Tag: yadda ake

  • Labari Mai Taken Fansar Hawayen Kakana

    Labari Mai Taken Fansar Hawayen Kakana

    15/5/2025. ADADIN KALMOMI:2876

    Gidan mu na gado yana tsakiyar badalar garin mu, shahararru ne a sanaʼar sarrafa fata wacce aka fi sani da dukanci. A wata sharariyar unguwa da ke zagaye da kasuwanni. Kasuwanci da kiwo shi ne alʼfaharin mu, kamar kowanne gidan bahaushe kakana malam Gambo yana da mata biyu Hauwaʼu ita ce amarya Rakiya uwar gida. Amarya ‘ƴa’ƴanta biyu duk mata, uwar gida ‘ƴa’ƴanta uku maza biyu mace ɗaya.

    Kakana shaharren badukku ne duk garin mu kowa ya san shi kuma duk wanda ya iya aikin dukanci a garin mu, gurin sa ya koya, masauratar garin na alfari da irin aikin sa, duk wani aikin fata da ake amfani da shi gidan sarauta tun daga kan takalmin sarki har kaya ƙwalliyar dawakai na fata kaka na ne da tawagarsa suke yin sa, lallai ya shahara kuma yana fidda su kunya a harkar dukanci.

    Kakanmu ya aurar da ‘ƴa’ƴansa mata ukun Lami, Hausu da Amina sai baban mu Auwalu da yayansa Sani, su ma duk da iyalan su wan babana ‘ƴa’ƴansa biyu duk mata Hadiza sai Rakiya da ta ci sunan kakarmu muna ce mata uwa, baban kuma duk maza ne Habu sunana ɗan uwana Muhammadu shi ne babba, kullum suna tare da ƙoƙarin koya mana sanar dukanci. A zauren gidan sa  yake aiwatar da aikin sa.

    Ƙwatsam!! Wata rana sai ga wata alʼumma haye kan ababan hawan su wasu dokuna, ƙurar su ta tokare sararin samaʼu, makaman su suna sheƙe da walƙiya a sama cikin duhun ƙurar da suka tayar, suna tafe cikin azama da ƙwarin gwiwa, kaɗe-kaɗe na tashi, wasu daga cikin tawagar mata da maza suna rawa cikin nishaɗi da burgewa da shaye shaye lallai wannan tawagar akwai abinda ta taka.

    Sun nufo garinmu, wasu irin mutane ne kafta-kafta masu zagayyayir fuska idanuwan su kamar an nitsawa sakwara yatsa da gajeren hanci kalar fatar su jajur kamar ƙosai, suna sanye da tufafin da aka yi da fatar dabbobi mai gashi gashi haka takalman su yake, kuma duk girman mutum rigar sa ba ta huce cibiya haka ɗankamfan da ke ƙugunsu bai huce ƙwawrun su kowannen su goyen da mashi a bayan  riƙe da garkuwa na kan doki da ƙafa adadin su yana da yawan ba zai harsasu ba.

    A kwai ƙananu garuwa da wannan tawaga ba ta bari sun kai labari, tuni sun murkushe  tare da kama bayi. Duk garin da su ka dunfara sai wani ba shi ba, domin ɗaurin butar malam duk inda suka ƙaddamarwa sukan kwashi dukiya da bayi, su afka masa wuta ba za su bar gurin ba sai sun ga kiyashi a gurin ba ya numfashi, bukkokin sun zama toka bishiyu sun zama gawayi, gonaki sun zama toka, sun tabbatar koʼina ya zama fili.

    Duk garin da suka hara basa shiga sai da dare, su ya-da zango a bayan gari su tura ‘ƴan leƙen asiri, su gane musu girman; yawan jamaʼar; ƙarfin masarautar, don sanin shirin da za su yi, duk wannan abun suna yi ne cikin ƙanƙani lokaci, salo da ƙwarewa. Inda suka hara garin mu, don babbar cibiyar kasuwancin kuma daular mulkin mu yake, duk garuruwan da sukai fatali da su a hanya gudun kar su haɗu su kawowa garin mu ɗaukin in sun kai musu hari duk salo ne na yaƙi.

    Waɗannan maharan duk da ba su san komai a kan garin mu ba, amma ba shi ne zuwan su na farko ba domin na gaya muka garin mu babban gari ne dalilai da dama suna kawo alʼummu misali: yawon buɗe ido muna da daɗaɗɗiyar alʼada ta gargajiya masu ban shaʼawa, gine-ginenmu wanda ba a koʼina ake ganin sa ba, tsarin zamantakewar mu bukukuwan alʼadu na suna da na aure, tsarin sarautarsu da ƙwarewarsu a kasuwanci.

    Wannan dalilin ya kawo waccan alʼumma garin mu dan ƙulla harkar kasuwanci mai ƙarfi tun ana harkar ban gishiri in ba ka manda. Alʼumma sun riƙe su da amana  zuciya ɗaya, duk da sun san tarihin su a gurin malam da suka addinin musulunci, mutanen mayaudara azzalima masu butulci ga Allah subhanahu  wata’ala. Wanne tudu wane gangare suka zo mana da halin su na asali suka yi ƙwanton ɓauna suka san sirri mu.

    Suka nufato mu da niyyar yaƙi,  suka shigo mu da ƙarfin tuwo domin sun san ƙarfin masarautar mu ba za ta ciyu da sauƙi ba, sun san zurfin tunani mayaƙa da ƙarfin  ƙwarewarasu a yaƙi. Abun da suka fi mu shi ne ilimin suna da makamai na zamani masu aiki da naʼura, an kai ruwa rana, an yi karan batta uwar barai da mayaƙan mu.

    Kowanne gari suka hara cikin awanni sun kai shi ƙasa, amma garinmu sai da aka yi fafatawar kwana biyu ba tsagaitawa, har sun fara sarewa duk da sun yi wa mutan gari laga-laga sun ɓarnata dukiyoyin, ba wani ragowar ƙarfi a waje mutane da yawa an kama su wasu an kashe su, wasu an raunata su ba su da kataɓus dan suna da yawa kuma suna da makaman zamani.

    Mu kuwa ba yawan jamaʼar, baƙi ne masu zuwa kasuwanci ko ci-rani tunda labarin rashin zaman lafiya fara yaɗuwa sai kowa ya ja jiki, duk da haka aka ci gaba sai da suka sa da karun suka zagaye garin. A wunin ƙarshe suka kaiwa masarautar hari cikin saʼa suka kutsa kai cikin gidan mai ɗinbin tarihi suka banƙara iya ɓanƙarawa suka kama tare da kashe manyan dakarun sarki,  wanda da su ne sarki yake jin shi sarki ne, suka yi wani salon ta ƙarƙashin ƙasa suka cimma iyalan sarki.

    Daga nan suka ci lagon yaƙi suka yi fatali da alʼadun da gadon  iyaye da masarauta da dukiyoyin. Wannan ta hura wutar gaba da ƙin jinin mayaƙa a zukata. Sun shiga da yaƙi na cin zalin da wulaƙanta sarakunan mu da zubar musu da ƙima sun karɓe mulkin da ƙarfin tsiya. Sun karɓi masaurata suka sa dakaru a gidan don  tsare sarki da iyalan sa da kuma manyan masarautar na tsahon ƙwanaki.

    Suka Afkawa lalitar gari da ma shirin su kenan. Masarautar garin duk yankin ita ce babba da ake gudanar da harkokin kasuwanci, duk wasu alʼummu garinmu ne karafkar. A haka aka cigaba da rayuwa a garin sun samar da dokoki da irin yadda suke so mulki ya gudana. Amma ba su sami yadda suke so ga talakawa sai da su ka biyo da sarakuna. Sarakuna ba su da kataɓus sai yadda suka dama haka ake sha.

    Hakan ‘ƴan mulkin mallaka suka ringa yin amfani da su domin zalinci. Sun ɗorawa talakawa haraji da jangali duk wani mai gidan ya dangata da ƙarfin samun sa, kowanne me unguwa ko mai gari zai karɓa a hannun talakawan sa, (jangali ko haraji kuɗi ne ko kadara da masu mulki kan karɓa a gurin talakawa). Kuma ba ruwan su da za ka iya ko ba za ka iya ba su dai buƙatar su ta biya.

    Za a yanka maka lokaci, ka nema idan ba ka samu ba za a kai ka gidan mai gari ko hakimi su yanke ma ka hukunci, ko ƙari kan abinda za ka biya a da, ko yari a haka  mutum ya zama bawa a kan rashin biyan haraji ko jangali. Gari ya zama ba daɗi sun kassara ƙwarjinin da tattalin arzikinsa. Wannan dalilin yasa alʼumma yin hijara daga mahaifar su zuwa ƙasashe maƙota don samun ƙwanciyar hankali, wasu dalilin su ke nan na barin garuruwan su.

    Daga nan cinikin bayi ya samu ƙafar kafuwa wanda mu ba mu san shi ba, suka ringa kama mutane su na fitar da su ƙasashen su  domin bautar da su aikin da injina ne ya kamata su yi, amma saboda zalinci, kuma duk wanda suka kama su kafitar da shi ya tafi kenan, an raba shi da iyalan sa da ‘ƴan uwansa kai uwa uba har da addininsa.

    A wannan lokacin addinin bai kama jiki da zuciya ba babu cikakken ilimin. Abu mafi muni da sa ɗacin zuciya shi ne yadda ake ɗaure mutane a matsayin bayi ko dabba aka yi wa an zalince ta, sarƙa ce za a sa a ƙafafuwansu a jera a layi a ɗora musu ƙaton icce a kafaɗunsu sannan abi kafaɗun su a zarga sarƙa ta wuyan su a ɗaure su katamau, sannan a tura su a gurin da in ka kirawo shi kabari ka yi daidai.

    Haƙiƙa alʼummar sun sha wuya a hannun azzalimai ‘ƴan mulkin mallaka sun yi wa kakkanin mu da iyayen cin zarafi da ƙetare iyakar mutunta. Wannan ta kaurara ƙin jini da ƙyamar su a zukatan alʼumma. Kaka na ya ce “Idan mu ka gano waɗannan mutanen  yayin rangandin su, mukan gudu ne don ɓuya kamar mun gano mayunwacin zaki domin ba su da imani ko tausayi in suka ga mutum lafiyayye shi kenan sun ga nama, don za su ɗauke shi a matsayin bawa, in sun yi masa da ƙauna su bar shi a tare da su ya ringayi mu su hidmar gida.

    In kuma ba haka ba su saka cikin wanda za su kai su can ƙasashen don yin aikin bauta musamman noma,”.Wannan na ɗaya daga cikin dalilin mutanen Afrika yin tsagu a fuska  in za su ɗauki bawa sai sun ga wanda ba wani lahani a wannan ɓangaren sun samu sauƙi, hakan yasa za ka ga kowacce ƙabila da irin nata tsagun na fuska. Haka suka ringa yi wa lamarin rayuwar ɗiban karan mahaukaciya, bayan sun gama kankane komai sun samu abinda ya kawosu.

    Sai suka fara tunani koyawa  mutanen mu yarensu da kuma irin ilimin su, suka daina kamen bayi, sannan suka rage zalinci da cikin zarafi. Hankula sun fara ƙwanciya an fara komawa harkoki, baƙi ma sun fara leƙowa sun samu labarin an daina tashin hankali da kamen Bayi.

    Kamar kowane mai sanaʼar hannu shi ma ya koma bakin aiki ya je kasuwa ya sisiyo duk kayan da yake buƙata a harkar dukancin sa, mun gyara ko ina ni da ɗan uwana an fito da kayan aiki kamar kullum abokan aikin sa sun hallara, mutum uku ne sai babana da ɗan uwa sa, idan an haɗa lissafin su mutun shida ke aiwatar da aikin samar da takalma da kayan fata irin su gafaƙa; bulala; kayan adon doki; kuben mashi da wuƙaƙe girma girma dai dai ɓukata.

    Soron gidan mu babbar masanaʼanta ce mai zaman kanta, baƙi na gida da na waje haka ake zuwa don siyan kayan da muke samarwa, mu aikin mu ba ya huce aike don siyo abubuwa da kuma aiken cikin gida ko taimakawa baƙi ɗaukan kayan da suka siya, ba ma nisa da gida muna kusa, kullum ta Allah abun da yake faruwa ke nan sanaʼar iyayen da kakkani mu ke nan duk a cikin ta aka haife mu  kuma aka koya mana hatta iyayen mu mata sanaʼar su kenan.

    Amma su sun fi manna kaya ƙyallin da ɗinka Rumi jikin takalmi ko kayan adon doki. Duk gari ya ɗauka ƴan mulkin mallaka za su fara koyar da jamaʼa ilimin da suka zo da shi , kakan mu “yace ilimin da ba na Allah ba!, Allah kar ka nuna min wannan rana lallai da wannan rana gara mutuwa ta, mai za a yi da ilimin taurin kai da bujirewa Allah”.

    Wata rana bayan sallar asuba a masallaci, dama a nan mai unguwa kan sanar da mutane saƙo, haka yau bayan shafa adduʼa mai unguwa ya tashi don isar da saƙon yace “Bayan sallama irin ta addinin musulunci, a jiya mun yi taro da sarakuna da hakimai sun ba mu saƙo zuwa gare ku, sun ce a gaishe ku kuma a sanar da ku shirye-shiryen ya kankama kan fara koyar da yaran mu da manyan ilimin ‘ƴan mulkin mallaka.

    Kuma dole ne a kan kowanne yaro da yake faɗin garin nan kuma sun ce in kunne ya ji, jiki ya tsira, ya ɗora da cewa tuni aka fara sa ‘ƴa’ƴan masu mulkin gargaji, awo na gaba ‘ƴa’ƴan talakawa za a ɗora, “cikin ɗan lokaci masallaci ya ɗau hayaniya masu aʼuziyya suna yi tare da neman ɗaukin Allah, domin babban balaʼi ya dumfaro ba mai iya masa sai Allah haka kowa ya ja jiki zuwa gida ba kuzari.

    Hantsi na ɗagawa duk mun fito gurin sanaʼa kowa ya fara aikin sa kamar kullum, tuni baƙin sun fara zuwa siyan kayayyaki, sai ga saƙo daga fada cewa sarki yana umartar kakana da ya ba da sunayen mu ni da ɗan uwana ƙarshen wata za a kai mu makaranta, da jin wannan saƙo kaka na yana zaune sai ya miƙe sai kuma ya tuna saƙon daga inda yake sai ya zauna cikin tashin hankali ya amsa da to kuma ya ce “a cewa sarki godiya yake”

    Ko da ‘ƴan saƙo suka tafi kakana buta ya ɗauka ya zagaya bayi, can ya dawo bai iya cewa kowa komai ba sai um sai um um haka wunin ranar kowa na zauren nan rai ba dadi, lokacin tashi kowa ya kama gabansa, a ƙaʼidar sa ba ya shiga gida sai ya yi sallar isha amma a ranar gida ya shiga don yana ta zaryar banɗaki. Ta ɓangare na ni abun ya yi min daɗi domin na harsaso sauyin rayuwa a tare da wannan ilimin da za a kai mu muddin ka yi amfani da shi yadda ya dace, na tabbarwa raina sai na yi ko da kuwa ba ya so, na saƙa hakan.

    Kowa ya ga kakan mu ya san yana cikin tashin hankali ko mai da zancen ake yakan ce yau na ga ranar haihuwar ‘ƴa’ƴa mata, ga ‘ƴa’ƴan Auwalu suna ɗakinsu na godewa Allah amma ‘ƴa’ƴan Sani, za su ja min magana kai tur!!! da wannan ranar takaici, haka dai muka ci gaba da murginawa da daɗi ba daɗi har Allah ya kawo mu ƙarshen wata, saura ƙwana ki biyu tafiyar mu aka ƙara turowa kakana cewa ya shirya mu jibi za a zo a tafi da mu.

    Tashin hankalin kakana ya ƙara taʼazzara, nan ya ƙara surar buta yay bayi wannan karan bai fito zaure ba cikin gida ya shiga ya sanarwa da iyayen mu mata, a ƙwana a tashi rana ta zo sai ga ɗan saƙo daga fada a tafi da mu, kakana tun yana daurewa sai da ƙwalla ta fito masa cikin hanzari yay cikin gida haka muka bi bayan sa, ni cikin zumuɗi na haɗo kayana amma muhammadu lamarinsa ba yabo ba fallasa.

    Aka tisa ƙeyar mu sai makaranta. Bayan tafiyar mu aka ba mu labari ranar ba a yi aikin dukanci ba kakana ya ƙule cikin gida ba wanda yake zuwa inda yake, haka rana ta biyu ma ba a yi aikin ba amma a wannan ranar tabarma aka fito da ita waje kakanmu ya lallaɓa ya fito aka yi ta yi masa jaje, duk wanda yace Alhaji Gambo ashe abun da ya faru kenan, ya  ce” ee haka ƙaddara ta samu amma Allah ka gani ba a son raina ba Allah kar ka kama ni da wannan laifin”

    Sai ya fashe da kuka, haka ya dinga kuka kamar ɗan yaye kusan ƙwana uku aka jera kakan mu yana karɓar jaje. A hankali aiki ya dawo daidai amma dai ya rage walwala kullum yana neman gafarar Allah. Ko hutu muka zo kaka ya dinga ja mana kunne mu kula da abinda ake koya mana gudun kar a koya mana kafurci, yace ku kula da sallah.

    A haka muka yi ƙarama da babbar makaranta matakai uku nan haka muka yi matakin farko da na biyu shekara shida shida matakin ƙarshe ne muka yi shekara huɗu kuma duk hukuma ce ta ɗau nauyin karatun mu. Wani hutu da muka dawo wanda shi ne in mun koma za mu yi jarabawar fita, muka zo muka tarar da kakanmu cikin jinya rai a hannun Allah, a wannan jinyar Allah yay masa rasuwa mun ji baƙin cikin rashin sa domin mutum ne jajurtacce a lamarin iyalin sa, bayan share makoki muka koma makaranta iyayen mu suka ci gaba da jan ragamar masanaʼantar mu ta dukanci.

    Alhamdulillah yau na zama cikakken maʼaikaci ƙarƙashin hukumar kula da lafiyar alʼumma bai ɗaya a matsayin likita, bayan gwagwarmayar makaranta ni da ɗan uwa na muhammadu inda shi kuma ya zama babban ɗan jarida a garin mu. Rayuwar mu ta yi kyau. Allah ba ya barin wani don wani, na so yau a ce kakanmu yana raye duk dangi suna alfahari da ba mu bauɗe a kan tafarki madaidaici da kaka yake tsoro ba, lallai Allah ya karbi adduʼar sa.

    Masu mulkin mallaka sun bar mana gari sun danƙa ragamar komai a hannu ‘ƴan gari, Amma ba su tafi ba sai da suka ga ilimin su ya karɓu a garin mu har ana tafiyar da harkokin ci gaba na rayuwa, kuma suna ci gaba da karɓar jangali da haraji a hannun shuganinmu kuma harkar mulkin har yanzu su ke gudanar da ita a fakaice, masu mulkin gargajiya na jagorantar wani ɓangaren.

    Na ci alwashin bunƙasa masanaʼantar kaka na ta zama ta zamani, a santa ko ina a duniya, na ci alwashi gina gidansa da irin ginin zamani duk da ba ya raye iyalansa sa mora. Na ci alwashin hawayen kakana ba zai tafi a banza ba, lallai karatuna gaba ɗaya fansar hawayen kaka na ne.

    Karanta Labari Mai Taken Wata Sabuwa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Labari Mai Taken Wata Sabuwa

    Labari Mai Taken Wata Sabuwa

    Taƙaitaccen labari ne duba da yanayin rayuwa da ake ciki don yin hannunka mai sanda ga alʼumma daga taskar uwar muminai💐💐💐💐. 07033941914.

    Yau ma kamar kullum na tashi raina a cunkushe kallon kowa nake kamar maƙiyi, nai ƙoƙari na jawo hisnulmuslim don yin azkar ɗin safiya. Duk halin da nake ciki ba ya hana ni yi, na gama na jawo wayata misalin 6am akwai Online classes na islamiya da nake bi duk safiya ina buɗe data telegram na shiga, inda na lalubo ajin da nake bi haka nan nake jin rai duk a ɓace cikin saʼa na samu Malam ya fara, na ci gaba da sauraro ina jotting some important points.

    Haka yanai min daɗi nakan ji sauƙi raɗaɗi da yake damuna wanda ban san ta inda ya samu ba, ban san dalilin da yasa na tsinci kaina ciki ba, na furza huci mai zafi daga baki na. 6:30am na bugawa na tashi yara don shirin makaranta ba na iya fita don taya su shiri kowa tasa ta fisshe shi kowa yay sabgar sa. Yarana biyar biyun farko mata ne babbar ita ce ‘ƴar shekara sha biyar me bi mata sha uku sai ƙannansu maza da ɗan shekara goma da takwas autan  kuwa shekara shidda yake.

    Gida ya kacame ‘ƴan matan ɗaya na gyara gida ɗayar na shirya musu abun kari su kuwa ‘ƴan mazan ba abun da suke sai dambe da ƙiriniya ni kuwa ko a jikina an tsikari kakkausa, Abbansu ne ya dawo daga masallaci ya same ni ɗaki yace kina jin yaran nan ba za ki musu magana ba? Ko ɗaga kai ban yi ba, domin ni yanzu ba na so yana shiga harka ta, cikin ɗaga murya yace ko ba ki ji ba, nai masa kallon hadirin kaji tare da figar wayata na bar ɗakin.

    A raina nace kan ka ake ji tun da na shiga wannan halin na fita harkar kowa, Kawai abun da na Sani Wani ɓangare na zuciyata Yana gaya min “ba ke ba ce ba halimatun nan mai ƙwazo da kazar kazar mai kula da komai da kowa, ni kai na ya shiga duhu na kasa gane komai kawai ina cikin ruɗani da taraddadi cikin raina.  Ina da haƙuri da kai zuciya nesa amma in aka ɓata min, ina da riƙo da sauƙin mantawa.

    Saboda haka yanzu ta shafi kowa ba na so kowa ya raɓo ni ko yara suka yi min abin da bai kai ya kawo ba za su sha duka. Kawai abun da na Sani yanzu na zama ba ni da haƙuri ga saurin harziƙa ba na ganin kowa da gemu kana yi min zan rama har in wuce makaɗi da rawa wanda hakan ba ɗabiʼa ta ba ce. Ba ni da abokin hira sai waya, wani lokaci ba wani abun kirki sai ɓata lokaci ban jin daɗin hira da kowa.

    Cikin ikon Allah ban faɗa hannun yan sharholiyar social media ba ina yawo na daga wannan class Sai wanna kuma duk Qur’an ake koyarwa ko abin da ya shafi addini amma wannan ƙunci ya hana ni kataɓus da zaizayar ruhi kullum fuskata kamar na kurɓi maɗaci, idan na ji sallamar Abban su sai in ji kamar an watsa min ruwan zafi, idan ina tsakar gida zan shiga ɗaki kafin ya zo na kwanta in kuwa ina ɗakin ne zan kwanta in rufe ido ni mai bacci, duk halin da nake ciki bai taɓa tambayata ko lafiya?

    Babban ɗan I don’t care ne Idan yana da abin faɗa ya faɗa in na ga dama na amsa wani lokacin ko ci kanka ba zan ce ba in ɗago in kalle shi ma zan ji kamar ana caka min wuka a ƙahon zuciya. Na kai sati cikin wannan hali na uƙubar rai da ruhi kawai abin da na sani bayan karatuna na online to in nai addu’a nakan ji sauƙi saboda haka ba na wasa da addu’a da roƙon Allah ya ba ni yarda da abinda ya ƙadarta mini kuma ya sa min albarka a cikin sa.

    Duk wannan halin da nake ciki gidan mu ba wanda ya sani, Ni yanzu wani abu da ke  damu na ma kawai sai in ji kamar ana ihu a maƙota cikin kiɗima da razana zan leƙo tsakar gida sai in ga kowa yana harkar sa kuma wani ɓangaren zuciya yana gayamin,  in kika koma ɗakin nan kama ki za a yi haka zan ta yi, zuciya ta cika da tsoro na rasa inda zan sa kaina ban yarda da kowa ba adduʼar ma yanzu so take ta gagare ni, da na fara sai in ji kamar an ƙwalla ihu, haka dai duk halin ko in kula na megida na ya fara karɓo turaren miyagu da na jinnu, wani lokacin har da rubutu amma kullum abu ƙaruwa yake don har na haƙura da zuwa aiki .

    Cikin dare misalin ƙarfe 3:30 ko makamancin haka kamar an tashe ina bacci, cikin firgici da razana wani tsoro ya kama ni ba dalili, na ji jikina na rawa domin wata ƙara na ji kamar aradu ban san sada na fara faɗin innalillahi waʼinnan ilaihirrajin cikin rawar muryaba, ji nake kamar ana wujijjiga ni tare da jin rugugin muryoyin mutane a ciki, na kasa gane komai, amma kamar an jefa ni cikin durum ban fasa kiran sunan Allah da neman agajinsa ba.

    Cikin ikon Allah na ji na fara dawowa hayyaci na jiki na dai na rawa zuciya ta cike da tsoro  na tashi na yo alwala daman ɗabiʼata ce na tada sallah sai a lokacin na ji idona ya ƙwararo ruwan hawaye, na gagara karanta komai ina tsaye zuciya tana ba ni tabbacin a nan ne maganin matsalar take tsahon lokaci ina tsaye can na fara karatu a hankali wata irin nutsuwa ta fara ɗiga cikin ruhina, na cigaba da sallah rakaʼa huɗu na gabatar  ɗaga hannu nai zuwa sama, nai godiya ga Allah tare da salati Manzon Allah sannan na fara kai kukana ga Allah nace, “ya Allah ba ni da kowa ba ni da komai ba ni da wayo ba ni da dabara.

    Allah kai kaɗai nake bautawa kuma kai kaɗai nake neman taimako, Allah ina cikin wani hali ban san shi ba, ya Allah ban san dalilin sa ba,  Allah ka kawo min ɗauki da agaji ka sauƙaƙa min ya Allah ka amintar da ni da abun da yake ba ni tsoro ka kawo min mafita, ya Allah” na rufe adduʼa ta da salatin Annabi, na miƙe na cika da wutri ina zaune ina jan istigfari kawai shawarar in ɗau azumi ta faɗo min nai niyya da sahur na jira fitowar Afiji dan sauke faralli.

    Alhamdulilla wunin ranar rai na sakayau  lokacin buɗe baki da adduʼoʼi na neman ɗauki daga Allah bayan na idar da sallar ishaʼi na ji kamar an fito da ni daga cikin buhu mai duhun da aka yi wa ɗaurin huhun goro iska ta koʼina na ratsa ni, raina yay fari kamar audiga na cigaba da jan carbi ina kai gaisuwata ga farin jakada Annabi ɗan gatan Allah a haka har bacci yay awon gaba da ni.

    Cikin farin ciki na wayi gari da ƙwarin gwiwa na ji ya kamata yau in yi wa ɗakina kwalema na daɗe ban yi shara ba kowani abu gyaran gwado ina miƙewa zanin gado da net na cire sai wanki sannan na dawo ɗaki na fara ɗaga saƙo da loko, in sakato shara yara suna taya ni, cikin ɗan lokaci komai ya koma hayyacinsa, wanda hakan ya yi daidai da lokacin walaha. Na shiga bayi nai wanka nan ɗauro alwala cikin  nishaɗi na gabatar da sallah na jawo wayata don lalubo ko cikin class ɗin da nake bi online zan samu masu gabatar da karatu.

    Na ci saʼa kuwa suna karatu nai joining layi na ya zo ni ma na karatu shafi guda cikin suratul hashar, ustaza tai min gyara inda na kasa aka gama karatu na ɗau carbi nai salatin Annabi dan ni shi ne madogarata. Na ɗora da adduʼoʼin godewa Allah tare da yin alƙawarin gyara alaƙa ta tsakani da mijina da ‘ƴa’ƴa da sauran alʼumma kai lokacin da na shiga wannan halin har kaina na zalinta, dan ina jin yunwa in ƙi cin abinci ko in ƙi gyaran jiki ko gyaran muhalli.

    Ni da yara ba walwala bare kuma mai gidana da nake masa kallon kanwa uwar gami. A hankali abubuwa sun dawo min na dawo cikin hayyacina na ƙara yarda Adduʼa takobin mumini ce tare da yarda da abin da Allah ya rubuta maka a rayuwa Bahaushe yace kowanne icce akwai bakin hayaƙin sa, in ka yarda da hakan ka zauna lafiya a wannan Rayuwa…….

    Danna nan don karantaLabari Mai Taken Ayar Allah

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Addu’ar Nema Wa ‘Ya’ya Tsari

    Yadda Ake Addu’ar Nema Wa ‘Ya’ya Tsari

    Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hasan da Husain tsari da wannan addu’ar:

    أُﻋ ِ ﯿﺬﱠِﺑِﻜَﻠِﻤَﺎتِﷲﻟﺘﱠﺎﻣﱠﺔﻣِﻦ ْﻛُﻞ ﺷَﯿْﻄَﺎن ٍﱢﱠو َھَﺎﻣﱠﺔٍ ِو َ ﻣِﻦ ْﻛُﻞ ﻋَﯿْﻦ ٍ ﻻَﻣﱠﺔٍ ُ

    Uʿīzu bikalimātillāhi t-tāmmati, min kulli shayṭānin wa hāmmah, wa min kulli ʿaynin lām.

    Ina neman muku tsari da Kalmomin Allah Cikakku daga dukkan Shaidan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa.

    Danna nan don karanta Yadda Ake Addu’ar Barka Ga Wanda Aka Yi Wa Haihuwa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Gizo Da Matarsa Ƙoƙi

    Tatsuniyar Gizo Da Matarsa Ƙoƙi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Koƙi matar Gizo ta fito fili ta matsa masa a kan zancen gona da amfanin yin noma. Gizo ya yi fushi, amma duk da haka ya je kasuwa ya auno tiya biyu ta irin gujiya ta shukawa. Da damina ta faɗi aka yi isasshen ruwa, sai ya ce da Koƙi ta je ta soya irin. Ta so ta yi masa musu, amma sai ta kanne, watau ta danne zuciyarta, ta je ta soya da gishiri
    kaɗan.

    Kamar da gaske, tun da asubar fari Gizo ya ɗauki sunguminsa da goransa cike da fura, sai gona. Yana isa gona sai ya je ya sami itaciya babba, mai cikakkiyar inuwa sansanya, ya zauna, ya buɗe burgamin irin gujiya da aka soya masa, ya dumbuzo, ya sa abinsa a gaba ya ci har ya yi nak.

    Sai ya ɗauki goran fura ya kaɗa, ya kwankwaɗi abinsa, ya yi gyatsa, ya yi rigingine, sai barci. Yana ta sharar barci har la’asar sakaliya ta yi. Da ya farka daga barcinsa, sai ya je kogi ya yi wanka, ya koma gida. Haka ya yi ta yi har gujiyata ƙare, matar tana ta yi masa sannu da aiki.

    Da kaka ta yi, kowa ya fara kai amfanin gona gida, amma Gizo bai kawo ko da ƙwaya ɗaya ba, sai matar ta tambaye shi zancen amfanin gona. Sai ya fara zuwa gonar Sarki yana ta labto gyaɗa yana kawowa gida suna ta tsinke ’ya’yan shi da matarsa Koƙi. Kowa a gari ana ta yin mamakin amfanin gonar da ya samu.

    Ana nan, sai rannan Sarki ya hau ya je gonarsa gewaya, amma sai ya ga gona kusan ba komai a cikinta. Da ya tambayi bayin da ke kula da gonar da maƙwabtansa na gona wane ne ya farɗe masa gyaɗa, sai suka ce ba su ga kowa ba. Sai ya nemi shawararsu a kan yadda za a gane mai ɗibar amfanin gonar Sarki ba izininsa.

    Kowa ya kawo shawara da dabararsa, amma Sarki ya ga duk ba wadda ta dace. Sai ya kawo tasa dabarar, suka amsa. Shawarar kuwa ita ce, ya sa aka tara ɗanƙo mai yawa, kuma aka yi masa mutum-mutumi irin ta kyakkyawar budurwa, kamar ka ce tashi mu tafi. Aka je aka sa mutum-mutumin nan a tsakiyar gona. Da safe Gizo ya je gona kamar yadda ya saba, ya ɗebi gyaɗa, ya tsaya yana gyaran gammo, can sai ya hangi mutum-mutumin.

    Sai ya jefar da gammo ya je wurinta, ya ga budurwa tana yin murmushi, zato yake tana yi masa ne. Cikin murmushi ya matsa kusa da ita ya yi mata magana, ba ta kula ba. Gizo dai sai ya ga kamar araha ta samu, sai ya matsa ya kai hannu ya taɓa mamanta. Nan take hannunsa ya maƙale, ya kai mari da na hagun, sai shi ma ya maƙale.

    Ya kai shuri da ƙafa, ita ma ta maƙale, ya rungume ta da ƙirji ya maƙale, suka faɗi rigingine ba damar tashi, ga shi ba a fara zafi ba, balle ɗanƙo ya narke. Can sai ga Biri ya iso, sai ya ce: “Yaya ne Gizo?” To, ga shi nan dai, Biri ya ga halin da Gizo yake ciki, tarko ya kama shi sai ya ce: “Tsiyarka Gizo, na san halinka in an yi maka rana, sai ka yi wa mutum dare.”

    Gizo ya yi ’yan rantse-rantsensa na ba zai cuci Biri ba, sai Biri ya kuɓutar da shi ya ɓalle shi amma shi ya manna kansa a jikin budurwar ɗanƙo. Da Gizo ya sami kansa sai gidan Sarki, ya durƙusa yace da shi, “Ranka ya daɗe, na kama maka ɓarawo”. Aka je aka kama Biri. Shi
    kuma ya yi ya yi, ya faɗi yadda aka yi, amma ina, an hana shi damar yin magana.

    Amma da yake Allah yana bayan mai gaskiya, sai wani Zagodo ya zo ya gaya wa Sarki yadda aka yi domin a gaban idonsa aka yi komai. Sarki ya ce Zagodo ya je ya kira Gizo. Zagodo ya je gidan Gizo ya tarar yana cin abinci, sai ya yi masa tayi, ya zauna kuma sai da ya yi ƙat, aka ƙara masa har ba ya iya magana. Gizo ya yi masa magana, sai kaɗa kai kurum yake iyayi.

    Da Gizo ya tabbatar ba ya iya magana sai ya ce su tafi wajen Sarkin. Da suka isa, sai Sarki ya ce wa Zagodo, ya faɗi maganarsa. Zagodo ya kasa magana, sai kaɗa kai yake yi kurum. Sarki ya yi fushi ya sa a je a yanka Zagodo da Biri. Gizo kuwa ya ci bulus, sai kawai ya yi ban kwana da Sarki, ya koma gidansa, inda shi da matarsa Koƙi suka yi ta amfani da gyaɗarsu. Duniya ke nan. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Duk wanda ya daka ta Gizo sai ya kwan ciki.
    • Illar yin katsalandan ga abin da bai shafi mutum ba.
    • Ƙarancin bincike kan jawo rashin adalci a shari’a.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Zomo Da Damo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Addu’ar Barka Ga Wanda Aka Yi Wa Haihuwa

    Yadda Ake Addu’ar Barka Ga Wanda Aka Yi Wa Haihuwa

    و َ ﺷَﻜَﺮ ْ ت َ ﻟَﻚ َ ،اﻟْﻤَﻮ ْ ھُﻮبِ ﻓِﻲﻟَﻚ َ ﷲَُ ﺑَﺎر َ ك َ.ﺑِﺮ َ هُ و َ رُزِﻗْﺖ َ ،أَﺷُﺪﱠهُ و َ ﺑَﻠَﻎَ ،اﻟْﻮ َ اھِﺐ َ

    Washakarat laka,al-mawhubi fīka,laka Allahu bāraka,bihī wa ruziqta,ashuddahu wa balagha, al-wāhibu.

    Allah ya yi albarka ga abin da aka azurta ka da shi, kuma Ya sa ka godewa Wanda ya ba ka
    (shi), kuma Ya sa shi ya rayu har zuwa ga matukar karfinsa, kuma a azurta ka da biyayyarsa.

    Karanta Yadda Ake Addu’ar Gamuwa Da Abokan Gaba Ko Wani Mai Iko 

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Zomo Da Damo

    Tatsuniyar Zomo Da Damo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Zomo da Damo suka yi abota, kowa na zuwa gidan abokinsa ya yini ko su yi hira. Rannan Zomo ya je gidan Damo ya tarar yana cin doya, suka ci tare suka ƙoshi. Bayan ‘yan kwanaki sai Zomo ya shirya tasa doyar, ya sa matarsa ta shirya manya-manyan, ya kira Damo cin doya.

    Damo ya zo ya ga irin doyar Zomo manya ba ƙanana, ga kuma gari. Da suka gama cin doyar, sai Damo ya tambayi Zomo yadda ya yi doyarsa ta zama manya haka? Zomo ya ce idan lokacin shuka ya yi, ya zo zai gaya masa yadda zai yi. Da lokacin shukar ya yi, sai Zomo ya gaya wa Damo ya kawo irin doyar da zai shuka gidansa duka, kada ya bar ko daya.

    Kuma ya tabbatar an dafa doyar duka, kuma ya ɗauki babba daga ciki ya ci. Kada ya ba kowa sai ya je ya shuka. Damo ya yi yadda Zomo ya shawarce shi. Da kaka ta yi kowa yana kawo doya gida, amma Damo in ya je ya haƙa sai ƙasa. Ya rasa yadda zai yi da ƙyar ya nemo musu abincin da zai kai su shekara shi da matarsa.

    Damo ya rantse sai ya sha fansar abin da Zomo ya yi masa. Sai ya shirya da uwarsa cewa zai haƙa ƙabari ya sa uwar a ciki kamar ta mutu, kuma za a binne ta, a bar ‘yar ƙofa inda za ta rinƙa miƙa wa ɗanta Damo kayan daɗi irin na lahira. Aka shirya kaf, bayan kamar sati biyu, sai Damo ya je ya gaya wa Zomo yau gyatumarsa za ta kawo masa kayan daɗi daga lahira, saboda haka yana gayyatar sa domin a yi komai tare da shi.

    Suka zo wajen ƙabarin uwar Damo, sai ya ce: “Iya ina soki aiko mini babbar riga mai aska takwas da rawani ɗan Kura da dara mai tunta da takalmi ɗan Zariya don za mu biki.” Sai ga dukkan kayan da ya ambata sun fito. Zomo ya yi ta al’ajabi, ya tambayi Damo yaya ake irin wannan abu.

    Sai Damo yace da shi, ai da man duk wanda uwarsa take lahira za ta riƙa aiko masa duk irin abin da ya nema. Da Zomo ya ji haka, sai ya fara tunani shi ma me yake jira tunda ga tasa uwar ta tsufa, ba ta yin amfanin komai a nan duniya, gara ta je ta dinga aiko masa da duk abubuwan da yake so daga lahira.

    Tun a hanyar komowa gida ya sami kulkin da zai kashe uwarsa. Da Zomo ya je gida ba ko sallama sai kawai ya sami uwarsa ya dinga kwaɗa mata kulkin nan. Nan take ta faɗi ta mutu. Yasa aka yi jana’iza. Bayan an yi bakwai sai ya aika wa Damo ya zo su je wurin gyatumarsa domin ya ga abin da za ta aiko masa daga lahira. Damo ya zo suka je wajen ƙabari.

    Zomo ya ce: “Mama, ina so ki aiko mini riguna shuɗiya da fara masu aska shida-shida.” Shiru ba wani abu da ya fito daga ƙabari. Sai Damo ya dubi Zomo ya ce, “In ba hauka ba, wa ya taɓa gani an mutu an dawo?” Ya ƙara da cewa: “Ka manta da abin da ka sa na yi da doyata? “To a cikinsu wa ya fi ƙwaruwa? Zomo ko Damo?
    Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    * Ramuwar gayya, ta fi gayya ciwo

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Wata Mata Mai ’Ya’ya Biyu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Labari Mai Taken Ayar Allah

    Labari Mai Taken Ayar Allah

    Shara nake a babban tsakar gidan mu. Mijina ne ƙarami aikina kenan safe da yamma, ban aune ba na tsinkayi Uwani a gabana tsaye wanda ya yi daidai da watsa sharar kan ƙafar ta, kamar me jiran ƙaɗan ta kuwa haske fuskata da wawan mari kwanyar kai na tai wuuuuu kamar katantanwa kafin na ankara ta ƙara ɗora min wani a ɗaya kunnen take nai ƙasa wanwar faɗuwar ‘ƴan bori da ba dan ina jiyo hayaniya ba sai in ce suma na yi, can cikin iskar da take guguwa a samaniya na jiyo muryarta tana cewa ” Idan  gidan ku ba a koya miki saurarawa manya zan koya miki”

    Gidan mu uku ne facaloli amma ko tari ba wacce ta yi, na fi minti biyar ina ji kamar ana yin sukuwar dawakai a ka. Haka ya faɗo ɗaki kamar wanda aka wurgo yana zare ido,  jiki na ya yi nauyi kamar dutse saboda ɗazu na maru ban iya ɗago kai na dube shi ba, bai ko damu da halin da nake ciki ba cikin gadara ya ke magana “shi fa matsiyaci ko an sa shi a tandun mai haka zai fito ƙandas, ya ja tsaki,  rai na ya dugunzuma amma na haɗiye.

    A rai na ce wannan cin zarafi ya ishe ni ba ya ganin kima ta ko ƙis! ballanta na facaloli na, gaskiya da sake an ba wa me kaza kai,  na yunƙura cikin ƙarfin hali da sanyi murya na ce kai na ke ciwo ko ido in na buɗe jiri nake ji ya taɓe baki ya ce “damuwar ki” sai na ji kamar an watsa min wuta a zuciya na nemi jirin na rasa nai masa duban hadirin kaji “nace anya Haruna ƙirjinka da zuciya? Anya akwai sofanen tausayi na a ranka? Shin har rashin darajar tawa a gunka ya kai haka?

    Ko ba komai ni ce uwar ‘ƴa’ƴan ka! Idan ba ka buƙata ta ka sawwaƙe min” kamar wani fusataccen kure ya taso kaina yana huci, na san halin sa dukan mace a gun sa shan ruwa ya fi shi wuya kamar walƙiya cikin zafi nama nai waje a miliyan, na faɗa wanda ka yi da ya isa amma yanzu ɗan ba ƙara.

    Rayuwar ba daɗi Rana zafi inuwa ƙuna, tsugune nake a gaban malallauta ina wanke-wanke ina ta saƙa da warwa cikin zuciya ta ba zan yarda in zama karkataciyar kukar kowa ba ni da ‘ƴa’ƴana mun zama kamar mujiya, kawai!!! Na ji an watso min ruwan datti,  a fusace na ɗago muka yi ido huɗu da Rakiya ɗaya daga cikin faccalata nai saroro da son fahimtar tana sane ne ko kuskure ne sai na hango rainin wayo a ƙwayar idon ta  lallai gidan nan suna son warware min zaren tunani na, lallai yau an kai haƙurina ƙarshe cikin himma na taso don rama abinda tai min.

    Amma wani ƙululun takaici ya tokare min maƙoshi na kamar an tusa min dusa nai ƙoƙarin yin magana ruwan hawaye ya riga yin awan gaba take fuskata tai sharkaf kamar an kunna famfo  don  gudun kar in kurma ihu gaban mutane na toshe baki  na shige ɗaki da sauri . Duk wani aikin tsakar gida a ɗaki nake yi, ko banɗaki za ni sai na faki ido a tsakar gida, duk facalolina sun haɗe min kai ban taka musu ba bare in zubar ba wacce muke shiri da ita a tunaninsu ni ‘ƴa boko ce kar in raina su,” ƙaramin sani ƙuƙumi”.

    Ba mai shiga sabga ta haka tasa ni yin leƙe ƙofar gida, cikin saʼa muka yi kacibus da megidana shi ma ya kawo kai ya ja da baya cikin shan mamaki kamar ya ga miciji yace ashe in na fita ke ma fitowa ki ke yi?   Inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kamar ya ari baki Ni dai da na ga ya gagara fahimta sai nayo cikin gida nan fa Uwani ta ara ta yafa me neman kuka an jefe shi da kashi tumakai ai kai yau kagani amma ta saba haka take cika ɗaki da samari sai dai ka jiyo shewa, daga ɗaki na ke jiyo ta nasan ƙarshen zance,  amma  kunci Amna kuma zan ɗau mataki kawai yace.

    Wannan karon sun zo min da makircin da na kasa fita, misalin ƙarfe takwas bayan idar da sallar isha na ji shigowar sa kamar kullum ba  sallama  gurin abincin sa ya nufa na ji ya ɓude ya fara ci kawai sai na ji ya danna wata Ashar tare da ƙwalla kiran sunana  cikin ƙaraji kamar saukar Aradu bai saurara ba ya ɗora”  ban yi zaton har kina tunani kashe ni ba munafuka fito nan, ƙirjina yay  tass!!!

    Wani gumi ya yanko min kamar an fisan ruwan zafi jikina ya hau bari kamar mazari ƙafafuwa sun kasa ɗauka ta na ja jiki zuwa inda yake muka yi arba ya ƙara zaburowa tuni jikina ya daskare saboda tsoro ya shaƙo ni idona ya fito jawur kamar an taka ƙwaɗo a ka yace “yau sai kin gayan dalilin da yasa ki ke so ki kashe ni, guba a abinci?  Bokon naki har ya kai haka?  Zaman ki ya ƙare a gidan nan,  daga wannan ban ƙara sanin  komai ba ko suma na yi oho?

    Buɗe ido na yi na ga jamaʼa cikin ɗaki sun zagaye ni ƙwalla ce ko gumi ne ya  jiƙe ni sharɓan ban sani ba. Wasu na sannu wasu na za ta aikata, mai ya faru? Dole in bar gidan nan kafin a ɗau gawata ba na iya gane fuskokin su don jiri ne ke ɗauka ta amma da yawa suna tofin Allah tsine wai na yi yunƙurin kashe mijina. Shurun da na ji ya ban damar yunƙurawa domin tabbatar da abun da yace, Ni Hajara ta ina na samu guba?  Loma ɗaya na sa a baki na na ji kamar an kunna min wuta na kasa juya abincin haka tasa na furzo shi waje.

    Ɗanɗanon darbejiya da uban gishiri ne ya kaure bakin kamar an mare ni ta waje cikin kuma kamar ana  datsa min harshe, na nace na shiga uku!!! Waɗannan bayin Allah yau ta nan suka biyo,  ba ni da mafita gurin alʼumma, ‘ƴa’ƴa sun samu tabo me muni uwar su ta yi nufin kashe uban su. Ban san lokaci da na kurma ihun mai ratsa zuciya na rasa ta ina zan sa kaina.

    Yau ba ni da mafuta ba mai goyan bayana daman ba na tunani samun furucin da zai ƙwantar min da rai cikin mutanen da suke tare da ni, abu ɗaya da na sani shi ne ba zan yafewa wanda ya aikata min wannan ba, cikin duhun dare tafiyar ƙafa me nisa na ɗau ‘ƴa’ƴa na muka bar gari don tsira da mutunci.

    Sunana Hajara Isah ‘ƴa ɗaya gun iyaye na babana babban malami addini ne a ƙauyen mu yana da buri in yi karatu boko duk da mutanen mu suna ƙyamar karatun musamman ga mata amma malam yakan ce” Ilimi gishirin rayuwa idan mutum ba shi da shi komai ɗaci yake masa”. Hawayen da ba na farin ciki ba ne ya zo lokacin da na karɓi takardar kammala firamare na domin mutuwa ta yi awon gaba da malam.

    Sitiyarin rayuwata ya koma gurin kawuna shi kuma ya ce “Karatu gadon maza ne ita mace a gida aka santa” hakan tasa aka aurar da ni a ƙanana shekaru ga Haruna ɗan abokin sa. Na shiga gidan aure ban shirya ba na samu rayuwar gidan mai cike da duhu da ruɗani. Allah ya azurta ni da yara biyu Isa mai sunan malam da Aminatu yau Aure na ya ƙare na nufi garin da a kan ‘ƴa ta ƙi zaman aure gara a kawo musu gawar ta, tsugune ba ta ƙare min ba Ni Hajjo.

    Na fahimci za muyi mutuwar kasko ni da ‘ƴa’ƴana dangina sun juyan baya na ƙi zaman aure hakan tasa na yunƙura dan tallafar rayuwar mu, gidan masu kuɗin garin mu nake aikatau ko mai ya samu yi nake  har ɗinki hula, na lashi takobin ‘ƴa’ƴana sai sun samu ingantaciyar rayuwa.

    Alhamdulillah ban so jiki na ba ina samun abun tasarifin Rayuwa, na sa yara na makarantar boko da ta islamiya ni ma na samu damar komawa yaƙi da jahilci. Lokaci ya shuɗe na kuma fuskanci ƙalubalen rayuwa wasu na ka-da su wasu sun kayar ni, yanzu takardar N C E  ce da ni kuma ina koyarwa a makarantar ‘ƴan mata ta ƙauyen mu, ina ba su ƙwarin gwiwa a kan su yi karatu ƙalubalen rayuwa ba ya hana cikar buri sai dai in ba manufa. A ko ina ilimi haske ne duhu ba zai hana shi haskawa ba.

    Wata uku masu zuwa za a yi bikin Aminatu Haruna mai goro da Dr. Husain Mukhtar, likita ne a asibitin da suka je yin practical bayan gama karatun ta da ta yi na zama cikakkiyar unguwar zoma, yanzu haka tana aiki a Asibitin garin mu, shi kuma Isha Haruna mai goro yana karatu a babbar jamiʼar ƙasar mu domin zama cikakken mai shariʼa yana aji huɗu…….

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Ittikafi

    Yadda Ake Ittikafi

    Ittikafi: shi ne dauwama a masallaci, domin yin ibadah, Salloli da tasbihi haɗi da tahlili, takbiri da salatin annabi da karatu alƙur’ani mai girma da sauransu a cikin masallacin Juma’a.

    حدثنى يحي عن مالك عن إبن شهاب عن عروة بن الزبير عن عَمْرَةَ بِنْتُ عَبْدُالرَّحْمَنْ عَنْ عَائِشَةُ زَوْجِ النَّبِيُ صَلَى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهَا قَالَتْ :كَانَ رَسول الله صلى الله عليه وسلم إِذَا عْتَكَفَ يُدْنِى إِلَى رَأْسَهُ فَأُرَجِّلُهُ ,وَكَانَ لاَ يَدْكُلُ الْبَيْتَ إِ لاَّ لِحَاجَةِ الإِ نْسَانِ.

    An rawaito daga Yahaya daga Malik daga Ibin Shihab daga Urwata bin Azzubairu daga Amrata binti Abdulrahman daga Aisha matar annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ita ce tace “Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance, idan yana ittikafi, yana kusanto kan sa kusa da ni (ma’ana sai annabi ya miƙa kansa ta taga , saboda gidansa yana kusa da masallaci ne) sai ta tsatstsefe (tatacewa) masa kansa, sannan (annabi) ya kasance ba ya shiga gida, don buƙatar wani mutum”. Idan yana ittikafi.

    Saboda haka mai ittikafi ba zai shiga gida ba, don buƙatar wani mutum daban, Haka ma mai Ittakafi ba zai fita cikin masallaci ba, sai don buƙatar kansa kamar su, rashin lafiya, abinci, idan babu mai kawo masa abinci da sauransu.

    Buku da ƙari kuma, mai Ittakafi ba zai tafi ziyarar maƙabarta ba, ba zai tafi zance ba ko gurin ɗaurin aure, ba zai kwana agidansa ba, sai dai idan a cikin masallaci ne, ba zai yawaita yawan surutu ba, sannan kuma dole ne a kan mai Ittikafi ya nisanci dukkanin abin da ya kamata ya nisanta. Misali kamar su kasuwanci, labaran duniya, kallon tsaraici, maganganun batsa ko kwarkwasa da sauransu.

    Haka kuma mai Ittikafi ba zai tafi gida ba, idan an ga wata (shan ruwa), har sai ya dawo daga masllacin idi kamar yadda ya zo a cikin wannan hadisin na annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla), sai dai idan akwai wani dalili mai ƙarfi.

    حدثنى يحي عن زياد عن مالك : أنه رأى بعض أهل العلم إذا عتكفوا العشر الأواخرين من رمضان ,لا يرد إلى أهاليهم حتى يشهدوا الفطر مع الناس .

    An ruwaito daga Yahaya daga ziyadi daga Malik (yace), haƙiƙa shi yaga sashin ma’abota Ilimi, idan suka yi Ittikafi na kwanaki goman ƙarshen watan Ramadan, ba sa dawowa gidan su (wajan iyalansu), har sai sun halarci masallacin Idi tare da musulmai.

    Sannan kuma babu laifi a kan mace ta yi Ittikafi kamar namiji, idan mace tana Ittikafi, sannan sai halarta ta same ta a cikin wannan hali (Ittikafi) me za ta yi?, Amsa idan mace hailarta ta same ta a wannan hali za ta koma gida ne, idan ta yi tsarki, sai ta dawo masallaci ta gina ko ta ɗora a kan abin da ya wuce na Ittikafinta, kamar macen da akwai ramuwar azumi wata biyu (60) a kanta, kuma waɗanda ake jera su, sai ta fara ramuwar azumi da ake binta, sai kuma halarta ta zo mata, sai ta tsaya da yin azumin, idan ta ɗauke mata, sai ta ɗora a kan abin da ta yi na aziminta.

    Hakan kuma babu laifi a kan mai Ittikafi yin aure ko Aure, matuƙar ba zai fita cikin masallaccin ba, sannan kuma ba zai sadu da matar ba, har sai bayan ya fito daga masallaci. Bugu da ƙari kuma, an hana saduwa da Iyali ga mai Ittilafi da safiya ne ko daddare ne, har sai bayan ya kammala Ittikafinsa.

    Sannan kuma babu laifi ga mai azumi, idan yana da mataye ko ‘yan uwa, sai su kawo masa ziyara cikin masallacin, amma kuma ba za su yi maganar wasa ba ko kwarkwasa. Har ila yau, mafi alherin Ittikafi kwana goma, ƙarancinsa kwana ɗaya da yini, haka kuma ba’a yin Ittikafi sai da azumi, kamar yadda Allah (S.W.A) ya faɗa a cikin Baƙara ayata (187)

    Sannan kuma mai Ittikafi ya shagaltul da karatun Alƙur’an ko nafilfili ko Istigifari ko ambaton Allah (S.W.A) dare da rana. Haka ma ya dage da neman kusanci ga Allah da mazonsa haɗi da neman addu’ar ci gaban addinin musulunci da musulmai da kuma kare su daga sharrin maƙiya da mahassada, domin alfarmar annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla). Bugu da ƙari kuma, babu laifi a kansa idan yana da wasu buƙatu ya roƙi Allah (S.W.A).

    Saboda haka Ittikafi yana ɗaya daga cikin manya-manyan Ibada masu girman gaske, sannan kuma shi Ittikafi riba biyu ce ko ma uku, na farko Ibadah ce mai girma , na biyu ga samun ƙarin girma a wajen Allah da manzonsa, matuƙar ya cika sharaɗan Ittikafi, na uku ga samun lada mai yawa haɗi da biyan buƙata da kuma samun farin jini a wajen al’umma da sauransu.

    Haka nema yasa ba kowa ba ne yake iya samun yin Ittikafi, saboda falalar da ke cikinsa, saboda duk wanda zai aikata abin da zai nisanta shi daga shiga wuta, sai shaiɗan ya ɗora masa kasala da gajiya, wajen ya ga ya hana shi aikata haka.

    Bugu da ƙari ma yana hana su yin aikin alheri kamar su kyauta, sadaka, ciyarwa, nafilfili da sauran su. Saboda haka sai ka ga mutane sun ƙi shiga Ittikafi, har sai ka ga masu shiga Ittikafin sun kammala, sun dawo suna zama tare da su, ka ga su, sun aikata Ibadah mai girma, sannan kuma sun dawo suna zama tare da su.

    Daga ƙarshe kuma, ina kira ga waɗanda ba su samu ikon shiga Ittikafi ba, to su samu abinci ko abin sha ko kayan marmari, su ba masu yin Ittikafi da sauransu, domin samun falalar da suke cikin, saboda duk wanda ya ciyar da mai azumi, Allah (S.W.A) zai ba shi lada kwatan-kwancin wanda ya yi azumi, ballantana ma a ce ka ba mai yin azumi kuma wanda yake cikin Ittakafi.

    Saboda haka ina ba da shawara ga waɗanda suke zuwa Umarah duk shekara, ga wata falala mai ɗimbin yawa, wanda ya kamata su dunga aikatawa, saboda kuɗin da suke kashewa a ƙalla zai iya ciyar da mutane abinci haɗi da nama na mutane guda dubu ɗaya, saboda haka yaya kake tunanin a cikin kowane gari a samu mutane guda goma su aikata haka, mutane dubu nawa ne za a taimakawa, a maimakon su dunga zuwa umrah duk shekara.

    Sannan kuma duk abin da mutum ya ciyar da wani mutum, to Allah (S.W.A) zai riɓanya masa sau ɗari bakwai (700) ko ma fiye da haka, sannan kuma ga samun zaman lafiya a tsakanin mawada da talakawa haɗi da yabo na karamci da addu’o`i agare su da sauransu.

    Muna roƙon Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) ya ba mu ikon aikata wannan Ibadah ya kuma sa mu dace, Ameen, domin alfarma annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasalla), sannan kuma mutum ya guji yin ƙarya a lokacin da yake yin ittikafi, saboda dukkanin wanda ya yi ƙarya ko kasuwanci ko saduwa da mace ko catin da waya (WhatsApp ko Facebook) ko yawan surutu, to ittakafin sa ya ba ce, sai ya sake wani, matuƙar ya shagaltu da aikata haka. Wasu malamai suka ce kuma ‘a a, ittikafinsa yana nan, sai dai ya rage ma kan sa lada”.

    Danna nan don karanta Lailatul Ƙadri

    Edita@rumasau-kallamu

  • Lailatul Ƙadri

    Lailatul Ƙadri

    Wasu kwanaki ne masu ɗimbin falala, waɗanda suka fi watanni dubu, sannan kuma ba a samunsu, sai a cikin watan Ramadan, a kwanaki goman ƙarshensa.

    حدثنى زياد عن مالك عن يزيد بن عبدالله بن الهاد عن محمد بن إبراهيم إبن الحارث التيمى عن أبى سلمة  بن عبدالرحمن عن أبى سعيد الخدرى أنه قال :كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يعتكف العشرالوسط من رمضان فاعتكف عاما , حتى إذا كان ليلة إحدى وعشرين وهى اليلة التى يخرج فيها من صبحها من اعتكافه قال : من اعتكف معي فليعتكف العشر الأوخر, وقد رأيت هذه اليلة أنسيتها , وقد رأيتنى أسجد من صبحها فى ماء وطين فالتمسوهافى العشر الأخر والتمسوهافى كل وتر ,قال أبو سعيد فأمطرت السماء تلك اليلة وكان المسجدعلى عريش فوكف المسجد قال أبو سعيد :فأبصرت عيناي رسول الله صلى الله عليه وسلم إنصرف و على جبهته وأنفه أثر الماء والطين , من صبح ليلة إحدى وعشرين .

    An ruwaito daga Ziyadi daga Malik daga Yazidu bin Abdulllah bin Hadi daga Muhammad bin Ibrahim bin Haris Al-tamimi daga Abu-Salma bin Abdullahman daga Abu-Sa’idul Kudri, haƙiƙa shi ne yace, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana Ittakafi a goman tsakiyar watan Ramadan, sai ya yi Ittikafi a wannan shekarar, har sai da ya kasance daren ashirin da ɗaya (ta same shi a cikin masallaci) ita ce da ya fita safiyarta, wanda zai yi Ittikafi a cikinta yace “Duk wanda zai yi Ittikafi tare da ni, to a daren goma ƙarshen (Ramadan), haƙiƙa ya ga a cikin wannan daren, sannan sai ya manta da ita, haƙiƙa na ganni ina sujjada a cikin safiyarta, akwai ruwa da taɓo, sannan (sai annabi yace) ku neme ta a cikin kwanaki goman ƙarshen (Ramadan ), sannan (ya ƙara cewa) ku neme ta a cikin kowace rana (na ranar).

    Saboda haka wannan hadisin ya yi magana a kan abubuwa guda biyu Ittikafi da lailatul ƙadri, Ibin Abdulbari yace wannan hadisi shi ne ya inganta a wannan babi, saboda annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana Ittakafi a kwanakin goman tsakiyar watan Ramadan.

    Haka kuma  imamu Hafiz Ibin Hajar yace, shi ne da yi wa wawin damma da kuma sin sakina (ɗauri ko mara wasali), sannan kuma Ibin Abdulbarri yace wannan ruwarta (ta Manzon Allah) yana Ittikafi  har sai da ya kasance a daran ashirin da ɗaya, ita ce daran da ya fice a cikin ta da safiyarta, domin yin Ittikafi’’.

    Wannan ruwayar tana ɗaya daga cikin ruwayar Yahaya da Abubakar da shafi`i, amma a cikin ruwayar kala biyu ce da ta  Ibin wahabi da Ibin Ƙasim, waɗanda suka fitar da ita (annabi yana Ittikafi), amma kuma basu ambaci safiyar ba.

    Amma kuma shi Ibin Hazim ya faɗa misalin wannan ruwayar, inda yake cewa a cikin huɗubar daran ashirin da ɗaya,  annabi ya shiga Ittikafi, ita ce daran ashirin da biyu, saboda abin da aka faɗa a ƙarshen wannan hadisi.

    Sai ya buɗe idonsa, sai ga  annabi (Sallallahu alaihi wasalla) a gefensa a ranar, sannan kuma sai ga alamar ruwa da taɓo a cikin safiyar daren ashirin da ɗaya.

    Abin nufi a nan shi ne, mutum ya shiga Ittikafi kafin daren ashirin da ɗaya (lailatul ƙadri), sannan sai ya manta da ita, sai yace “annabi ya ga mala’ika da haske da idansa”, sannan kuma ya gani  a farkon wannan daran ya ga kaza da kaza a cikin daren, ya ga masallaci, mai girma kuma ga haske, sannan kuma a saman masallaci, ruwa yana zuba, saboda haka alamomin da ake iya gane daren lailati ƙadri ne.

    Misali kamar su gushewar rana, zubar ruwan sama, washewar sararin samaniya, gari ya yi tsit, rashin jin sautin karnuka ko dabbobi, da sauransu. Sannan kuma ana iya samu daren lailatul ƙadri a ranar daren ashirin da ɗaya ko da uku ko da biyar ko da bakwai, ko da tara waɗannan su ne ranakun da ake iya samun lailatul ƙadri.

    Amma Abi-Sa’id yace, sama ta kece da ruwa a wannan daren, sannan masallacin ya kasance tamkar ginshiƙi, sai masallacin ya tsaya, sannan kuma  Abi-Sa’id yace sai annabi (Sallallahu alaihi wasalla) ya buɗe idanunsa, sai ya juya sai ga goshinsa da hancinsa akwai alamar ruwa da tabo a daren Asubahin da ya shiga na watan Ramadan.

    An ruwato daga Ziyadu daga Malik daga Abudullah bin Dinari daga Abdullah bin Umar (yace) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) yace’’ ku binciki (ku kirdado) daren lailatul ƙadri a cikin bakwai ɗin ƙarshe.

    Abun nufi a nan shi ne a kwanaki ashirin da bakwai ɗin ƙarshen.

    حدثنى زياد عن مالك عن هشام بن عروة عن أبيه : أن   رسول الله صلى الله وسلم قال “تحروا ليلة القدر فى العشر الأخرين من رمضان.

    An ruwaito daga Ziyaddu daga Malik daga Hishamu ‘’ku binciki daran Lailatul ƙadri a cikin (kwanaki) ashirin ɗin ƙarshen watan Ramadan.

    حدثنى زياد عن مالك عن أبى النضر مولى عمر بن عبيدالله : أن عدالله إبن أنيس الجهني قال لرسول الله صلى الله عليه وسلم : يا رسول الله , إنى رجل شاسع الدارفمرنى ليلة أنزل لها , فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم ” أنزل ليلة ثلاث وعشرين من رمضان ”

    An ruwaito daga Ziyadu daga Malik daga Abi-nadhir mai yi wa Umar bin Ubaidullah hidima (yace), haƙiƙa Abdullah bin Unaisu Aljuhaniyyu yace da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla), ya manzon Allah ni mutum ne mai rushe-shshen gida, ka umarce ni da daren da aka saukar da ita (Lailatul ƙadri), sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) yace da shi “An saukar da daran (Lailatul ƙadri), ashirin da uku a cikin watan Ramadan”.

    Amma Ibin Abdulbarri yace wannan ruwayar yankakkiya ce, saboda Abi-nadhir bai riski Abdullah bin Unaisu ba, sannan kuma bai gan shi ba, amma haƙiƙa Imam Muslim ya sadar da wannan hadisin ta hanyar Dhahaku bin Usman daga Abidi daga Busra bin Sa’id daga Abdullah bin Unaisu da lafazin Hadisin Abi-Sa’id daga Daud ya sadar da shi ta hanyar Ibin Ishak daga Muhammad bin Ibrahim Attamimu daga Umrata bin Abdullah bin Unaisu daga mahaifansa kamar yadda wannan hadisin na Muwaɗɗa Malik ya nuna haka.

    An ruwaito daga Ziyadu daga Malik daga Humidu Aɗɗawilu daga Anas bin Malik, tabbas ne yace, Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) ya fita tare da mu a cikin watan Ramadan, sai yace ‘’ni na ga mutane biyu suna jayayya, sai suka ɗaga ta,(sai yace da su) ku neme ta a cikin (ashirin da) tara ko bakwai ko biyar’’.

    حدثنى زياد عن مالك أنه بلغه : أن سعيد بن المسيب كان يقول : من شهد العشاء من ليلة القدر , فقد أخذ بحظه منها.

    An ruwaito daga Ziyadu daga Malik (yace) haƙiƙa shin labari ya same shi lalle Sa’id bin Musayyibin ya kasance yana cewa, duk wanda ya shaida (ya yi sallah) Isha’i a cikin Lailatul ƙadri (Ai a cikin ranakun da ake sa ran ganinsu), haƙiƙa ya riski daren lailatul ƙadri.

    Haka kuma Ibin Abdulbarri yace, wannan ba zai iya kasancewa ba, sai kawai ra’ayi ne, sannan ba zai riƙi komai ba, sai  dai neman dacewar Allah (Subhanahu wata’ala) a cikin wannan ranar.

    Saboda haka malamai sun ƙarawa junarsu sani a kan daren Lailatul ƙadri, saɓanin mai yawa, daga cikin su akwai maganar baban malamin nan Al-araki, saboda ita (Lailatul ƙadari) ba ta yi dai-dai da sauran shekaru ba ko ranaku.

    Ma’ana ganin wannan daran sau ɗaya ya taɓa faruwa azamanin Manzon Allaah (Sallallahu alaihi wasalla), sannan kuma an faɗa awata maganar, wannan daran yana kewayawa ne a kowace shekara, a wata faɗar kuma an ce Lailatul ƙadri tana cikin rabin watan Sha’aba, sannan kuma wasu sun ce, A’a an keɓance ta ne a cikin watan Ramadan.

    Sannan za a iya samunta a cikin kowanne dare (Ramadan), Bugu da ƙari kuma Sheikh Sabkiyu ya yarinjar da shi, amma malam Sarkhisu ya faɗa a cikin sharhin ‘’ Hidayatu’’. Maganar Abi-Hanifa yace zamu samu ta (daren Lailatul ƙadri) an ciro ta ne a cikin dukkanin Ramadan, haka nan ma abokinsa ya faɗi haka sauransu.

    Haka ma an ruwaito daga Ibin Abi-Asim daga Anas yace, babu wanda ya sani daga cikin mu (ranar ganin Lailatul ƙadri), sai wani malami daga cikinsu yace, A a, Lailatul ƙadri, tana cikin rabin watan Ramadan, sai kuma wani mutum yace, A a tana cikin daren goman sha shida ne, na Ramadan.

    Sai kuma wani yace, A a tana cikin daren goman sha bakwai, sannan sai wani yace, A a tana cikin daren goma sha takwas, sai kuma wani ya ƙara cewa, A a tana cikin daren goma sha tara ne, sai kuma wani ya sake cewa, Aba tana cikin daren ashirin ga watan Ramadan.

    Haka kuma sai wani yace, A’a ita Lailatul ƙadri abar so ce, sannan kuma tana cikin goman tsakiyar watan ramadan, sai kuma wani yace A’a ita kuma abin so ce, sannan tana cikin goman ƙarshe.

    Sai kuma wani yace, A a, Lailatul ƙadri tana cikin daren ashirin da biyu na watan Ramadan har zuwa daren talatin ga watan Ramadan, sannan kuma wasu suka ce Lailatul ƙadri, tana ci kin goman tsakiyar watan Ramadan, wasu kuma suka ce tana cikin goman ƙarshen.

    Amma a cikin mazahabar Imam shafi’i jamhurum Sahabbai (mutanan mu) suka ce. haƙiƙa ita Lailatul ƙadri tana goman ƙarshe watan Ramadan, sannan kuma abar so ce a kan mu, sai dai ita abar ayyanawa ce a kan wannan al-amari, sannan kuma wannan daren na Lailatul ƙadri ba za ta gushe ba, har zuwa ranar lahira, kowanne ranaku goman ƙarshe (na wata) abar ɗaukakawa ce.

    Daga ƙarshe kuma, mazahabar imam shafi’i sun rinjayar da daren ashirin da ɗaya shi ne daren Lailatul ƙadri, sannan kuma dukkanin mazahaban nan guda huɗu sun yi bayani a kan kwanakin sa ran ganin Lailatul ƙadri.

    A takaice, alamomin daren lailatul ƙadri suna da yawa, amma dai idan ana cikin tsananin zafi ko sanyi, to a ranar daren za a samu sauƙi, idan kuma garin akwai duhu, to za a samu haske a garin da sauransu.

    Danna nan don karanta Azumin Watan Ramadan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Wata Mata Mai ’Ya’ya Biyu

    Tatsuniyar Wata Mata Mai ’Ya’ya Biyu

    Ga ta nan, gata nanku.

    Akwai wata mata tana da ’ya’ya biyu, ɗaya mace, ɗaya kuma namiji. Macen ce babba, namijin kuma shi ne ƙarami. Tana nan, tana nan sai wata rana ta kamu da rashin lafiya. Tana cikin rashin lafiyar ta kira ’ya’yanta, tana yi wa macen wasiyya cewa, ko da bayan ranta yaron ya ce zai yi wani abu to kada ta hana shi, ta bar shi.

    Bayan uwar ta rasu sai suka bar gidan, suka kama hanya suka nufi wani gari daban. Suna tafiya a cikin daji kwana da kwanaki, rannan sai wata babbar tsuntsuwa ta ɗauke su ta tashi sama da su, ta yi ta tafiya har suka isa daidai wani babban gari. Sai yaron ya ɗauki tsinke ya ce da yayarsa zai tsokale zumɓutun tsuntsuwar, amma sai ta ce idan ya tsokale tsuntsuwar ai za ta yar da su.

    Da ya ji haka sai ya ce mata ba uwarsu ta ce ta bar shi ya yi duk abinda yake so ya yi ba? Da yarsa ta ji haka sai ta yi shiru. Ya samo tsinke ya tsokali zumɓutun tsuntsuwar nan. Ita kuwa sai ta zubar da su a wannan gari.Can sai suka ga wani gida suka shiga, to ashe na wata tsohuwa ne. Da ta gan su sai ta yi maraba da su, ta ba su ruwa suka sha, ta tambaye su daga inda suke, sai suka kwashe labari suka ba ta.

    Sai ta ce da su za ta riƙe su, amma kuma akwai wani dodo da yakan zo da dare yana cinye mutane kullum a garin. Da dare ya yi aka kulle gida, sai yaron nan ya ce a ba shi ƙarafa guda uku, waɗanda zai yi amfani da su ya soke dodon, kowa ya huta a garin. Da tsohuwa ta ji abin da yaro ya faɗa, sai ta ce da shi ba zai iya ba, amma sai ya dage a kan shi dai a ba shi.

    Tsohuwa ta yi masa yadda ya nema amma ba da son ranta ba. Yaro ya hura wuta, ya zuba ƙarafan a ciki. Da suka yi ja, sai ya ji waƙar dodon yana cewa:

    “Wane ne ya isa ya ja da ni, a garin nan?

    Wane ne ya isa ya ja da ni, ni dodo?

    ”Sai can yaron nan ya ce: “Ni ne na isa na ja da kai a garin nan. Ni ne na isa na ja da kai, Ni Auta, har ma na fi ka.” Da dodo ya ji haka sai ya buɗe bakinsa ya yi wani irin ƙaraji. Sai Ɗan auta ya yi wuf, ya jefa masa ƙarfe ɗaya da ya yi jajir a cikin bakin. Sai dodon ya cafe ya haɗiye ƙarfen, yaron ya jefa masa ƙarfe na biyu, dodo ya cafe ya ƙara haɗiyewa.

    Da yaron ya jefa masa na uku ya haɗiye, sai dodon nan ya faɗi rigija. Nan take ya mutu a ƙofar masallaci, ko shurawa bai yi ba. Ganin haka sai Ɗan auta ya bar takalminsa a wajen mushen dodo. Da asuba ladan ya je ƙofar masallaci domin ya shirya ya kira salla, amma sai ya ga mushen dodon nan shim. Sai ya je ya gayawa Sarki abin da ya gani.

    A cikin murna Sarki ya je ya ga mushen dodo, kuma ya tambaya ko wane ne ya kashe shi, domin an ga takalmin wanda ya kashe dodo, amma ba a san ko na wane ne ba. Abu kamar wasa, sai Sarki ya ce duk wanda ya sa takalmin nan ya yi masa daidai, to shi ne ya kashe dodon, kuma Sarki ya yi alkawari zai ba wanda ya kashe dodon ladan rabin garin nan.

    Masu kwaɗayin wannan kyauta suka ta zuwa suna gwada takalmi, amma bai zauna musu daidai ba. Can sai aka ba Sarki labarin wata tsohuwa da ta yi baƙi, sai Sarki ya sa aka kira ta ta sa takalmi bai yi mata daidai ba. Daga ƙarshe dai Ɗan’auta ya sa takalami, kuma ya yi masa daidai. Da dai aka tabbatar shi Ɗan’auta ne ya kashe dodo, sai Sarki ya cika alƙawarin da ya yi, watau na ba shi rabin garin.

    Yaron kuwa ya karɓi rabin gari ya ci gaba da mulki cikin nasara, shi da yayarsa. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mai biyayya lamarinsa ba ya ɓaci.
    • Kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa a wannan duniya.
    • Duk mai mugunta sai ya gamu da wanda ya fi shi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar ’Yan Mata Masu Kamun Kifi

    Edita@rumasau-kallamu