Tag: wikihausa

  • Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa

    Kunun gyaɗa na ɗaya daga cikin abin sha mai daɗi da amfani a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan da ake buƙata;

    Farar shinkafa

    Ɗanyar gyaɗa 

    Sugar daidai misali

    Yadda ake haɗawa

    A gyara farar shinkafa sai a wanke ta, a tsane tsaf. Bayan haka, a soya gyaɗa sama-sama a murje, bayan an bushe, sai a markaɗa, bayan an markaɗa a tace.

    Sai a zuba tataccen ruwan gyaɗar a tukunya, in ya tafasa, sai a ɗauko wanna shinkafar da aka wanke aka tsane, sai a zuba ta a ciki, su yi ta dahuwa har sai ta dahu sosai.

    Don gudun kada ya tsinke, za ki iya zuba ruwan lemon tsami kaɗan. Idan kuma an ga bai yi kauri ba, sai ki ɗan ɗibi gasarar koko a dama da ruwan sanyi sai a zuba a juya sosai zai yi kauri.

    Domin sanin Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Tsaba Da Wake

    Yadda Ake Tsaba Da Wake

    Abubuwan Buƙata

    Gero

    Wake

    Kuli

    Maggi

    Gishiri

    Citta

    Kanunfari

    Barkono

    Cucumber

    Tomato

    Albasa

    Cabbage

    Man gyaɗa

    Yadda Ake Haɗawa:

    Ki samu surfaffen geronki, Wanda babu dusa a jiki, sai ki wanke shi, ki rege shi, da koko saboda tsakuwa sai ki tsame shi a ruwa, ki ɗan sami ruwa mai kyau, ki zuba mishi yadda zai riƙa jiƙuwa. Dama kin gyara wakenki, kin wanke shi.

    Sai ki tsaida sanwa ki zuba waken in ya yi rabin dahuwa, sai ki zuba geronki ki sa maggi da ɗan gishiri ki juya kada ki bari ta kama, za ki riƙa dubawa akai-akai, in ruwa bai isa ba, sai ki ƙara

    Amma ba a son ruwa ya mata yawa in ta dahu sai ki sauke, dama kin tanadi dakakken ƙulinki wanda kika dake shi da kayan ƙamshi da barkona da maggi & gishiri, dama kin soya man gyadarki, a gefe kuma ga cabbage, cucumber, albasa, tomato waɗanda kika yanka su ƙanana. Bayan haka, sai ki samu mazubi mai kyau da za a zuba wa mai gida,

    Sai ki jejjera su cabbage ɗin akai, ki kawo wannan ƙulin, ki zuba kina barbaɗawa sai ki zuba man gyadar, shi kenan a ci lafiya.

    Domin karanta Yadda Ake Noman Wake danna nan.

  • Yadda Ake Burabusko

    Yadda Ake Burabusko

    Burabusko: Burabusko abincin gargajiya ne, wanda ya samo asali daga Barebari; wanda ake yin shi da gero.

    Gero na ƙunshe da sinadiran calcium, copper, iron, magnesium, manganese, selenium, potassium, phosphorus da kuma bitamins kamar su niacin, riboflabin, pantothenic, folate, folic acid, bit B6, bit C, bit E.

    Abubuwan Da Ake buƙata:

    1. Gero
    2. Mai
    3. Gishiri

    Yadda Ake Haɗawa

    A wanke gero a shanya shi ya bushe sai a ɓarza shi,

    A ɗora ruwa a kan wuta kamar rabin tukunya, sai a kawo madambaci a ɗora a kan tukunyar; sai a shimfiɗa buhu a kan madambaci.

    Sai a kawo ɓarzajjen geron da kika bakace aka fitar da dusar a zuba a cikin madambacin; a yayyafa ruwa a kai, Idan ana so ma, ana iya jiƙa kanwa ‘yar kaɗan a yayyafa ruwa a kan geron saboda ya yi laushi sosai.

    Sannan a bar shi ya turaru, Idan ya ɗauko turaruwa za a ga ya fara curewa,

    Sai a sauke daga kan wuta, a zuba mai da gishiri ko maggi a mutsittsika; domin ya warware a rage ruwan da yake cikin tukunyar, a bar shi daidai yadda zai yi.

    A ɗauko turarren geron a zuba a cikin ruwan, sai a ɗan juya kamar ana ruɗe,

    Amma wannan da ƙauri. Sai a kawo leda a rufe, sannan a kawo murfin tukunya a ɗora a kai. Idan ya yi, za a ji gida ya turare da ƙamshi, kuma idan an taɓa za a ji ya yi laushi.

