru kowacce ta haifi ’ya’ya. Ana nan, sai aka aika musu uwarsu ta rasu; sai dai su ba su san cewa ubansu maye ne ba, kuma shi ne ma ya cinye uwar tasu.

    Shi ke nan yaran nan suka je gidan ubansu saboda zaman makoki, amma sai suka tarar uban nasu ya cinye gawar uwar tasu, domin yunwar maita ta kama shi, kuma babu wanda zai ci sai gawar. Da ya ji muryar ’ya’yansa, sai ya kulle kansa a cikin ɗaki don kada su gani, su gane.

    Duk sanda suka kai masa abinci, sai yace su ajiye a ƙofar ɗaki. Bayan sun yi kwana biyu a gidan, sai a dare na uku ya tara su, ya fara zaro harshe yana haɗiyar yawu. Sai suka gane cewa shi ya cinye babarsu, kuma yana so su ma ya cinye su. Da man sunan ɗaya Nkwa, ɗaya kuma Sektiraye.

    Sai ya fara kiran su yana cewa: “Nkwa da Sektiraye duk da ’ya’yanku, Ku jira ni ina zuwa, Zan cinye ku, Da man ina jin yunwa.” Da suka ji haka sai suka kama ’ya’yansu suka ɓuya, kuma suka ajiye kabewa a kan gado suka lulluɓe ta. Da dare ya yi tsaka, sai
    kawai ya tashi ya kama cin kabewar da ke kan gado.

    Da ya gane ba nama ba ne, sai haushi ya kama shi. Can kuma sai ɗaya daga cikin jikokinsa ya fara kuka a inda suka ɓuya. Da ya gane inda suka ɓuya, sai ya yi kukan kura ya auka musu, amma bai cafki ko ɗaya ba. Sai ’ya’yan nasa da jikokin suka fito da gudu, suka kama hanyar dajin da ke kusa da garin, shi kumayana bin su.

    Suna cikin gudu a dawan nan sai ya kama ɓarin jikinsa ya cinye, har dai ya zama saura ƙashi a jikinsa kawai. A hakan yake bin su da gudu yana cewa: “Dun kwalak, ka dun kuci kal.” Da suka isa wani guri a cikin dajin, sai suka tarar wuta tana cin ciyawa, sai suka keta ta cikin wutar a guje.

    Saboda yawan wutar, har ta kama cin hanya. Da uban nasu wanda ya zama ƙwarangwal
    ya isa wurin wutar nan, sai ya faɗa cikinta, wuta kuwa ta cinye ƙasusuwansa, ya ƙone ƙurmus. ’Ya’yan nan nasa da jikokinsa sun sami tsira. Da gari ya waye, sai wasu mata masu neman tokar miya suka tarar da tokar wannan maye a kan hanyar, ba su san ta mutum ba ce.

    Sai ɗaya daga cikinsu ta ce su deɓi tokar miya. Sai suka ɗiba, suka koma gida. Sai ɗaya daga cikin matan ta haɗa tokar za ta yi miya da ita. Bayan ta ɗora tukunyar miya da tokar a ciki a kan wuta, sai ta ji miyar tana cewa: “Ki juya ni a hankali, domin wuta ta ƙona ni da yawa.” Da ta ji haka ba ta ce uffan ba, kuma ba ta daina girki ba, har sai da ta gama.

    Da ta gama, ta zuba, ta kai wa mijinta abincinsa a akushinsa. Data je ajiye akushin sai ta ji an ce: “Idan za ki ajiye ni, ki ajiye ni a hankali don wuta ta ƙona ni da yawa?” Da mijin ya ji, sai ya kira matarsa ya ce mata: “Na ji kamar miyar tana magana.” Sai ta dubi mijin tana murmushi ta ce: “Kai anya, ba kunnenka ba ne kuwa?”

    Sai mijin ya sa hannu zai buɗe akushi ya fara cin tuwo da miya, sai miyar ta ce: “Idan za ka deɓe ni, ka deɓe ni a hankali, don wuta ta ƙona ni sosai.” Da mijin ya ji haka, sai ya dubi matar ya ce: “To ashe ke mayya ce ban sani ba.” Sai matar ta ce: “A a ai a cikin jeji na samo tokar miya.”

    Sai mijin ya ɗauki miyar ya kwara mata a ƙirji. Nan take ƙirjinta ya fitar da haƙora gatso-gatso, abin gwanin ban tsoro. Da mijin ya ga haka, sai ya kore ta, sai ta shiga daji, ta koma can da zama. Duk wanda ya je dajin da take zai tarar da ita tana yawo, tana cin fari da kwaɗi. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Tsautsayi ba a sa maka rana.
    • Mai mugun hali tun a duniya sai ya ɗanɗana kuɗarsa.
    • Aikin da ba a yi shi da kyakkyawar niyya ba ƙarshensa nadama.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Binta ’Yar Sarki

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Binta ’Yar Sarki

    Tatsuniyar Binta ’Yar Sarki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wani Sarki a wani gari mai mata biyu, kowacce tana da’ya. Yarinya ɗaya sunanta Binta, ɗayar kuma Falmata. Sarki yana ji da’ya’yan nan nasa, to amma fa ya fi son Binta don ita ce ƙarama, kuma ’yar amarya.

    Ana nan, rannan sai Sarki ya tafi wani gari mai nisa, kuma zai daɗe a can. Bayan ya tafi da ’yan kwanaki, sai ciwo mai zafi ya kama amaryarsa, watau mahaifiyar Binta. Da ta lura ciwon kamar ba wanda za ta tashi ba, sai ta kira kishiyarta ta gaya mata cewa tana jin ba za ta tashi ba, amma idan ta cika, tana roƙonta ta kula da’ya’yansu cikin amana.

    A cikin tausayi kishiyar ta ce da ita: “Zan yi bakin ƙoƙari na in kula da su.” Bayan kwana biyu da yini ɗaya, sai amaryar Sarki ta rasu. Sarki dai bai dawo daga tafiyar da ya yi ba har wasu ’yan kwanaki suka wuce. Rannan sai kishiyar uwar Binta ta sa ta ɗauko ruwa a rafi a cikin wani masaki, kuma ta gaya mata lallai a rafin Apko mai cinye mutane za ta ɗebo ruwan, watau ba a ɗaya rafin mai lafiya ba.

    Ɗaya rafin mai lafiya wanda daga shi mutanen suke ɗaukar ruwa sunansa Diddire. Binta ta ɗauki masaki ta garzaya wajen kabarin mahaifiyarta, tana kuka tana waƙa, tana cewa:

    “Baba, baba, babar Binta,

    Kishiyarki ta ce in je Apko in ɗebo ruwa,

    In je Apko ko in je Diddire?”
    Daga cikin kabarin sai ta ji mahaifiyarta ta amsa mata dawaƙatana cewa:

    “Ki je Diddire,

    Kada ki je Apko,

    Domin Apko zai apka da ke.”

    Sai Binta ta tafi rafin Diddire ta ɗebo ruwa. Da kishiyar uwarta ta ga ba ta ɗebo ruwan Apko ba, sai ta hau ta da duka. Ta ma zubar da ruwan da ke cikin masakin, ta ce lallai maza ta je ta ɗebo mata ruwa daga kogin Apko, kuma ta gaya mata cewa idan ta kuskura ta ɗebo mata ruwan Diddire, to za ta yanka ta.

