Tag: tatsuniya

  • Tatsuniyar Gwaidayara

    Tatsuniyar Gwaidayara

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can bakin Rafin Kada akwai wani mutum da yake zaune tare da matansa su huɗu; sai dukkaninsu suka sami ciki a lokaci ɗaya. Da watansu ya kama suka haifi ’ya’ya duka mata. Bayan mako guda na al’ada, ya raɗa wa uku daga cikin yaran nan sunaye. Ɗaya sunanta Halima, ɗaya Jummai, ta ukun kuma A’isha.

    Amma sai ya ƙi rada wa ’yar matarsa ɗaya suna. Sai mahaifiyar tata ta tambaye shi: “Me ya sa ni ba za ka sa wa ’yata suna ba?” Bai dai amsa ba, amma ya ce zai raɗa mata suna. Haka dai ta riƙa tuna masa, har wata rana a cikin gatse ya ce: “Ki je sunanta Gwaidayara.”

    Kwanci tashi, yaran nan huɗu suka data, suka isa aure, shi kuma ya tsaya ya tabbatar Halima da Jummai da A’isha kowacce ta sami mijin aure, watau ban da Gwaidayara. Kuma ya yi haka ne saboda bai cika son uwarta ba. Da uwar ta ga haka, sai ta durƙusa ta ce da shi: “Shin Mai gida, me ya sa ba za ka yi wa’yata aure kamar yadda ka yi wa ’yan’uwanta ba?”

    Sai ya dube ta ya ce: “Ki gaya mata ta riƙa bi na daji.” Uwar Gwaidayara kuwa ba ta jinkirta wajen sanar da ’yarta abin da mai gida ya ce ta gaya mata ba. Haka kuwa aka yi. Duk sanda uban zai je daji sai ta bi shi. Kullum haka, abu kamar da wasa ya ɗore. Wata rana da suka je tsakiyar daji sai wani baƙin maciji ya wuce sululu ta gabansu.

    Sai uban ya ce da Gwaidayara: “Ga mijinki nan, ki bi shi duk inda ya dosa.” To saboda biyayya irin wadda ta ga uwarta na yi wa mahaifinta, sai ta ce da shi: “To, Baba, na gode.” Daga nan ta dinga bin maciji, ba tare da jin tsoro ko shakka ba. To, ashe shi ba maciji ba ne, mutum ne kuma ɗan sarki.

    Da ya ga yarinyar na bin sa kamar yadda ubanta ya ce ta yi, kuma ya lura uban yarinyar ya kama gabansa, sai ya rikiɗa ya koma mutum; sai ya tambayi Gwaidayara: “Baiwar Allah me kika zo yi a nan?” Ganin abin da ya faru, sai tsoro da ɗimaucewa suka sa ta kasa yi masa wani bayani.

    Ya dai ji ubanta ya ce: “Bi macijin nan shi ne mijinki.” Da ƊanSarkin nan ya lura da ɗimautar da Gwaidayara ke ciki, sai ya ce da ita: “Kada ki dami kanki, ki ma daina jin tsoro; mu je garinmu a ɗaura mana aure, ai mahaifinki ya ba ni ke.” Sai shi da ita suka kama hanyar garin mahaifinsa; har suka isa, ta ga ana ta faɗuwa kasa ana gaishe shi.

    Da ya shiga gida, ya kai ta ta huta, sai ya ce su je wurin mahaifinsa. Suka je suka gai da Sarki, sai ya tambayi dansa: “Yarima Babba, lafiya na gan ka da wata yarinya; wace ce?” Sai ya ce da shi: “Ka daɗe, mai duniya, wannan yarinya da na zo da ita, ina neman izininka ne in aure ta.”

    A nan take kuwa Sarki ya amince. Bayan kwana biyu aka ɗaura musu aure, Sarki ya kawo dukiya mai yawa ya ba ɗansa da surukarsa. Ɗan Sarkin nan kuma ya ɗebi dukiyar ya je daji daidai inda surukinsa ya bar ’yarsa ya ƙanƙara gida suka tare shi da amaryarsa. Suna nan, wata rana sai uban Gwaidayara ya je gona, sai ya tarar da wasu mata na jan ruwa a rijiyar da ke kofar kataferen gidan nan.

    Waɗannan mata kuyangin Gwaidayara matar Yarima Babba ne. Ya roƙe su ruwan sha, amma suka hana shi, tare da bayanin cewa: “Ko za mu ba ka sai mun cika duk randunan Gwaidayara.” Da ma Gwaidayara ta saba takan leƙa ƙofar gidan ta taga. Da ta leƙa sai ta hango mahaifinta yana magana da ’yan aikinta.

    Sai ta kira ɗaya ta tambaye ta: “Me mutumin nan yake cewa ne?” Sai ’yar aikin ta ce: “Ya ce mu ba shi ruwan sha ne, muka ce sai mun gama cika randunanki.” Sai Gwaidayara ta ce: “Ku ba shi ruwan ya sha. Idan ya sha kuma ku ce ya shigo.” Bayan mahaifin Gwaidayara ya sha ruwa, sai ya ji a cikin ladabi ɗaya daga cikin kuyangin nan ta ce: “Gwaidayara matar Ɗan Sarki ta ce ka shiga gidan nan.”

    Sai ko ya shiga ya zauna a zaure, yana jira ya ga abin da zai faru. Kafin ta aika a gaya wa mai gidanta cewa mahaifinta ya zo, sai ta ji motsin shigowarsa gida. Bai tsaya a zaure ba, ko da yake ya ga baƙon mutum, amma bai san ko wanene ba.Sai Gwaidayara ta tunkari mijinta bayan fadawa sun tsaya a soro ta ce: “Yaya ka wuce mahaifina ba ka gai da shi ba?”

    Sai ya ce: “Yana ina? Ban gan shi ba.” A cikin karairaya irin ta matan da suka iya kissa ta ce da shi: “Ai shi ne a zaure, ai gara ku gaisa.” Sai mijin ya je suka gaisa, aka ba shi masauki irin na alfarma, ya yi wanka da ruwan ɗumi, ga tufafi sababbi an kawo masa; ya zaɓa, ya saka.

    Bayan mahaifin Gwaidayara ya ƙara hutawa, can da la’asar surukin da matarsa suka kawo kyankyandi gomiya ɗaya da biyar, cike da tufafi da kuɗi, suka ba shi. Wasu kayan nasa ne, wasu kuma tsarabar da zai kai wa matansa ce. Ya yi mamaki da godiya; bayi da fadawa suka ɗauki kayan, aka raka shi har gida.

    Da ya kai kayan tsarabar ya yi wa matan gidan bayani, sai suka ce: “Wannan tsarabar ’ya’yanmu ne suka aiko; wa zai ba Gwaidayara arziki haka?” Haka dai suka rabe kayan suka hana mahaifiyarta. Bayan ’yan kwanaki sai mahaifin su Gwaidayara ya shirya zai ziyarci sauran ’ya’yansa, wato Jummai da A’isha da Halima.

    A gidan Halima ya tarar ita da mijin ba su da abinci idan ban da birrai da ɓeraye saboda tsananin talauci; jikinta ya yi kirci, ba ta da ko sabulun wanka. Hatta tabarmar kwanciya ma ba ta da ita. Bayan ya gama ziyararsu zai tafi, sai ta ƙunshe masa kan biri da jelar ɓeraye biyar a tsumma ya kai wa mahaifiyarta tsaraba.

    Da uban ya je gidan Jummai, sai ya tarar ba su da wani abinci sai ganyen yaɗiya da gautan daji da tsamiyar ƙasa. Babu rumbu balle masussuka a gidansu. Bayan ya gama ziyararta, ita da mijin suka roƙo gaskami daga makwabta, ta sa a wani kata don ya kai wa mahaifiyarta tsaraba.

    A’isha ce mijinta yake da ɗan ƙarfi, domin ɗan abin da yake da shi, har dusa yakan samo ta tuƙa musu tuwo. Wani lokacin kuma sukan ci zogale da wake, kuma tana da zane sakakke da turmi da tabaryar yin aikatau. Da zai tafi gida ta ɗebo dusa mai yawa ta ba shi ya kai wa mahaifiyarta tsaraba.

    Da mijin ya koma gida, sai ya ce da matan nasa: “Ina so duk yaran nan kowacce ta zo da mai gidanta ranar Laraba mai zuwa.” Aka aika musu, kowacce ta ci ado, daidai arzilinta, ta taho tare da mijinta. Gwaidayara ce ta fara zuwa tun da sanyin safiya, ta shiga ɗakin mahaifiyarta da ke kusa da ƙofar gida, sauran matan gidan ba su san ma ta iso ba, tare da tarin kyankyandi cike da dukiya mai yawa.

    Sauran kowacce ta zo dukkaninsu suna fama da rama da gajiya, ga shi ba su da suturar kirki. Kowacce ta shiga ɗakin mahaifiyarta wai suna jiran ganin mugun halin da Gwaidayara da mijinta suke ciki. Can kuma sai ga mazansu su ma sun iso. Mijin Halima ya sha lagen wani luru da ya huje; mai gidan Jummai kuma ba komai a jikinsa sai bante.

    Mijin A’isha ne mai dama-dama, domin ya sa ’yar shara wadda ya aro a wurin abokinsa. Mijin Gwaidayara kuma ya tunkaro. Tun yana nesa ƙamshin turarensa ya cika gari, fadawa suna gaba, masu algaita na busa, makaɗa na ta kiɗa; sai kirari ake yi masa ana cewa: “Lafiya Yarima Babba Ɗan Sarki,angon Gwaidayara.”

    Bayan kowacce ta fito tare da mijinta, sai iyayensu mata suka kama kuka da nadamar halin da Jummai da Halima da A’isha da ake so suka shiga a gidajen aurensu. Nan take suka ba mahaifiyar Gwaidayara haƙuri bisa matsa mata lamba da wulaƙancin da suka dinga yi mata a baya. Ita kuma ta ce ta yafe musu.

    Gwaidayara ta kawo tufafi da kayan abinci da abin zaman gari mai yawa ta ba ’yan’uwanta kowacce da mijinta, ta ƙara wa kishiyoyin uwar kayan tsaraba waɗanda ba su taɓa jin labarin irinsu ba, suka yi godiya. Daga nan kuma uban ya ce ba sauran a wulaƙanta kowa a gidansa. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Illar nuna bambanci da tsana ga ɗaya daga cikin ’ya’yan da mutum ya haifa.
    • Haƙuri da biyayya ga iyaye da jure wa ƙuntatawarsu abu ne mai kawo arziki da nasara a rayuwa.
    • Nuna wa yaro gatanci da shagwaɓa shi wata hanya ce ta lalacewa da talauci da shiga halin da-na-sani.
    • Allah ne kaɗai yake arzutawa kuma yake talauta wanda ya so.
    • Allah gatan kowa.
    • Mugun nufi ba ya kashe ɗan kurciya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar ’Yan Mata Biyu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ’Yan Mata Biyu

    Tatsuniyar ’Yan Mata Biyu

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wasu ’yan mata, ya da ƙanwa ne uwarsu ɗaya, ubansu ɗaya. Allah ya yi musu ƙira mai kyau, har ma wasu kan ce kyansu kamar na aljanu. Wata rana ƙaramar ta fita ƙofar gida tana rigar aya, sai wani mutum ya gifta ya gan ta ya yi mata sannu. Da ta amsa sai ya ce da ita: “Kin san kyan da kike da shi kuwa amma a ce wai ke ce kike rege aya?”

    Da ta ji haka sai mamaki ya kama ta, ta ce masa: “Ai da ka ga yayata da ba ka ce da ni kyakkyawa ba domin ta fi ni kyau nesa, ba kusa ba.” Kamar da wasa, sai wannan baƙo ya ce: “To kirawo ta mu gani.” Ta shiga ta gaya wa yayarta yadda suka yi da mutumin nan.

    Sai yayar ta ce: “Gaya masa ina aiki, ba zan sami damar fita wurinsa ba a yanzu.” Haka mutumin nan ya tafi. Jim kaɗan sai ya je ya rikiɗa, ya koma wani mutum daban, ya sake komowa, ya roƙi ƙanwar ta kirawo masa yayarta. Ta shiga ta gaya mata, suka fito tare.

    Baƙo ya ga tabbas; ya yarda da cewa yar ta fi ƙanwar kyau. Bayan sun gaisa, sai ya ce mata: “Na tura ƙanwarki ta kirawo ki ne domin in sanar da ke ina ƙaunarki.” Jin haka ya sa ta sunkuyar da kai saboda kunya tana murmushi ta ce: “To, na gode.” Shi kuma baƙon ya ce da ita: “Amma fa gidana a bayan gari yake, ina fata za ki yarda mu je ki gani.”

    Ba tare da musu ba kuma ta yarda. Amma kafin su tafi, sai ƙanwarta ta yi farat ta ce: “Ni ma zan bi ku, amma kafin mu tafi zan nemo izinin mahaifiyarmu tukuna.” Baƙon da yayarta suka ce: “To. Za mu je da ke, sai ki shiga ki gaya mata.” Bayan yarinyar ta gaya wa mahaifiyarsu kuma ta amince, sai suka kama hanya.

    Bayan sun ’yar tafiya ƙaramar ta yi tuntuɓe. Da ta gaya musu sai ta ji mutumin nan ya ce: “Idan jini ya fito zan shanye.” Sai ta ce: “A a, ai jini bai fito ba.” Haka dai suka ci gaba da tafiya, har suka isa gidan mutumin. Da isa sai suka lura ashe gidan an gina shi ne da gangar jikin mutum.

    Wannan fa ya sa su tsorata, amma dai suka danne tsoron. Ya buɗe ƙofa, suka shiga suka taɓa hira a gidan, sai ya rako su gida. Bai daɗe yana neman aure ba kuwa, aka ba shi ita, ta tare a gidansa, ƙanwarta kuma ta bi ta saboda ta riƙa taya ta aikin gida.

    Haka suka zauna kullum sai yayar ta kai wa mijin abinci, amma kuma ba ya cin abincin da suka kai masa da miyarsu, sai ya zubar da miyar, ya riƙa ci da jini. Ashe tsafi yake yi, yana tsotsar jinin ƙanwar matar ba a sani ba. Har wata rana yayar ta ce wa ƙanwar: “Kai amma kin rame.”

    Kanwar dai ba ta san abin da za ta ce ba. Ana nan kullum haka, har wata rana wata mata da ta ziyarce su ta ga mai gidan nan yana cin abincin da aka kai masa da jini. Sai ta je ta sami yayar yarinyar da ƙanwarta, ta gaya musu abin da ta ga mutumin nan yana yi, watau cin abinci da jini.

    Jin haka sai suka tambaye ta: “To, yaya za mu yi?” Sai ta ce: “Mu tona rami, mu sa ƙanwarki a ciki.” Da mutumin nan ya daina ganin ƙanwar matarsa ta kai abinci, sai ya tambayi matar: “Ni kuwa ina ƙanwarki ne? Na ga yanzu ba ta kawo mini abincina.” Sai ta ce: “Maigida, ai wannan yarinya ta tafi kallon wasa ne a ƙauyen kwaɗi.”

    Tun yana tambaya jefi-jefi, har ya zama a kullum sai ya tambaya. Kuma duk sanda ya tambaya sai ta ce: “Kanwata ta tafi kallon wasa.” Bayan ɗan wani lokaci sai ya ce da matar: “Ke ni fa zan je kauyen kwaɗin nan da kaina in dawo da ita.” Da ta ji haka sai ta ce: “To, ni ma ai na fi so ta dawo.

    Ka san ko banza tana taya ni aiki, kuma ita ke kawo maka abinci kullum.” Wata rana da mijin ya fita yawonsa, sai matar ta tura ƙanwarta gida, domin ta yi wa mahaifansu bayanin halin da suke ciki. Ta ƙara yi wa kanwar bayani da cewa: “Ki gaya musu za mu zo ganin gida tare da shi.

    Don haka ina son su haka rami mai zurfi, su haɗa wuta a ciki, ta ruru da kyau, sannan su rufe ramin da kirare; sai a yi shimfiɗa a kai, yadda idan ya zauna zai rifta cikin wutar, kowa ya huta da wannan aljanin mutum.” Iyayensu na jin wannan bayani, sai suka shirya duka yadda aka ce a yi.

    Mijin da matar suka shirya zuwa ganin gida, suka kama hanya. Suna isa gidan surukansa aka nuna masa shimfiɗarsa. Bai jima da zama ba ya fara jin ɗumi, sai ya tambaya: “Ina jin wani dumi-dumi, ko dai jikina ne?” Sai matar ta ce: “Lallai kam jikinka ne.” Kafin ta gama rufe baki, kiraren da aka rufe ramin da su, aka ɗora shimfiɗar da ya zauna a kai sun cinye.

    Nan take ya auka cikin ramin wutar nan ya ƙone ƙurmus, amma kuma sai ya tokarsa ta tsira ta zama bishiyar aduwa. Labarin yadda aduwar nan ta fito har ya kai kunnuwan Sarkin garin. Sai ya sa aka yi yekuwar, ya hana kowa shan ’ya’yan aduwar. Amma wata rana matan Sarki sun fita unguwa, sai suka riƙa cewa su sai sun sha ’ya’yanta, amma da wasa suke faɗi.

    To daman ɗaya daga cikin matan, tana da ciki, sai kwaɗayi irin na masu ciki ya sa ta tsinki ɗaya ta sha. Shanta ke da wuya sai bishiyar aduwar ta riƙa bin ta har ƙofar fadar Sarki. Sai aka gaya wa Sarki cewa ga fa aduwar nan ta biyo iyalinsa, har ma za ta shigar masa fada.

    Nan da nan Sarki ya shiga gida, ya tambayi matan yadda aka yi, suka yi masa bayani. Sai ya ce: “To, ba komai; za mu yi maganin wannan hatsabibin mutum, domin yana nema ya dami jama’ar ƙasata.” Sai Sarki ya umarci Sarkin baka ya magance wannan fitina.

    Nan da nan ya haɗa wani irin turare. Da hayaƙin turaren ya bugi bishiyar nan, sai ta narke kowa ya huta. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa 

    • Halin kirki shi ne abin duba ga mace ko namijin da za a aura ba kyau ba.
    • Hatsari ne a auri wanda ba a san asalinsa ba.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Nasiru Da Nisiru

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Nasiru Da Nisiru

    Tatsuniyar Nasiru Da Nisiru

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can ƙasar Mazarƙwaila an yi wani yaro ɗan Sarkin Zaƙi, mai suna Nasiru. Yana da wani aboki wai shi Nisiru. Ana kiran baban Nasiru Sarkin Zaƙi ne, domin ya fi kowa yin kayan zaƙi a garinsu. Shi Nisiru yakan je ya sami Nasiru su tafi cin zuma, watau su ƙona itace hayaƙi ya kori ƙudan zuma, su kuma su kwaso saƙarta da ruwan.

    Haka suke yi kullum. Ana nan, ana nan, sai mahaifiyar Nasiru ta rasu. Rasuwarta ke da wuya sai kishiyarta ta shiga ba Nasiru wuya. To amma ɗan kishiyar uwar mai suna Aliyu yana son Nasiru sosai; ba ya nuna masa ƙiyayya ko kaɗan. Wata rana sai Aliyu ya ce wa Nasiru da abokinsa: “Yau zan raka ku cin zuma.”

    Da Nasiru ya ji haka sai ya ce da shi: “Ni fa ina tsoro kada mahaifiyarka ta yi faɗa.” Sai Aliyu ya ce: “Ba komai, ba za ta yi faɗa ba sam-sam.” Daga ƙarshe dai Nasiru ya haƙura, ya amince zai je da Aliyu. Lokacin da Nasiru da Aliyu suke wannan maganar, ashe wata mata magulmaciya ta ji su, sai ta je ta sami uwar Aliyu ta ce da ita: “Kin ga Nasiru da abokinsa Nisiru za su ja ɗanki daji su halaka shi.”

    Uwar na jin haka sai ta ce da matar nan: “Yanzu yaya za mu yi?” Da ’yar zugar ta sami gangara, kawai sai ta ce: “Akwai wani hatsabibin boka wanda za mu je ya ba mu maganin da zai kashe Nasiru kawai mu huta.” Wannan shawara ta tsorata uwar Aliyu, sai ta ce: “A a, ni fa ina tsoron kashe mutum.”

    Sai matar nan mai ingiza kantu ruwa ta ce: “Idan ba ki kashe yaron nan ba sai ya fi ɗanki arziki domin yana da ƙashin arziki.” Uwar Aliyu na jin wannan gurguwar shawara, sai ta ce: “To, shi ke nan mu je.” Uwar Aliyu da mai zuga ta suka je gidan boka suka yi masa bayani. Nan take kuwa ya kawo magani ya ba su, ya ce su zuba a nono.

    Ya tabbatar musu idan Nasiru ya sha maganin to zai mutu. Suka dawo gida, uwar Aliyu ta dama fura da nonon da aka zuba wa magani, ta ajiye wa Nasiru ita a gindin randa, ta danta Aliyu kuma ta ɗora a kan randar. Nasiru da Aliyu suka shiga gida, aka nuna wa kowa furarsa.

    Nasiru ya ɗauko tasa daga gindin randa zai fara sha, sai ya ga uwar Aliyu ta sa shi a gaba tana yi masa fara’a, har da wasa da dariya. Ganin haka ya sa shi shan jinin jikinsa. Sai ya ce da ita zai koma waje ya sha. Da ya fita waje, sai ya sami wani ɗan akuya ya ba shi furar ’yar kaɗan. Shan ta ke da wuya sai nan take ɗan akuyan ya faɗi matacce.

    Nasiru na ganin haka, sai ya yi rami ya binne ragowar furar, ya kwanta nashe-nashe, kamar ya mutu. Jim kaɗan sai ga mahaifiyar Aliyu ta leƙo sai ta ga Nasiru a kwance kamar ya mutu. Ba ta san sanda ta yi subur da baka ba cikin murna ta ce: “Yawwa, madalla. Tun da aka haifi yaron nan nake neman yadda zan gama da shi, ban sami nasara ba sai yanzu.

    Ba shakka wannan boka hatsabibi ne, na gode masa.” Tana cikin wannan murna, idanunta a rufe, ta ɗauki Nasiru ta kai shi bayan gari ta jefar; ko tunanin a rufe gawarsa ba ta yi ba saboda tsananin ƙiyayya. Shi kuma Aliyu ɗan’uwan Nasiru sai ya nemi uwar ta gaya masa inda yake.

    Da ƙyar dai ta yi masa bayanin da ya gane cewa yana bayan gari, sai ya fita nemansa, ya ci sa’a kuma ya rera wata waƙa a kusa da inda aka jefar da shi:

    Nasiru, Nasiru, Nasiru,

    Nasiru ɗan Sarkin Zaƙi,

    Nasiru tashi mu je shan zaƙi.

    Nasiru ya bar duniya,

    Nasiru ya tafi lahira.”

    Duk da cewa Nasiru yana kusa da Aliyu, bai mayar masa da wannan waƙa ba. Sai Aliyu ya koma gida a cikin matsanancin tashin hankali. Har ma dai ya ce da uwar shi fa ba zai ji daɗin zaman duniya ba, muddin ba ya ganin Nasiru. Can kuma, abokin Nasiru shi ma ya shiga tashin hankali rashin ganin abokinsa.

    Shi kuma sai ya sami uwar Aliyu ya ce:

    “Mamayo, mamayo, mamayo,

    Nasiru ya bar duniya,

    Nasiru ya tafi lahira.

    Nasiru ya bar duniya,

    Ni mazantafi lahira.”

    Da uwar Aliyu ta ji wannan waƙa, sai ta ce da Nisiru: “Ina ruwana ka tafi gaba da lahira ma, duk ɗaya ne.” Zuciyarsa cike da baƙin ciki ya kama hanyar daji. Yana cikin tafiya sai ya ga wani mutum a zaune ya gama kai da gwiwa; sai ya matsa kusa da shi ya ce: “Bawan Allah me ya same ka haka?” Yana ɗago kansa, sai abokin nan nasa ya gane ashe wanda ya fito nema ne sai ya tsorata.

    Amma abokin nasa sai ya ce da shi: “Haba mutumina, kada ka ji tsoron komai. Ni ne Nasiru.” Hankalin Nisiru ya kwanta, suka sami wuri suka zauna. Bayan sun yi ’yar hira, sai suka yanke shawarar barin garin don gudun mugun halin uwar Aliyu. Sai suka koma wani gari mai babbar kasuwa da karkara mai dausayi, ga filayen noma nan sai an zaɓa.

    Da yake su duka muzakkarai ne, sai halin zaƙaƙurancinsu ya sa suka shiga neman abin kansu. Kafin shekara ta dawo kowannensu ya mallaki dukiyar da an jima ba a ga masu kamarta ba. Wata rana bayan kamar shekara biyar Nasiru da abokinsa suna cikin halin baƙunta a wani gari, sai suka yanke shawarar cewa ya kamata su je ganin gida.

    Nan da nan ko suka yi laftun dukiya suka ɗora wa raƙuma, suka tafi da ita garinsu. Nasiru ya tarar da uwar Aliyu tana cikin mummunan talauci, ga tsufa ya kama ta, ƙanensa Aliyu kuwa ba ya komai, sai baranta a gidan wani tajiri. Nan take Nasiru ya ba ta dukiya mai tarin yawa.

    Ta shiga cin daɗi, ba da daɗewa ba ta murmure. Ya kawo jari mai kauri ya ba ƙanensa Aliyu. Shi da abokinsa kuma suka shirya suka koma wurin sana’arsu. Duk sanda uwar Aliyu ta zauna, sai ta shiga tunanin ƙetar da ta shirya wa Nasiru, da kuma irin alherin da ya saka mata da shi, ta yi da-na-sani. Ta roƙi gafararsa, ya yafe mata. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Ba a rama alheri da mugunta.
    • Duk wanda ya daka ta magulmaci zai tsinci kansa a cikin nadama da dana-sani.
    • Mai hankali ba ya rama mugunta da sharri sai da alheri.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Marowata

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Marowata

    Tatsuniyar Marowata

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani mutum a wata ruga da ke gefen Dajin Ganji. Yana zaune tare da matarsa da ’ya’yansu biyu. Suna da matashin sa ɗaya. Wata rana mai gidan da matar suka yanke shawarar cewa ya kamata su yanka san nan su ci nama. To amma su marowata ne na ƙin ƙarawa.

    Sai suka shirya cewa za su je dawa su yanka san inda ko ƙuda ba za su bari ya taɓa naman ba. Da zuwansu dajin sai suka tsuguna, suka yi kashi. Nan da nan ƙudaje suka rufe kashin; sai suka bar wurin wannan kashi, suka je wani wurin daban suka yi wani kashin. Nan ma ƙudaje suka yi cincirindo a kan kashin.

    Da haka da haka har suka yi kashin da ba wani ƙudan da ya bi. Sai mai gidan ya ce: “To, a nan za mu yanka san nan.” Bayan sun yanka san tun kafin su feɗe shi, sai ga wani ƙaton Zaki ya zo, sai ya ce da su: “Kai, me kuke yi a nan?” Mai gida na jin haka sai ya ce da shi: “Mun yanka sa ne, to amma ba wutar da za mu gasa shi.”

    Da Zaki ya ji haka sai ya ce: “To ku sam mini naman.” Duk da irin zafin rowarsu, sai suka yankar wa Zaki naman suka ba shi. Amma maimakon Zakin nan ya yi musu godiya sai ya ce: “Ku ƙara mini zan yi muku wata waƙa mai daɗin gaske.” Tun ma kafin su ƙara masa, sai ya fara rera waƙa yana cewa:

    “Ɗan ƙanƙanen abin nan, dungum,

    Waburga-burga ne, dungum,

    Naburga a ɗanɗane ni, dungum.

    Aboki yana kiran aboki, dungum,

    Aboki yana kiran aboki, dungum.”

    Da Zaki ya gama waƙar, sai suka sake yankar masa nama suka ba shi. Sai suka ce ya sake yin waƙar su ƙara masa. Da haka da haka, har naman ya ƙare. Sai suka ce da shi: “Ka ƙara yi mana waƙa mu ba ka ɗanmu.” Ba ko tare da Zaki ya yi gardama ba, sai ya rera musu waƙa, suka miƙa masa ɗansu.

    Daga nan kuma suka ce ya ƙara yin waƙar, za su ba shi ’yarsu. Zaki kuwa ya rera musu har ma ta fi waƙoƙin da ya yi a ba ya daɗi. Yana gamawa suka danƙa masa ’yar maƙwabtansu da ta biyo su dajin saboda taya su aikin nama. Can sai mutumin ya dubi Zaki ya ce: “Ƙara yin waƙar nan in ba ka matar nan tawa.”

    Abu kamar wasa, Zaki ya yi waƙa, mai gida ya ba shi matarsa. Abu kamar wanda aka jefa, sai ya ce da shi: “Ka ƙara yi zan ba ka kaina.” Zaki sa’a ta samu; sai ya yi waƙar, mai gida kuma ya miƙa kansa ga Zaki. A taƙaice dai Zaki ya sami uwa da uba da ’ya’ya biyu da naman saniya; sai ya kai su gidansa ya ajiye, ya tafi neman itacen da zai dafa naman san nan.

    Kafin ya dawo mai gida ya kwashi iyalinsa da naman sansa sun gudu. Bayan mai gida da iyalinsa sun yi ’yar tafiya, sai ya tsaya ya ce zai ƙirga su, don ya tabbatar ba a bar kowa a gidan Zaki ba. To, idan ya taɓa matarsa sai ya ce: “Ɗaya.” Ya taɓa ɗansa ya ce: “Biyu.” Da ya taɓa ’yarsa ya ce: “Uku.” Sai ya manta da kansa, saboda haka lissafi bai tashi daidai ba.

    Haka ya dinga yin wannan shirme, har wani mutum ya zo, ya ga abin da ke faruwa, sai ya ce da mai gida: “Idan na samo maka cikon mutum na huɗu lissafi ya cika, me za ka ba ni?” Sai mai gida da matar baki ɗaya suka ce: “Duk abin da ka zaɓa daga cikin abubuwan da muke da su za a ba ka.” Sai ya ƙirga su lissafi ya cika daidai.

    Daga nan sai ya dubi mai gida da matarsa ya ce: “To, ku cika alƙawari.” Sai mai gida da matarsa da ’ya’yansu suka tuɓe takalmansu suka rife; mai gida ya gyara hularsa, matar ta yi ɗamara, ’ya’yan kowa ya shirya. Baki ɗayansu sai suka zura da gudu, suka bar mutumin yana mamaki, amma cikin raha, saboda ya ga gwanayen wauta. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mai hankali ba ya rama mugunta da sharri sai da alheri.
    • Son kai yakan jefa mai yin sa cikin haɗari.
    • Marowaci yana iya zama tamkar dabba har ma ya cuci kansa.
    • Karshen azzalumi da-na-sani.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Wani Mutum Da ‘Yarsa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Wani Mutum Da ‘Yarsa

    Tatsuniyar Wani Mutum Da ‘Yarsa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana wani mutum da ke garin Yamutsawa ya je gidan Sarkin garin ya ce yana so zai ba Sarkin ‘yarsa ya aura. Shi kuwa Sarkin Yamutsawa ya daɗe da matansa biyu. Da Sarki ya ji haka sai ya sanar da shi cewa ba zai ƙara aure ba, idan ma ya auri mace ta uku, to kuwa zai gille mata kai.

    Sai mutumin ya ce: “Na ji, na yarda ka aure ta ko za ka gille mata kan.” Shi kuma mutumin daman malami ne ɗanbaiwa. Shi ke nan, Sarki ya aure ta. Kamar yadda Sarki ya faɗa, washe-garin ranar da amarya ta yi kwanan farko a gidansa, sai ya sa aka fille mata kai. Amma kuma kullum idan an fille kanta jim kaɗan sai ga wani kan ya fito.

    Ana nan, sai matan Sarki biyu suka sami ciki, amma ita ba ta samu ba. Ganin haka sai uban amarya ya sauya mata kama ya umarce ta da ta bi Sarki lokacin da zai fita farauta. Sai ko ta sami juna biyu a wannan lokaci. Bayan ‘yan watanni ciki ya fito, Sarki ya tambaye ta: “A ina kika sami ciki?”

    Ba ta tsaya wata inda-inda ba sai kawai ta ce: “Kai ne ka yi min.” Shi kuma ya musanta. Amma sai ta yi masa bayani dalla-dalla cewa ai ta sauya kama ne sanda suka haɗu, lokacin da ya je farauta. Da Sarki ya ji haka sai ya ce: “Ai mai waɗancan kamannin da kika faɗa ta fi ki kyau.” Da ta ƙara yi masa bayani, sai ya amince lallai shi ne mai cikin.

    Bayan wani ɗan lokaci kuma, sai Sarki ya tara matan nan su uku ya ce: “Kowacce ta je ta haihu a gidansu.” Sai kowaccensu ta kwashe kayanta, ta tafi gidansu. Ba da daɗewa ba kuwa sai ɗaya daga cikinsu ta haifi Ɓera, ɗayar kuma ta haifi yaro Ƙadangare, ita kuma amarya ‘yar mallam, ta haifi ɗa kuma ya yi kama da ubansa, watau Sarki.

    To daman ita wadda ta haifi Ɓera ta haihu ne a cikin toka. Wadda ta haifi Ƙadangare kuma ta haihu ne a daji. Ita kuma ‘yar malami, ta haihu ne a gidan ubanta, shi ya sa ta haifi mutum. Bayan sun gama wanka, jikin kowacce ya yi ƙwari, sai kowacce ta koma ɗakinta, watau gidan Sarki.

    Bayan ‘yan kwanaki da komawar matan Sarki, sai ya ƙ kulawa da amaryar domin shi har yanzu bai yarda da cewa ita ce ta haifi yaron nan ba. Sai ya yanke shawarar cewa a kai yaron reno gidan danginsa, kuma kada ɗaya daga cikin matan ta sake ganin sa har sai ya girma sai a kawo shi ya nuna uwarsa da kansa.

    A kwana a tashi, yaro ya girma, sai Sarki ya sa aka tara mutanen garin domin su ga abin da zai faru. Ya sa matansa su uku suka fito, ya tura a zo da ɗan. Yaro ya zo a kan Doki. Manufar taron dai ita ce yaron ya fidda wadda ta haife shi daga cikin matan Sarki. Sai kawai aka ji ya kama wannan waka: ”

    Wace ce uwata?

    Tambaya nake, Wace ce gyatuma ta?

    Wace ce iyata, wo-wo.

    Ina kara tambaya, Wace ce mahaifiya ta?”

    Sai matar Sarki wadda ta haihu a daji ta karɓi waƙa:

    “Ga ni, ga ni, ni ce, ɗana,

    Ga ni, ni ce mahaifiyarka,Ya kai ɗana.

    Ga ni, ni ce gyatumarka, wo-wo,

    Zo in rungume ka, Ya kai dana.”

    Da yaron ya ji bayanin da ta yi masa a cikin waƙar, kuma bai gamsu ba, sai ya rera wata waƙar yana cewa: “A a, a ina kika haife ni? Gaya mini, a ina kika haife ni? Aina kika haife ni, wo-wo?”

    Da mutanen gari da Sarki sai duk suka yi shiru, suna jira su ji abin da za ta ce, ko zai tabbatar ita ce uwarsa, ko kuma ba haka ba ne. Sai ta kashe murya wadda ta fi ta da zaƙi tana cewa: “Ai a daji na haife ka, A Dajin Ƙarangiya na haife ka. Kai Yarima, Ai a daji na haife ka, Ni a daji na haife ka, wo-wo.”

    Ba tare da wani ɓata lokaci ba, sai kawai ya ce: “Je ki gaba, Ki yi gaba, Ba ke ce mahaifiya ta ba. Je gaba,Ba ke ce mahaifiya ta ba Wo-wo, Ba ke ce mahaifiyata ba.” Haka ta kare, ta wuce tana jin haushi. Wadda ta haihu a toka ma ta zo, ita ma ya ce ba ita ce uwarsa ba.

    Da aka zo kan mahaifiyarsa, wadda ita ce ta ƙarshe da ta faɗi inda ta haife shi, sai ya yi wani gwauron tsalle don murna har sai da ya shallake rimin da ke kusa da fada. Jama’a ma suka ɓarke da sowa, sai ɗan Sarki ya je ya rungume uwarsa don murna. Shi kuma Sarki saboda jin haushin matansa sun yi masa ƙarya dangane da haihuwar magajinsa, sai ya sa aka fiffille musu kawuna.

    Ya sa aka raba ƙasarsa biyu. Shi ya ci gaba da mulkin rabi daga fadarsa, ɗaya rabin kuma ya mallaka wa ɗan. Malamin nan kuma uban matar Sarki ya riga ya tsufa. Jikansa ɗan Sarki kuma ya gina masa gida a ɓangaren ƙasar da uban ya mallaka masa. Labarin wannan abin mamaki ya wuce garin Yamutsawa domin ya gama ko’ina a garuruwan da suke kusa da shi. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wajibi ne shugaba ya yi kyakkyawan bincike kafin ya zartar da kowane hukunci don ya kauce wa yin kuskure.
    • Son zuciya ɓacin zuciya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Biri Da Kare

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Biri Da Kare

    Tatsuniyar Biri Da Kare

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Kare yana yawo a cikin gari, sai ya haɗu da Biri. Sai Biri ya tambaye shi inda za shi, ya ce: “Ina yawo ne ko zan sami ɗan abin da zan ci.” Shi ma Kare ya tambayi Biri inda za shi, ya ce: “Ai ni kullum a daji nake wuni, in ci abinci in ƙoshi.” Biri ya ce da shi: “Ko za ka bi ni ne?” Kare ya ce: “Ni ban taɓa zuwa daji ba.”

    Daga nan Biri ya tambayi Kare: “Shin kai ma kana da wayo irin nawa?” Kare ya mayar da jawabi da cewa: “Wayona goma ne.” Biri ya ce: “Ka ga ni wayona ɗaya ne, amma kullum a daji nake wuni, ballantana kai babba mai wayo goma, shi ne ka zauna a gida? Haba, kada ka ba ni kunya mana.” Sai Kare ya ce: “To, bari in shirya mu tafi.”

    Biri da Kare suka kama hanyar daji. Suna cikin tafiya sai suka isa wani lambu. Ba tare da ɓata lokaci ba, Biri ya tsallake shingen lambu, ya dinga cin kayan marmari, sai da ya ƙoshi. Kare kuwa yana jin yunwa amma tun da ba ya cin kayan lambu sai ya ce: “Kai Biri ni fa yunwa nake ji.” Biri ya ce: “To, shi ke nan mu je gaba, ko ma sami abin da za ka ci.” Haka suka ci gaba da tafiya.

    Can sai Kare ya hango wata jaɓa ta fito daga rami; sai ya bi ta, ya kama ya cinye ya ce da Biri: “Yanzu kam na ɗan sami ƙarfi, mu ƙara gaba.”Suka ci gaba da tafiya. Can sai suka hango ‘ya’yan Kura su biyu, sai Kare ya ce wa Biri: “Kai ni fa zan koma na ga ‘ya’yan Kura.” Biri ya ji haka, kuma ya gane Kare ya tsorata, sai ya ce masa: “Haba, kada ka ba ni kunya mana.

    Yanzu da girmanka kake tsoron ‘ya’yan Kura?” Sai Kare ya ɗaure suka ci gaba da tafiya. Da ‘ya’yan Kura suka ga Biri da Kare, sai ɗaya daga cikinsu ya ce da ɗayan: “Je ka kira iya, ka ce mata ga nama ya zo har guda biyu.” Ɗan Kurar ya sami uwarsu a rami ya ce mata: “Iya, mun ga nama har biyu suna yawo.” Nan take Kura ta yaƙe baki, yawu ya zubo, ta yi miƙa, ta tambayi ɗan ta ce: “Me da me kuka gani?”

    Ya ce: “Biri da Kare.” Da ta ji haka sai ta ce: “Ka je ka kira ɗan’uwanka ku dawo gida.” Sai ya fita da gudu ya kira shi suka koma rami, uwarsu ta ce: “Ku je ku hura wutar da za mu dafa namansu idan sun zo.” Nan da nan’ya’yan Kura suka samo itace, suka hura wuta. Shi kuma Biri sai ya ce wa Kare ya raka shi zuwa wurin abokinsa.

    Sai suka tafi, ba su tsaya ko’ina ba sai bakin ramin Kura sai ya ce: “Bari in shiga ka jira ni a nan.” Biri ya shiga, ya gai da Kura, kuma ya ce: “Yau na zo tare da wani amini na ne domin mu gaishe ki.” Da Kura ta ji haka sai ta yi murna, Biri kuma ya leƙa, ya kirawo Kare. Da ya shiga ya ga Kura a tsugune, sai nan take ya faɗi a sume.

    Biri kuma da ya ga haka sai ya yayyafa masa ruwa, ya farfaɗo. Da Kare kuma ya lura an hura wuta, sai ya sake ƙifewa, ya ƙara suma. A nan ma dai Biri ya sake ta da shi ya ce da shi: “Ka je ka taya su hura wuta.”Da Kare ya je ya hura wuta sai ya riƙa yin waƙa yana cewa: “Biri ya kawo ni gidan mutuwa, Biri ya kawo ni wurin halaka, Da Biri ya ji haka, kuma ya tabbatar Kura ma ta ji, sai ya ce: “Kai Kare ba ka iya hura wuta ba; ba ni ka gani.”

    Da Biri ya karɓi hura wuta, sai ya kama wannan waƙa: “Na kashe Kura tara, Yau zan kashe ta goma, Ni da Kare mu sha nama, Na hura wutar dafa Kura ta goma, Yau zan kashe Kura ta goma.” Da Kura ta ji haka sai tsoro ya kama ta; sai ta ce: “To, ashe sun zo kashe ni ne?” Sai wata dabara ta faɗo mata, yadda za ta gudu tare da ‘ya’yanta.

    Sai ta kira ‘ya’yanta ta ce: “Ku je ramin kawuna ku gani ko ya dawo daga farauta. Maza ku dawo ku gaya mini fa; kada ku tsaya wasa a hanya.” Da suka fita suka ɗan daɗe, sai Kura ta ce: “Biri, ka ga fa yaran nan sun daɗe, bari in bi sawunsu in gani ko sun tsaya wasa a hanya.” Kura na fita ta hango ‘ya’yanta suna dawowa, sai ta yi sauri ta sha gabansu ta ce su gudu, idan ba haka ba Kare da Biri za su kashe su.

    Da Kare da Biri suka gane abin da ya faru, sai suka fito daga ramin Kura suka ci gaba da neman abincinsu; ba sauran wani tsoro kuma, domin Biri ya yi wayo ya kori Kura da dabara. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Girman kai rawanin tsiya.
    • Durƙusa wa wada ba kasawa ba ne, ba ya hana ka tashi da tsawonka.
    • Ƙarfin hali da juriya suna karya gwiwar abokin gaba kome ƙarfinsa.
    • Haɗama da rashin godiya ga Allah sukan sa a yi da-na-sani.
    • Igiya ba ta ɗaure kaya, sai dabara.
    • Banza ta kori wofi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta tatsuniyar Ɗan Kutungayya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Arɗo Da Ndoffiwa

    Tatsuniyar Arɗo Da Ndoffiwa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wani makiyayi wai shi Arɗo a can kusa da wani baƙin daji da ake kira Dajin Gafiya. Yana zaune da matarsa ɗaya, wai ita Hodanego. Shi Arɗo kullum yakan yini a daji ne wurin kiwo, amma ita matarsa ta ha’ince shi, domin tana da kwarto mai suna Ndoffiwa.

    Kullum idan mijinta ya tafi kiwo, sai ta kama kaza daga cikin kajin gidan ta yanka wa kwartonta, ta shirya abinci mai daɗi su ci tare. Ana nan, wannan abu yana tafiya, har dai wata rana wata maƙwabciyar Arɗo ta kira shi ta ce da shi: “A gaskiya Arɗo duk lokacin da ka tafi kiwo sai matarka ta kira kwartonta, ta kama kajinka ta ɗebi hatsinka ta yi abinci, su ci tare.

    Idan kana son ka kama su, ka yi kamar ka tafi kiwo, sai ka dawo jim kaɗan ka gani.” Sai Arɗo ya amince da shawarar. Rannan sai ya yi yadda ya saba, ya fita kamar ya tafi kiwo, amma sai ya laɓe a gidan maƙwabciyar nan tasa, ya shiga fako. Can sai ya ga matarsa ta kama kazarsa ɗaya ta yanka ta gyara ta kuma ɗora girki sai ƙamshin daɗi ke tashi.

    Da ta gama abinci, ta zuba a akusa, ta rufe da faifai ta ɗauka ta fita, ta kama hanyar gidan kwarton nan tiryan-tiryan, ba tsoro, ba shakka. Sai da ta ɗan yi nisa, sai ya bi ta a baya. Ba ta tsaya ko’ina ba sai gidan kwartonta; amma ta tarar ba ya gida. Arɗo kuma yana daga inda ya raɓe ya ga ta shiga, ta ajiye abincin ta fita daga gidan, amma shi Arɗo sai ya laɓe, har sai da ta yi nisa.

    Sai ya je ya shiga gidan, ya zarce har ɗakin da ta ajiye abincin, ya zauna ya cinye shi kakaf. Daga nan sai ya ɗauki akushin tuwon, ya yi kashi a ciki ya kuma ɗauki akushin miya ya yi fitsari a ciki, shi ma ya rufe, ya sai kai ya yi tafiyarsa.Shi kuwa Ndoffiwa ashe wurin hirarsa ya je.

    Da suka gama hira, sai ya gayyaci abokansa su je cin abinci a gidansa. Duk da cewa ba shi da mace, ya tabbatar kwartuwarsa za ta kai abinci. Suka shiga gida, ya ɗauko akusa. Yana buɗe akushin tuwo, sai ya ga tsibin kashi. Da ya buɗe akushin miya kuma, sai ya ga fitsari; zarnin fitsarin da ɗoyin kashin suka buge shi tare da abokansa.

    Kamar sun haɗa baki, sai suka ce: “Ka gayyato mu gidanka domin ka wulaƙanta mu shi ya sa ka ba mu kashi ko? Lallai ka cika mara kunya.” Haka a fusace suka fice, suka bar shi. Shi kuma kwarto sai ya shirya a zuciyarsa zai kawo wata kwartuwar, domin ya ɓata wa Hodanego rai saboda ta kai masa kashi da fitsari a madadin abinci.

    Sai ya tafi wajen wata kwartuwar. Bai jima da fita ba, Hodanego ta koma gidansa ɗibar akusa. Da ta ɗaga, sai ta ji da ɗan nauyi sai ta ɗaga faifan da ke kai domin ta ga ko bai ci abincin ba ne. Tana buɗewa sai ga wani gandareren kashi, wanda ya kume ɗakin da ɗoyi. Wannan abu ya baƙanta mata rai.

    Sai ta fusata, baƙin ciki ya kama ta. A cikin zuciyarta ta ce: “Amma Ndoffiwa ba shi da mutunci. Na kawo masa abinci a mutunce, amma kuma ya saka mini da kashi da fitsari a akusa? Bari zan yi maganinsa.” Nan take ta juye kashin nan da fitsari a kan gadonsa. Ta sa kai ta yi tafiyarta.

    Ba da daɗewa ba, Ndoffiwa ya koma gidansa tare da sabuwar kwartuwarsa. Da suka shiga ɗaki ta zauna a kan gado, sai ta ji alamar laima, sai ta taɓa da hannunta, ta ji. Nan da nan ta gane ashe kashi ne. Nan take ta miƙe a fusace, ta shiga ƙwala wa Ndoffiwa ashariya, ta ce ashe shi ƙazami ne.

    Ta zazzage shi ta more, sai ta kaɗe zanenta, ta fita daga ɗakin, ta bar gidan. Da fitarta, sai ya kwashe kayan ɗakinsa ya wanke. A cikin daren nan kuma Arɗo ya zagaya inda ya yi shanya, ya kwashe kayan. Sai ya kai su rafi ya zuba, suka bi ruwa. Da gari ya waye Ndoffiwa ya je kwaso shanya, amma bai ga ko bante ba.

    Baƙin ciki ya cika shi, sai ya yanke shawarar ya bunƙa wa ɗakinsa wuta; gobara ta tashi ya yi kururuwa, mutane suka taru aka kashe gobara. Wani ya kawo wani tsumman riga ya ba shi. Da ya sa rigar, kuma ya lura hankalin mutane na wajen kashe gobara sai kawai ya sulale, ya bar garin. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Aure ba wasa ba ne; dole a kiyaye ƙa’idojinsa ko kuma a yi da-na-sani.
    • Abin kunya kan sa mutum garinsu ya gagare shi zama.
    • Rama cuta ga macuci ibada ne.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Marainiya Mai Turmi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Janniya

    Tatsuniyar Janniya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata mata mai ɗa wai shi Janniya. Suna zaune ita da kishiyarta tare da mijinsu cikin lumana. Wannan mata kuma tana da garken shanu. Bijimin da ke cikin shanun kuma yakan yi magana kamar mutum. Ana nan, ana nan, wata rana uwar Janniya da kishiyarta suna zaune suna taɗi, sai ta ce da kishiyar: “Ina jin fa na kusa mutuwa. Idan na mutu ki kula da Janniya.”

    Da kishiyar ta ji haka sai ta ce: “Haba! Ai ko ba ki faɗa ba ma zan kula da shi, ai ɗana ne.” Sai uwar Janniya ta ce: “To, na gode da kika yi wannan alwashi.” Bayan kamar kwana huɗu da yin wannan zance, sai uwar Janniya ta ce ga garinku nan! Ita kuwa kishiyar sai ta mallaki shanun da uwar Janniya ta bari.

    Suna nan, kullum sai ta zuba wa Janniya magunguna na asiri iri-iri a cikin abincinsa. To amma duk sanda Janniya ya zo cin abincin, sai wannan bijimin sa ya gaya masa, kuma ya hana shi ci. Sai ya rinƙa rera waka yana cewa:

    “Janniya Jannati,

    Janniya Jannati.

    Kishiyar uwa Janniya, Jannati, Janniya,

    Ba uwabace Janniya Jannati.

    In za ta ba ka tuwo,

    Tuwo damagani, Janniya Jannati.

    In ta ba ka, Janniya Jannati,

    Ka tona rami, Janniya Jannati,

    Agindin turkena, Janniya Jannati.

    Ka binne tuwon, Janniya Jannati.

    Kar ka ci, Janniya.”

    Kullum haka, amma duk da rashin cin abinci kamar yadda ya kamata, wannan bai sa Janniya ya rame ba. Yau da gobe sai kishiyar uwar ta gane wannan san ne ke tona mata asiri, sai ta matsa wa mijinta ya amince a yanka san nan mai magana. Shi kuma san duk ya ji abin da aka shirya, sai ya ce da Janniya: “Idan an yanka ni, ka ce a ba ka kai da ƙafafuwana da kayan ciki.

    Sai ka binne su. Yin haka zai karya duk wani makaru da za ta yi maka.” Shi ke nan da aka yanka sa, sai Janniya ya roƙi a ba shi duk waɗannan abubuwan. Aka ba shi, shi ko ya je ya binne. Sai kishiyar uwar ta ci gaba da ba shi sammu iri-iri, to amma saboda ya yi abin da san nan ya faɗa, sai duk makarun da take yi ba wanda ya kama shi.

    Kullum sai haske yake ƙarawa, ita kuma baƙin ciki na damunta. Wani Falke ya ce, baƙin ciki kan kashe irin waɗannan mutane. Haka ko aka yi. Ta ci gaba da lalacewa, har dai a ƙarshe bakin ciki ya kashe ta. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Duk wanda yace zai canza hukuncin Allah ƙarshensa nadama da halaka.
    • Mugun nufi ba ya kashe ɗan kurciya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Maharbi Da Zaki

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Maharbi Da Zaki

    Tatsuniyar Maharbi Da Zaki

    Ga ta nan, ga ta nan ku.

    An yi wani maharbi da ke gefen Dajin Shiddar, a can yamma da ƙasar Sarkin aljanu. Wata rana ya fita farauta a daji, sai ya ga wani rami, bai yi wata-wata ba sai ya kutsa kai ya shiga. Ashe ramin nan na Zaki ne. Zaki ko na ganin sa sai ya yo kansa. Mutumin nan ya fito ya kama gudu, har ya fita daga dajin ya shiga karkara.

    Zaki dai na bin sa, har ya tarar da wani manomi, ya ce da shi: “Mai gida ka taimake ni.” Manomin ya ce: “Me ya koro ka haka?” A cikin tsoro da ɗimuwa maharbin nan ya ce: “Zaki ne, Manyan Dawa. Sai manomin ya ce: “A gaskiya tun da Zaki ne ya fafaro ka, abin ya fi karfina; ba zan iya taimaka ma ba.”

    Da ya ji haka, sai ya ci gaba da gudu. Har dai ya tarar da wani manomin a wata gonar yana tiƙar aiki. Shi ma sai ya ce da shi: “Don girman Allah ka taimake ni mana, Zaki ne ya biyo ni zai kashe ni.” Shi ma dai wannan manomi ya gaya wa maharbi ba zai iya taimakon sa ba, domin Zaki ya fi ƙarfinsa.

    Sai maharbin nan ya ci gaba da gudu, har ya tarar da Gizo. Shi ma ya yi masa bayani cewa Zaki ne yake bin sa zai kashe, kuma yana son taimakonsa. Sai Gizo ya yarda zai taimake shi. Nan da nan ya kama shi, ya jefa shi cikin yanar da ya saka. Can sai ga Zakin nan ya tunkaro a guje.

    Sai ya tsaya ya tambayi Gizo ko ya ga wani maharbi? Gizo ya ce bai gani ba. Sai Zaki ya fusata, ya ce da Gizo: “To, idan ba ka gan shi ba, kai zan cinye ka.” Kamar da wasa, sai ya kai wa Gizo wawura. To, da man ɓangaren yanar Gizon da Zakin ya auka wa yana da dafi, yanar kuma tana da ƙwarin da ko Zaki ba zai iya tsinka ta ba.

    Yanar ta dabaibaye Zaki, dafin jikinta kuma yana daɗa raunana shi. Tausayin Zaki ya kama maharbin nan da Gizo, har suka fara yin ƙoƙarin kuɓutar da shi; to amma saboda dafin yanar nan da kuma shaƙe wuyan Zaki da yanar ta yi, kafin su gama warware yanar har rai ya yi halinsa.

    Su kuma manoman da maharbi ya roƙa su taimake shi suka ki, tsegumi ya sa sun biyo bayan Zaki domin su ga yadda zai kashe maharbin nan. Amma da suka isa inda Gizo yake, suka tarar da yanarsa da dafin da ke jikinta, sun halaka Zaki, kuma ga maharbi garau, sai mamaki ya kama su.

    Saboda borin kunya, sai ɗaya daga cikinsu ya ce: “Da man ina da niyyar taimakon ka, amma ba ka tsaya ba. Na san kuwa shi Gizo da ya taimake ka, bai fi ni kirki ba.” Sai baki daya suka fashe da dariya, suka fara haƙa ramin da za su binne Zaki don gudun kada ya yi wa Gizo ɗoyi a mazauninsa. Kurunkus.

    Abubuwan DaLabarin Yake Koyarwa

    • Rashin kyakkyawan tunani kafin aikata abu yakan jefa mutum cikin halin ƙaƙa-naka-yi.
    • Taimakon Allah yana iya zuwa ta inda ba a zata ba.
    • Kowa ya ɗebo da zafi,

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kurege Da Kura

    Tatsuniyar Kurege Da Kura

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Kurege da ƙawarsa Kura suka fita farauta. Suna cikin tafiya, sai suka tarar da inda hanya ta rabu biyu. Hanyar da ta yi dama, doguwa ce, wadda ta yi hagu kuma gajeriya. Sai Kurege ya ce da Kura: “Tun da ke ce babba, sai ki bi doguwar hanyar, watau ta dama, ni kuma ƙarami in bi gajeriyar, wadda ta yi hagun.”

    Kura ta ce: “A a, kai ƙarami ka bi babbar hanya, ni zan bi ƙaramar.” Sai ya ce: “To, shi ke nan mu tafi.” Kowa ya kama hanyarsa. Kura da ta bi gajeriyar hanya ba ta sami komai ba, sai wani ɗan ƙanzo. Da lokacin da za su haɗu ya matso, sai ta je inda suka shirya za su haɗu da Kurege, ta tsuguna tana jira.

    Shi kuwa Kurege mai doguwar hanya, sai ya yi ta tafiya har ya gaji. Sai ya sami inuwar wata bishiya ya zauna yana hutawa. Da sanyin inuwa ya ratsa shi, sai ya ce: “Kai, amma wannan inuwada daɗi take.” Sai kawai ya ji bishiya ta ce: “Ai ma sai ka ɗanɗana ganyena ka ji irin daɗinsa!” Sai Kurege ya tsinki ganyen bishiyar nan ya sa a baki ya tauna.

    Sai ya ce: “Kai, amma wannan ganye da daɗi yake!” Sai bishiya ta ƙara da cewa: “Ai don ma ba ka ɗanɗana cikina ka ji ba?” Sai Kurege ya tambaye ta ya ce: “Yaya zan yi in ɗanɗana cikinki?” Sai ta ce: “Idan kana so ka shiga cikina sai ka ce: ‘Buɗe bus’ sai ka shiga.

    Idan ka ce: ‘Rufe kif’ bayan ka sha zumar, za ta rufe.” Kurege ya yi godiya, ya matsa kusa da bishiya ya ce: “Buɗe bus.”Tana jin haka sai ta tsage, Kurege ya shiga ya tarar da zuma ya zauna ya sha, har ta yi masa karo. Ya ɗebi wata kuma ya cika jakarsa. Da ya fito daga cikin kogon bishiya, sai ya ce: “Rufe kif.”

    Sai bishiya ta rufe, ya yi godiya, ya kama hanyar zuwa inda suka shirya za su haɗu da Kura. Da ya isa inda suka yi alƙawarin haɗuwa da Kura sai ya tarar da ita tana barci. Ya shure ta, ta farka. Sai ta gan shi yana tanɗar baki, alamun ya ci daɗi, ta tambaye shi, “Kai, me ka samo ne mai daɗi haka?”

    A cikin yanga da burga, Kurege ya ce da Kura: “Na samo wani abu ne mai daɗi, ke kuma fa?” Cikin nadama da mairairaita ta ce: “Ni kam ban samo komai ba sai wani ɗan kanzo. Yunwa ma nake ji. Ɗan ba ni abin da ka samo in ɗanɗana mana.” Sai ya ce: “Idan na ba ki a cikin jaka, za ki cinye har da jakar, amma bari in dangwalo miki.”

    Kurege ya sa tsinke ya dangwalo zuma, ya miƙa wa Kura; ta karɓa ta sa a baki sai ta lumshe idanu da zaƙin zuma ya ratsa ta; sai ta cinye har da tsinken. Nan take fa sai kwaɗayinta ya motsa, ta ce da Kurege: “Gaya mini inda ka samo wannan zuma mai daɗi domin ni ma in je in samo.” Sai ya yi mata kwatancen bishiyar da ta ba shi zuma; Kura ta kama hanya.

    Da ta isa ko hutawa ba ta yi ba, sai kawai ta tsunki ganyen bishiya ta sa a bakinta. Sai daɗi ya sa ta ce: “Amma wannan ganye da daɗi yake.” Da bishiya ta ji haka sai ta ce: “Ai wannan ma kaɗan ne, ba ki ɗanɗana abin da ke cikina ba.” Kura ba tare da ta tambayi yadda ake shiga cikin bishiyar ba, sai kawai ta ce: “Buɗe cikin in shiga in ci daɗin da kika faɗa.”

    Nan take bishiya ta buɗe wa Kura cikinta, ta shiga ta fara warwason zuma, tana sha. Da daɗin zuma ya kwashe Kura sai ta fara wannan waƙar: “Buɗe bus, Rufe kif, Mu sha zaƙi, Kurege ba wayo, Nafi shi shan zuma, Zuma mai daɗi, Ke bishiya rufe kif.” Sai ko bishiya ta rufe.

    Bayan wani ɗan lokaci sai ta ce da Kura: “Ki yi maza ki gama, masu ɗakin nan fa sun kusa dawowa.” Amma saboda wauta irin ta Kura, sai ta ce da bishiya: “Ba komai ko sun zo, ai ina da ƙarfin da zan kore su. Idan sun gan ni ma za su gudu.” Sai ta ci gaba da shan zuma. Ta sha ta ƙoshi, amma kuma ta mance abin da za ta faɗa ƙofa ta buɗe.

    Tana cikin wannan hali ne fa kudan zuma suka dawo daga cin furanni. Suna shiga saƙarsu da ke cikin kogon bishiya suka tarar da Kura; nan take suka far mata da harbi, tana kuka da kugi irin wanda aka san ta da shi. Ta ruɗe, ta rinƙa cewa: “Kif, bishiya kif” maimakon ta ce: “Bus.” Can dai ta yi sa’a ta ce: “Buɗe bus.”

    Bishiya ta buɗe, Kura ta fito da ƙyar, duk jikinta ya kumbura saboda harbin zumar da ta sha; sai ta kama gudu, tana haɗawa da waiwaye, ta doshi inda Kurege ke jiranta. Da Kura ta matsa kusa Kurege ya ga yadda jikinta ya zama, sai ya nemi sanin abin da ya faru.

    Sai ta kwashe labari ta gaya masa; shi kuma ya ce da ita: “Kin cika mantuwa.”Haka dai Kura ta koma gida tana jinya.Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Rashin yin abu da kyakkyawar niyya shi yake sa yin nadama.
    • Yin abu da zuciya ɗaya zai kawo taimakon Allah.
    • Haɗama da rashin godiya ga Allah sukan sa a yi da-na-sani.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Tatsuniyar Sarkin Maƙera Da Dodo

    Edita@rumasau-kallamu