    Domin sanin Yadda Ake Dashishi danna koren rubutun nan

    Domin sanin Yadda Ake Hada Lemon Gyada, Shinkafa Da Dankalin Hausa (Groundnut, Rice, Sweet Potato Shake) danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga

    Yadda Ake Kunun Kwakwa Ga Masu Ciwon Siga

    Kunun kwakwa yana ɗaya daga cikin abin sha mai riƙe ciki, sannan ba shi da wahalar narkewa a ciki.

    Yana rage hawan suga ga masu ciwon suga, ruwan kwakwa yana wanke koda da samun fitar fitsari cikin sauri da inganta aikinta wajan tace abubuwa da sauransu.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Kofi ɗaya na Farar shinkafa
    Kofi ɗaya na Kwakwa
    Kofi ɗaya na Gyada
    Kofi ɗaya na Madara
    Sai a zuba ruwan zuma gwargwadon yadda ake buƙata ko sikarin da suke amfani da shi na masu ciwon siga.

    Yadda ake haɗa kunun kwakwa

    1. Da farko za a wanke shinka fara, sai a jiƙa ta da ruwan zafi tsawon minti talatin (30)

    2. Sai a jiƙa gyadar, a surfa ta, a wanke ta (kamar yadda ake wanke wake).

    3. Sai a juye su (Shinkafa, gyaɗa, kwakwa) a abin da za a markaɗa (blender). A zuba ruwan kwakwar a yi blending sosai; (Za a iya ƙara ruwa idan ruwan kwakwar bai isa ba)

    4. Sai a tace a ɗaura a tukunya a yi ta juyawa har sai an ga ya yi kauri.

    5. Sai a zuba zuma ko sikarin masu ciwon siga (gwargwadon yadda ake buƙata) da madara kofi ɗayan nan a motsa. Sai a kashe wutar, a bar shi ya kama jikinsa kamar na minti biyar

    Wannan abin shan, yana da kyau ga masu ciwon siga da ‘yan sama da shekara arba’in (40). Su mayar da shi abincin darensu, domin ƙarin lafiyarsu.

    Domin sanin yadda ake Buredin Kwakwa danna koren rubutun nan.

    Domin sanin yadda ake Yadda Ake Biredin Gyaɗa (Groundnut Bread) danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Rage Zafin Kishi

    Yadda Ake Rage Zafin Kishi

    Kishi wani al’amari ne babba. Kuma ɗabi’ace da Allah Ya halicci mutane da ita.

    Maza da mata, kuma kowacce mace na da kishi. Matan Annabi (SAW)  sun yi kishi.

    A’isha (R.A)  tana cewa :

    Ban taɓa yi wa wata mace kishi ba, kamar Khadija (RA) sai dai su kishinsu akwai ilmi, hikima, da tsoron Allah.

    A yanzu kuwa, akwai matsalolin da muke fuskanta da yawa. Saboda zafin kishi da ke sanya ayyukan da-na-sani. Da kawo rabuwar aure. Da gurɓacewar tarbiyyar yaranmu.

    Domin maganin matsalar zafin kishi. Sai maza sun fahimci ɗabi’un mata. Tabbas mace ba ta son abokiyar zama. Amma fa akwai yadda za a bi da ita. A yi amaryar nan cikin lumana. Haka ma dai mata su fahimci irin ɗabi’un maza. Ba shakka maza suna son mata. A wajensu fa zama da mace ɗaya larura ce. Kuma maza suna da kishi mai zafi har ya fi na mata ma. Duk da yadda wasu mata ke da kunya, daraja, da kamun kai, har ma da kiyaye abin da zai motsa kishin mazajensu. Amma fa sai kin ji wasu mazan na zafafa kishi, yadda matansu kan rasa inda za su ji sanyi a ransu.

    Saboda haka dole ne mata mu yi kaffa-kaffa da mu’amalarmu da ‘yan uwanmu waɗanda su ka balaga. Abokan aiki da na karatu. Domin ta irin wadannan hanyoyin muke rura zafin kishin mazajenmu.

    Maza masu tsananin kishi har iyayenka sai sun nuna ma ba sa jin daɗi. Dole kawai a fifita ra’ayin miji sama da na kowa. An ce zama lafiya ya fi zama ɗan Sarki. In ba haka ba kuwa, kullum  babu kwanciyar hankali.

    Shi Namiji mai kishi na da daɗi,  muddin babu zargi a ciki. Domin irinsu na ƙoƙarin killace matansu sosai. Kamar kai su unguwa. Da damuwa sosai, su dinga kula da al’amarin matansu. Ba irin wanda za ki bar gida. Bai damu da tuntuɓar ki ba. Komai daɗewar ki, ko kwanaki ma. A addinance ma ba a son namijin da ba ya kishin matarsa.

    Wasu mazan su ne ke haukata mata da gangan. Su ke jefa su cikin matsalar zafin kishi. Za ki ga ƙarfe 1:am wani na waya ko chatting da wata a kan shimfiɗarki. To ko  zuciyar katako ce da mace, dole ne fa ranta ya ɓaci.

    Ba shakka hakan da ciwo ainun. Amma wai masu juriya irin wannan ba sa kishin mazajensu ne?  Tsoron Allah, Natsuwa,  da Iya taku  kawai . Duk fa haukan da za ki yi, ba zai magani ba. Sai dai ma ya ƙara yin nesa dake. Ya cigaba da harkokinsa. Kawai ki nemo hanyoyin da Za a raba shi da chatting ɗin da ba na aiki ba ne cikin siyasa. Yawanci wasu matan ba raba shimfiɗa muke da mazan ba. Mu bar kaɗaici ya da mu mazajenmu . Ni ko kai ka ce mu raba ɗaki, ba zan iya ba. Zan ce ba na iya barci, dole sai na manne da  kafaɗa, hannu ko kan ƙirjinka.

    Wasu matan ma su ke manne wa wayoyinsu, su yi ta chatting da ƙawaye, ba sa ma kallon mai gida. Ba sa ɗan tura masa komai. Hotunan Zuciya, furanni, waƙoƙin soyayya, hira. (Chatt, Love pictures, Cards, video shows,… etc).

    Wannan dabarun ma za su yi amfani. Sai mace ta zama tana da tasiri wajen mijinta. Ko  ta hanyoyin sadarwa na zamani,  ba a bar ta a baya ba.

    Wasu matan na zuba kishi har ya ƙetare Shari’a. Wata ta nakasa mijin, ko tai ta bala’i ya gaji ya sake ta. Ko a kulle ta ma a kurkuku.  Shi kuma da aka yi, domin shi ya sake sabuwar amaryarsa. Ko ta hallaka miji ta yi wa kanta asarar duniya da lahira. A garƙame ta a kurkuku tun daga nan duniya. Ta jefa iyayenta, danginta baƙin ciki da gori. Allah Ya raba mu da aikin da-na-sani.

    Bai kamata muna ɗaukar hukunci a hannunmu ba.

    • Hanyoyin da za mu bi,  domin rage zafin kishi

    1 – Mata mu dinga duba ƙarin aure nassin Alkur’ani ne da ya fara daga mata biyu. Ubangiji ne ya halatta musu.”Ku auri abin da ya muku daɗi daga mata biyu, uku, hudu….. “.(Nisa’i :3)

    2 – Maza ku dinga duba muhimmaci yin adalci.
    : “.. Idan  kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, ku auri guda …. “.(Nisa’i:3) Tabbas kwatanta adalci na kawo zaman Lafiya.

    3 – Idan miji ya shigo da zalunci, sai ki yi ta masa addu’ar Allah ya shirye shi. Ko ki kai ƙarar sa wajen Allah. Allah Yana karɓar addu’ar wanda aka zalinta.

    4 – Nasiha, rarrashi, da amfani da hikima na sa maza su yi nasarar maganin zafin kishi matayensu. Haka kuma mata masu yi wa maza nasiha, ‘yan hikimomi. Har ma wasu na da jarumta. Na ta ya mijinsu neman aure. Haka na janyo musu samun alkharai masu yawa.

    5 – Idan abubuwa sun cakuɗe, sun girmama. Sai ki shigo da manya a ciki. Domin a yi maganin matsalolin.

    6 – Yawan ambaton Allah, karatun Qur’ani, da ƙiyamul laili na kashe zafin kishi. Yayin da mijinki ke neman aure, amarya, hulɗa da wasu mata da bai dace ba.

    5- .Kowacce mace ta san kanta, yadda ko mijinta ya yi mata abokiyar zama, za ta fita biyayya, tattalinsa, kwalliya da iya girki. Haka zai sa ya gane ashe dai shayi ruwa ne. Sai uwargida ta fi amarya matsayi.

    7 – Maza su dinga koyon irin kulawa da kyautatawa da mata ke buƙata. A irin lokacin da kake ƙarin aure. Irin su sanar da mace, da gyara mata ɗakinta, da turaruka, da zannuwanta muddin akwai halin haka. Ya kamata mu dinga sara muna duban bakin gatari. Zafin kishi na ƙarewa ne a mutuwar aure, ko aikin da-na-sani.

    Na ji wani hadisi Annabi (SAW)  ya ce “Ina kashedin ku da kishi,  domin shi mabuɗi ne na saki.. “Zai fi kyau mazanmu da mata kowa ya nuna wa abokin zamansa ya ji tsoron Allah.

    Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya ce, “Ka so wa ɗan uwanka abin da kake so wa kanka”.

    Mace ta kula da haƙƙoƙin mijinta. Su ma Maza su kula da haƙƙoƙin matayensu. Kuma da sanin yadda ake gyara soyayya zai tamaka mana  gyara a matsalar zafin kishi.
    Danna koren rubutun nan domin samun bayanin Yadda Ake Gyara Soyayya.

  • Yadda Ake Taimama

    Yadda Ake Taimama

    Taimama hanyar da ake yin tsarki ce idan an rasa ruwa, ta hanyar amfani da ƙasa; ana shafar fuska da hannaye biyu da ƙasa mai tsarki, da niyyar ɗahara.

    Ga bayani dalla-dalla yadda ake taimama:

    1 – A doki ƙasa da hannayensa biyu, bugu ɗaya.

    2 – Sannan ya bushe su, don ya rage ƙurar da take kansu

    3 – Sannan sai ya shafi fuskarsa da hannayensa sau ɗaya

    4 – Sannan sai ya shafi bayan tafin hannunsa, ya shafi bayan tafin hannun dama da cikin hannun hagu, sannan bayan hagu, da cikin hannun dama.

    Dalilin wannan siffar ta taimama shi ne, hadisin Ammar Allah ya ƙara yarda da shi ya ce; “Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya doki ƙasa da tafin hannayensa biyu, ya busa a cikinsu; sannan ya shafi fuskarsa da hannayensa da su” [Bukhari Da Muslim ne suka rawaito shi].

    Ga bidiyon yadda ake taimama domin ƙara fahimta sosai:

    Domin ƙarin bayani a kan duk wani abin da ya shafi taimama danna nan

    Domin ƙarin bayani a kan Sallar Alwala Da Falalarta danna nan

  • Mene Ne Hukuncin Yi Wa Mace Kaciya?

    Mene Ne Hukuncin Yi Wa Mace Kaciya?

    Kaciyar mata a Musulunce ba ta da wani hukunci na a yi, ko kar a yi cikin shari’ar Musulunci.

    Saboda duk hadisan dake cikin littattafai kamar su: Sunan na Turmuzi da ragowar littattafai, ba su yi magana kan wajibi ne yin kaciyar ko sunna ba. sun yi bayanin al’ada ce na masu yi a waɗancan lokutan baya, tsari na kiwon lafiya kuma, ya nuna hakan na yin lahani ga ‘ya mace, tunda haka ne kuma, Musulunci na karewa duk wani Musulmi abubuwa guda biyar (5) ciki harda lafiyarsa, “ka ga kuwa bai halatta a yi ba, matsawar akwai cutuwa a ciki”.

    Sassa bakwai (7) na jikin ɗan Adam, diyarsu daidai take da diyar rai, domin su ne suke tafiyar da rai da Allah ya busa maka. Sassan su ne kamar haka:

    1. Ido
    2. Kunne
    3. Hanci
    4. Harshe
    5. Wuya
    6. Baya
    7. Al’aura.
    A likitance kuma:
    Yi wa yarinya mace kaciya kamar rage mata daraja ne, kuma ba wani amfanin yi ma mace kaciya. Kuma yin haka yana sa a hukunta duk wanda ya yi ma ‘yarsa mace kaciya.
  • Yadda Ake Amfani Da Na’urar Gwajin Ciki (Juna Biyu)

    Yadda Ake Amfani Da Na’urar Gwajin Ciki (Juna Biyu)

    Za a iya gwajin ciki da na’ura a kowane lokaci na rana; amma dai da sassafe shi ne mafi dacewa. (fitsarin farko).

    Ki yi fitsari a cikin roba ko kwano mai tsabta ko kofi ko duk abin da kike ganin fitsari zai iya zama a ciki.

    1. Sai ki yi fitsari a ciki, daidai gwargwado, wanda na’urar ba za ta lume duka a ciki ba
    2. Sai ki saka na’urar a cikin fitsarin; iya wajan tsinin ake so ya taɓa fitsarin.

    Kar ki taɓa wajen nuna sakamakon ko wajan tsinin da hannunki

    1. Sai a tsaida na’urar a tsaye kada fitsarin ya wuce alamar (MAX)
    2. Sai ki bar shi ya ɗan jima a ciki kada ya yi ƙasa da sakon biyar (5)
    3. Bayan ya ɗan jima a ciki, sai ki ciro nau’rar daga cikin fitsarin.
    4. Sai ki sa na’urar ta kalli sama wajan ɓangaran da aka rubuta (MAX).

    Idan ba za ki iya riƙe ta a hannu ba, za ki iya ajiye na’urar a waje mai tsafta domin jiran sakamako, ta yadda wajen alamar rubutun MAX din yana kallon sama.

    Sakamako

    • Idan ki ka ga layi mai launi wanda ya turu sosai guda biyu; to kina da ciki kamar yadda aka nuna a hoton nan.
    • Idan kuma ki ka ga layuka guda biyu masu launi, amma ba turarru ba, kina da ciki.
    • Idan kuma ki kaga layi ɗaya, to ba ki da ciki.
    • Idan kuma ki ka ga layi ɗaya mai launi turarre ɗayan kuma ba turarre ba shi ma ba ki da ciki.

    Karin bayani

    • Yayin da ki ke jiran sakamako, za ki iya lura da layi mai launi yana motsawa a cikin wajen nuna sakamakon, wannan ba matsala.
    • Kina buƙatar jira minti 10 don tabbatar da sakamakon.
    • Ba a amfani da sakamakon da gwajin ya bayar bayan minti 30.
    • Sakamako yakan iya canzawa ya danganta da irin na’urar da ki kai amfani da ita, amma wannan shi ne wanda aka fi amfani da shi.
  • Yadda Ilimi Zai Zama Hasken Rayuwarka

    Yadda Ilimi Zai Zama Hasken Rayuwarka

    Ma’anar Ilimi Da Matakansa

    1. Ma’anar Ilimi

    A wannan gaɓar za mu yi magana a kan ma’anar Ilimi a madarar lughah (a harshe Larabci) da kuma Isdilahi (mahangar yaren shari’ar musulunci) a taƙaice.

    2. Ma’anar Ilimi A Lughah

    Kalmar Ilm a lughah tana nufin duk abin da yake warware jahilci ya kawar da shi.

    2.1. Ma’anar Ilimi Isdilahan

    Ilimi a mahangar shari’ah shi ne, duk abin da za a riska a haƙiƙanin yadda yake ta fuskar karatu ko binciken nazari ko gwaji ko ƙwarewa da taimakon wahayi ko hankali ta ɗayan hanyoyin riska guda biyar na ɗan Adam.

    2.2. Matakan Ilimi

    Wasu ma’abota ilimi suna kallon ilimi ta nahiyar yadda ake riskar shi, sai su raba shi gida biyu Ilmud Daruriy ad-dabi’iy da Ilmun Nazariy al-Muktasab. Wasu kuma suna kallon shi ta fuskar addini da rayuwa, su ce akwai Ilmus Shar’iy da Ilmul Kauniy, wasu kuma ta nahiyar addini kaɗai su ce.

    Akwai Ilmul Ghayah (Aqeedah, Qur’an, Hadith) da kuma Ulumul Wasa’il (Ulumul Qur’an, Usulul Fiqh, Musdalahul Hadeeth, Usulut Tareekh, Lughawiyyat d.s).

    Ibnu AbdulBarr (Allah ya masa rahma) yana cewa: “Matakan ilimi a wajen dukkanin masu addini Uku ne; (a) Ilimi mafi ɗaukaka shi ne na addini da babu wanda ya halatta ya yi Magana a cikin sa ba tare da abin da Allah ya saukar ba a littafinsa ko  harsunan manzanninsa -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare su- (b) Ilimi na tsakiya wanda ya ƙunshi sanin ilimin duniya ta hanyar nazari da bincike kamar Ilmud Dibb da Handasah da makamantan su (c) Ilimi na ƙasa wanda yake da alaƙa da koyan kyautata wata ƙwarewa ta iya zaman duniya kamar koyan zane, tsalle-tsalle, motsa jiki, iya ruwa da sauransu.

    Ibnu Hajar (Allah ya kara masa rahma) ya ce: “Abin da ake nufi da Ilimi shi ne na shari’ah da mukallafi zai san abin da ya wajaba a kansa na al’amuran ibadah, mu’amalah da sanin Allah (Tauhidi).

    ____________

    1. Atthaqafah al-Islamiyyah na Prof. Shaukat Muhd Ulayyan sh108.
    2. Al-Fawa’id na Ibnu Qayyim sh137.
    3. Lisanul arab na Ibnu Manzur al-Ifrikiy 6/145.

    Domin karanta cikakken bayani akan Islamiya Daɗi danna nan.