    A kan dole Binta ta ɗauki masakin ta tafi rafin Apko ɗiban ruwa. Tana shiga za ta ɗebi ruwan, sai rafin ya cinye ta. Tana nan a cikin ruwa, har wasu ’yan kwanaki. Ita kishiyar uwarta ba ta sa an je nemanta ba, kuma ita ba ta je ba. Ko fadawa ma ba ta gayawa ba, har ranar dawowar Sarki.

    A ranar da Sarki ya dawo sai fadawa da jama’ar gari suka fita bayan gari suna yi masa barka da zuwa. Masu tambura suka goce da kiɗa, ana yi masa kirari ana cewa: “Baban Binta ya dawo, Sarki baban Binta ya dawo.” Da Binta ta ji ana buga tambarin babanta, ga shi kuma ba za ta iya fita daga ruwan ba, sai ta kama kuka da waƙa tana cewa:

    “Falmata ce ’yar Sarki,

    Babanta ya dawo,

    Falmata kin ji daɗi,

    Falmata ’yar Sarki.”

    Sarki ya sa ido ko zai ga Binta a cikin masu tarye, amma bai gan ta ba, kuma ya saɓa idan ya yi tafiya ya dawo akan ɗoro ta a kan doki, a kai ta gabansa, su gaisa. Ya sake dubawa bai ga Binta ba sai Falmata. Sai hankalinsa ya tashi, har dai ya kasa daurewa ya tambayi fadawansa inda Binta take.

    Sai suka ce ai Binta ta ɓata, ba wanda ya san inda take. Suka ƙara da cewa ai ma yau kwana goma sha tara kenan da uwarta ta rasu. Hankalinsa ya tashi, amma ya yi
    ta maza, ya shanye halin damuwar da yake ciki. Da ya shiga gida, sai ya kira uwargidansa, ya tambaye ta inda Binta ta je.

    Sai ta ce ba ta sani ba, tun da dai ta fita yawo ba ta sake komawa gida ba. Yana jin haka, sai ya sa aka shiga neman Binta. Wasu daga masu nemanta suka bi ta rafin Apko. Da fari ba su ga alamun kowa a can ba, to amma daga baya sai suka ji muryar mutum na waƙa a cikin rafin. Da suka kasa kunne da kyau, sai suka ji ana waƙa ana cewa:

    “’Ya’yan uwa kada ku zo Apko,

    Idan kun zo zai apka da ku,

    Ni kishiyar uwa ta aiko ni nan,

    Har ya apka da ni.”

    Da masu nemanta suka ji haka sai kawai suka koma suka shaida wa Sarki abin da suka jiyo a kogin Apko. Sai Sarki yace da su da sauran fadawansa su je tare da shi bakin rafin ya ji. Nan da nan suka dunguma, kuma suka tarar Binta tana yin wannan waƙar. Sarki ya kasa kunne, kuma daga ƙarshe dai ya fahimci cewa muryar Binta ce.

    Sai nan da nan ya ce da Sarkin maroƙa ya shiga gari ya yi yekuwa cewa duk wanda ya fito da Binta dagakogin Apko za a ba shi dawakai da dukiya mai yawa. Da fari ba wanda ya ce zai gwada, amma can sai wani tsoho ya zo ya ce zai shiga ruwan ya tsamo ta. Sai wasu mutanen garin suka ce: “Amma tsohon nan da rigima kake.

    Ga mu nan duk da ƙarfinmu mun kasa, ballantana kai da ka tsufa?” Sai Sarki ya ce: “A bar shi ya gwada.” Tsoho ya faɗa ruwa, zuwa wani ɗan lokaci sai ya fito da Binta a hannunsa. Da Sarki ya ga ’yarsa sai ya ji kamar ya zabura da gudu ya rungume ta saboda murna da farin cikin da yake ciki.

    Amma sai ya nuna halin manya, ya jure. A cikin murna da farin ciki Sarki da fadawansa da jama’arsa suka yi ta gode wa tsohon nan. Da aka koma fada ya sa aka kwanto dawakai Asbin da kili da fari da ja da baƙi da ingarma da kuru da dai dawakai iri-iri masuyawa da dukiyar da ba a taɓa ganin irinta ba a ƙasar, aka ba tsoho.

    Bayan an tashi daga zaman fadanci Sarki ya shiga turakarsa, sai ya kira matarsa da Falmata, ya tambaye su yadda aka yi Binta ta faɗa ruwa. Sai suka yi shiru. Da dai ya gane munafunci suka yi, sai ya kore su, ya ci gaba da rayuwarsa da ’yarsa Binta. Shi ya sa duk wanda ya je garin zai ji ana cewa: “Binta ’Yar Sarki.” Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Alkawari kaya ne.
    • Kowa ya ci amana sai amana ta ci shi.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar ’Ya’yan Sarki Da Ƙadangare

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ’Ya’yan Sarki Da Ƙadangare

    Tatsuniyar ’Ya’yan Sarki Da Ƙadangare

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani Sarki da ’ya’yansa mata su biyu kyawawa. Amma tun suna ƙanana ya hana su fita waje domin tsaron lafiyarsu. Kullum suna gida har suka girma, suka isa aure. Ganin sun kai munzalin aure, sai ya bari suka ɗan fara fita waje.

    Ana nan, rannan dai Sarki ya ce zai aurar da su. Manema suka fito. Wannan ya zo, a ce a a, bai yi ba. Wancan ya zo, a hana shi. Wata rana dai sai Sarki ya ce a tara mutane, duk wanda ya kira sunan ɗaya daga cikinsu, to shi za a ba wadda ya faɗi sunanta. Shi
    ke nan aka sa ranar tara mutane don a ji wanda zai faɗi sunan.

    Matasa da sauran waɗanda ba su wuce auren budurwa ba, kowa ya shiga neman sunayen ’yan matan; abu dai ya gagara. Sai Biri ya sami labari kuma ya ce ya san dabarar da zai yi. Sai ya je ya samo mangwaro nunannu kyawawa guda biyu. Da ya make mangwaron nan biyu, sai ya garzaya cikin lambun Sarki inda yaran suke hira, ya zauna a kan bishiyar da suke zama a gindinta ya shiga jira.

    Da suka fito, sai ɗaya daga cikin ’yan matan ta je gindin bishiyar da Biri yake kai, sai ya jefa mangwaro ɗaya. Da ta gani sai ta ɗauka tace: “Kirindi zo ki ga wani nunannen mangwaro na samu.”Wannan ya sa Biri murna saboda ya ji sunan ɗaya daga cikinsu. Da ɗayar ta doshi wajen wadda ta kira ta don ta je ta ga mangwaron Kirindi, sai ya jefa ɗaya mangwaron, sai ita ma ta ganshi.

    A cikin murna da ɗoki ta ce: “Ai ni ma na samu Karanda.” Biri na ji sai ya kama murna yana cewa: “Yawwa ai ni zan aure su tun da na ji sunayensu.” Bayan lokacin da Sarki ya yanka wa mutane ya cika, sai aka tara mutane ana tambayar su ko sun sami sunan ’yan matan.

    Wannan ya zo ya ce kaza ne, a ce masa a a, wancan ma ya zo bai canka ba. Haka dai aka yi ta fama har aka zo kan malam Biri. Ana zuwa kansa sai aka ji a cikin raɗa saboda tsoro ya ce: “Kirindi da Karanda.” Sai Ƙadangare da ke gefensa ya ji, sai kawai ya yi farat da ƙarfi ya ce: “Kirindi ce da Karanda.”

    To shi kuma Sarki ya riga ya yi alkawarin duk wanda ya faɗi sunayensu, zai ba shi su aure. Ba tare da ɓata lokaci ba, aka ba Kadangare auren ’ya’yan Sarki. Ashe Biri ya ji haushin ƙwacen da Ƙadangare ya yi masa, kuma ya saɓi laya sai ya ɗauki fansa a kan Ƙadangare.

    Saboda haka bayan an gama bikin amaren Ƙadangare sun tare a gidansa, sai
    rannan Biri ya haura dangar gidan gonar Sarki inda Sarki ke kiwo. A cikin dabbobin da Sarki ke kiwo kuwa, akwai wata babbar kazarsa wadda ya fi so a kan duk sauran abubuwan da yake kiwo a gonar.

    Sai Biri ya kama wannan kaza ya yanka, ya fige, ya dafa ya cinye. Da ya cinye ya sha ruwa, sai ya kwashe duk gashinta da ƙasusuwanta ya je ya haura dangar gidan Kadangare ya zuba. Gari na wayewa, sai labari ya je ga Sarki cewa an sace masa kaza. Sai ya sa fadawa su bi gida-gida su nemo kazar nan kafin a zahar.

    Fadawa na shiga gidan Kadangare, sai suka tarar da gashin kazar Sarki da ƙasusuwa. Suna ganin haka, sai suka kai wa Sarki labari. Saboda kunya da kara irin ta manya, da Sarki ya ji cewa a gidan surukinsa ne aka sami gashi da ƙasusuwan kazarsa, sai ya ce a bar maganar, kuma ya hana a hori Kadangare.

    Biri dai bai ji daɗin haka ba. Duk domin ya yi ramuwar gayya, sai ya yanka akuya ya dafa aka yi romo mai kayan yaji. Ya ɗauka ya kai gidan Kadangare, romo da naman akuya suna tafasa saboda zafi. Da Kadangare ya buɗe mazubin, sai ya ga naman akuya da romo, ga ƙamshinsa ya cika gari.

    Sai kwaɗayinsa ya tashi, bai yi wata- wata ba sai ya kai bakinsa. Yana ɗosana bakinsa kuwa sai yaƙone, ya ja baya. Matansa na fitowa sai hankalinsu ya tafi kan mazubin nan. Da suka buɗa, suka ga naman akuya ne a cikin romon da ya sha kayan yaji, sai su ma suka kwasa, suna kai wa bakunansu sai zafi ya sa kowacce ta ƙwala ihu, ta tofar da wanda ta guntsa.

    Dukkansu uku, watau Kadangare da matansa biyu ba wand abai ƙone ba. Da Biri ya ga haka, sai ya fita daga inda ya maƙe, ya kama hanya ya tafi yana dariyar ƙeta da jin daɗi, ya bar su da jinya. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kowa ya cuci wani zai ga mummunan sakamako.
    • Duk abin da ka samu ta hanyar rashin gaskiya ba za ka moreshi ta hanyar jin daɗi ba.
    • An ɓata goma ɗaya ba ta gyaru ba.
    • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Tsurondi

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Tsurondi

    Tatsuniyar Tsurondi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana wani Dodo ya rikiɗa ya zama mutum, ya shiga wani gari neman aure. Da ya je mazaunin wasu mutane sai ya gaishe su. Ya sanar da su cewa shi baƙo ne, amma neman aure ne ya kawo shi garin. Ya ƙara yi musu bayani cewa ya fi son kyakkyawar mace, wadda babu kamar ita a garin.

    Shi ke nan, sai mutanen nan suka yi masa kwatancen gidan wasu ’yan mata biyu, Awa da ƙanwarta Tsurondi. Da ya je gidan ya yi sallama, sai mai gidan ya fito suka gaisa. Daga nan baƙo ya yi wa mai gida bayanin abin da ya kawo shi. Sai uban ’yan matan ya ce: “To bari in turo su, duk wadda tace za ta aure ka sai in ba ka ita.”

    Ya shiga cikin gida. Jim kaɗan sai Awa, watau babbar, ta fito. Da ya gan ta nan take ya ce yana sonta. Da ta gan shi kyakkyawa kuma baƙo ne sai ita ma ta yarda. Aka shirya biki, aka gama. Aka raka su bayan gari ita da mijinta za su tafi garin mijin. Bayan ango da amarya sun kama hanya, sai ƙanwarta Tsurondi ta ce za ta raka ta.

    Amma sai Awa ta ce kada ta bi su. Ƙanwar ta yi juyin duniyar nan, amma Awa ta ƙi yarda. Sai Tsurondi ta zama ƙuda ta faɗa kan kayan amarya, suka kama hanya. Can lokacin da suka isa dokar daji, sai iska ta ɗauke hular ango. Da matarsa Awa ta ga haka sai ta ce: “Mai gida hularka ta faɗi.” Sai ya ce da ita: “A nan na tsince ta da man.

    Haka dai ya yi ta zubar da kayan jikinsa har ya zama tsirara. Sai kawai ya zama wani
    dodo mai babban ƙaho a tsakiyar kansa da doguwar jela mai gasuka kowanne kamar girman adda. Ganin haka ya sa Awa ta razana. Nan take ta ɓarke da kuka, amma fa tana bin sa har suka isa gidansa.

    Bayan sun huta a gidan Dodo, kuma ya fita shan iska, sai ƙanwarta ta rikiɗa zuwa mutum. Da Awa ta gan ta, sai murna da mamaki suka kama ta, kuma ta dubi
    ƙanwar ta ce: “Tsurondi yaya aka yi kika biyo ni?” Sai ta ba ta labarin yadda ta yi. Shi ke nan kullum idan lokacin dawowar Dodo ya kusa, sai ta ɓoye ƙanwarta, kuma in gari ya waye, Dodo ya tafi farauta, sai ta fitar da ƙanwar.

    Haka dai suka yi ta fama har Awa ta sami ciki. Da lokacin haihuwa ya kusa, sai ta ce da ƙanwar ta kama hanya ta je gida ta gaya musu za ta zo haihuwa, amma kuma idan sun isa, a yi dabarar da za a kashe Dodon. A haka suka yi ban kwana. Tsurondi ta zama tsuntsuwa ta tashi sama fir, sai garinsu.

    Tana isa gida ta ba mutanen gari labarin abin da Awa ta aura. Da suka ji haka, sai suka fara shirin kashe Dodo. Suka tona rami a ɗakin mahaifiyar Awa, a daidai inda Dodo zai zauna ranar suna. Da watan haihuwar Awa ya kama, sai ta gaya wa Dodo za ta je gida domin ta haihu a cikin ’yan’uwanta.

