Tag: wikihausa

  • Yadda Ake Colorful Prawn Crackers

    Yadda Ake Colorful Prawn Crackers

    A yau za mu koyi yadda ake Prawn cracker, Prawn cracker abinci ne da yara ke matuƙar so, yana da daɗin ci da sauƙin sarrafawa.

    Abubuwan da ake buƙata

    Mai
    Siga
    Madara

    Yadda ake haɗawa

    1- Da farko za a ɗora mai a kan wuta sai ya ɗau zafi sosai.
    2- Sai a ɗauko prawn crackers a buɗe, sai a dinga zubawa da kaɗan-kaɗan.
    3- Ana zubawa za a ga ya tashi fuuuu sai a kwashe a colander, sai a zuba sugar da madara.

    Domin sanin Yadda Ake Miyar Ƙoda danna nan

  • Yadda Ake Miyar Ƙoda

    Yadda Ake Miyar Ƙoda

    A yau za mu koyi yadda ake miyar ƙoda; Miyar ƙoda miya ce da ake iya cin shinkafa, taliya, da makamantansu. Ƙoda na da matuƙar amfani a jikin mutum.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Ƙoda
    • Mai
    • Maggi
    • Gishiri
    • Curry
    • Attaruhu da tattasai
    • Albasa

    Yadda ake haɗawa

    1. A zuba mai a tukunya kaɗan a saka albasa.
    2. A wanke ƙodar a zuba, sai a ɗan bar ta, ta yi ‘yan mintuna ruwanta su fito, sai a zuba maggi, curry.
    3. Idan ya tafaso sai a zuba yankakken karas da aka gyara, a bar shi ya dahu sai a sauke.

    Domin sanin Yadda Ake Kunun Aya danna nan

  • Yadda Ake Kunun Aya

    Yadda Ake Kunun Aya

    Aya tana ƙara ƙarfin garkuwar jiki ga mai yawan amfani da ita. Aya tana inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita ƙuruciya, tana ƙarfafa yanayin gudanar jini, sannan tana ƙara kuzari na zahiri.

    Haka kuma Aya tana da amfani ga sha’anin da ya shafi ciki da hanji, tana ɗauke da sinadarin dake hana cushewar ciki da kuma kumburi. Har ila yau, tana taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral mara kyau a cikin jini.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Aya
    • Suga
    • Ɗanyar citta
    • Flavour
    • Kwakwa
    • Madarar ruwa
    • Dabino

    Yadda ake haɗawa

    1. A jiƙa aya ta jiƙu, a wanke ta, a saka kwakwa 1 da dabino kamar 7 ko 10, da citta ɗanya ko busasshiya, sai a niƙa.

    2. Sai a tace, a zuba madara a ciki, a sa suga da flavour a juya, a jefa ƙanƙara ko asa a fridge.

    Domin sanin Yadda Ake Spicy Meat danna nan

  • Yadda Ake Spicy Meat

    Yadda Ake Spicy Meat

    A yau za mu koyi yadda ake spicy meat. Spicy meat abin ci ne da ake yin yinsa da nama.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Nama
    • Mai
    • Tafarnuwa
    • Gishiri
    • Maggi
    • Curry
    • Kwai
    • Attaruhu
    • Albasa

    Yadda ake haɗawa:

    1. A markaɗa ɗanyan nama mara kitse, tare da albasa curry maggi gishiri da tafarnuwa,
    2. Idan ana son attaruhu za a iya sawa, amma in ba a so ba dole ba ne.
    3. Sai zuzzuba a leda a ƙulle kamar alala, a zuba a tukunya a dafa idan ya yi kamar minti 30 a sauke.
    4. Sai a cire shi daga ledar, za a ga ya cure, sai a yi masa yankan da ake so, sai a fasa ƙwai a sa magi 4 a kaɗa, a dinga tsomawa a ƙwan, a na soyawa za iya ci da komai.

    Domin sanin Yadda Ake Alalan Shinkafa danna nan

  • Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa

    Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa

    A yau zamu koyi yadda ake alalan shinkafa.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Shinkafa ta tuwo
    • Ƙwai
    • Nama
    • Hanta
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Magi
    • Gishiri
    • Curry
    • Main gyaɗa

    Yadda Ake Haɗawa:

    1. A wanke shinkafa a shanya ta, ta bushe a kai a niƙa ta.
    2. A tankaɗe a kwaɓa da ruwa kamar ƙullun alala, a jajjaga attaruhu a zuba a yanka albasa a zuba a yanka dafaffiyar hanta ƙanana a zuba, a daka dafaffen naman a zuba.
    3. A zuba dafaffen ƙwai da aka yanka, a zuba maggi da gishiri da curry a sa mai yadda zai yi.
    4. Sai a jujjuya a zuba a leda a dafa kamar alala, idan kuma na gwangwani za a yi, sai a zuba mai a jikin gwangwani a zuba ƙullun a turara shi, idan ya yi, sai a kwashe a zuba filas.

    Domin karanta Yadda Ake Faten Wake Da Doya ko Yadda Ake Tsaba Da Wake danna koren rubutu.

  • Yadda Ake Yin Crepes Da Vegetable

    Yadda Ake Yin Crepes Da Vegetable

    A yau za mu koyi yadda ake crepes da vegetable. Crepes da vegetable abin ci ne da yake da matuƙar daɗi a wajen karin kumallo.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Fulawa
    • Ƙwai
    • Madara
    • Bakin powder
    • Maggi
    • Gishir
    • Cabbage
    • Carasrot
    • Koren tattasai
    • Albasa

    Yadda ake haɗawa

    1. A kwaɓa fulawa da ƙwai da butter da madara da baking powder, a sa maggi da gishiri kaɗan,
    2. A yi kwaɓin kamar za a yi wainar fulawa, amma kar ya yi ruwa kwaɓin
    3. Sannan a yanka vegetables a soya su a ajiye a gefe
    4. Sai a ɗora frying pan a sa mai kamar za a soya wainar fulawa, a zuba kwaɓin fulawar a ɗan rufe.
    5. Idan ya soyu a cire, sai a zuba kayan haɗin a ciki, a dinga naɗewa,

    Domin sanin yadda ake danbun nama danna nan

  • Yadda Ake Dambun Nama

    Yadda Ake Dambun Nama

    A yau na zo mana da yadda ake haɗa dambun nama; na kaza ko dai na jan nama. Danbun nama na daga cikin abincin da ake samarwa daga nama. Yana da matuƙar daɗi.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Nama/kaza
    • Taruhu
    • Albasa
    • Tafarnuwa
    • Seasoning
    • Man gyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za a wanke nama, ko kaza, a zuba cikin tukunya, a zuba albasa da taruhu da tafarnuwa.
    2. A ɗora a wuta, a bar shi, ya yi ta dahuwa kamar awa 4/5 yana dahuwa.
    3. Idan an sauke, sai a raba shi da ƙashi da kitsensa, ko fata duka, a cire a mayar da tsokar a sa muciya a tuƙe shi, a sa seasoning da spices.
    4. Sai a zuba man gyaɗa har ya rufe naman a soya. Ba za a ɗaga ba, a na yi ana juya shi har ya yi.
    5. Sai a kwashe a saka a cikin abun tata a matse man. A tabbatar ba sauran mai, sai a zuba cikin sieve ko colander. A ci lafiya

    Domin sanin Yadda Ake Egg Muffin danna nan

  • Yadda Ake Egg Muffin

    Yadda Ake Egg Muffin

    Egg muffins abinci ne da ake yin sa daga ƙwai; ƙwai na da matuƙar amfani. Egg muffin yana da daɗi a karin kumallo ko tarar baƙi.

    Abubuwan da ake buƙata

    • Ƙwai Dafaffe
    • Dankali Turawa
    • Dafaffafen nama
    • Koren tattasai
    • Tarugu
    • Albasa
    • Maggi
    • Curry da thyme
    • Gishiri kaɗan
    • Butter Ko mai
    • Baking power

    Yanda ake haɗawa

    1. A yayyanka nama, albasa, taruhu da dafaffen ƙwan. Amma kar a sa dafaffen dankali
    2. A kawo Curry da thyme kaɗan a sa, A ɗauko Maggi na ruwa a sa (za a iya amfani da su ne normal Maggi). Sai a juye a ajiye a gefe
    3. A sami ƙaramin kwano a fasa kwai, a ciki sai a sa baking powder sai gishiri kaɗan Sai a kara juyashi
    4. A ɗauko muffin pan a shafa mishi mai ko butter
    5. Sannan ki ɗauko Dafaffen dankali (yankakke) kisa a ciki
    6. Sai a sa a cikin oven a gasa, har sai ya gasu (ya zama golden brown)
    7. Za a iya ci haka ko kuma a haɗa shi da soyayyen dankali Turawa. A ci daɗi lafiya

    Domin sanin yadda ake potato balls danna nan

  • Yadda Ake Potato Balls

    Yadda Ake Potato Balls

    Potato Balls abinci ne wanda a Hausance ake kiran sa da Ƙwallon dankali, wanda ake yin sa da dankalin Turawa. Yana da matuƙar daɗi musamman ma idan a karin kumallo za a ci shi.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Dankalin Turawa (irish)
    2. Taruhu
    3. Albasa
    4. Kayan Ɗanɗano
    5. Man gyaɗa
    6. Ƙwai
    7. Fulawa

    Yadda ake haɗawa

    1. Farko za a dafa dankali, har ya dahu sai a bari ya huce sannan a yi mashing ɗin shi, a kwashe.
    2. A daka taruhu da albasa a zuba, a saka spices da seasoning.
    3. A saka lawashi, sai a juya ko’ina ya haɗe. A dinga ɗiban wannan mixture ana yinsa kamar ƙwallo a hannun ana ajiyewa.
    4. Sannan a barbaɗa masa fulawa. Za a kaɗa ƙwai, a sa masa gishiri, a ɗaura tukunya, a zuba mai.
    5. Idan ya yi zafi, a na ɗauko wannan haɗin da aka mulmula kamar ball, a sa cikin mai, ana soyawa.

    A ci daɗi lafiya.

    Domin sanin yadda ake cabbege sauce danna nan

  • Yadda Ake Cabbage Sauce

    Yadda Ake Cabbage Sauce

    Cabbage sauce miya ce wadda ake yinta da kabeji da jajjagen kayan miya, tana da daɗi da lafiya a jiki musamman ma idan aka kula da tsabtace da kayan girkin.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Cabbage
    2. Green pepper
    3. Peas
    4. Green beans
    5. Taruhu
    6. Tattasai
    7. Seasoning
    8. Gishiri
    9. Man gyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. Farko za a yi granding din taruhu da tattasai da albasa a yanka lawashi a ajiye a gefe.
    2. A yanka cabbage da green pepper su ma, a ajiye su gefe.
    3. Sannan a zuba man gyaɗa a tukunya, idan ya yi zafi, sai a zuba albasa a juya.
    4. A zuba taruhu da tattasai ana juyawa.
    5. Sai a ɗan rufe na mintina biyu sai a wanke veggies a zuba, amma ban da cabbage da albasa su ne na ƙarshe.
    6. A juya, a sa seasoning a sake rufewa.
    7. Za a buɗe idan ya dahu, sai a zuba cabbage da albasa.

    Ita wannan sauce ana ci da abubuwa da yawa, tun daga farar shinkafa, da chapati, Fateera, har ma su jollof rice.

    Domin sanin Yadda Ake Moi-moi danna nan