Tag: wikihausa

  • Yadda Ake Dambun Nama

    Yadda Ake Dambun Nama

    Dambun nama nau’in sarrafa nama da ake yi a Arewacin Nijeriya. Ana iya yin dambun nama da kalolin nama kamarsu: naman rago, naman akuya ko kuma naman kaza da sauran dangogin nama. Ana ajiye dambun nama domin tarairayar mai gida, ko kuma saukar baƙi na musamman.

    Ko kun san za ku iya ajiye dambun nama na tsahon lokaci mai yawa, ba tare da ya yi komai ba.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    1. Nama
    2. Kayan ƙamshi
    3. Kori
    4. Thyme
    5. Sinadarin ɗanɗano
    6. Yaji haɗaɗɗe
    7. Albasa da tafarnuwa

    Yadda Ake Haɗawa

    1. Da farko za a sami nama, a yanke wajen da babu kitse sai a wanke nama ya fita tas.

    2. A cikin tukunya babba a zuba wannan nama da wadataccen ruwa, sai a zuba su albasa, kayan ƙamshi, kori, thyme da ɗan sinadarin ɗanɗano.

    3. A bar naman ya dahu sosai, har sai naman ya fara dagargajewa….in ruwa ya kusa ƙarewa sai a ƙara ruwa domin ya isa dafa naman.

    4. Cikin turmi mai tsafta a zuba nama a daka har sai ya daku.

    Daga Hafsat_Shettimah: Wasu daga wannan gaɓar suke zuba mai a cikin tukunya, su yi ta juyawa, har sai naman ya soyu amma ni ga yadda nake nawa.

    5. A zuba wadataccen mai cikin tukunya mai zurfi, sai a zuba wannan dakakken nama, a yi ta juyawa da muciya, har sai nama ya fara yin ja, sai a ɗebo wannan yaji a zuba. A nan za a sake jin ƙamshin ya tashi sosai.

    6. A wannan lokaci naman ya kusa sauka, sai a kula da wajen juyawa domin kar nama ya soyu da yawa ko ya ƙone. A kula wurin juyin, domin in an bar shi zai ƙone.

    7. A sami kalanda mai kyau, da tukunya sai a juye sai a bar shi har sai man jiki ya tsane tas da kansa…

    8. Wurin ajiyar dambun kuma, ana iya samun aluminium foil paper sai a juye sannan a saka cikin roba mai murfi a ajiye. Wannan zai iya yin shekara ba tare da ya yi komai ba.

    Domin sanin Yadda Ake Girebe danna nan.

  • Yadda Ake Gireba

    Yadda Ake Gireba

    Gireba abin maƙwalashe ce, da ta samo asali daga fulawa; kuma ana yin ta ne da abubuwan amfanin yau da kullum, masu sauƙin samuwa. Ku dai ku biyo mu domin ku ga yadda za a yi wannan girebar.

    Abubuwan haɗawa

    Fulawa
    Suga
    Riɗi(kantu)
    Man gyaɗa

    Yanda ake haɗawa

    1. Da farko uwar gida za ki tankaɗe fulawarki a roba mai ɗan faɗi. Sai ki jiƙa suganki.

    2. Ki zuba man gyaɗa kaɗan, sai ki juya shi sosai, za ki ga ya yi wara-wara.
    Sai ki ɗauko jiƙaƙƙen suga, ki kwaɓa fulawarki, kar ta yi ruwa, za ki yi shi kamar na cincin.

    3. Ki ringa ɗiba kina sawa a hannunki, ki na dunƙulawa da ɗan faɗi, har ki gama.
    Sai ki barbaɗa riɗi a kai, sai ki ɗauko tiren oven ɗinki, ki shafa man gyaɗa, sai ki jera ki sa a cikin oven ɗinki, ki gasa idan ya yi sai ki ɗauko ki kwashe. sai a ci.

    Domin sanin Yadda Ake Cookies danna nan

  • Dabarun Yadda Ake Girki Mai Ɗanɗano

    Dabarun Yadda Ake Girki Mai Ɗanɗano

    Shin ko an san mene ne dalilan da suke sa girke-girken iyayenmu na da ya fi namu daɗi da lafiya?

    Ko an san dalilan da yasa girke-girkenmu ke da ƙamshi, amman ba ɗanɗano?

    Ko mun yi namu ba ya yin garɗi, kamar na iyayenmu mata da suka manyanta?

    Bari a ji sirrin nasu:

    1. Yayin da ake girki a yanzu, muna amfani da tukwanen ƙarfe, muna rufe su da murfayensu na ƙarfe, maimakon mu yi amfani da FAIFAI na kaba.
    2. Muna amfani da gas ko risho a maimakon MURHU na gargajiya.
    3. Muna amfani da dukkan abubuwan da suke da alaƙa da Turawa; mun guji na gargajiya kwata-kwata, muna amfani da colender maimakon MADAMBACI (GITTERE)
    4. Wajen niƙa kayan girki; blender maimakon DUTSEN NIƘA, mixer maimakon TURMI
    5. Yanzu za ku ga gidaje da yawa ba sa amfani da turmi, wai ya yi ƙauyanci kuma da jijjiga jiki; gaskiya yana da kyau mu gyara.

    Domin sanin Yadda Ake Ɗan Sululu danna nan

  • Yadda Ake Ɗan Sululu

    Yadda Ake Ɗan Sululu

    A yau za mu koyi yadda ake ɗan sululu, ɗan sululu abincin gargajiya ne na  Bahaushe wanda ya kasance ana samar da shi daga garin rogo, wannan abincin akasari na yara ne ko masu kwaɗayi.

    Abubuwan da ake buƙata

    Garin rogo
    Ruwa
    Manja
    Yaji
    Maggi
    Gishiri
    Albasa

    Yadda ake haɗawa

    1. A kwaɓa garin rogo da ruwa. Sai a mulmula kamar yadda ake mulmula gullisuwa.
    2. Sai a ɗora ruwa a tukunya, idan ya tafasa sai a zuba, bayan ya dahu sai a tsame ana zubawa a ruwan sanyi. A Wanke Shi tas.
    3. Sai a zuba a plate a zuba manja, yaji, Maggi. sai a yayyanka albasa.

    Domin sanin Yadda Ake Faten Dankali danna nan

  • Yadda Ake Cookies

    Yadda Ake Cookies

    A yau za mu koyi yadda cookies. Cookies wani nau’i ne daga cikin nau’ika na biskit. yana da sauƙin sarrafawa. yana da matuƙar daɗi musamman ma a wajen yara.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Butter 250 gram
    2. 31/2 cups Flour
    3. Vanilla flavor 1 tspn
    4. 1 cup Sugar
    5. Tbspn Baking powder 1
    6. 1 Egg
    7. Tbspn Coacoa powder

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za a zuba butter a bowl da sugar a yi mixing sosai, har ya haɗe sai a zuba ƙwai

    2. A sa vanilla flavour

    3. Sannan a haɗa flour da baking powder a juya, sannan sai a zuba a cikin haɗin butter a juya har ya haɗe.

    4. Bayan nan, sai a gutsira dough ɗin kaɗan sai a ɗakko wannan cocoa powder a zuba a ciki a juya ya haɗe jikinsa sosai, a dinga mulmulawa ƙanana.

    5. Sannan sai a ɗauko farin a dinga faɗaɗa shi, ana sa brown din a ciki ana mulmulawa sai a ɗan taɓa shi, sannan a sa cokali a dinga tsagawa kaɗan-kaɗan.

    6. Bayan nan sai a ɗakko ɗaya mulmulallan a ɗora a tsakiya sai a sa a oven a gasa tsawon minti goma sha biyar an gama.

    Domin sanin Yadda Ake Faten Dankali danna nan

  • Yadda Ake Faten Dankali

    Yadda Ake Faten Dankali

    A yau za mu koyi yadda ake faten dankali; Faten dankali abinci ne mai daɗi da sauƙin sarrafawa.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Dankali
    Attaruhu
    Albasa
    Maggi
    Citta
    Kifi (ice fish)
    Alayyahu
    Kori
    Man gyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. A fere dankali, a yanka daidai misali.
    2. Sai a wanke kifi, a cire dattin, a yanka gunduwa-gunduwa; a zuba albasa da maggi da citta a kai, sannan a ɗora a wuta.
    3. Bayan haka, sai a jajjaga attaruhu da albasa da citta a ajiye.
    4. Idan ya tafasa a sauke a bar shi ya ɗan huce, in ya huce, sai a ɓare shi a ajiye.
    5. A nan sai a ɗauko tukunya, a zuba man a yanka albasa a ciki, a bar shi ya soyu kaɗan.
    6. A sa jajjagaggen attaruhu da aka jajjaga, sai a zuba ruwa daidai misali, a rufe ya yi mintina ya tafasa.
    7. Idan ya yi, sai a zuba dankalin, a sa maggi da gishiri kaɗan da kori da citta, a rufe ya dahu.
    8. In ya yi sai a zuba kifi da alayyahu da albasa, a juya, sai ki rufe, a bar shi ya yi minti biyar.

    Domin sanin yadda ake kifi mai fulawa danna nan

  • Yadda Ake Kifi Mai Fulawa

    Yadda Ake Kifi Mai Fulawa

    Kifi yana ɗauke da wasu sinadirrai masu matuƙar amfani ga lafiyar jikin ɗan Adam, kama daga ƙananan yara, manya da kuma tsofaffi. Ana kiran Sinadiran dake ciki da suna Omega Three Fatty Acids. Sinadaran da ake samu ga kifi nan take fiye da wanda ake samu ga wasu nau’ikan abinci.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Kifi
    Tafarnuwa
    Flour
    Maggi
    Gishiri
    Curry
    Mangyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. A wanke kifi da venigar ko lemon tsami, a tsame shi a ɗora a plat ya sha iska sosai.

    2. Sai a jajjaga attaruhu da albasa da tafarnuwa, a juye a bowl, a dan sa ruwa kaɗan tare da maggi da spices, sai a sa flour kaɗan ba da yawa ba.

    3. Sai a gauraya su, su haɗe jikinsu, sai a ɗaura man gyaɗa a kan wuta, in ya yi zafim sai a rinƙa ɗaukar kifin ana sawa a ruwan fulawa ana soyawa a mai,

    4. Idan gefe ɗaya ya soyu, sai a juya ɗayan gefen ma.

    Domin sanin Yadda Ake Peppered Chicken danna nan

  • Yadda Ake Peppered Chicken

    Yadda Ake Peppered Chicken

    A yau, za mu koyi yadda ake peppered chicken; Peppered chicken abinci ne da ake yin sa daga kaza, yana da matuƙar daɗi a wajen ci, musamman ma idan aka kula da tsaftar abubuwan haɗawar.

    Abubuwan da ake buƙata

    ▪Chicken/Kaza
    ▪Onions
    ▪Red pepper
    ▪Green pepper
    ▪2 Chilli pepper
    ▪Soy sauce
    ▪pinch of Tumeric
    ▪Curry
    ▪Coriander powder
    ▪Garam masala
    ▪parsley
    ▪Maggie
    ▪Salt
    ▪Dried ginger
    ▪Oil

    Yadda ake haɗawa

    1. A dafa nama tare da attarugu, Maggi, albasa, gishiri, citta, curry idan ya dahu sai a sauke a soya ta a mai.
    2. A zuba mai a cikin kasko sai a zuba yankakkiyar albasa a ciki.
    3. Sai a ɗan motsa kaɗan a sa Maggi, coriander powder, garam masala, red pepper, chilli pepper, turmeric, curry, soy sauce.
    4. A ɗan motsa kaɗan, sai a zuba kazar a ciki, a ci gaba da juyawa har jajjagen ya shiga ko’ina na jikin nama.
    5. Bayan sauce in ta kama nama, ko’ina ya ji sai a zuba green pepper da parsley a ɗan juya.

    Domin sanin Yadda Ake Miyar Kuka danna nan

  • Yadda Ake Miyar Kuka

    Yadda Ake Miyar Kuka

    Ganyen kuka wanda da ita ake miyar kuka, na da matuƙar amfani ga lafiyar ɗan Adam. Tana ɗauke da sinadarai da dama, waɗanda suka haɗa da ‘Vitamin C’, ‘Vitamin A’, ‘Beta Carotene’, ‘Potassium’, ‘Calcium’ da sauransu da dama.

    Waɗannan Sinadarai kuma na taimakawa wajen magance wasu matsaloli da cututuka kamar su tari, tsutsar ciki, ciwon ƙoda, ciwon asthma, sanyin dake taruwa a ƙirji da sauransu.

    Abubuwan da ake buƙata

    Kuka
    Attaruhu
    Daddawa
    Albasa
    Bandar kifi
    Nama
    Magi
    Man ja

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za a ɗora ruwa a wanke nama, sai a yayyanka masa albasa da gishiri kadan. Sannan a rufe ya yi ta dahuwa har sai naman ya yi laushi sai a sauke a ajiye a gefe.

    2. A ƙara ruwa kaɗan a kan silalen romon naman, sannan a yayyanka albasa sai a daka daddawa a zuba da jajjagen attaruhu mai tafarnuwa.

    3. A wanke bandar kifi a zuba. Su yi ta tafasa har sai bandar ta dahu, sannan a zuba magi da manja a rufe su ƙara tafasa.

    4. Bayan haka, sai a zuba kuka kaɗan, a riƙa kaɗawa ko da maburgi ko cokali domin kada a samu gudaji a ciki. Sai a ɗan rufe bayan ya ɗan tafasa sai a sauke.

    Domin sanin Yadda Ake Fruit Salad danna nan

  • Yadda Ake Fruit Salad

    Yadda Ake Fruit Salad

    A yau za mu koyi yadda ake fruit salad; Fruit salad abin sha ne, da yake ɗauke da nau’ika daban-daban na kayan marmari. Yana da matuƙar amfani a lafiyar jikin ɗan Adam, ga daɗi wurin sha.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Ayaba
    2. Lemo
    3. Abarba
    4. Mangoro
    5. Sugar

    Yadda ake haɗawa

    Za a tsaftace kayan lambu a saka su a tire, sai a samu roba mai ɗan girma, a sa ruwa a ciki.

    Sannan a ɗauko wuƙa a fere ko a yanka kankana ƙanana. Sannan a ɗauko lemo a ɓare shi da wuƙa, a wanke shi. Sai a yanka kowane sala ana cire yayansa, da shi za a yi amfani.

    Sai a ɗauko sauran kayan fruits din su ma, a yanka su ƙanana, in an gama, sai a sa sugar a sa a fridge ya yi sanyi. In kuma ana da ƙanƙara sai a sa.

    Domin sanin Yadda Ake Prawn Cracker danna nan