    Mijin kuwa ya ba ta izini, har ma ya sa ta a hanya, ta isa gida lafiya. Bayan ’yan makonni da isarta gida, sai ta haihu, kuma aka aika masa ya zo ya ga ɗansa. Sai ya yi murna, kuma ya sa ranar zuwansa. A ranar da Dodo zai isa tun da safe iyayen Awa suka hura wuta a ramin da suka tona. Suka jefa manyan guma-gumai, wuta ta haɗu sosai. Daga nan suka ɗora gadon kara a kan ramin, sannan aka shimfiɗa tabarma a kai.

    Da Dodo ya zo, aka zaunar da shi a kan tabarmar, aka kuma miƙa masa ɗansa domin ya gani. Can sai ya fara ji kamar ana muntsinar sa a duwaiwai, bai san ramin wuta ne a ƙarkashinsa ba. Da wuta ta ci karan, sai suka ɓurma shi da ɗansa. Nan dai ya yi kici -kicin jefo ɗan waje, amma aka sake mayar masa shi, har dai suka ƙone ƙurmus a cikin ramin nan.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kyau ba shi ke kawo daɗin zaman aure ba.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Ceto daga Ubangiji ne abin dogaro ba na ɗan’adam ba.
    • Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.
    • Mai rabon ganin baɗi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kurege Da Wayo

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kurege Da Wayo

    Tatsuniyar Kurege Da Wayo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani lokaci da aka yi yunwa, ba abinci. Wuya ta sa Kura da Maciji da Alade da Kurege suka haɗa kai, suka haɗu domin su haɗa gwiwa su yi noma tare. Sai suka zaɓi wani fili a dajin da suke, suka gyara, ya zama gonarsu.

    Ana nan, jim kaɗan kafin damina ta faɗi, sai Maciji ya ce shi ne zai yi sassabe, watau zai gyara gona, ya sare lallagowa ya kawar da yayi. Alade ya ce: “Ni zan yi mana huda.” Kura ta ce: “Ni zan nome mana gonar.” Kurege kuwa sai ya ce: “Ni kuma zan nemo mana irin shukawa.”

    A daidai lokacin da ya dace, sai Maciji ya tuge bishiyoyin gonar ya ƙone. Alade ya yi musu huda. Kura ta nome. Kurege ya tafi neman irin shuka a kasuwa, sai ya ga wata mata ta tara dawa da masara da gyaɗa da wake. A daidai lokacin da ta tashi tafiya gida sai Kurege ya ruga, ya je gabanta ya kwanta kamar ya mutu.

    Da matar ta gan shi sai ta ce: “Kai ga nama ya samu. To amma fa idan na ɗauka zai cinye mini dawa ta kare da wuri.” Sai ta tafi ta bar Kurege, ba ta ɗauka ba. Da Kurege ya ga haka sai ya tashi ya kama gudu, ya sha gaban matar nan ya kwanta. Da ta ga wannan Kuregen ba ta san na baya ba ne sai ta ce: “Allah ne ya ba ni.”

    Sai ta ɗauki Kurege ta sa a bakin ƙwaryarta, ta shiga gefen daji domin ta samo ɓawon kargo ta ɗaure Kuregen ko ta ji daɗin tafiya da shi gida. A lokacin da ta ajiye ƙwarya ta je ta yo ɓawon kargo sai Kurege ya ɗauki ƙwaryar nan cike da irin dawa ya gudu.

    Da matar nan ta dawo, sai ta ga ba ƙwarya, ba Kurege. Hankalinta ya tashi, kuma ranta ya ɓaci. Haka dai matar nan ta kama hanyar gida da ɗan abin da ba a rasa ba, tana kuka. Shi kuwa Kurege ya kai iri suka shuka tare da abokan nomansa. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Idan an hada kai komai zai zo cikin sauki.
    • Iya ruwa fidda kai.
    • Neman araha kan sa mutum ya rasa abin da yake hannunsa.
    • Kwadayi mabudin asara/wahala.

    Karanta Tatsuniyar ƊanAuta Da ’Yar Gwaggo

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ƊanAuta Da ’Yar Gwaggo

    Tatsuniyar ƊanAuta Da ’Yar Gwaggo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani mutum yana da ’ya’ya biyu mace da namiji. Macen ce babba, namijin ne ƙarami. Ita sunanta ’Yar Gwaggo, shi kuma sunansa Ɗan’auta. Da iyayensu za su rasu sai suka kira ’Yar Gwaggon suka ce: “Za mu bar miki ƙaninki Ɗan’auta. Kada ki ba shi wahala, duk abin da yake so ki ba shi; kuma duk abin da ya ce zai yi, kada ki hana shi; ki bar shi ya yi.”

    ’Yar Gwaggo ta ce: “To na ji.” Sai iyayen suka kwanta, suka rasu. To da ma iyayen sun bar musu dukiyar abinci da kadarori. Bayan ’yan kwanaki da rasuwarsu sai Ɗan’auta yace su tattara dukiyar da abincin da gidan baki ɗaya su ƙona. Sai ’Yar Gwaggo ta ce: “Haba Ɗan’auta, idan muka ƙona kuma me za mu ci, kuma a ina za mu zauna?” Sai Ɗan’auta ya ce: “Ba su baba sun ce idan ina son komai ki ba ni ba, kuma duk abin da zan yi kada ki hana ni?”

    Sai ta ce: “To shi ke nan, ka tashi mu tara kayan a ƙona.” Suka tara kayan da abincinsu rumbu-rumbu, suka ƙona. Da yunwa ta fara damun su sai ’Yar Gwaggo ta ce to su tafi bara. Suka kama hanya har gidan Sarki sai suka tarar da ’ya’yan Sarki suna wasan kirbe-kirbe, sai yace shi ma sai ya yi.

    Sai ’Yar Gwaggo ta ce: “Haba Ɗan’auta, wannan fa gidan Sarki ne, kuma ’ya’yan Sarki suna wasa. Idan aka kama mu fa?” Sai ya ce: “Ba su iya da baba sun ce duk abin da na ce zan yi ki ƙyaleni ba?” Sai ta bar shi ya shiga wasan ’ya’yan Sarki. A cikin wasan ya ɗaga ɗaya daga cikinsu, ya ƙwala da kasa sai cinyarsa ta karye.

    Sai Sarki ya sa fadawa su kama shi. Ganin haka sai ’Yar Gwaggo ta kama hannun ƙanenta suka kama gudu, har cikin jeji, dogarai suna bin su. Can sai suka hau kan wata bishiya, suka ɓuya. Da dogarai suka zo sai suka rasa hanyar da suka bi, sai suka ce bari su huta a gindin bishiyar nan. Su Ɗan’auta na kan bishiyar.

    Da ɗaya daga cikin dogaran ya kwance rawaninsa domin ya sha iska, ga shi ya aske kansa ƙwal-ƙwal yana ƙyalli, sai ɗan’auta ya auna kan dogarin sosai, sai kawai yace wa ’Yar Gwaggo: “Zan yi kashi.” Tsoro ya kama ’Yar Gwaggo, domin idan dogaran nan suka ji motsi za su kama su. Sai ta ce: “Haba Ɗan’auta, idan ka yi kashi za su gan mu, su kama mu fa.”

    Sai ya ce: “Ba iya da baba sun ce duk abin da zan yi ki ƙyale ni ba?” Sai ta ce: “To shi ke nan yi kashinka.” Sai ya tuɓe wandonsa ya auna daidai kan dogari sai ya ɓarke da kashi. Da kashi ya zuba kan dogari sai ya ce: “Wannan wane ɗan iskan tsuntsu ne ya yi mini kashi?”

    Da suka ɗaga kai sama sai ga su Ɗan’auta da ’Yar Gwaggo, sai suka fara sarar bishiya, saura kaɗan ta faɗi, sai ga wata ’yar tsuntsuwa za ta wuce, sai ’Yar Gwaggo ta ce: “‘Yar tsuntsuwa ki taimake mu mana.” Sai tsuntsuwar ta ce: “To ku hau bayana.” Suka hau bayan ’yar tsuntsuwa, ta tashi da su sama suka fara tafiya.

    Bayan sun fara nisa a can sama, sai Ɗan’auta ya ga gindin tsuntsuwa na ta motsi, yana budewa ya rufe. Sai kawai ya ce zai tsokale gindin tsuntsuwa. Yayarsa ta ce: “Haba Ɗan’auta, ita da ta taimake mu. Da an kama mu an kashe. Ka yi haƙuri mana.” Sai ya ce: “Ba inna da baba sun ce idan na ce zan yi abu kada ki hana ni ba?”

    Sai ta ce: “To ka yi.” Sai ya sa kara ya tsokale gindin tsuntsuwa. Sai ta juyar da su, suka faɗa cikin wani babban rafi. Suka yi ta iwo har suka kai bakin ruwa. Sai suka fita a daidai wani ɗan ƙauye. Da suka shiga ƙauyen sai suka fara neman masauki. Sai suka haɗu da wata ’yar tsohuwa suka gaya mata su baƙi ne masu neman masauki.

    Sai tace: “To zan ba ku masauki, amma fa a garin nan ba a fita da daddare don akwai wani dodo da yake cin mutane; har sarki ya yi alƙawari zai ba duk wanda ya kashe dodon rabin gari kuma ya aura masa ’yarsa.” Sai suka ce: “To shi ke nan.” Da dare ya yi sai Ɗan’auta ya ce shi fa sai ya ga dodon da yake hana mutane fita.

    Yayarsa ta yi, ta yi da shi kada ya fita waje, ya hura wuta a gefensa. Da wuta ta ruru, sai ya saka duwatsu bakwai a cikinta, har suka yi jawur. Sai ya zauna a tabarmarsa, ’yar tsohuwa kuma don tsoro sai ta shiga randarta ta buya a ciki. Da dodo ya iso gari ya shiga waƙa yana cewa: “Wa ya yi da ni a garin nan, Wa ya yi da ni, ni dodo in cinye shi?”

    Sai Ɗan’auta ya mayar masa yana cewa: “Na yi da kai a garin nan, Na yi da kai ni Ɗan’auta.” Da tsohuwa ta ji sai ta fara zawo a cikin randar don tsoro. Sai dodo ya nufo inda Ɗan’auta yake. Da Ɗan’auta ya ga ya buɗe baki, sai ya ɗauki dutsen nan da ya yi jawur da wuta, ya jefa a cikin bakin dodo.

    Sai dodon nan ya hadiye. Ya ci gaba da matsowa, shi kuma Ɗan’auta ya ci gaba da jefa duwatsun nan, har ya zo kan na ƙarshe. Da ya jefa na bakwai, sai kawai dodon ya faɗi matacce. Da Ɗan’auta ya ga haka, sai kawai ya koma ya kwanciyarsa. Da gari ya waye sai aka aika wa Sarki cewa an kashe dodon da ke damun mutanen gari.

    Sarki kuwa ya ce duk wanda ya kashe dodon za a ba shi rabin gari, kuma a aura masa ’yar Sarki. To da ma shi Ɗan’auta ya manta takalmansa a inda ya yi faɗa da dodo. Da aka tara mutane suka zo suka yi ta gwada takalma amma bai yi ba, sai da suka nemi baƙin da suke garin.

    Da Ɗan’auta ya gwada takalma sai suka yi daidai da shi. Nan take aka ba shi rabin gari, Sarki kuma ya cika alƙawari, wato ya ba shi auren ’yarsa. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wauta ne a sakar wa yaro linzami ya yi abin da ya ga dama.
    • Mai wayo ya fi mai zafin nama cin nasara.
    • Ya kamata a karɓi bako da hannu bibbiyu don ba a san alhairindazai kawo ba.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Sarki

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Gizo Da Sarki

    Tatsuniyar Gizo Da Sarki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wata tsohuwa a wani ɗan ƙauye; tana da ɗan maraƙinta kyakkyawan gaske; ga shi ƙosasshe. Ana nan wata rana Gizo ya je gidan wannan tsohuwa bara sai ya ga wannan maraƙi. Sai ya fasa bara ya fita daga gidan, ya sheƙa a guje sai gidan Sarki.

    Ya faɗi a gaban Sarki, ya ce: “Ko kunnuwan Sarki nawa ne?” Sarki ya ce: “Biyu.” Sai ya ce wa Sarki: “Ƙara biyu, a kan biyu ka sha labari.” Sarki ya ce: “Na ƙara.” Sai Gizo ya ce: “Akwai wani kyakkyawan sa a gidan wata tsohuwa, in ba gidanka ba, to sai gidana.” Sai Sarki ya ce: “To shi ke nan.”

    Sai Sarki ya tura dogarai don a kamo kuma a kawo masa wannan san. Da dogarai suka kama hanya ba su tsaya a ko ina ba sai a gidan tsohuwa. Suka same ta, suka isar da saƙon Sarki. Da ta ji bayanin dogaran Sarki sai ta ce: “To yaya zan yi yau.” Dalilin tsohuwa na faɗin haka shi ne wannan sa ba ya yin komai sai dai zninta.

    Dogaran Sarki suka yi, suka yi su kwance sa daga turkensa su tafi da shi amma abin ya gagara. Can dai sai tsohuwa ta saka san a gaba tana yi masa waƙa tana cewa:

    “Tafi tafiye tirke,

    Sarakan bana kwaɗayi gare su,

    Abu kadan a kai ka fada,

    Abu kadan a kai ka fada, Har gaban Sarki.”

    Haka ta rinƙa rera wannan waƙa san yana yi mata biyayya har suka isa gidan Sarki. Da suka isa fada Sarki ya ga sa sai ya ce za a yanka shi. Sai ya tambayi tsohuwa abin da take so daga jikin san. Sai ta ce ita abin da take so kawai shi ne kayan ciki. Sarki ya ba da umarni aka yanka sa, aka feɗe aka ɗebi kayan ciki aka ba tsohuwa.

    Da tsohuwa ta koma gidanta sai ta shanya kayan cikin nan, ta mai da hankalinta a kan aikinta na gona. Wata rana ta dawo daga gona sai ta tarar an yi mata shara a gida da sauran aikace-aikacen gida. Sai abin ya ba ta mamaki tana tunanin ba ta da kowa, kuma wanene zai zo ya yi mata wannan aiki.

    Kashe-gari ma aka sake yi mata aikin. Ashe da ma kayan cikin nan da tsohuwa ta shanya su ke rikiɗa su koma ’yan mata kyawawa guda biyar. Kullum idan ta tafi gona, sai su fito daga ƙarƙashin gadonta inda suke kwana su yi mata hidima. Wata rana sai tsohuwa ta ce tun da ba ta san mai taimaka mata ba, za ta shirya kamar za ta gona sai ta ɓuya a bayan danga domin ta ga mai yi mata wannan hidima.

    Haka kuwa aka yi. Ta ɓuya a bayan danga, can sai ga ’yanmata kyawawa sun fito daga ƙarƙashin gadonta. Nan da nan suka fara aikace-aikacen gida, suka buɗe randunanta suka cika da ruwa, suka yi share-share da duk sauran ayyukan da suka kamata. Can sai kwatsam tsohuwa ta faɗo tsakar gida suka gan ta.

    Ta yi musu magana. Daga wannan rana sai ’yan matan nan suka daina ɓuya, suka zauna da tsohuwa suna taya ta aikace-aikacen gida. Bayan wasu ’yan kwanaki sai tasa wa kowacce budurwa suna. Akwai Ta-kitse da Ta-hanji da Ta-tumbi da Ta-hanta da Ta-huhu.
    Ana nan, ana nan wata rana Gizo ya sake komawa bara gidan tsohuwa, sai ya hango waɗannan ’yan mata kyawawa a gidan tsohuwa.

    Ya fita da gudu sai gidan Sarki. Da ya isa sai ya ce: “Sarki, Sarki kunnenka nawa?” Sai Sarki ya ce: “Biyu.” Sai Gizo ya ce: “Ka ƙara biyu ka sha labari.” Sai Sarki ya ce: “Na ƙara.” Daga nan sai Gizo ya kwashe labarin ’yan matan da ya gani ya gayawa Sarki. Nan take sai Sarki ya tura fadawa a kawo masa guda ɗaya daga cikinsu.

    Sai dogarai suka je gidan tsohuwa suka yi sallama da ita. Da ta fito sai ta ga fadawan sarki ne. Sai ta koma gida ta fara waƙa tana cewa: “Ta-hanta, Ta-hanta, Ɗebo ruwa ki kai wa baƙon da ke waje.” Sai Ta-hanta ta ce: “Tabɗi, in ɗebo ruwa Ta-huhu tana nan.”

    Sai tsohuwa ta sake rera waƙa ta ce: “Ta-huhu, Ta-huhu, Ɗebo ruwa ki kai wa baƙon da ke waje.” Sai ta ce: “Tabɗi, in ɗebo ruwa in kai wa baƙon da ke waje, ga Ta-hanji
    tana nan?” Da haka, da haka har tsohuwa ta gama zagaya ’yan matan nan, har ta kai
    kan Ta-kitse. Ita ce ta ƙarshe.

    Sai ta ɗauko ƙoƙo, ta ɗebi ruwa ta kai wa baƙon da ke waje. Tana fita da ruwan nan sai fadawa suka kama ta, sai gaban Sarki. Da Sarki ya gan ta sai ya ce zai aure ta. Nan da nan kuwa ya aure ta ya sa ta cikin matansa. Amma ba ta fita rana, kuma ba ta zuwa kusa da wuta domin ita kitse ce, idan ta sha rana ko zafin wuta ya buge ta sai ta narke.

    Wata rana Sarki ya tafi yaƙi, sai kishiyoyin Ta-kitse suka ce sai ta fito ta yi girki, tun da ita ma auro ta aka yi kamar su. Da suka matsanta sai ta yi girki, sai ta je bakin murhu. Tana zuwa sai ta narke. Da tsuntsun Sarki ya ga abin da ya faru sai ya yi tsalle ya tashi sai filin daga inda su Sarki suke fafatawa da abokan gaba.

    Sai tsuntsun nanyafara waka yana cewa: “Sarki, Sarki, Ka mai da yaƙi baya, Ta-kitse ta narke, Ta narke ta zama ruwa.” Da Sarki ya ji waƙar tsuntsun nan sai ya bar yaƙi ya komo gida. Sai ya tarar har Ta-kitse ta gama narkewa. Saboda laifin da matansa suka yi masa na sa Ta-kitse girki a kan dole, sai ya kore su gaba ɗaya ya yi zamansa shi kaɗai. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Son zuciya ɓacin zuciya.
    • Abin da ka shuka shi za ka girba

    Karanta Tatsuniyar Kura Da Kurege (Na Huɗu)

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Riya Da Tasirin Social Media

    Riya Da Tasirin Social Media

    RIYA A MUSULUNCI:

    Duk wata ibada da musulmi zai yi don neman lada a wurin Allah, sharaɗi ne ya zama an yi shi ne saboda Allah Shi Shi kaɗai, ba tare da an haɗa Shi da wani mahaluki cikin wannan ibadar ba. Dole ne musulmi ya nufi Allah da kowace irin ibada da niyyar Allah ne Ya ba da umarnin a yi kuma Shi zai bada lada. Ya tabbata a hadisin Mahmud Bin Labid RA cewa Allah SWT zai faɗa wa waɗanda suka aikata wani aiki ba don Allah shi kaɗai ba, Allah zai ce musu ku je wurin waɗanda kuka yi aikin domin su a duniya su duba ko su na da ladan aikinku.

    A hadisin Imam Ahmad, Manzon Allah SAW ya ce “ Babban abinda na fi ji muku tsoro, ƙaramar shirka. Sahabbai suka ce; mecece ƙaramar shirka? Manzon Allah SAW ya ce Riya” Riya ƙaramar shirka ce ta fuskar neman yardan Allah da kuma neman yabon mutane. Shi kuma Allah, in dai ibada ce, toh Shi kaɗai ƙwallin – ƙwal a ke yi dominSa ba a haɗa Shi da wani – ko waye shi. Ita wannan shirkar bata fitar da mutum daga musulunci, amma tana ruguje ladansa, ta sa ya rasa ladan gaba ɗaya, sai dai ma ya ƙare da zunubi.

    Saboda haɗarinta, Manzon Allah SAW ya ja hankalinmu game da ita a hadisin Abi Musal Ash`ari, ya ma gargaɗe mu da mu guje ta. A wani hadisi Manzon Allah SAW ya ce: Riya tana shiga aiki – ba tare da mutum ya sani ba, kamar yadda Tururuwa ta ke tafiya akan dutse a cikin duhun dare” Jin tafiyar Tururuwa a kan dutse a cikin duhun dare abu ne mai wahala, toh haka tantance Riya cikin aiki, ta hanyar shin da wani nufi ko niyya aka yi aikin.

    TASIRIN SOCIAL MEDIA:

    Wannan dandali ko saha ta zama ruwan dare mai gama duniya, kuma tasirinsa ya wuce duk yadda mutum ya ke tsammani. Cikin `yan sakanni, duk wani abinda ya faru zai iya karaɗe duniya batare da bata lokaci ba. Wanɗanda su ke manyan birane ko cikin surƙuƙin daji duk zasu gani ko su ji. Sannan tasirin sa yanzu ya kai yana iya canza komai.

    Tasirin social media, ya kai yana iya canza wani ra’ayi na manyan mutane ɗaiɗaiku, yana iya tasiri a kasuwanci a kasuwanci, siyasa kai har uwa uba yana canza ƙudurorin gwamnatocin ƙanana da manyan ƙasashe. Idan akwai abinda zai iya girgiza gwamnati cikin ‘yan sakanni a wannan zamanin babu kamar Social Media.

    Cikin `yan kwanakin nan shugaban ƙasar Amurka Trump ya yaɗa wani shaguɓe da barkwanci a ɗaya daga cikin dandalin social media inda ya nuna shi ne “Yesu” wanda zai ceto duniya. Kafin ka ce wani abu, duniya ta sako Trump a gaba nan da nan ya goge abinda ya wallafa.

    Misali na biyu; bayan hare haren da Isra`ila ta kai wasu garuruwa a ƙasar Labanon, ranar 16 zuwa 17 ga watan Afrilu, 2026 sai wani bidiyo ya yi ta yawo a Social Media inda aka gano wasu sojojin Isra`ila sun karya wani mutun-mutumin “Yesu” suna faffasa shi da guduma.

    Wannan abin ya janyo kakkausar sukar ƙasar Isra’ila, duk da an san yadda Israila take da taurin kai ga duk ƙudurorinta ko abin sojojinta suka aikata, amma sai ga shi hukumomi a Isra`ila suna ba da haƙuri game da abinda ya faru, har da hukunta sojojin da suka aikata abin da hukuncin dauri na kwana 30 a gida, da kuma samar da wani mutun-mutumin sabo da mayar da shi inda yake nan take cikin kwanaki da bai wuce biyar ba. Wannan abin ba wanda ya isa ya sa Isar`ila ta yi wannan abin duk duniya in ban da tasirin Social Media ba.

    MUTANE A YANZU DA SOCIAL MEDIA:

    Ɗan adam, Allah ya halicce shi da son burgewa, neman ɗaukaka da shuhura. A yanzu dandalin Social Media ya zama hanya mafi sauƙi wurin samun waɗannan abububwan, nan da nan mutum zai shahara ko`ina a sanshi a ganshi, sunansa ya yaɗu. Akwai mutanen da ban da tasirin social media ba, da har su mutu ba wanda zai san suntaba rayuwa, sai `yan kaɗan da suke kusa da su, sai kuma a labari da hira in ta kama.

    Misali, irin manyan shehunan malaman da aka taɓa yi a ƙasaittacen birnin Kano waɗanda muke jin labari da wasu ma da har yanzu bamu sansu ba – Allah yayi musu rahama, Ya sa suna aljannah- da yanzu ne da sun karaɗe sosial media ko`ina an sansu ana ganinsu kamar yadda a yanzu muke ganinsu Prof. Bashir Aliyu Umar, OON da sauransu. Muna jin labarin Barau ƙwallon- shege da aka taba yi shi ma a Kano. Da yanzu ne da duk duniya sai ta san labarinsa kamar yadda aka san su Umar Bush da sauransu.

    Shugannin ƙasashe, manyan jagororin kasuwanci da na manyan shugabannin wuraren hada hada a duniya, yanzu sun fi maida hankali wurin nuna manufofinsu ta waɗannan hanyoyi na social media. Daga cikin shugabanni, kan gaba wurin amfani da social media akwai shugaban Amurka Trump, manyan `yan kasuwa akwai su biloniyan nan Elon Musk da kamfanisa na Tesla.

    RIYA DA SOCIAL MEDIA

    Wannan tasiri da ake gani na wannan sahar da dandali, ya sa wasu mutane dan neman shuhura da neman ɗaukaka, yin amfani da waɗannan hanyoyi ta yadda ba su tsaya neman duniya kaɗai ba, sai suka zarce har da aikin ibada. Mutane kowa yana neman hanyar da zai yi shuhura, wasu sun rungumi tallace tallace da kasuwanci, wasu bada ilimin addini da tarbiyya, wasu sana`o`i da ilimin zamani, wasu ɓarna da fasadi.

    Waɗanda suka ɗauki yaɗa ayukan ibadan da suke yi a social media, dan neman ɗaukaka da shuhura, su sani, wannan ba dai dai ba ne. Abin ya zama ruwan dare, sai ka ga mutum zai taimaka wa wani ko wasu masu buƙata, amma sai ya ɗora a media, ko bayan ya yi ibadar sa, sai kuma ya zo media yana ba da labari.

    Kai mai imani da ka yi don Allah, ina ka ga tallatawa a social media? Allah mabuwayi ne, kuma baya taɓar da aikin bawa, idan bawa ya yi ne dan Shi, sai Allah ya bashi ladan aikin cikakke kuma ya sa mutane suyi ta yaba masa ba tare da ya tallata a social media ba.

    Hadisin Abi Huraira wanda Imamul Bukhari ya fitar da shi, Manzon Allah SAW ya ce: “ Mutane bakwai suna cikin inuwar Al`arshi ranar da babu wata inuwa sai ita (ranar ƙiyama)- daga cikin waɗannan mutane, akwai wanda yayi sadaka da hanun damansa amma hanun hagunsa ba sani ba” a wannan hadisin yana nuna mana tsantsar ikhlasi da boye aikin ibada dan Allah shi kaɗai.

    Mu sani, duk wanda ya yi aikin ibada, idan har ya yi ne don a gani, ko don a yaba masa, ba shi da ladan komai a wurin Allah. Allah zai faɗa wa waɗanda suke aikin ibada dan a gani a yaba ranar tashin ƙiyama, Ya ce musu: “Ku je wurin waɗanda kuka yi aiki dan su, ku duba ko suna da ladan da za su ba ku” wanda ya yi aikin ibada a nan duniya ya ɗora a social media don ya sami comment da likes, to waɗannan comments da likes ɗin su ne ladansa, ba shi da komai a wurin Allah.

    Allah SWT ya ce “ Sai mu gabatar da ayukan da suka aikata, sai kawai mu sheƙar da shi kamar ƙura”S25:23, wasu malamai sun fassara wannan ayar ta cikin suratul Furƙan da cewa; waɗanda suka yi aiki ne ba dan Allah ba, sun yi ne dan su sami yabo, shuhura da ɗaukaka (likes, commnets and share), ko dan a san sun yi ko suna yi, to Allah sai ya sheƙar da ladan su kamar ƙura. Duk wanda ya yi aikin ibada dan likes, kuma ya samu, toh an biyashi, haka wanda yayi dan comments, share, view ko followers.

    Daga ƙarshe, mu ji tsoron Allah mu kyautata niyar ayukanmu, mu sani, Allah ne ya yi umarni da dukkan aikin ibada, kuma Allah ne zai bada lada. Wanda ya yi imani da Allah akan haka, ya sani Shi Allah duk inda bawa yayi aikin ibada – cikin dare ko rana, a bayyane ko a ɓoye, a birni ko a ƙauye- Allah ya sani kuma zai bashi lada cikakke. Shi tsantsance aiki ga Allah, shine duk lokacin da bawa zai gabatar da aiki kar ya nufi kowa da wannan aikin a zuciyarsa in ba Allah Shi kaɗai ba.

    Allah yana fada a wani hadisil ƙudsi wanda Abi Huraira ya raiwato, Imam Muslim ya fitar da shi, Allah ya ce: “Ni mawadaci ne ga duk wani mai haɗa Ni da wani a cikin aiki, duk wanda ya yi aiki ya haɗa Ni da wani, toh Ni bana buƙatar wannan aikin” Ɗan’uwa musulmi, mai imani da Allah bazai so a ce Allah ya ce baya bukatar aikinsa ba, ranar da yake cikin tsananin bukatar ladan aikinsa.

    Allah ka datar da mu, ka kaɓi ayukan mu. Amin.

    Danna nan don karanta Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kura Da Kurege (Na Huɗu)

    Tatsuniyar Kura Da Kurege (Na Huɗu)

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Kurege yana farauta a daji sai ya ga mushen Kurciya, sai ya ɗauka ya ajiye a kan itace. Ya ci gaba da tafiya sai kuma ya ga mushen Giwa, ya matsa kusa, ya dubi mushen da kyau, ya yi dariya. Daga nan sai ya kai wa Kura ziyara.

    Ya same ta tana saka zana sai yace: “Ki bari in kwanta a kan zanar nan taki.” Sai Kura ta ce: “To, kwanta mana.” Da Kurege ya kwanta sai ya lumshe idanunsa. Jim kaɗan kuma ya buɗe; sai ya ce da Kura: “Na yi mafarki wai mun je yawo da ke sai muka sami kan Kurciya mai kyau.”

    Kura na jin haka sai ta ce: “Kai-kai, ai gara ka sake kwanciya ko ka ƙara yi mana mafarki mai daɗi fiye da wannan.” Kurege ya rufe ido, ya buɗe sai ya ce: “Kai na sake yin mafarki wai kin sami mushen Giwa ke kaɗai.” Kura na jin haka sai ta ce da Kurege: “To mu tafi mu bi sawu.”

    Da ya ji sai ya ce: “Yanzu dare ya yi, sai dai can idan gari ya kusa wayewa.”Bayan zakara ya yi cara sai Kura ta sake cewa da Kurege su tafi, shi ko yace ta bari sai da hantsi. Kura ta kasa haƙura, sai ta hura wuta a kan ɗakinta wai hantsi kenan. Amma Kurege sai ya gane, ya ce da ita: “Ai wannan wuta ce kika hura a kan ɗakinki.”

    Daga ƙarshe dai da gari ya waye hantsi ya ɗaga, sai suka kama hanyar bin sawun mafarki. Suna cikin tafiya sai Kurege ya tura Kura wajen kan Kurciya. Da ta gani ta kirawo shi suka raba. Suna cikin tafiya sai Kurege ya tura ta wajen mushen Giwa. Da ta gani sai ta je ta yi kashi domin ta kasayar da abin da ke cikinta, domin ta sami damar cin naman mushen Giwa sosai, tun da ga nama kamar ba iyaka.

    Kurege da Kura suka shiga gyara nama. Suna cikin wannan aiki kenan sai ga ‘ya’yan Giwa sun bi sawun uwarsu. Sai tsoro ya kama Kurege da Kura. Sai Kurege ya ce: “Zan shiga cikinta in buya.” Sai Kura ta ce: “Kai yaro ne, ni babba ce zan shiga ciki.” Da Kura ta dage sai ta shiga cikin Giwa, shi sai ya shiga mafitsarar mushen Giwar.

    Da ‘ya’yan Giwa suka je kan mushen uwarsu, sai suka fitar da mafitsarar suka yar da Kurege a ciki. Da Kurege ya fita daga cikin mafitsarar, sai ya ga wata ƙarama daga cikin ‘ya’yan Giwar tana yankan ciyawa sai yace: “Wayyo, wa ye ya zuba mini ruwa?” Sai ‘ya’yan suka ce: “Ayya sannu ba mu san kana nan ba.”

    Sai ya ce: “A a, me ya sami kakata?” Sai baki ɗayansu suka ce: “Ba mu sani ba.” Sai Kurege ya ce: “Ku kawo jar dawa in zuba a ruwa in yi muku duba.” Da suka ba shi jar dawa sai ya ce: “Abin da ya kashe kakar nan tawa yana cikinta. Abin da za ku yi sai ku ɗauko sanduna ku yi ta dukan cikin.” Sai ko ‘ya’yan Giwa suka yi kamar yadda Kurege ya faɗa.

    Da duka ya ishi Kura sai ta ce: “Ba ni kaɗai ba ce, ni da Kurege ne.” Kurege ya ce: “Kada ku saurari maganarta, ku bugi wajen gefen bakinta.” Haka suka yi ta jibgar Kura, ta fito daga cikin Giwa jina-jina, ta gudu ta tsira da ƙyar. Sai ‘ya’yan Giwa suka ɗauki sauran mushen uwarsu suka kai gida domin su binne. Sai Kurege ya roki su ba shi kan kakarsa dominwai yabinne a gidansa. Sai suka yarda suka ba shi.

    Niyyarsa yana so ya dafa ne. Da zuwansa gida sai ya sa a tukunya aka hura wuta, aka sa tukunya akan murhu, kuma ya ce wa ‘yarsa: “In wuta ta mutu sai ki zo ki faɗa mini cewa ciyawa ta kare a gaban doki.” ‘Yar Kurege ta ce: “To baba, na ji.” Shi kuwa Kurege ya sa kai ya koma wurin ‘ya’yan Giwa zaman makoki.

    Da wuta ta cinye icen, sai ‘yar ta je gidan Giwa inda ubanta ke zaman makoki tace masa: “Baba ciyawa ta kare a gaban doki.” Kurege na jin haka ya ɗauki hannu, kuma ya tashi ya bi ‘yarsa suka tafi gida. Ya tarar naman kan Giwa bai gama dahuwa ba, sai ya ƙara ice, ya koma gidan makoki. Bayan wani dan lokaci da kan Giwa ya gama ɓararraka, sai yarinyar ta koma gidan Giwa inda ake zaman makoki ta ce masa: “Baba ai kan kaka kamar ya nuna.”

    Da ‘ya’yan Giwa suka ji haka, sai suka ce: “Ashe ba binne kan ka yi ba, dafawa kake yi? To sai a kama shi a kashe nan take.” Da ya ji haka sai ya falle da gudu tal-tal-tal ana bin sa, sai ya tarar da wani Kurege yana saƙa. Sai Kurege mai saƙa ya ce da Kurege mai gudu: “Me ya koro ka?” Sai Kurege mai gudu ya ce da Kurege mai saka: “Ai Sarki ne ke son wutsiyar Kurege dubu, sai mu gudu.”

    Da jin haka sai Kurege mai saƙa ya falle da gudu shi kuwa Kurege mai laifi
    ya yi zamansa ya kama saƙa. Da ‘ya’yan Giwa da masu taya su bin sawun Kurege mai laifi suka ga wancan Kurege yana gudu, sai suka bi shi, har suka kama shi, suka kashe. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Zafin nema ba ya kawo samu.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Dabara ta fi ƙarfi.

    Karanta Tatsuniyar ‘Yar Sarkin Da Ta Saci Ɗinya

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu