Tag: yadda ake

  • Tatsuniyar ‘Yar Sarkin Da Ta Saci Ɗinya

    Tatsuniyar ‘Yar Sarkin Da Ta Saci Ɗinya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani Sarki yana da ‘ya’ya maza da mata da yawa. Wata rana an kawo masa ɗinya sai ya ajiye ta a dakinsa. Rannan sai tafiya ta kama shi. Sai ɗaya daga cikin ‘ya’yansa ta ɗauki dinyar ta cinye. Da Sarki ya dawo sai ya tarar an cinye masa ɗinya. Sai ya tara matansa da ‘ya’yansa ya tambaye su ko waye ya cinye masa ɗinya.

    Sai suka shiga yi masa rantsuwa cewa ba su suka ɗauka ba. Bayan an yi, an yi babu wanda ya amsa cewa shi ne ya ɗauka, sai Sarki ya ce da fadawansa su tara matan da ‘ya’yan a kai su Kogin Rantsuwa su rantse, kuma duk wanda ya ɗauka to ruwa ya cinye shi, ya tafi da shi.

    Suka yarda aka kama hanyar kogi. Da aka isa sai aka fara rantsuwar da matan Sarki. Duk wadda ta shiga cikin ruwan sai ta fara waka tana cewa: “Kogi, kogi, In ni ce na ci ɗinyar Sarki, Ka tafi da ni, Kuma ka dawo da ni. Kada ka hadiye ni.” Matar farko ta fita ruwa bai tafi da ita ba.

    Ta biyu ma ta shiga ruwan bai tafi da ita ba, har matar ƙarshe ta shiga ita ma ruwa bai tafi da ita ba. Daga nan sai aka shiga kan ‘ya’yan Sarki maza. Aka zuba su gaba ɗaya suka rantse, su ma ruwa bai cinye ko ɗaya daga cikinsu ba. Shi ke nan aka zo kan ‘ya’yan matan.

    Su ma aka shigar da su, ba wadda ruwa ya ci har aka zo kan ta ƙarshe wadda ta cinye ɗinyar. Sai ta shiga ta fara waƙa tana cewa: “Kogi, kogi, Idan ni ce na ci ɗinyar baba, Ka tafi da ni, Kuma ka dawo da ni, Kada ka haɗiye ni.” Sai Kogin Rantsuwa ya tafi da ita. Sai matan Sarki da sauran ‘ya’yansa suka juya, suka koma gida, aka je aka gaya wa Sarki abin da ya faru.

    To ashe duk jama’ar gidan Sarki ba su san cewa wannan yarinya da ruwa ya tafi da ita Sarki na matuƙar son ta ba. Dalili kuwa ita ce ‘yar autarsa, sai ya yi ta kuka. Ruwa kuwa da ya tafi da ita sai ya kai ta wani baƙin jeji. Tana nan a rufe, can sai ta ga wata tsohuwa tana kama kwaɗi.

    Da tsohuwa ta ƙyallara ido ta ga yarinya, sai ta ɗauke ta, ta kai ta gidanta. Yarinya ta shari barcin gajiya. Da ta farka sai tsohuwa ta tambaye ta labarin abin daya faru. Sai ta kwashe labari ta gaya wa tsohuwa. Da tsohuwa ta ji labari sai ta ce wa yarinya: “Zan taimake ki, in sauya miki kamanni.

    Amma da sharaɗi, idan kin sami mijin aure zai kawo mini buhunan tsutsa biyu.” ‘Yar Sarki ta yarda. Nan take tsohuwa ta haɗiye ta sau bakwai. Da ta yi amanta ta haɗiye ta sau bakwai sai ga yarinya ta sauya kamanni baki ɗaya, ta zama fara jawur kamar ‘yar Sarkin aljanu.

    Bayan wasu shekaru, wata rana sai yarinya ta je cin kasuwa, sai ta haɗu da wani ɗan Sarki. Shi kuwa ɗan’uwanta ne na jini, to amma ba ta sani ba, don sun girma ba za ta gane shi ba. Shi kuma da ma ba zai gane ta ba saboda tsohuwa ta sauya mata kamanni. Shi ke nan sai ɗan Sarki yace zai aure ta. Sai ta ce sai dai ya je wurin kakarta su yi magana.

    Sai ya amince, suka je wurin tsohuwa. Da tsohuwa ta ji bayanin ɗan Sarki sai ta ce ya je ya kawo mata buhunan tsutsa biyu. Ɗan Sarki ya tashi cikin mamaki. Ya je ya nemo buhunan tsutsa biyu, ya kawo wa tsohuwa. Daga nan sai aka ɗaura masu aure. Ya ɗauki matarsa ya kai ta garinsu.

    Bayan ya kai ta gidansu, sai ta ga ashe gidan babanta ne. Sai kawai ta shiga cikin gida gayar da surukanta. Sai ta ga ai wadda ta haife ta ce surukarta. Shi kuma mijin yayanta ne, ubansu ɗaya. Da ta gane sai hankalinta ya tashi, amma babu yadda za ta bayyana wannan al’amari a gamsu tun da tsohuwa ta sauya mata kamanni.

    Kullum idan za ta yi daka sai ta fitar da turmi a tsakar gida tana daka tana waƙa tana cewa: “Babana da ya haife ni ya zama surukina, Innata da ta haife ni ta zama surukata
    Yayana da nake binsa ya zama mijin aurena, Kannena da suke bi na sun zama abokan wasana, Zan daki turmin gidanmu, Zan daki turmin gidanmu timkwalan-kwalan.

    Ana cikin haka kullum, sai wata tsohuwa ta kasa kunne ta ji abinda amarya take cewa. Rannan dai sai tsohuwar nan ta kira yaron ta gaya masa idan ya fita kamar za shi zaman fadanci, to ya laɓe a cikin gida ya saurari waƙar da matarsa take yi idan tana daka, ya ji abin da take cewa. Rannan sai ɗan Sarki ya fita, kamar ya tafi, sai ya laɓe.

    Jim kaɗan da amarya ta fara daka sai ta kama waƙar tana maimaita abin da take cewa kullum. Da ya ji waƙar matarsa sai ya fahimci abin da take faɗa, kuma ya gane cewa ƙanwarsa ce. Sai ya ruga da gudu, ya kama ta, yana kuka ya ce: “Ashe ke ce ‘yar autar baba, amma kika ki faɗa?”

    Ya ɗauke ta sai wurin babansa. Da ya yi gaisuwa, ita ma ta gai da Sarki, yace ta ba mahaifinta labarin abin da ya faru. Sai ta kwashe labari yadda ta cinye ɗinyar babanta, har ruwa ya tafi da ita. Ta faɗi yadda tsohuwa ta ɗauke ta, da yadda ta haɗiye ta ta sauya mata kamanni.

    Bayan ta kammala ba su labari, sai baki ɗayansu suka yi ta kukan murna, ‘yarsu ta dawo. Daga nan sai aka raba wannan aure, domin mutum ba ya auren ‘yar uwarsa. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Ba a tausaya wa ɓarawon da aka kama.
    • A kowane jinsin mutane auren zumunta yana da ƙa’ida

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Rimi Da ‘Yar Amana

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Rimi Da ‘Yar Amana

    Tatsuniyar Rimi Da ‘Yar Amana

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wani gari mai yawan jama’a da Sarkinsu mutumin kirki. Shi ke nan akwai wani mutum mazaunin wannan gari shi da matarsa da’yarsu ɗaya. Suna nan sai wata rana ciwon ajali ya kama matar wannan mutum. Kafin ta rasu sai ta kira shi ta ce: “Mai gida, ni fa ina jin ba zan tashi daga ciwon nan ba, amma ga amanar ‘yarmu nan ka kula da ita sosai.

    Kada ka bari wani mugun abu ya same ta.” Mijin ya amsa. Da matar ta rasu sai shi kuma uban yarinyar ya ci gaba da renon ‘yarsa har ta yi wayo. Sai wata rana shi ma ciwon ajali ya kama shi, sai ya rasa yadda zai yi da ‘yarsa, kuma ba shi da kowa a garin.

    To amma akwai wata tsohuwar bishiyar rimi a kofar gidansa, sai ya fito ya ɗauko yarinyar ya kawo ta gindin rimin. Sai ya dubi rimin nan ya ce ya ba shi amanar ‘yarsa domin yana jin wa’adinsa ya kusa cika. Daga nan ya koma gida, bai sake fitowa ba, har ya rasu.

    Bayan rasuwarsa da ‘yan kwanaki, duk sanda yarinya ta ji yunwa sai ta je wurin rimin ta kama waƙa tana cewa: “Rimi, rimi uwata, Rimi ubana ya ba ka amanar Allah, Uwata ta ba ka amanar Allah.” Da ta yi wannan waka sai rimi ya ba ta abin da take so. Kullum haka sai wata rana Gizo ya fita yawo sai ya ga ‘yar budurwa tana wanki a gindin rimi.

    To da ma sunanta Jummai. Da Gizo ya ga kyaunta sai ya garzaya gidan Sarki. Ya sami Sarki a fada tare da fadawansa, ya faɗi ya yi gaisuwa yace da Sarki: “Sarki, Sarki kunnenka nawa?” Sai Sarki ya ce da Gizo: “Biyu.” Shi kuma Gizo ya ce: “Ƙara biyu ka sha labari.”

    Sai Sarki ya yi murmushi ya dubi Gizo ya ce: “Na ƙara.” Da Gizo ya sami yadda yake so, sai ya kwashe labarin Jummai ya gayawa Sarki. Da Sarki ya ji haka sai ya tura fadawansa su ɗauko yarinya. Da suka isa wurin rimi sai yarinyar ta gan su, kuma ta razana ta je ta rungumi rimi ta fara waka tana cewa:

    “Rimi, rimi uwata, rimi ubana, Uwata ta ba ka amanar Allah, Ubana ya ba ka amanar Allah.” Sai rimi ya ce: “Yi wankinki, Yi wankinki, Yi wankinki Jummai, Cikin ɗari da goma, Ɗaya ya koma, Cikin ɗari da goma, Ɗaya ya koma.” Da dogarai suka matsa sai duk suka mutu.

    Da Sarki ya ji labari sai yasa a je a sare wannan rimi. Da aka taru za a sare, idan aka sara jikin sai ya sake tohowa. Idan an sake sara ma haka, har dai masu saran suka gaji, suka haƙura. Har yanzu wannan rimi da ya riƙe amana yana can a garin, mutane suna zuwa kallon sa. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Rikon amana garkuwa ne ga kowane mahaluki.
    • Azzalumi ba shi da riba a harkokinsa na zalunci

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Damon Sarki

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Gizo Da Damon Sarki

    Tatsuniyar Gizo Da Damon Sarki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Sarki ya kawo Damo babba. Sai ya kai shi gonarsa bayan gari. Bayan ‘yan kwanaki kaɗan ya sake kawo wasu don kiwo, kuma yasa aka yi shela a gari cewa kada a taɓa su, tare da bayanin cewa duk wanda ya yanka ya ci zai mutu.

    Ana nan, sai wata rana kwaɗayin nama ya kama Gizo, sai ya zagaya inda Damon Sarki suke. Ba tare da jin wani tsoro ba ya kama ɗaya ya yanka, ya kawo wa matarsa ta dafa masa ya cinye. Da ya ji daɗi sai kullum ya zagaya ya kama ɗaya ya yanke, har sai da ya gama Damon Sarki duka shi kaɗai.

    Da ya ƙarasa cinye naman Damo sarai, rannan sai ciwo ya kwantar da shi. Sai ya aika wa Ƙoƙi domin ta zo ta kai shi wurin magani. Da Ƙoƙi ta ɗauki Gizo suka kama hanya za su neman magani, suna cikin tafiya sai suka haɗu da Kura a cikin jeji. Sai Kura ta ce: “Ke Ƙoƙi ina za ki?” Sai ta ce: “Zan kai Gizo ne gidan magani.”

    Sai Kura ta ce: “In kin je ki gaya masa ba zai yi rai ba don ya ci Damon Sarki.” Sai Ƙoƙi ta ce: “Wai, wai ashe cutar ba ta warkewa ba ce. Gwanin zafi, gwanin zaƙi.” Haka dai suka ci gaba da tafiya. Can kuma sai suka haɗu da Zaki. Sai Zaki manyan dawa ya dubi Ƙoƙi ya ce: “Ke Ƙoƙi ina za ki?” Sai ta ce: “Mai girma Manyan Dawa zan kai Gizo ne gidan magani.”

    Sai Zaki ya ce: “In kun je ku gaya masa Gizo ba zai yi rai ba.” Sai Ƙoƙi ta yi salati, ta ce: “Ashe cutar ta fitar rai ce. Gwanin daɗi, gwanin zafi.” A nan ne fa Ƙoƙi ta sauke Gizo daga bayanta, ta yar da shi ta ce: “Tunda ka ci Damon Sarki, ka ci mutuwarka. Bari in bar ka a nan idan ka mutu kada ka yi musu wari a gari.” Sai Ƙoƙi ta koma gida, ta bar mijinta Gizo a cikin ciwon ajali. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
    • Ba a karya dokar Sarki a kwana lafiya.
    • Kowa ya ɗebo da zafi, bakinsa.

    Karanta Tatsuniyar Talipaku Da Kurciya

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Talipaku Da Kurciya

    Tatsuniyar Talipaku Da Kurciya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana tsuntsuwa Talipaku da Kurciya suka yi sheƙa a bishiya ɗaya. Da lokacin saka ƙwan da suka ɗauka ya zo, sai suka haɗa ƙwansu a wuri ɗaya. Bayan sun gama kwanci, sai suka ƙyanƙyashe ƙwayayensu, suka sami ’ya’yansu guda biyu.

    Suna nan a haka, kullum sai su fita neman abincin’yan tsakinsu. Kansu ya haɗu, komai na tafiya rumui-rumui. To ashe ita Talipaku ba ta jin daɗi da bakin ’yarta ya yi tsawo fiye da na’yar Kurciya, wadda ba wani abu da ya dami ’yarta, kyakkyawar gaske. Duk lokacin da za su fita neman abincin ’ya’yansu, sai a karɓi renon’yar Kurciya, amma a bar ’yar Talipaku a sama cikin sheƙa.

    Shi ke nan sai wata rana Talipaku ta yanke shawarar sace ’yar Kurciya ta gudu da ita. Wata rana suna wurin neman abinci, sai Talipaku ta sulale, ta je ta sace ’yar Kurciya ta gudu da ita. Da Kurciya ta ɗaga kai ba ta ga Talipaku ba, kuma suna daf da tafiya gida, kuma ta nemi ƙawarta har ta gaji, sai ta dawo gida ita kaɗai.

    Da ta shiga sheƙa, sai ta ga ba ’yarta, sai ɗiyar Talipaku. Sai ta fita ta kama cigiya. Sai
    aka ce mata ai an ga Talipaku ta ɗauki ’yar Kurciya sun yi yamma. Da jin haka sai Kurciya ta koma sheƙarsu ta ɗauki ’yar Talipaku ta fito fur ta kama waƙa tana cewa:

    “Talipaku, Talipaku,

    Don bambancin ’ya’ya,

    Nawa a gabanki,

    Naki a bayana,

    Kika ɗauki mai kyau,

    Kika bar mummuna.

    Garinmu, garinmu,

    Garinmu da Sarki,

    Mai yawa in kin je,

    Sai idonki ya ɓata,

    Mu je mu, mu je mu.”

    Haka dai ta dinga yin wannan waƙa, tana tafiya tana ci gaba da bincike har ta haɗu da wasu manoma. Sai ta gaishe su, suka amsa, sai ta tambaye su ko sun ga Talipaku ta wuce? Sai suka ce: “E, tun ɗazu ta wuce.” Kurciya ta ɗauki ’yar Talipaku tana waƙa ta ci gaba da tafiya ta je wajen masu kiwo, sai ta tambaye su ko sun ga Talipaku? Sai suka ce: “E, ba ta daɗe da barin wurin nan ba.”

    Haka dai Kurciya ta ci gaba da tafiya tana waƙa, tana tambaya. Ita kuwa Talipaku tuni har ta isa garin Sarkin tsuntsaye ta tambayi hanyar gidan Sarkin. Aka kai ta gidan Sarkin tsuntsaye. Sunan Sarkin Miki. Da ta je gaban Sarkin, sai Sarkin ya tambayi Talipaku ko me ke tafe da ita?

    Sai tace ta zo ne ita da ’yarta a ba su wuri a garin domin ta zauna. Da Miki ya ji haka, sai ya ce: “To ai ’yar da kika zo da ita ba ta yi kama da ke ba. Ba ’yarki ba ce. Ina kika samo ta?” Ita kuwa Kurciya tuni ta haɗu da wasu mutane a jeji ta tambaye su ko sun ga Talipaku?

    Sai suka gaya mata cewa yanzu ta tambaye su hanyar gidan Sarkin tsuntsaye. Sai suka nuna wa Kurciya hanyar, suka ce ta yi sauri ko ta same ta a gidan Sarkin tsuntsaye. Nan take ta kama hanyar zuwa gidan Sarkin tsuntsaye. Tana zuwa gidan, sai ta tarar ana tambayar Talipaku a inda ta samo’yar da ba ita ta haifa ba.

    Sai Kurciya ta fara rera waƙa ta faɗi a gaban Sarkin tsuntsaye ta yi gaisuwa, ta kuma yi wa Sarki bayani a kan yadda suka yi da Talipaku. Sai Sarkin ya sa aka ƙwace ’yar Kurciya, aka ba ta ’yarta. Ita ma Talipaku aka ba ta ’yarta. Sarkin tsuntsaye ya ja kunnen Talipaku da kada ta kuskura ta sake satar ’yar wani tsuntsu.

    Idan kuma aka sake kawo ƙararta, to za a kashe ta. Sai aka sallame su. Kurciya ta ɗauki ’yarta. Ta yi godiya ta tafi. Ita kumaTalipaku ta tafi da ’yarta. Ƙurunƙus.

     Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Maciyi amana ba shi da mabuya a duniya.
    • Baƙin ciki da abin da Allah ya yi wa wani ba zai ƙara komai ba sai faɗawa cikin wahala.
    • Maci amana yana tare da jin kunya.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Yarima Da Labbi

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Yarima Da Labbi

    Tatsuniyar Yarima Da Labbi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wani Bafulatani yana yawo a jeji sai ya tarar da wata mata a zaune a gindin wata kuka. Yau da gobe yana zuwa har suka saba. Kullum haka yakan same ta bayan azahar ko kuma dab da azahar. Duk sanda ya je takan ba shi ruwa ko kunu ya sha. Bayan sun yi hira kuma sai ya koma yaci gaba da kiwon dabbobinsa.

    Wani lokacin kuma yakan kai mata madarar shanu da dambu. Ashe da man matar nan ba mutum ba ce, kasa ce da ke zaune a cikin kogon wannan kukar take rikiɗa ta zama mace. Sannu a hankali sai ƙauna ta shiga tsakaninta da Bafulanin nan, har dai suka yi aure.

    Bayan wasu watanni da aurensu, sai ta ɗauki ciki. Daga ƙarshe ta haifi ’ya. A ranar suna aka taru, aka sa wa jaririyar suna Labbi. Bayan ’yan shekaru, sai kasar nan ta ce da ’yarta: “Ba za ki zauna a wannan jejin ba, ki tafi ko wani gari ki zauna.” Sai ’yar ta tafi Hawul ta sauka a gidan Sarkin garin ta zauna.

    To shi Sarkin yana da ɗa mai suna Yarima. Wannan yarinyar kuwa mummuna ce; ba ta da kyau ko kaɗan. Ana nan, sai wata rana yarinyar ta ce za ta je garinsu. Da ta isa garinsu, watau dajin da uwarta kasa take, sai ta gaya wa mahaifiyarta cewar za a yi
    wasa a kofar gidan Sarkin Hawul.

    To da ma Sarkin yana so ɗansa Yarima ya aure ta, amma Yarima ba ya sonta saboda muninta. Labbi dai duk ta kwashe wannan labari ta gayawa mahaifiyarta kasa Uwar ta ji haka, sai ta ɗauki Labbi ta hadiye, ta amayar da ita sai ta ga ba ta yi mata kyau ba. Sai ta sake haɗiye ta, har dai haɗiya ta kai uku, sai yarinya ta futo kyakkyawa, ba irinta a duk duniya.

    Uwar kuma ta kawo kujerar zinare ta ba Labbi. Yarima ya hango wannan yarinya, ya je kusa da ita ya ce: “Ina ne garinku?” Sai ta dube shi ta ce: “Daga nan zuwa garinmu tafiyar wata uku ce.” Yarima ya ba ta wani zobensa na kawa.

    Dila ya ga zobensa a cikin gayan furar ne fa ya gane ashe ita ce matarsa. Nan da nan ya ce da ayarinsa kowa ya karya linzami, su koma gida domin matarsa tana gida. Da Yarima ya dawo gida sai ya sa aka kira Labbi yace zai aure ta…

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa:

    • Alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza.
    • Matar mutum kabarinsa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Budurwa Mai Neman Ganyen Miya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Budurwa Mai Neman Ganyen Miya

    Tatsuniyar Budurwa Mai Neman Ganyen Miya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata budurwa mai suna Yakadi a wani ɗan ƙauye da ke nan kusa da bakin rafi. Wata rana sai mahaifanta suka aike ta lambu ta samo ganyen miya. Ta shirya ta kama hanya tare da ƙannenta, suka je, suka samo ganyen miya. A kan hanyarsu ta dawowa gida sai suka haɗu da wata tsohuwa ta ce da su: “Sannunku ’yanmata, don girman Allah ku taimake ni da ganyen ɗan kaɗan mana.”

    Sai ita Yakadi ta ce: “Ba za a bayar ba.” Suka ci gaba da tafiya, da suka kai kusa da wani dutse sai suka ce za su huta. Bayan sun zauna sun huta, sai ƙannenta suka tashi
    tsaye za a fara tafiya, amma ita Yakadi sai ta kasa tashi domin duwawunanta sun manne a jikin dutse.

    Suka yi ƙoƙarin ɓanɓare ta domin su tayar da ita amma suka kasa. Da iyayensu suka ji haka, sai suka nufi gida da gudu don su sanar har inda ’yarsu ta maƙale. Suna isa, suka yi ta ƙoƙarin ciro ta, amma abu ya gagara. Sai suka yanke shawarar gina ɗaki a kanta, haka kuwa aka yi. Tana nan, kullum suna kai mata abinci.

    Duk sanda mahaifiyarta ta je wurinta a ɗakinta, sai ta yi wata waƙa, in ta ji muryar mahaifiyarta ne sai ta buɗe mata ƙofar ɗaki ta shiga, in kuma ta ji wata murya ce daban, sai ta ƙi buɗewa. Haka ta ci gaba da rayuwa har zuwa wani lokaci da Kura ta garin yawo ta tarar da ɗakin da Yakadi ke ciki, ta yi ƙoƙarin shiga, amma ta kasa.

    Ana nan, wata rana Kura ta ɓuya, ta ji irin yadda uwar yarinya take yin waƙa a buɗe, ta shiga. Bayan uwar yarinyar ta tafi, sai Kura ta je ta yi waƙar, to amma da yake muryar ba irin ta uwar yarinyar ba ce, sai Kura ta ki buɗewa. Da Kura ta ga haka, sai ta tafi
    inda ake gyaran murya, aka gyara mata. A kan hanyar zuwa inda Yakadi take, sai yunwa ta kama Kura.

    Da ta ga kuda, sai ta kama shi ta haɗiye. Da Kura ta isa ƙofar ɗakin, ta fara waƙa sai muryarta ta shaƙe, ta koma kamar ba a gyara ba. Yarinya kuwa ta ƙi buɗe ƙofa, Kura kuwa ta sake komawa wajen gyaran murya, mai gyara ya ce mata in ta kama hanya kada ta ci komai, sai ta yi waƙar ta gama.

    Sai Kura ta yarda, ta kama hanya. Kura tana cikin tafiya, sai yunwa ta sake kama ta. Da taga sauro, sai ta kama shi, ta haɗiye. A nan ma muryar Kura ta sake gyara mata murya, suka haɗa ta da mai kula da ita har sai sun je bakin ɗakin da yarinya take. Da yake Kura ba ta ci komai a hanya ba da ta yi waƙa a ƙofar ɗakin Yakadi, sai ta ji murya kamar ta mahaifiyarta, ta ja ƙofa ta buɗe.

    Kura ta shiga ta cinye ta, amma ta bar kai da ƙafafu. Bayan Kura ta tafi, sai uwar yarinya ta je, ta tarar an cinye ’yarta, in ban da kai da ƙafafu. Sai ta fara kukan baƙin ciki. Tana cikin kuka sai tsohuwar nan ta zo ta rarrashe ta, kuma ta gaya mata idan ta je gida ta kona zuba sai ta rinƙa kiran sunayen gangar jikin Yakadi ɗaya bayan ɗaya, har sai ’yarta ta haɗu.

    Sai ta yi wa tsohuwa godiya, ta tattara kai da ƙafafun ’yarta, ta koma gida. Da ta koma gida sai ta yi yadda tsohuwa ta umarci ta yi. Da ta fara kiran sunayen ɓangarorin jikin ’yarta, sai duk ɓangaren da ta ambata ya faɗo, har dai ta gama kiran dukkan sauran sassan jikin yarinya, sai ta ga ’yarta ta dawo da rai kuma kyakkyawa kamar yadda take a da, ta ci gaba da rayuwa har lokacin da aka yi mata aure. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Rowa sanadin tsiya.
    • Alheri danko ne ba ya faɗuwa ƙasa banza.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Dagaci Da Malaminsa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Dagaci Da Malaminsa

    Tatsuniyar Dagaci Da Malaminsa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wani Dagaci a wani gari yana da matarsa, to amma matar ba ta taɓa haihuwa ba. Ba tare da saninsa ba, wata rana matar wani babban malami ta je wurin matar Dagaci hira a gidansa. Suna cikin hira sai matar Dagacin ta fara ba matar malamin labarinta shi ne halin da take ciki na rashin haihuwa.

    Kuma ga shi maigidanta, watau Dagacin, ya ce yana son ya sami ’ya’yan da za su zo su gaje shi. Kuma ya ba matar tasa wasu ’yan watanni, idan ba ta sami ciki ba zai kore ta, ya auro wata matar. Wannan barazana ce fa ta sa matar Dagaci ta fara kuka da baƙin ciki. Da matar malami ta ji yadda labarin yake, sai ta tausayawa matar Dagaci.

    Shi ke nan, sai matar malamin ta ce mata: “Kin gani yanzu ina da ciki wata biyu, sai ki fara dunƙula tsumma ki ɗaura a cikinki ki gaya wa mijinki cewa Allah ya ba ki juna biyu.” Abinda matar malami take son yi shi ne idan Allah ya sauke ta lafiya, za ta kawo wa matar Dagaci abin da ta haifa, domin ta nuna wa mai gidanta cewa ta haihu.

    Wannan hikima ta faranta wa matar Dagaci rai, kuma ta yarda aka yi alƙawari da matar malami, har matar Dagaci ta durƙusa tana yi mata godiya. Bayan ’yan kwanaki sai ta gaya wa Dagaci cewa ta yi ɓatan wata, kuma tana tsammani tana da ciki wata biyu. Da Dagaci ya ji wannan labari sai ya shiga murna.

    Ya fara faɗa wa fadawansa da mutanen gari cewa yanzu kam matarsa tana da juna biyu, kuma in Allah ya yarda ba da daɗewa ba za ta haifa masa ɗan da zai gaje shi. Saboda farin cikin da Dagaci yake yi, sai ya ba da umarni a kai matarsa wani gyararren gida. Yasa a riƙa yi mata duk abin da take so.

    Kuma ya ce kada ta taka ko ƙofar ɗaki don kada ta wahala a lokacin da take renon cikin har ranar haihuwarta. Ana nan sai mutane suka fara tsegumi a kan ai da ma matar
    Dagaci ba ta haihuwa, yaya kuma yanzu za a ce tana da ciki? Surutai suka yi yawa a gari, har wasu suka bugi ƙirji, suka sami Dagaci suka fara yi masa irin wannan magana.

    Wani daga cikin su ya ce, idan matar Dagacin nan ta haihu, to a ɗauki rumbun zuba amfanin gonar gidan Dagaci a ɗora masa a kansa. Wani kuma yace, in ta haihu a ɗaura masa igiya a kwankwaso a zagaya gari da shi har ya mutu. Can na ukunsu ya ce, in har ta haihu, to zai cinye buhun barkono goma shi kaɗai.

    Wani kuma ya ce, shi idan ta haihu to zai cinye dutsen da yake bayan gari. Haka dai suka ci gaba da maganganu, shi kuwa Dagaci bai ce komai ba, aka ci gaba da renon ciki har ya kai lokacin haihuwa. A ranar da matar malami ta haihu sai aka ce ai matar Dagaci ta haihu. Kamar yadda aka yi alƙawari, sai matar malami ta ɗauki jaririnta ta kai wa matar Dagaci ba tare da wani ya san an yi haka ba.

    Bayan labari ya bazu a gari sai masu rantsuwa suka dawo gaban Dagaci suka ce har idan an fito da yaro aka yi masa aski ranar suna, to za su cika alƙawarinsu da suka ɗauka, amma idan kuma zancen ƙarya ne, to za a kashe matar Dagaci. Dagaci ya yarda da haka. Matar Dagaci ta ci gaba da renon jaririn matar malami har ranar suna ta zo.

    Ana gobe suna sai matar malami ta dawo ta ce mijinta ya ce shi ba zai ba da ɗansa ba, saboda haka a dawo masa da ɗansa. Matar Dagaci na jin haka, sai ta ce: “Haba matar malam, bayan mungama magana da ke kuma kin ɗauki alƙawari yanzu ki ce in dawo ki ce ba zai yiwu ba, ai wannan cin amana ne.

    Idan Dagaci ya ce ina jariri bayan kowa ya ji na haihu, to me zan gaya wa Sarki? Kuma an ce idan ba a fita da yaro ba gobe ranar suna, za a kashe ni. Ki yi min rai mana!” Haka dai ta yi, ta yi, amma matar malami ta ƙi yarda, daga ƙarshe ta karɓi ɗanta ta tafi gida, matar Dagaci ta rasa yadda za ta yi. Da ta ga ba mafita sai ita da ƙanwarta suka shirya za su gudu cikin dare.

    Da dare ya yi suka kama hanyar daji suna cikin tafiya, sai suka ji wata tsawa a gabansu sai suka ga ƙasa ta tsage, sai ga wani jariri a cikin tsumma yana kuka. Sai matar Dagaci ta yi godiya ga Allah, ta ɗauki yaro suka kama hanyar gida. Ba su jima da komawa gida ba gari yawaye.

    Fada kuwa ta cika fal da mutanen gari da maƙada da mawaƙa da wanzamai za a yi wa ɗan Dagaci aski, kuma a raɗa suna. Su kuma masu alƙawari suna gefe suna jiran burinsu ya cika a ce babu yaro. Sai Dagaci ya tura a kawo jariri. Aka shiga cikin gida aka fito da yaro kyakkyawa mai kama da Dagaci. Nan take waɗanda suka ɗauki alkawari idanu suka raina fata.

    Shi kuma malami mamaki ya kama shi, aka dai yi wa yaro aski, aka raɗa masa suna. Sarki ya sa aka kamo waɗanda suka ɗauki alƙawari aka fara hukunta su, ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, har suka mutu. Shi kuma malami ya kama hanyar gida ya kwashe labari ya gaya wa matarsa yadda aka yi. Sai malami ya ce da matarsa ta ɗauko yaron su ma su raɗa masa suna.

    Da ta je ta ɗauko yaro, sai ta tarar ya mutu. Matar malami kuma baƙin ciki ya kama ta, ta kama hanyar gidan Dagaci. Da ta shiga ta sami matarsa sai ta yi ta ba ta haƙuri game da laifin da ta yi mata. Ita ko matar Dagaci ta ce ba komai, zance ya wuce, ta ci gaba da zaman daɗi da mijinta har lokacin da mai rabawa ta raba. Ga ɓera nan, ga ɓera nan, duk wanda ya ji tsoro alhaki a kansa. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Da kyautar Allah.
    • Alheri ya fi mugunta

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta

    Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wani mutum a wani ɗan ƙauye yana da mata da ’ya’ya. Ana nan, sai ɗaya daga cikin matansa ta haifa masa yarinya kyakkyawa. Bayan kwana bakwai sai ya raɗa mata suna Kwambal. Sannu a hankali, kwanci-tashi, yarinyar ta girma, kyanta ya ƙara bayyana, har ya kasance duk garin ba mai kyau kamar nata.

    Da ta isa aure sai mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa neman aurenta, wancan ya zo, amma sai ta ƙi, haka aka yi ta fama amma babu wanda ya yi nasarar samunta. Kwatsam sai wani yayanta, wanda suke ’yan turaka, mai suna Dawi ya ce zai aure ta. Da Kwambal ta ji niyyarsa, sai ta ƙi ta ce yaya za ta auri wanda suke ubansu ɗaya da shi?

    Shi ko Dawi da man ɗan baiwa ne. Wata rana sai ya ɗauke ta a kan raƙumi suka tafi cikin wani ƙungurmin daji ihunka banza, inda babu mutane. Ashe da man ya ja ta dajin ne domin ya nuna mata hatsabibancinsa ko ta ji tsoro ta aure shi. Da fari ya rikiɗa, ya zama wani babban baƙin maciji, mai gemu da jajayen idanu da ’yan kunne.

    Sai ya fasa kai, ya ƙura mata jajayen idanunsa masu kama da garwashi, ya ce ta yarda ya aure ta, ko kuma ya cinye ta. Ita ko da kafewa, sai ta ƙeƙasa ƙasa ta ƙi. Da ya ga haka, sai ya zama wani dodo mai haƙora gatso-gatso da farata masu tsawo da kaifi da kofatai a ƙafafunsa. Yana cikin wannan hali ya sake cewa ta yarda ta aure shi, ko kuma a bakin ranta.

    Ita kuma ta sake kafewa faufau, ta ƙi. Haka dai ya rinƙa rikiɗa, yana fito mata a kamanni da halittu daban-daban masu ban tsoro don ta ji tsoro, amma ta ƙi yarda, har ya gaji. Sai ya dube ta ya sanar mata da aniyarsa ta komawa gida ba tare da ita ba, watau zai bar ta a dokar dajin nan tun da ta ƙi yarda.

    Yana gama gaya mata haka, sai ya kwantar da raƙuminsa, ya ɗare, ya karya akala, raƙumi kuwa ya kama tafiya. Da ta ga ya bar ta, sai ta gyara muryarta tattausa, mai daɗin sauti da ratsa rai, ta kamawaƙa tana cewa:

    “Dawi ɗan’uwana,

    Ɗora ni a kan raƙuminka.”

    Da ya ji wannan waƙa, sai ya mayar da waƙa yana cewa:
    “Ki ce ni mijinki ne,
    In ɗora ki a kan raƙumi.”

    Sai ta mayar masa a cikin wannan baitin:
    “Ba ni iya faɗa, Kai dai ka ɗora ni a kan raƙumi.”

    Duk da waƙoƙin da suke yi, bai tsaya ba, ita kuwa ta rinƙa binsa tana yi masa waƙa da magiya ko ya ɗauke ta ya kai ta gida, amma sai ya ƙi, ya yi tafiyarsa shi kaɗai. Da ta gaji, sai ta zauna a gindin wata bishiya tana kuka. Can sai wani dodo ya ɓullo. Tana ganin dodo ta razana, ta yunƙura za ta tashi ta gudu.

    Da dodo ya ga haka sai ya buɗe bakinsa mai feshin wuta da hayaƙi ya ce da ita: “Idan kika gudu zan cinye ki yanzun nan.” Tana jin haka sai ta tsaya. Da dodo ya ga kyawunta sai yace mata: “Idan kin amince kika aure ni, zan kai ki gidanku, amma idan kika ƙi zan cinye ki.” Da ta ga ba mafita, sai ta yarda ya aure ta.

    Suka tafi gidan dodo, ta dangana, ta zauna da shi. Suna nan, har dodo ya tambaye ta irin abincin da takan ci, sai ta ce nama ta fi so. Duk yayin da ya fita farauta sai ya kaso namun daji ya kawo mata nama da yawa. Duk dare ’ya’yan dodon sai su fara cewa suna jin warin mutum, kuma suna so su ci naman mutum.

    Ita tana can inda babansu ya ɓoye ta. Da zarar ta ji irin wannan magana ta ’ya’yan dodo, sai ta wurga musu irin naman da ubansu ya kawo, sai su ɗauka su tafi. Kullum haka take fama da su. A can gidan su Kwambal kuwa, baƙin cikin duniya ya dami mahaifiyarta, kuma tuni ta shiga cigiyarta, har wata rana ta haɗu da tattabara.

    Bayan sun gaisa da tattabara, sai ta tambaye ta ko ta ga ’yarta Kwambal? Da tattabara ta ji wannan tambaya, sai ta kaɗa fuffuke, ta dubi gyatumar Kwambal ta kaɗa baki ta ce: “E, na ganta amma tana gidan dodo suna zaman aure.” Jin wannan labari ya ƙara tayar da hankalin uwar, nan take ta ɓarke da kuka.

    Can dai ta daina kukan, ta share hawaye ta dubi tattabara ta ce da ita: “Akwai kuwa yadda za a yi a kuɓutar da ita daga hannun dodo?” Tattabara ta ce: “E, akwai wata dabara. Tun da dodon yana da gashi, a aika wa Kwambal cewa ta gaya masa za ta yi masa kitso a gindin kuka.

    ”A cikin ƙagara uwar Kwambal ta ce: “To daga nan fa?” Sai tattabara ta ci gaba da bayani: “Idan ta yi ƙananan tsoraye sai ta nuna masa daga nan kuma sai ta ɗebi gashinsa mai yawa ta ɗaure shi da shi a jikin kuka. Idan ta ɗaure shi bajau, sai ta tashi ta kama hanyar gari da gudu”

    Da uwar Kwambal ta ji wannan shawara sai ta ji daɗi, ta yi wa tattabara alƙawari idan ’yarta ta kuɓuta za ta ba ta tukuici mai yawa. Sai tattabara ta tashi sama ta kama hanya har gidan dodo, ta sauka a kan ɗakin Kwambal, ta fara waƙa tana kiran sunan Kwambal tana cewa:
    “Kin yi tagumi ’yar auta,

    Ki daina kuka ’yar autar iya,

    Idan ya dawo ’yar auta,

    Ki kai shi gindin kuka ’yar auta,

    Ki yi masa kitso ’yar auta,

    Ki kitsa ƙanana ’yar auta,

    Ki nuna masa ’yar auta,

    Ki ɗebi mai yawa ’yar auta,

    Ki ɗaura a jikin bishiyar kuka ’yar auta,

    In ya ɗauru ki kama hanyar gida.”

    Ta rinƙa maimaita waƙa har Kwambal ta fara jin waƙa sai ta fita. Ta saurari waƙar tattabara da kyau sai ta fahimci bayanin tattabara. Washegari da dodo ya zo ɗakinta sai ta ce za ta yi masa kitso amma a gindin kuka, sai ya yarda ya fara jin daɗi matarsa za ta yi masa kitso.

    Suka tafi gindin bishiyar kuka ta fara yi masa kitso, idan ta kitsa ɗan siriri sai ta nuna masa sai ya ji daɗi, idan ta ɗebi gashi mai yawa sai ta ɗaura a jikin bishiya har ta gama yi masa kitso. Da ta ga daɗin kitso ya sa ya fara gyangyaɗi, sai ta yi sanɗa ta janye jikinta ta fara gudu ta kama hanyar gari.

    Da ya farka sai ya hangi matarsa na gudu, idan ya yunƙura zai tashi sai ya ji kansa a ɗaure a jikin bishiya. Ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kuɓuce amma sai abu ya gagara. Ita kuwa Kwambal tana ta sheƙa gudu ba ta tsaya ba har ta isa gida. Haka ta bar dodo ɗaure a gindin bishiyar kuka yana ta birgima. Da ba domin Gizo ba da na yi muku ƙarya. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • So amanar zuciya.
    • Sabo da maza jari.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)

    Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Kurege ya je gidan Kura ya ce su tafi farautar kayan daɗi a jeji. Kura ta amince. Suka shirya suka kama hanyar daji. Da suka isa bakin rafi sai Kura ta ce, to su rabu a nan. Ta ce tunda shi Kurege ƙarami ne ya bi cikin ciyawa, ita kuma Kura da yake babba ce, za ta bi kan hanya.

    Da fari Kurege ya ƙi yarda, amma daga baya ya haƙura, ya bi cikin ciyawa yana tafiya har ya kai ga gidan zuma, ya tarar ƙudan Zuma suna ciki. Sai ya saurare su ya ji duk sanda za su fita sukan ce: “Buɗe bus,” sai ƙofar gidan ta buɗe, su fita. Idan sun dawo sai su ce: “Rufe kif,” sai kuma ƙofar ta rufe.

    Da ya gane yadda suke yi, sai ya laɓe har ƙudan Zuma suka fita sarai. Da ya ga haka sai ya matsa kusa yace: “Buɗe bus,” sai ƙofa ta buɗe. Sai Kurege ya shiga ya kwashi zuma ya sha, ya cika jakarsa da ita, ya fito, ya dubi ƙofa ya ce: “Rufe kif,” sai ƙofa ta rufe, ya kama hanya ya dawo inda suka yi alkawari za su haɗu da Kura.

    Ita kuma Kura da ta kama hanyarta, ta rinƙa tafiya ba ta ga komai ba, ga shi ta fara jin yunwa. Can dai ta hango zawayi a malale a gindin bishiya, ta je ta kama shan zawo har ta ƙoshi. Daga nan ta ɗebi sauran zawayin nan ta zuba a jakarta, ta kama hanyar inda suka yi alƙawari za su haɗu da Kurege.

    Da ta iso sai ta tarar ashe Kurege ya riga ta dawowa. Kurege ya dubi Kura, ya ce: “Kura ga shi kin ciko jakarki da kayan daɗi, sai ki ɗan ɗebo mini abin da kika samo.” Da Kura ta ji haka sai ta ƙi, ta ce ina nasa? Sai ya ce to zai ɗan ɗebo mata, ita ma ta ɗebo masa nata, amma idan na Kurege ba daɗi, zai biya ta nata.

    Kurege ya yarda. Da Kura ta buɗe jaka sai Kurege ya fara jin warin kashi, ya dubi Kura ya ce mata ya fasa shan abin da ta zo da shi. Da ta ji haka, sai ta ce to shi ke nan, amma ya ɗan ba ta nasa. Kurege ya buɗe jakarsa ya ɗeba mata, ya ba ta. Da ta ji zaƙi sai ta jefar da jakarta ta kuma ce sai Kurege ya nuna mata inda ya samo wannan zumar.

    Kurege ya ce to su tafi ya nuna mata. Suka kama hanya, har suka je gidan Zuma, ya gaya mata yadda za ta buɗe ƙofar gidan Zuma. Nan take Kura ta je ta buɗe gidan zuma, ta fara shan zuma har ta ƙoshi, ta cika jakarta. Amma kuma sai ta manta yadda za ta buɗe ta fita, sai ta rinƙa cewa: “Rufe kif.”

    Ta dai kasa fita har Ƙudan Zuma suka dawo daga cin furanni, suka faɗa Kura da harbi, duk jikinta ya kumbura. Kurege ya gudu ya bar ta, daga baya ta koma gida duk fuskarta a kumbure. A gida aka tambaye ta me ya same ta, sai ta ce: “Ai na yi yaƙi ne da wasu namun daji, amma duk na kashe su sai dai jikina ya kumbura.”

    Da ta je gidan Kurege sai ya buya, ya ce: “A gaya mata ba na gida.” Kura ta ce: “Idan ya dawo a gaya masa in bakinsa ya yi masa ƙaiƙayi, to ya daka da dutse kafin mu haɗu,” sai ta yi tafiyarta. Da ba don Gizo ba da na yi muku ƙarya. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Natsuwa maganin kuskure.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Cin Kasuwar Sama

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Cin Kasuwar Sama

    Tatsuniyar Cin Kasuwar Sama

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Da Zanzaro da Barangunda suka ƙulla abota. Wata rana suka je cin kasuwar sararin sama, da nufin su dawo da yamma. Da suka je suka dawo sai suka tarar Gizo ya fito ya zauna ya kame a kan kujera, yana shan iska. Da man hanyar ta bi ta ƙofar gidan Gizon ne.

    Da Gizo ya gan su sai ya tashi ya yi musu maraba, suka amsa masa, har suka ba shi tsarabar kasuwa. Gizo da matarsa Koƙi suka ji daɗin tsarabar, sai Koƙi ta shawarci Gizo da ya bi su ko shi ma ya samo kayan daɗi. Gizo ya je da dare ya roƙe su, su taimake shi, su je tare.

    Zanzaro yace: “Kai Gizo al’amarinka fa da wuya, ka cika fallasa.” Gizo ya tsaya da rantse-rantse, yana cewa: “Ai na bar halin da kuka san ni da shi a da.” Da ƙyar dai suka amince, suka ce gobe ya shirya za sutafi tare. Da tsakar dare Gizo ya je wurinsu, ya nemi ya tashe su daga barci, wai asuba ta yi. Suka far masa da faɗa cewa yaya zai zo musu da tsakar dare haka?

    To idan haka zai yi musu su ba za su je tare da shi ba, domin ya fara halinsa na zumuɗi. Ya dai haƙura ya koma gida, amma ya kasa barci, ya laɓe a hanya har asuba ta yi. Sai suka ji ana kuwwa, ana cewa: “Wayyo Allah, na halaka.” Suka fito suka same shi, suka tambaye shi: “Gizo me ya faru?” Gizo yace: “Yunwa za ta halaka ni. “Sai Barangunda ta ce da shi, “Shiga hancina ka ci abinci”.

    Da ya shiga sai ya tarar da wata babbar kasuwa, ya ci abinci har ya ƙoshi. Can bayan wani ɗan lokacin sai Barangunda ta ce da Gizo: “Fita mana, ai yanzu ka ƙoshi.” Sai Gizo ya ce: “Tukuna.” Ashe har Gizo ya ɗauki ƙosai, yana talla. Can dai Barangunda ya harzuƙa, ya yi atishawa sai Gizo ya faɗo tare da faifan tallar ƙosan. Sai Barangunda ya ce masa ya koma cikin hancin ya mayar da ƙosan.

    Nan da nan Gizo ya shiga ya mayar, suka ci gaba da tafiya. Can kuma sai suka ji ihu, da aka tambayi Gizo ya ce ƙishirwa ke damun sa. Zanzaro ya ce ya shiga mararsa ya sha ruwa, ya shiga ya sha. Da ya ji sanyin wurin sai ya ƙi fitowa, ya ce sai ya yi wanka tukuna. Zanzaro kuwa bai ɓata lokaci ba, sai kawai ya matsa mararsa Gizo ya faɗo tim!

    Haka dai suka yi ta tafiya. Da suka isa bakin kasuwar sama sai suka sami wani wuri suka ajiye kayansu, suka shiga kasuwa. Da Gizo ya ga sun ɓace masa cikin kasuwa sai ya tashi ya shiga kasuwa yana tara yara, yana gaya musu, su zo zai koya musu irin wasan garinsu.

    Yara suka taru ya ce musu zai yi waƙa su kuma su amsa. Ya ƙara da cewa: “In kun ji na ce marmaron Zanzaro na sha ruwa, sai ku ce hancin Barangunda da kasuwa.

    “Sai ya fara:

    “Marmaron Zanzaro na sha ruwa,

    hancinBarangunda da kasuwa”

    Suka shiga tsakiyar kasuwa, Gizo yana ta rawa, yana tsalle. Zanzaro da Barangunda suka sami labari sai suka zo, suka saurari duk abin da Gizo yake faɗi, suka yi baƙinciki, suka rasa yadda za su yi, suka ma kasa isa wurin Gizo. Shi kuwa da ya gaji sai ya zo ya kwanta, barci ya kwashe shi. Da Zanzaro da Barangunda suka zo suka ga yana barci, sai suka ce madalla, abin nema ya samu, suka ciccire fukafukan da suka ba shi aro, suka sauƙo suka bar shi a sama.

    Da Gizo ya farƙa ya ga ba fukafukai, sai ya fita ya yi ta yawace- yawace ko zai gan su, amma bai gan su ba, ya rasa yadda zai komo gidansa, sai ya fashe da kuka. Da yaran gari suka gan shi, sai suka tambaye shi abin da ya faru, ya yi musu bayani, suka ce za su taimake shi. Suka sami doguwar igiya da ganga da abin kiɗa. Suka ɗaura wa gangar igiyar suka ce da shi ya hau saman gangar.

    Ya hau suka ba shi abin kiɗa, suka ce idan ya isa ƙasa sai ya kaɗa gangar don idan sun ji
    muryarta sun san ya isa kenan, sai su saki shi. Suka fara zura shi. Da ya zo rabi sai ya tambaye su irin muryar da gangar take da ita wadda za su ji ta daga sama. Sai ya ce bari ma ya ji muryar, sai ya kaɗa gangar da abin kiɗa.

    Da yaran suka ji muryar sai suka saki igiyar, Gizo ya surmiyo ƙasa, ya faɗi ya yi rugu-rugu. Da ƙyar aka tattara tarkacensa aka kai wa matarsa Koƙi ta shiga jinyarsa. Ya daɗe yana jinya kafin ya warke. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kowa ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu