Tag: tatsuniya

  • Tatsuniyar Gizo Da Kura

    Tatsuniyar Gizo Da Kura

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Gizo ne yana yawonsa sai ya tarar da tarin kashi a wani wuri. Bai tsaya ba, ya tsallake ya yi tafiyarsa. Jim kaɗan sai Kura ta bi ta wurin, ita ma ta ga kashin, sai ta kama da ci, kuma ta ji kashin yana da daɗi, sai ta ce: “Lallai duk wanda ya yi kashin nan, namansa zai zama mai daɗin gaske.”

    Nan fa ta yanke shawara a kan sai ta gano wanda ya yi kashin. Saboda haka ta hau wani kututture ta shiga jira. Ta daɗe amma ba ta ga kowa ba. Haka ta haƙura; a cikin fushi ta kama hanyar barin wurin. Tana cikin tafiya sai ta ga wani tarin kashin a ƙarƙashin wata bishiya.

    Wannan kashi ya tayar mata da kwaɗayi; nan take dai ta cinye shi sarai. Ta yi gaba, sai kuma ga wani kashin. Shi ma ta cinye shi duka. Haka dai ta dinga tarar da kashi tsibi-tsibi tana cinyewa, ba ta rage ko kaɗan ba. Amma har yanzu tana mamakin wanda yake yin sa, saboda haka sai ta sake hawa wani kututture mai tudu tana jira.

    Nan ma ba ta ga kowa ba. Ganin haka, sai ta sake dabara, ta tona rami ta shiga fako. Nan ma ba ta ga komai ba. Daga nan sai ta buɗe bakinta, wai komai kashin ya zo ya shiga ciki ta cinye shi. Ba ta jima da bakinta a buɗe ba, sai Gizo ya je ya yi kashi, kashin kuma ya faɗa bakinta.

    Ta ji kashin Gizo da daɗi ta ce: “Ashe da man Gizo ne ke yin wannan kashi. Ko ina yakan sami naman da yakan ci ya sa kashinsa ya yi daɗi haka?” Kura dai ta ga gara ta ci gaba da fakon Gizo, sai ta sake hawa sama, ta shiga jiran komawarsa. Shiru, shiru. Gizo bai je ba sai washegari.

    Ya sake zuba kashi; yana gama yi sai Kura ta sauka ta yi kansa. Ta kama shi ta riƙe gam-gam; sai ta tambaye shi inda yake samun naman da yake ci. Da fari Gizo ya ce ba zai gaya wa Kura ba don yana tsoron kada a kashe shi idan ya faɗa. Kura ta ce: “Ko ka gaya mini ko kuma in kashe ka.”

    Saboda tsoro, sai Gizo ya ce: “To, za mu yi alƙawari a yau kawai. Wato zan gaya miki.” Kura ta amince; suka kama hanya Gizo ya kai ta inda yake samun naman. Da zuwansu wurin sai ya ce: “Buɗe, buɗe, buɗe.” Sai wata ƙofa ta buɗe, suka shiga. A ciki sai ga gwafanni da sanduna a kafe an rataye nama ba iyaka a jikinsu.

    Da shigarsu sai Gizo ya ce: “Rufe, rufe, rufe.” Nan take ƙofa ta rufe. Da yake masu tsaron ƙofar sun saba ganin Gizo, ba su hana su ba, kuma ba su nemi sanin abin da ya kawo su ba. Gizo ya kwaso nama da yawa ya ba Kura, ta ci, ta yi guzurin wani mai yawa. Daga nan suka fita, suka kama hanyar gida.

    Da dawowarsu gida Kura ta shiga tunanin komawa wurin naman nan ita kaɗai. Bayan kamar mako guda sai ta sami labarin Sarki ya tafi rangadi. Sai ta sami ’yar rakiya daga cikin danginta bisa cewa za su je ziyara ne. Suka kama hanya har suka isa inda suka je cin nama tare da Gizo.

    Ta yi irin maganar da ta ji Gizo ya yi a wancan lokaci: “Buɗe, buɗe, buɗe.” Sai ƙofa ta buɗe. Suka shiga, suka ci nama har suka ƙoshi, suka lafci wanda za su tafi da shi
    gida, sun ga banza ta faɗi. Ba da dadewa ba Sarki ya dawo daga rangadi. Ya tarar
    naman da ya yi tanadi ya ragu ƙwarai.

    Ya tambayi masu tsaro, amma suka kasa yin bayani mai gamsarwa. Sarki ya sa aka tara mutanen garin duka. Ya gaya musu ya yi alƙawari duk wanda ya gaya masa wanda ya sace masa nama zai aura masa ’yarsa. Gizo ya san masu gadi kan iya tona masa asiri, sai yace ya san wanda ya yi ɓarnar.

    Fadawa suka ce ya faɗa. Nan da nan ya nemi izini, aka ba shi domin ya je ya zo da wanda ya yi wannan ta’adi. Bai zame ko’ina ba sai a ƙofar ramin Kura. Da ya tambaya aka ce ta yi tafiya, sai ya ce: “Kash, ashe ba za ta sami irin naman da Sarki yake ba jama’ar da ya tara a fada ba kenan.

    Idan ta dawo a gaya mata ta je fada Sarki zai yi rabon nama mai yawa.” Da jin haka sai Kura ta fito daga inda ta ɓuya ta ce: “Gani. Ba inda na je. Mu tafi in sami rabona.” Suka fita. Ba su tsaya ba sai a fada. Da isarsu ’yan tsaron nama suka ce: “Ba shakka, Kura ce ta cinye naman Sarki.”

    Kafin ta farga, tuni an hau ta da bugu. Da aka kai ta ƙarshe, sai aka farke cikinta. Hanji da tumbi da uwar kashi da tubura da huhu da zuciya da kashi, duk suka zuba. Kura dai a taƙaice nan ta mutu. Sarki kuwa dama mai jan girmansa ne. Nan take ya cika alƙawari, watau Gizo ya zama surukinsa. Suka yi zamansu lafiya. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Iya gani iya ƙyalewa.
    • Alƙawari kaya ne.
    • Mai rabon shan bugu, ba ya jin kwaɓa.
    • Kowa ya daka rawar wani, ya rasa turmin daka tasa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Tasalla Mai Kifi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kwaɗayi Mabuɗin Wahala

    Tatsuniyar Kwaɗayi Mabuɗin Wahala

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana mutuwa ta je wani ƙauye da saniya da ta turke, tana neman wanda zai sayi wannan saniya a ƙauyen. Mutane suka tsorata baki ɗaya suka ƙi. Can Gizo ya dubi mutuwa ya ce shi yana so. Suka yi yarjejeniya a kan baɗi Mutuwa za ta dawo ta yanke kunnuwan Gizo.

    Wato kunnuwan sun zama kamar da su zai biya saniyar. Nan da nan sai Gizo ya yanka saniyar shi da matarsa Koƙi suka dafa, suka ci, suka ƙoshi. Da shekara ta kewayo sai ga Mutuwa ta zo fansar bashi. Ta fara cigiyar wanda ya sayi saniyarta. Ta shiga gari tana cigiya, har ta kai gidan Gizo.

    Gizo na nan amma kuma ya gaya wa matarsa Koƙi ta gayawa Mutuwa cewa ya yi tafiya. Amma kuma ya ɓuya ne a cikin ramar da aka shuka a tsakar gidan. Saboda haka da Mutuwa ta tambaya sai Koƙi ta gaya mata cewa ai mijinta ya yi wata doguwar tafiya bai
    dawo ba. Mutuwa ta yi mamakin jin haka, ta ce: “Yaya Gizo zai yi tafiya bayan kuwa mun yi alkawari a kan yau ne lokacin haɗuwarmu?”

    Saboda haka sai Mutuwa ta tuna da wata dabara wadda za ta yi ta kama Gizo. Sai ta tafi kasuwa ta sayo ganga ta zo gidan Gizo ta yi ta kaɗawa tana waka, tana cewa:

    “Ina Gizo, Koki ina Gizo?”

    Koƙi ta fito ta nanata cewa: “Ai maigidana ya yi tafiya yau da wata uku bai dawo ba.” Mutuwa ta san Gizo yana da wayo. Saboda haka ta cewa Koƙi: “Kin ga kuwa Gizo ya tafka asara. In da yana nan zan ba shi wata saniyar ne. Da mun yi haka din sai in tafi in dawo baɗi in karbi kunnuwa biyu.”

    Koƙi dai ta zauna a kan cewa maigidanta ya yi tafiya. Amma da Gizo ya ji zancen Mutuwa za ta ba shi wata saniyar, sai kwatsam ya fito yana cewa: “Ai ga ni nan; rabu da Koƙi, ƙarya take; ina nan.” Da fitowar Gizo sai Mutuwa ta kama shi ta yanke kunnuwansa. Ta kuwa yanke su a gurguje ta yanda Gizo bai san kowane ne ya yi masa wannan shigar sauri ba.

    Ya ma zaci ko Mutuwa ce ta turo ɗanta ya yi wannan aiki. Har yau an ce Gizo na can ƙauyen yana jinyar yanke masa kunnuwa da Mutuwa ta yi. Duk mutanen gari suka yi ta yi wa Gizo dariya da ba’a suna cewa: “Ai ga irinta nan. Kwaɗayi mabudin wahala.” A taƙaice dai, ba wanda ke tausaya wa Gizo a kan abinda ya same shi. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Alƙawari kaya ne.
    • A halin zaman duniya ya kamata mutum ya tsaya ga magana guda don yawan canza magana yakan zubar da mutunci.
    • Kowa ya ci ladan kuturu, ya yi masa aiki.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Yelwa Da Tsohuwa Da Sarki

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Yelwa Da Tsohuwa Da Sarki

    Tatsuniyar Yelwa Da Tsohuwa Da Sarki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wata yarinya mai suna Yelwa. Tana da ƙawaye da yawa. Wata rana Sarkin garinsu ya umurci ‘yan matan garin su je rafi, su kamo kifi bisa sharaɗin cewa duk wadda ta kamo ta yi masa miya mafi daɗi, ita zai aura. Da man sauran ‘yan matan sun tsani Yelwa.

    Saboda haka bayan sun kamo kifi sai suka haɗa baki suka jefa ta a cikin kogin ta nutse. Da farko har ruwan zai tafi da ita, to amma ta yi sa’a, wata tsohuwa ta zo ta tsamo ta. Wannan tsohuwa kuwa tana da baiwa. Yelwa kuma ta kwashe labarin duk abin da ya faru ta gaya mata. NantTsohuwar nan ta ji tausayinta.

    Nan da nan ta kama wani ƙaramin kifi ta ba ta, kuma ta ba ta wata ‘yar tukunya, ta ce mata ta sa wannan kifi a cikin tukunyar ta rufe, ta kiwata shi. Washe-gari da Yelwa ta buɗe tukunyar sai ta ga wani babban kifi a ciki. Ta yi mamakin yadda kifin ya girma haka. Ta kama kifin ta dafa, ta ɗauka ta nufi fada.

    Kafin ta je an soma biki har an rufe ƙofa. Ta roƙi dogarai suka buɗe mata, ta shiga. Kafin zuwanta Sarki ya riga ya ɗanɗana dukkan miyar da ‘yan matan suka kai, amma babu wadda ya gamsu da ita. Saboda haka da Yelwa ta kai tata miyar, Sarki bai so ya ɗanɗana ta ba, sai da tsohuwar nan ta matsa kusa da shi ta raɗa masa cewa ya taɓa.

    Sarki ya taɓa ya ji miyar Yelwa zaƙi cakwai, abin ba dama. Ba da ɓata lokaci ba washe-gari Sarki ya bayyana mata buƙatarsa ta aurenta. Yace in ta yarda ta je ta shaida wa iyayenta a ɗaura musu aure nan da kwana biyu Yelwa ta tafi tana kuka saboda baƙin cikin maraici, domin tuni mahaifanta suka mutu.

    Ta fara batun zuci tana cewa: “Kaito, yaya zan yi da raina yanzu, ga ni ba ni da iyaye.” Can sai ta kama waƙa tana cewa:

    “Ke tsohuwa mai ceto,

    Ke tsohuwa mai baiwa,

    Sarki na so ya aure ni.

    Ke tsohuwa mai ceto,

    Sarki yana so ya aure ni,

    Amma ga shi ba ni da iyaye,

    Yaya zan yi a halin yanzu?”

    Can sai ga tsohuwar ta bayyana, ta ce mata ta daina kuka, kar ta damu, komai zai yi kyau. Ta umurce ta da ta je ta samo ƙwari biyu ta kawo mata. Da ta kawo sai tsohuwar ta mai da su mutane, mace da namiji, wato sun zama iyayen Yelwa ke nan. Daga nan suka tasam ma fada, aka ɗaura aure.

    Nan fa sai ƙawayen Yelwa suka ji kunya, suka nemi gafararta. Yelwa kuma ta yafe musu saboda halinta na haƙuri. Ita da ƙawayen suka zauna lafiya, har kowaccensu ta yi nata auren. Sai dai akwai ɗaya daga cikin ƙawayen mai mugun hali. Ba ta daina jin haushin rasa auren Sarki ba.

    Saboda ƙyashi da hassada, sai ta shiga ƙulle-ƙulle da haɗa husuma domin ta kashe wa Yelwa aure. Ba abin da take so a duniya kamar ta ga auren Yelwa da Sarki ya mutu. Wata rana ta kama hanya ta je fada da nufin kashe Yelwa, amma ba ta yi nasara ba. Dogarai suka kama ta.

    Duk da cewa ta so kashe Yelwa, amma ita ba ta so a hukunta muguwar ƙawar nan tata ba. Ta roƙi mijin a ƙyale ta domin ƙila ta gyara halinta. Sarki ya yarda, ya kuma tara mutanensa kaf ya shaida musu matuƙar ƙaunar da ke tsakaninsa da Yelwa. Ya tabbatar musu har ita kanta cewa a ko da yaushe iya ransa zai yi duk abin da ya dace don ya kyautata zama da soyayyar da ke tsakaninsu. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Taimakon Allah yana samun bawansa ta hanyoyi daban-dabaninda bai zata ba.
    • Yafe wa wanda ya musguna maka wani alheri ne da zai sa mai laifin ya canza halinsa nan gaba.
    • Rabo dangi ajali.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Tatsuniyar Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku

    Tatsuniyar Tsohuwa Da ‘Yan Mata Uku

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wata tsohuwa mai ‘ya’ya uku mata. Sannu a hankali suka girma, har suka kai munzalin aure. Saboda haka ta ce da kowaccensu ta fid da mijin aure. Nan da nan Allah ya ba kowacce wanda za ta aura. Suka yi aurensu, kowacce ta tare a gidan mijinta a garuruwa daban-daban.

    Bayan ‘yan kwanaki kaɗan, sai tsohuwa ta ce ya kamata ta ziyarci kowacce a gidanta a garuruwan da suke. Ta fara da zuwa garin ‘yarta ta fari ta tarar kusan dukkan mutanen garin kowa maye ne. Ga shi kuma suna da jela da kunnuwa dogaye, kamar dodanni. Ta tambayi inda gidan ‘yarta yake. Mutane suka kwatanta mata.

    Da ta je gidan ‘yarta ta karɓe ta a cikin murna matuƙa. Ita ma ‘yar ta zama mayya, tana kuma da wutsiya da dogayen kunnuwa. Sai uwar ta tsorata. Ko da yake an karɓe ta da fara’a, ta yi tunanin cewa ya kamata ta koma garinsu da wuri. Ba da sanin uwar ba ashe ‘yar da mijinta sun shirya a kan za su cinye ta cikin daren.

    Da dare ya yi sai suka saɗaɗa cikin ɗakin da suka saukar da ita a ɓoye, amma suka tarar ba ta yi barci ba. Sai suka koma a kan cewa washe-gari za su ƙara yin ƙoƙari ko za
    su same ta ta yi barci. Ita kuma ganin haka sai ta shirya da sassafe za ta gudu ta bar garin. Gari yana wayewa, ko ban kwana ma ba ta yi da su ba, ta kama hanya.

    Ta shiga dajin Allah tana ta hanzari ba ta tsaya ba sai gidan ‘yarta ta biyu. Ita ma wannan ‘yar ta karɓe ta da murna ƙwarai, sai dai ta gaya wa uwar cewa a ƙauyen idan dare ya yi sukan rikiɗa su zama fari, su je su kwana a kan wata bishiya. Uwar ta ce ba ta damu ba, za ta bi su.

    Da dare ya yi dukkan mutane suka koma bayan gari suka rikiɗa, suka zama fari. Suka ɗunguma gaba ɗaya sai kan itacen da suka saba kwana. Tsohuwa dai ba ta bi su ba, ta zauna ita kaɗai a gida. Ba a daɗe ba hadari ya taso, aka yi ruwan sama mai yawa, ta jiƙe sarai. Da gari ya waye sai ta bar wannan garin ta nufi ‘yarta ta uku.

    Da ta je garin sai ta tarar mutanen suna soya naman shanu. ‘Yarta ta karɓe ta da hannu bibbiyu. Sun ɗan sammata naman amma da gargaɗin cewa kar ta cika cikinta domin a garin ba a ƙashi da fitsari. ‘Yar ta ce in fa ta karya dokar to Sarkinsu zai sa a kashe ta. Uwar ta yi banza da gargaɗin; ta ci naman sai da ta ƙoshi.

    Can cikin dare ta ta-da ‘yarta a kan cewa tana so ta je bayan gari. ‘Yar ta ce: “To, ba ga abin da na gaya miki ba. Daman na gaya miki abin da ke faruwa a garin.” Ba da ɓata lokaci ba ta ɗauki uwar ta kai ta bayan gari. Da gari ya waye sai mutanen garin suka dinga jin wari ta ko’ina, suka je suka shaida wa Sarki.

    Sarki ya ce lalle akwai wani baƙo da ya shigo garin. Da ‘yar ta ji haka sai ta yi maza ta ɗauke mahaifiyarta, ta raka ta har sai da ta bar garin. Sarki ya aika a nemo ta, amma ba su gan ta ba. Ta riga ta gudu. Tsohuwa tana kan hanyar komawa gida ne ta gamu da wani mutum. Bayan sun gaisa sai ta tambaye shi ko zai ci naman da ta yo guzurinsa.

    Ta ce da mutumin idan ya ci naman ya je garin ya yi kashi, zai sami wata kyauta. Mutumin kuwa ya karɓi naman ya ci. Da ya je garin ya yi kashi sai aka kama shi. A maimakon a ba shi wani abin arziki sai suka kashe shi a zaton shi ne ya yi kashin nan na kwanan baya. Ita kuma tsohuwa ta koma ƙauyenta lami lafiya. Ta ɗauki
    alƙawari cewa ba za ta ƙara karambanin zuwa ziyarar ‘ya’yanta ba. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Wajibi ne ga baƙo ya saurari gargaɗin masu masaukinsa.
    • Kowane tsuntsu, kukan gidansu yake yi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Dogarawa Uku

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ɗantsintuwa

    Tatsuniyar Ɗantsintuwa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata mata da mijinta, suna zaune a wani ɗan kauye. Sun daɗe tare, to amma Allah bai ba su haihuwa ba. Wata rana matar nan ta je gona, sai ta tarar da jinjiri a kan dutse, sai ta ɗauko. Ashe wannan yaro ba mutum ba ne, ɗan aljani ne, ba ta sani ba.

    Sai ta kawo yaron gida. Da mijin ya ga yaro, sai ya tambaye ta inda ta samo shi. Sai ta ce, ai ɗan tsintuwa ne, sai mijin ya ce, anya wannan mutum ne kuwa? Sai matar ta ce ai da ma ta san zai ƙi amincewa da yaron. Don gudun zuciyar matarsa, sai ya ce: “To, shi ke nan na yarda mutum ne, kuma ki riƙe shi.” Suka ci gaba da renon yaron.

    To, matar kullum tana zuwa gona da yaron. Daga ƙarshe dai ta samo yarinyar da za ta riƙa yi mata reno a gidan idan ta tafi gona. Kullum idan za ta tafi sai ta dafa musu abinci. To, da zarar ta tafi gona ta bar su da mai renon, sai ya rikiɗa ya zama babba ya kama yarinyar nan ya ɗaure, ya cinye abincin duka ya hana ta, ya yi ta wasanni iri-iri da rawa.

    Sai ya lura matar nan ta kusa dawowa daga gona, sai ya kunce mai renonsa ya koma yaro, ya yi ta birgima a ƙasa yana kuka. Idan iyayen sun dawo sai su hau kan mai reno da duka. Idan za ta yi magana ko bayani, sai su ce ta yi shiru, domin su a ganinsu yaron yana kuka ne saboda ta hana shi abinci, kuma tana dukan sa, har yana birgima.

    Kullum haka, sai wata rana wata tsohuwa maƙwabciyarsu ba ta je gona ba. Tana ɗaure dangarta, sai ta hango ɗan jariri ya miƙe, ya ɗauko igiya ya ɗaure mai renonsa, ya fara waƙa, yana rawa. Ya kuma cinye abinci duka, ya hana ta, tana ɗaure. Haka tsohuwa ta yi ta leƙen su, har yamma ta yi.

    Sai ta ga ya koma yaro, ya kama birgima, yana kuka, har iyayen suka dawo. Washe-gari sai tsohuwa ta yi kiran masu gidan, ta zana musu duk abin da ta gani. Ta ce idan sun shirya za su gona, su je gidanta su ɓuya, za su ga duk abin da yake yi. Sai suka amince. Washe-gari, suka shirya tafiya gona, amma sai suka shiga gidan tsohuwa suka ɓuya.

    Can sai yaron ya fara yin abin da ya saba, suna gani, abin ya fara ba su mamaki, har ya gama. Da suka dawo gida, sai suka ƙi dukan mai reno, shi kuma sai ya ƙi barin kuka. Sai matar ta shirya, ta tafi gidan boka, ta yi masa bayani.

    Sai boka ya ce, idan ta je gida washe-gari da safe ta sayo ɗan akuya ƙosasshe, ita da mijin su ja shi su yi ta tafiya, sai sun ga wata babbar bishiyar kuka. Ya ƙarasa da cewa: “Sai ku ajiye yaron, ku ce za ku huta. Sai ku ɗaure ɗan akuyan. Sai mijinki ya ce zai je ya yi fitsari, sai ya gudu. Ke kuma, sai ki ce za ki dubo shi, sai ki bi shi, kada ku juya”.

    Sai suka amince. Da gari ya waye, sai suka je suka samo ɗan akuya ƙosasshe, suka ɗaura igiya a wuyansa. Sai suka ce za su je wani ƙauye gaisuwa, sai matar ta ɗauki yaro ta goya, suka kama hanyar daji. Suna cikin tafiya, sai suka hango wannan babbar kuka, sai mijin ya ce su je su huta a gindinta.

    Da suka je, sai suka yi duk yadda bokan nan ya ce su yi, watau suka yi dabara, suka gudu. Da suka isa gida, sai tsohuwar ta sami matar ta ce to daga yau ta daina ƙwadayin sai ta sami ɗa ta kowace hanya, kuma ta rungumi ƙaddara sai abin da Allah ya yi da ita a rayuwarta.

    Da ɗan aljani ya gaji da jira, ya ga shiru, sai ya miƙe ya kunce ɗan akuya, ya riƙe, ya kama hanyarsa, ya shiga ƙungurmin daji, bai sake komawa gidan mutanen nan ba. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Zafin nema ba ya kawo samu.
    • Yi haƙuri da godiya ga abin da Allah ya ƙaddara a rayuwarka ta duniya.
    • Tsintacciyar mage ba ta yin kyanwa
    • Son zuciya, ɓacin zuciya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Ɓarayin Albagadadi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ɓarayin Albagadadi

    Tatsuniyar Ɓarayin Albagadadi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani attajiri a wani gari ana kiran sa Albagadadi. Ba abin da yake so kamar ya ji wani yana neman taimako, domin ya taimaka masa. Duk ranar Jumma’a mutane kan taru maƙil a ƙofar gidansa, suna karɓar sadaka.

    Ana nan, ana nan, wata rana sai wani saurayi ya je wajensa ya ce masa yana son masauki, ko ya sami aikin yi a garin. Sai Albagadadi ya sauke shi a gidansa. Sannu a hankali, sai yaron nan ya zama hadiminsa, watau ya riƙa yi masa aikace-aikacensa na gida. Yaron kuma makarancin Alkur’ani ne sosai.

    Kullum idan Albagadadi zai je unguwa, ko dai wani wuri, to tare za su. Sai mutane suka sa wa yaron suna Sheikh Ali Albagadadi. Tun da yaron nan ya shiga gidan Albagadadi, sai komai nasa ya sauya; arziƙin uban gidansa ya yi ta bunƙasa. Duk abin da ya saya, ko gonar da ya noma, sai riba ta riɓanya ta da.

    Wata rana Albagadadi ya zauna tare da abokansa, sai ya kira Sheikh Ali ya ce yana son duk wanda yake wurin ya ba shi wani labari da zai faranta masa rai, zuciyarsa ta kwanta. Sai Sheikh Ali ya ce: “Wanda duk ya yalwata wa wanda ke cikin matsi, to shi ma Allah zai yalwata masa duniya da lahira.

    Wanda ya rufa asirin wani a yayin da yake buƙatar rufin asiri, to shi ma Allah zai rufa masa asiri duniya da lahira. Kuma duk wanda ya ba da sadaka tamkar wanda ya yi shuka ne, domin idan aka shuka masara kwaya uku, za katarar ta tsiro fiye da dubu uku. Kamar haka ne Allah yake saka wa masukyauta.”

    Duk wurin aka yi tsit ana jin bayaninsa. Sai ya ci gaba da cewa: “Ita sadaka takan gusar da bala’i da masifa, ta karya maƙiyi da Shaiɗan, kamar yadda ruwa yake kashe wuta, kuma ta goge zunubin mutum.” Kafin Sheikh Ali ya gama zancensa mai amfani, sai ya ga hawaye na kwarara daga idanun Albagadadi.

    Ganin haka sai ya dakatar da maganarsa. Rannan suna gida da daddare, sai suka ji muryar mutane a cikin gida. Ashe ɓarayi ne riƙe da makamai suka dira gidan da nufin yin sata, to amma ba sa iya ganin komai a cikin gidan. Can dai Ali Albagadadi ya yi tari, kuma tarinsa sai ya fasa ɓarayin, suka runtuma da gudu.

    A garin gudu, ɗaya ɓarawon ya faɗa rijiya, wuyansa ya karye. Na biyun kuma ya faɗa wani gida a kan wani dutse mai kaifi, shi ma ya mutu. Na ukunsu da ya samu ya fita bayan gari yana gudun ’yan bin sawu, sai ya yi ƙundunbala ya faɗa a kan wani kwazazzabo da yake zato tafki ne.

    A nan take shi ma ya sheƙa lahira. Da gari ya ƙarasa wayewa, jama’a suka daɗa taruwa, sai aka ɗebi ɓarayin nan aka binne su a rami. Mutanen garin suka yi ta mamakin yadda ɓarayin nan ba su saci komai a gidan Albagadadi ba, kuma sai suka riƙa cewa Allah ne ya kare shi saboda taimakon da yake yi wa mutane.

    Wannan kariya da Allah ya ba Albagadadi daga muguwar aniyar ɓarayi ce sanadiyyar da mutanen garin idan za su nemi tsari daga maƙiyansu sukan ce: “Kamar mutuwar ɓarayin Albagadadi.” Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Ladabi da biyayya kan jawo arziƙi.
    • Mai arziƙin da ke tallafa wa mabuƙata Allah ne zai kare shi ya daɗa bunƙasa arziƙinsa.
    • Kyauta sadaka ba sa tauye arziƙin kowa.
    • Aikata alheri ga kowa, sakayya na wurin Allah.
    • Sadaka maganin asara.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Ƙuda Mai Kwaɗayi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ƙuda Mai Kwaɗayi

    Tatsuniyar Ƙuda Mai Kwaɗayi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata ƙuda da ’ya’yanta. Kullum sukan je mahauta a kasuwa neman abin da za su ci, idan sun ƙoshi su koma gida. Wata rana sai ƙudar ta ja ƙawarta suka je mahautar neman abinci tare.

    Bayan sun samo, sai suka kama hanyar gida domin ita mai ’ya’yan ta kai musu gida, ta yi wa ƙananan cikinsu ƙoto. A kan hanyar komawa sai suka gamu da wani mai zuma. Sai ƙudar ta ba ƙawarta ƙunshin abincin da ta samo wa ’ya’yan ta kai musu, saboda za ta bi mai zuma ko ta kalato musu zumar.

    Kawarta ta karɓi jaka ta nufo gida, ta ba yara; sai babbar cikin ’ya’yan ta tambayi inda mahaifiyarsu ta tafi. Kawar ta ce mata ta bar gyatumarsu a kasuwa, wurin mai zuma. Ko da ta ji haka, sai ta kama kuka ta ce ai kwanan uwarsu ya ƙare, tun da ta bi mai zuma.

    Sai yarinyar da ƙawar uwarta suka yanke shawarar gara su je kasuwar su gani ko za su taho da ita. Sai suka hangi mai zuma, suka leƙa jikin ƙwaryarsa, sai suka gan ta a manne cikin sakar zuma, ta mutu.

    A nan duk suka fashe da kuka, suka tashi fir, ba su tsaya ba sai gidansu. Da suka ba da labarin rasuwarta, sai aka shiga zaman juyayi. Duk inda kuka ga ƙudaje sun taru cunkus, to zaman juyayin suke yi. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kwaɗayi mabudin wahala.
    • Garin neman gira, an ya da ido.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Auta Da Dodanniya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Auta Da Dodanniya

    Tatsuniyar Auta Da Dodanniya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani gari wai shi Shadafi. Mutanen wannan garin koyaushe suna zaune cikin tsoro, saboda wata dodanniya da takan cinye duk wanda ya fita waje daga faɗuwar rana har gari ya waye. Ana nan, ana nan, sai dodanniyar nan ta lura takan zagaye garin baki ɗaya ba tare da ta sami wanda za ta cinye ba.

    Sai ta dinga yi wa kanta kirari tana cewa:

    “Wa zai iya da ni,

    Ni dodanniya,

    Wa zai ja da ni,

    Ni dodanniya.”

    Kowa ya yi shiru, ba wanda ya taɓa tanka mata, ko da sau ɗaya. Kwanci tashi, sai kawai wata rana wani baƙon saurayi ana kiran sa Auta ya je garin yawo. Da ya nemi masauki, sai kowa ya ki saukar da shi a duk faɗin garin, sai can dai wani tsoho ya ce masa zai ba shi masauki a wani gidansa da ba kowa a ciki, idan ba ya jin tsoro.

    Sai saurayi ya ce wa tsoho shi ba ya fita hira. Sai tsoho ya ce da shi to kada ya fita da daddare, domin idan ya fita, to tasa ta kare, saboda ƙila dodanniyar nan da ta addabi garin ta cinye shi. Saurayi ya yi murmushi, ya dubi tsoho ya ce: “Ba abin da zai sami mutum wanda Allah bai nufa ba.”

    Tsoho ya raka shi masaukinsa. Suka yi sallama tsoho ya koma gida, ya bar shi. Ko da suka rabu sai Auta ya zaro wata doguwar wuƙarsa ta farauta ya wasa, ta yi kaifi. Daga nan ya ɗauko wata ƙatuwar fitila, ya ajiye. Can cikin tsakiyar dare, sai ga dodanniya ta fito tana cewa wa zai iya ja da ita a garin nan, “Wa zai iya bugawa da ni, ni dodanniya?”

    Da Auta ya ji, sai ya kunna fitila, ya ajiye a daf da bakin ƙofa, ya ɗauko wuƙa ya riƙe a hannu. Sai ya kare inda zai tsaya da wani tsumma don kar fitila ta haska shi. Sai ya buɗe kofa, ya dubi inda dodanniya take, ya ce mata: “Ga ni, ni ne Auta, ni zan iya ja da ke; kuma in tsiya ce, har ma na fi ki.”

    Kafin ka ce kwabo ta zo da gudu, buguzum-buguzum, wai kar ya gudu ta rasa nama. To da man ido ɗaya ne da ita, kuma sai ta karkata kai ta leƙa ɗakin da idon da ke gani. Ba ta ga Auta ba saboda yana cikin duhu, haske kuma ya kashe mata idonta mai rai. Tana sa kai, sai ya sa wuƙarsa mai kaifin gaske ya cake idon mai kyau.

    Zafin dafi da kaifin sihirtacciyar wuƙar farautar nan ya kama ta; ta kiɗime, ta yi wani namijin ƙarajin da ya cika gari. Iskar bakinta ta karya dangar karan gidan da ɗan Auta ke ciki. A nan take muguwar ta faɗi, ta shiga birgima. Can sai ta yi wani irin gwauron numfashi, na fitar rai. Haka dai ta mimmiƙe a mace.

    Da gogan naka ya ga ta mutu, ba ta sauran motsi, sai ya tuɓe takalminsa ɗaya, ya ɗora a kan mushen muguwar. Ya shiga ɗaki, ya garƙe ƙofa, ya kwanta ramuwar barci.Da gari ya waye, rana ta daga kowa ya fito a garin sai ya ga dodanniya shirim, ba su san ta mutu ba. Duk wanda ya gan ta kwance sai ya gudu gidan Sarki ya ba shi labari.

    Daga bisani Sarki ya fito, ya je ya ga dodanniya a mace, ga wuƙa an caka a idonta, ga kuma takalmi ƙafa ɗaya a kan ruwan cikinta. Sai Sarki ya ce duk mutumin da ya zo da irin wannan takalmin, to shi ya kashe ta. Aka nemi gano ko wane ne, amma aka rasa saboda Auta yana ɗaki yana biyan bashin barci.

    Can hayaniyar jama’a ta sa ya farka, kuma da ya gane abin da ake yi, sai ya fito da ɗaya takalmin; ya je kan mushen dodanniyar, ya zare wuƙar da ya caka mata a ido; ya goge jinin jikinta, ya zaro kuben wukar, ya sa ta a ciki. Daga nan sai ya shiga masaukinsa, ya ɗauko jakarsa zai tafi.

    Duk abubuwan nan da ya yi, har ya gama bai ce wa kowa komai ba. A nan ne fa Sarki ya kira shi, ya tambaye shi daga inda ya fito ya zo garin nan, domin sun jima suna wahala saboda dodanniyar nan, ba tare da sun san da jarumi kamarsa a garin ba. Auta ya ce wa Sarki da mutanen garin su gode wa Allah da tsohon da ya ba shi wurin kwana, domin da bai ba shi ba, da ya bar garin ya wuce.

    Sai Sarki ya ce su tafi gida. Da suka isa, Sarki ya yi masa kyauta mai yawa; ya raba garin biyu ya ba shi rabi, kuma ya naɗa shi Sarkin yaƙin ƙasarsa. Auta ya zama babban jarumi wanda, a dalilinsa aka sami zaman lafiya da walwala a garin.

    Yanzu haka ma duk da ya tsufa, masana kan ce ya fi Iliya Ɗan Maiƙarfi iya yaƙi. Wasu kuma suka ce da kaɗan Sarkin Yaƙi Ganɗoki ya fi Auta gwaninta da jiƙuwa da magunguna. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Alheri danƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa banza.
    • Zaman duniya cuɗe ni in cuɗe ka ne.
    • Komai ya wuyato akwai maganinsa.
    • A karɓi baƙo da mutunci saboda gobe.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Samarin Ɓarayi Uku

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Muwa Muwa

    Tatsuniyar Muwa Muwa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can wani daji an yi wata raƙumar dawa mai suna Muwa. Ba ta da ɗa ko ɗaya. Kullum in ta dawo daga kiwo, sai ta yi ta kuka saboda rashin haihuwar nan. Cikin ikon Allah rannan sai ta haifi ‘ya’ya huɗu. Saboda murna ta raɗa wa babban cikinsu suna Muwa Muwa, mai bi masa kuma Caccikarimba, na ukunsu kuma Malaladumba.

    Amma sai ta ƙi raɗa wa na huɗun suna, don ya fito a rame, ba ta son sa. Saboda yawan son ‘ya’yanta nata uku, sai ta gina musu ɗaki, ta saka su don kada ruwa da ƙura su taɓa su, amma sai ta bar ƙaramin a waje, ko ya mutu, ko ya yi rai, babu ruwanta.

    Kuma sai ta ce wa ‘ya’yanta ukun: “Idan kun ji muryata, ku buɗe ƙofa; idan ba muryata ba ce, to kada ku buɗe.” Kullum idan ta dawo daga kiwo sai ta ce: “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.” Sai su fito su sha, su koma.

    Wata rana, Kura ta zo wucewa sai ta ji raƙumar nan tana cewa: “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.” Sai suka fito suka sha, suka koma. Bayan uwarsu ta tafi, sai Kura ta zo bakin ƙofar da ƙatuwar murya mara daɗi ta ce:

    “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.” Sai yaran suka yi ihu, suka ce: “Ba muryar mahaifiyarmu ba ce.” Sai wannan abu ya sa Kura ta ji haushi ta bar wurin, tun kafin raƙumar ta koma wajen ‘ya’yanta.

    Kura na tafiya sai ta haɗu da wani Biri mai ba da magani. Sai ta ce idan dai gaskiya ne yana ba da magani, to ya mayar da muryarta kamar ta raƙumar dawar nan. Sai Biri ya nuna mata yin haka abu ne mai sauƙi a gare shi, amma da sharaɗin ba za ta ci komai a hanya ba, domin idan ta ci, muryarta za ta koma kamar da.

    Kura ta ce ta yarda. Sai Biri ya ba ta magani, da ta yi magana sai ta ji muryar kamar ta Muwa. Kura ba ta doshi ko’ina ba, sai wurin ‘ya’yan Muwa. Daga zuwanta sai ta ce: “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.”

    Sai suka buɗe ƙofa, sai Kura ta yi wuf ta cinye su, ta tafi abinta. Ashe ƙaramin da uwar ba ta so, watau ramammen nan, yana ganin ta. Can da raƙumar ta dawo ɗakin ‘ya’yanta sai ta yi kamar yadda ta saba: “Muwa, Muwa zo ka sha, Caccikarimba zo ka sha, Malaladumba zo ka sha.”

    Sai da ƙaramin ya bari ta gama kiran su baki ɗaya, sai ya dube ta ya ce:”Muwa, Muwa ba ya nan, Caccikarimba ba ya nan, Malaladumba ba ya nan.” Sai uwar ta ce: “To, kai ɗin ma zo ka sha.” Sai ya je ya sha nononta, kuma daga wannan rana ta shiga son sa, har ya zamana in za ta fita kiwo sai su fita tare. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Bai kamata a nuna bambanci tsakanin ‘ya’ya ba, domin Allah kaɗai ya san mai amfani cikinsu.
    • Wuya maficiya ce.
    • Mai rabon ganin baɗi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.
    • Bora ya koma mowa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Abotar Biri Da Kifi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Abotar Biri Da Kifi

    Tatsuniyar Abotar Biri Da Kifi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani Biri da kullum yakan je rafi wanka, bayan ya gama yawon cin ‘ya’yan itatuwa da tsalle-tsallensa ya gaji. Wata rana ya je wanka rafin da ya saba zuwa, sai ya haɗu da wani Kifi a cikin ruwa. Sai Kifin ya nemi su ƙulla abota da Birin. Biri ya amince, kuma suka yi wa juna alƙawari ba za su ci amanar junansu ba.

    Suna nan, abotarsu ta yi ƙarfi. Wata rana sai Biri ya ce zai je ganin gida, watau a can wani daji da danginsa suke. Da Kifi ya ji haka, sai ya shirya wa Biri kayan tsaraba, ya ba shi; suka yi ban kwana, Biri ya kama hanya, ya tafi. Bayan ya tafi, sai sauran kifayen da suke cikin ruwa suka fara gunaguni wai su ba su son abokinsa Biri.

    Har ma dai sauran kifayen suka shirya taro a ɓoye. A wurin taron waɗansu kifaye suka ce a kashe Biri, ko a kashe Kifin da ke abota da Biri. Sai babban kifayen ya ce: “A a, ba maganar kisa, domin kisan kai zai jawo gaba mara amfani tsakaninmu kifaye, ko kuma tsakaninmu da Birai.”

    Haka dai suka ci gaba da shawarwari, har wani ya kawo shawarar cewa a kira Kifi a gaya masa za a ba shi sarauta a fadar Sarkin Kifaye, amma sai ya zo da zuciyar abokinsa Biri kafin a naɗa shi. Duk suka amince da wannan shawara. Aka kira Kifi abokin Biri, aka yi masa bayani.

    Da ya ji bayanin da kifaye suka yi masa, sai ya ce da su: “Amma fa ni da Biri mun yi alƙawari ba za mu ci amanar juna ba. Kuma ni ba zan iya cin mutuncinsa ba idan aka ba ni sarautar.” Sai Kifi abokin Biri ya ce da danginsa kifaye su bari Biri ya dawo daga ganin gida, ya san zai yi duk yadda ya nemi ya yi.

    Suna nan, sai Biri ya dawo daga tafiya, sai ya je wajen Kifi kamar yadda ya saba, ya kai masa tsarabar da ya zo da ita daga gida. Suka gaisa sosai, kuma suka shiga hira. Can sai Kifi ya sanar da Biri cewa bayan ya yi tafiya ‘yan’uwansa kifaye sun ce za su ba shi sarauta, ya zama Sarkin Kifaye.

    Da Biri ya ji haka sai ya ce: “Kai, amma wannan labari da daɗi yake.” Sai Kifi ya ce: “To amma fa za ka raka ni cikin ruwa don ka gaishe su.” Biri ya ce: “To, ai sai mu je.” Suka yi nutso, har wajen taron kifaye. Sai abokin Biri ya ce: “Amma fa abokina, an ce sai na kawo wani abu kafin su ba ni sarautar.”

    Da Biri ya ji haka, sai ya dubi Kifi ya tambaye shi: “To mene ne suke so? Ka ba su mana.” Kifi kuma ya ce da Biri: “Ai abin da suke so a jikinka yake.” Biri ya ce: “Mene ne, fadi zan ba ka.” Sai Kifi ya ce: “Sun ce in kai musu zuciyarka ne.” Sai Biri ya ce: “Ai don wannan babu komai, zan ba ka.

    Amma ka san ba na yawo da zuciyata; tana can a kan bishiya na rataye ta. Bari in je in ɗauko maka.” A cikin murna Kifi ya ce: “To.” Ya raka Biri har bakin ruwa domin ya je kan bishiya ya ɗauko zuciyarsa ya kawo wa Kifi a nada shi sarauta.

    Da Biri ya samu ya fita daga cikin ruwan, sai ya hau bishiya ya ceda Kifi: “Daga yau ba zan sake abokantaka da kai ba. Kuma ba zan sake shiga ruwa ba.” Da wannan dabara Biri ya gudu. Shi ya sa har yau din nan Birai ke tsoron shiga ruwa. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kowa ya ɗauki amana ya kamata ya riƙe ta da gaskiya.
    • Hassada ga mai rabo taki ce.
    • Kafin ka ga biri, biri ya ganka.
    • Dabara kashin kwance.
    • Iya ruwa, fidda kai.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Cin Amanar Ɗan’uwa

    Edita@rumasau-kallamu