Tag: tatsuniya

  • Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    ‎‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    Wani mutum ne dai ya ba wani malami kuɗi don a yi masa asiri. Sai malamin ya ce sai an samo hauren giwa domin ya haɗa maganin da shi. Sai mutumin ya je cikin jama’a ya ce, ‘Wa zai iya samo min hauren giwa in ba shi kuɗi? ’Aka rasa wanda zai iya. Sai Gizo ya ce shi zai iya.

    Sai mutumin ya ce, ‘To shi ke nan sai ka samo ka kawo.’ Shi ke nan, sai Gizo ya je gida ya daka nakiya mai zaƙin gaske. Sai ya je gidan giwa da ɗan ƙunshin nakiyar a hannunsa, ya ce, ‘Gafaya dai.’ Sai giwa ta ce, ‘Maraba da Gizo.’

    ‎Ya ce, ‘Yauwa. Wata nakiya ce na kawo miki da na samo a pa.’ Shi ke nan sai giwa ta ce, ‘To’. Ta gutsiri nakiya ta kai bakinta. Da ta ji zaƙin nakiyar, sai ta ce, ‘Don Allah Gizo, ni ma ka raka ni in je in samo?’

    ‎Sai ya ce, ‘Haba yaya! Me zai hana? Ki zo gobe in kai ki.’ Shi ke nan, sai ta zo washegari suka je wajen kan pa. Sai ya ce da ita, ‘Idan kika doka bakinki sau ɗaya, kika doka sau biyu, a na ukun sai ki ga nakiya rubus a bakinki.’ Shi ke nan, sai giwa ta doka bakinta sau ɗaya fas a kan pa. Ta kuma dokawa.

    Da ta doka na ukun sai haƙorinta ya balle ya faɗo ƙasa. Sai jini shar. Sai Gizo ya ce, ‘Assha, assha. Yaya aka yi haka kuma?’ Ya yi maza ya ɗauki haƙorin giwar ya sa a aljihunsa. Ita ba ta gani ba. Tana ta kanta.

    ‎Shi ke nan sai gizo ya bar giwa a nan. Ya yi sauri ya kai wa mutumin nan haƙorin. Mutumin ya ba shi ladansa. Sai gizo ya je daji ya tattara namun daji suka je gidan da giwa ta ke a kwance. Suka tarar kanta ya kumbura, suntum.

    Sai gizo ya gaya wa namun dajin, ‘In na ce, “Babbanmu da giɓi,” ku ce, “Ɓurum ɓaɓurka.”’ Sai ya fara waƙar: Babbanmu da giɓi. Sai suka amsa: Ɓurum ɓaɓurka. Shi ke nan sai suka gama, suka koma. Gizo ya bar giwa a wahala. Shi kuwa ya karɓe kuɗinsa.

    Shi ke nan. Kurunk us.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata yarinya kyakkyawa, wadda ko tabo ɗaya babu a jikinta. Shi ke nan, sai ta ce ita fa ba za ta auri wanda yake da tabo ko da ɗaya ne tak a jikinsa ba. Manema wannan ya zo, wancan ya zo, amma duk suna da tabo.

    Ana nan, sai ga wani saurayi wai shi Ɗandisheri wanda ba shi da tabo a jikinsa, in ban da wani ƙarami a kan ɗan yatsansa, shi ma ya je saran itace ne ya yi sartse. Da ya je, sai ta ce ba ta son sa. Ya haƙura.

    Rannan sai wani maciji ya ji labarin halin wannan budurwa, ya gayawa abokansa, suka rikiɗa suka zama mutane samari kyawawa, waɗanda ba ɗaya daga cikinsu wanda yake da tabo ko ɗaya a jikinsa. Sai suka je wurinta, ta bincike kowannensu sarai, ta ga babu tabo a jikinsa.

    Nan take ta ce ta yarda ɗayansu ya aure ta. Aka taru aka ɗaura aure da ɗayansu. Shi ke nan ta tattara kayan ta suka tafi da amaryarsu. Da suka je jeji sai suka ce: “Yawwa mun iso gida.” Ita ko tace: “Ina gidan a nan?” Sai suka ce da ita: “Ai nan ne gidan. Amarya ta yi zuru-zuru, babu yadda za ta yi domin ta riga ta auri ɗayansu.

    Kuma ga shi sun kai ta dokar daji, inda ba za ta iya komawa gari ba. Daga nan suka saka ta a kogon bishiya, suka rikiɗe macizai suna lasar jikinta har ta zama fara fat, babu kyan gani, kuma abin ƙyama. Ana nan kwanci-tashi har ta sami ciki. Bayan wani lokaci mai tsawo, sai wata rana Ɗandisheri suka yi ƙarancin ciyawar akuyarsu, sai ya tafi can cikin ƙungurmin jeji yana yankan ciyawa.

    Sai matar macizai ta hango shi, ta fara rera masa waƙa tana cewa:

    “Ɗandisheri – Ɗandisherina,

    Ɗandisheri ƙanin Babati.

    Idan ka je gida ka gai da iyata,

    Idan ka je gida ka gai da Babati.

    Ni mai zaɓar maza babu tabo,

    Ga ni yau a kogon kukati,

    Maciji na lasa ta mulai,

    Kunama na harbi na mulai.

    “Sai Ɗandisheri ya ɗau waƙa, ya amsa mata yana cewa:

    Ina ruwan Ɗandisheri,

    Daga fari ke aka bai wa ni,

    Daga gani sai kika raina ni,

    Domin tabon ɗan yatsana.

    Da ya je gida sai ya gaya wa iyayenta halin da take ciki. Da suka ji labari, sai suka yi shiri domin su je su gani. Da suka je sai suka same ta a cikin kogo. Suka rasa yadda za su fito da ita. Dole aka sare bishiyar, aka fitar da ita, iyayen suka tafi da ita gida.

    Daga baya ta haifi ɗa namiji, rabin jikinsa ɗan mutum, rabi ɗan maciji. Da mazanta macizai suka ji ta haifu sai suka ƙara zama mutane, suka zo karɓar ɗansu. Da suka isa gidan, sai danginta suka tona makeken rami, aka shimfiɗa musu tabarma a kai, aka kuma hura wuta a ƙarƙashi, aka yi wa ɗansu wanka aka yi masa kwalliya aka kira su, suka zauna suka karɓi ɗansu.

    Suna cikin hira sai su ji ‘nyas-nyas,’ sai suka ce: “Kai akwai abin cizo a gidanku?” Masu gida suka ce: “E wallahi. Jim kaɗan sai tabarma da yayin suka kama wuta, su da shimfiɗar suka faɗa cikin wutar. Yayin da suke ƙonewa sai suka wurgo yaron sama, aka cafe shi, aka ƙara wurga musu, haka dai suka yi ta yi har suka ƙone rumus da su da ɗansu.

    Da ba domin Gizo ba da na yi muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mai ruwan ido gama kasuwa da yawo.
    • Jiki magayi.
    • Ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani jarumin sarki wanda a fagen yaƙi ba ya ja da baya. Duk inda ya sa gaba sai ya sami nasara. Yana da mata uku: amaryarsa kitse ne, sauran kuma mutane ne. To Sarkin nan ya fi son Takitsen. Duk lokacin da zai je yaƙi sai da ita yake tafiya.

    Ana nan, sai wata rana wani yaƙi mai haɗari da zafi ya taso. Sai ya yanke shawarar cewa wannan yaƙin ba irin wanda zai je da mata ba ne. Amma kuma yana tsoron barin amaryarsa a gida. Da sauran matansa biyu suka ji haka, sai suka ce ya bar ta a gida, babu komai za su kula da ita kamar yana nan.

    Sai ya amince da alƙawarin da suka yi, ya hau shi da barade suka dunguma zuwa filin daga, ya bar amaryarsa a gida. Bayan tafiyar Sarki sai matan nan suka sa amarya girki. Tana nufar murhu sai ta narke saboda zafin wuta. Ganin haka fa sai suka fara kuka, suna cewa: “Takitse ta narke ta zama ruwa.

    “To daman akwai wani tsuntsu a gidan Sarki. Da ya ji abinda matan Sarki suke faɗa a cikin kuka, sai ya tashi ya nufi wajen yaƙin, yana cewa;

    Sarki. Sarki. Sarki ka mai da yaƙi baya,

    domin Takitse ta narke ta zama ruwa.

    Haka ya yi ta yi, har Sarki ya kasa kunnensa, ya ji ana cewa ya bar yaƙi ya koma gida, domin matansa suna can a gida suna yin kuka. Fadawa da baraden Sarki ma suka tsaya, suka ji abin da tsuntsu ke cewa. Sai ya tambaye su abin da suka ji daga bakin tsuntsu, sai suka ce, ai Takitse amaryarsa ce ta narke.

    Nanda nan Sarki ya karya linzami, aka koma garinsa. Da ya isa fadar, sai ya shiga cikin turakarsa, ya sa Jakadiya ta kira matan, ya dube su ya ce: “Wace ce ta sa Takitse girki?” Sai matar Sarki tatsakiyarta yi farat ta ce: “Uwar gida ce. A fusace, Sarki ya umarci dogarawa su sare mata kai. Nantakesuka fille mata kai. Ba a wasa da umarnin Sarki. Kurunkus.

    Abubuwvan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Karya al kawari cin amana ne.
    • Soyayya amanar zuciya

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Ga ta nan ga ta nan ku.

    Wata mata ce dai ba ta taɓa haihuwa ba, tun da take. Sai ta ce, ‘Allah, Allah, ba ka ba ni ɗa ba, ko da Dankadafi ne? Allah sai ya karɓi roƙonta, sai ta haifi ɗanta namiji. Shi ke nan, yaro yana nan yana girma. Sai ran nan ta goya shi. Da ta gaji da goyo, sai ta ce da shi, ‘To, sauko ka kwanta Ɗan inna.’

    ‎Sai ya ce, ‘Mhm, a baya.’ Ta kuma cewa, ‘Sauko a wanke maka ido.’ Ya ce, ‘Mhm, mn, a baya.’ Kome dai ta ce, sai ya ce, ‘Mhm, Mn, a baya.’ Sai ran nan ta ce, ‘Kai ni dai na gaji.’

    ‎Gun malami za ni ko yana da abin da zai yi mini in rabu da ɗan nan na gaji. Sai ta je wajen malami. Malami ya ce, ‘Duk abin da aka gaya miki kya iya?’ Sai ta ce, ‘I, zan iya.’

    ‎Sai ya ce, ‘To sayo sa guda ki kawo mini.’ Sai ta sayo sa ta kai wa malami. Sai ya ce, ‘To, biyu za a raba, ki ɗauki rabi, in ɗauki rabi.’ Ta ce, ‘To.’ Aka raba naman sa kashi biyu, malami ya ɗauki rabi, ta ɗauki rabi.

    ‎Sai ya ce, ‘Ki soya wannan ki tafi da shi daji ki haɗa da majanyi da zane. In kin sauko yaron yana cin naman sai ki gudo ki baro shi can.’ Sai ta ce, ‘To.’ Ta je gida ta soya nama. Ta tafi daji da shi. Ta ce, ‘Dan Inna, Dan Inna, sauko ka ci nama.’

    ‎Sai ya ce, ‘Mn, a baya.’ Sai ta ce, ‘Ga naman naka nan sauko ka ci.’ Sai ya sauko. Da ya sauko yana cin naman, sai uwar ta waiga, ta waiga ba ta ga kowa ba, sai ta gudu ta bar shi da majanyi da zane. Fatar bayanta har ta kwaye saboda goyo.

    ‎Shi ke nan sai ga kura, ita da ’yan uwanta suna wasa. Sai ta ce, ‘Dan kanena, dan kanena, sam min dan naman in ci in goya ka.’ Shi ke nan, ya ba ta. Sai ta ɗauke shi ta goya shi suna wasa. Sai ta ce, ‘Sauko in huta.’ Sai ya ce, ‘Mn, a baya.’ Kome dai ta ce, sai ya ce, ‘Mn, a baya.’

    ‎Da ta yi ta yi ta cire shi daga bayanta ya ƙi, sai ta kira ’yan uwanta su cire mata shi. Da suka zo garin cire shi sai fatar bayan kura ta ciro, ta ce, ‘Na gamu da jaraba.’ Sai suka gudu suka bar shi nan.

    ‎Can sai ga dodo ya zo ya ɗauke shi ya ɗora a bayan dokinsa, shi kuma yana gaba yana cewa:

    Za ni za ni za ni,

    Za ni za ni,

    Za ni da namana,

    Za ni da namana,

    Za ni da kai sharɓa,

    ‎Dankaɗafi za ni da namana. Suna cikin tafiya a daji, sai Gizo ya ga dodo da yaro, sai ya sauke yaron, ya ajiye a ƙasa. Shi kuma ya hau kan dokin dodo. Dodo bai sani ba yana ta waƙa.

    ‎Shi ke nan sai ana ta tafiya da Gizo, sai kurciya ta ga Gizon a kan dokin dodo sun kusa da kogi, sai ta ce da Gizo, ‘Ku ne a yi muku rana, ku yi wa mutum dare.’ Gizo ya ce, ‘A’a, ba zan yi miki ba.’ Shi ke nan, sai kurciya ta ɗauke Gizo a fiffikenta.

    ‎Da dodo ya je bakin kogi, sai ya waiga don ya ɗauko yaro ya cinye ya sha ruwa, sai ya ga ba kome. Baƙin ciki sai ya sa shi ya faɗa cikin ruwan nan, ya zama gawayi. Shi kuwa Dankaɗafi kura ta cinye shi a can dajin da aka ajiye shi.

    ‎ Shi ke nan.

    Kurunkus.

    ‎Wannan rubutu an ciro shi ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Gizo Da Ɓaure

    Edita@rumasau-kallamu

  • ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    ‎‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata barewa ce, sai ta rikiɗa, ta zama mace kyakkyawa. Sai ta ɗauki ɗan kwatashinta ta ɗora a ka ta tafi tsakiyar karofi ta ajiye. Da ta ajiye, sai ta ce duk wanda ya jefa ’yar tsakuwa ta buɗe kwatashin nan, shi ne mijinta.

    ‎Sai wannan ya ɗauki tsakuwa ya jefa bai buɗe ba, wancan ya jefa tsakuwa bai buɗe ba. Sai aka sami wani ya jefa ’yar tsakuwa, sai ya buɗe. Sai ta ce ta sami miji, shi za ta aura. Sai suka tafi garin ita yarinyar, wurin iyayenta za a ɗauro mata aure da wannan mutumin.

    ‎Sai aka ɗaura musu aure ta zo ta tare gidan mijin. Kullum ranar girkinta sai a ce ta je ta ciro kuɓewa a gonar mijin ta yi miya. Da ta je gonar, sai ta yar da zanenta ta yi birgima a ƙasa ta zama barewa ta yi kiran ’yanuwanta, ta yi waƙa ta ce:

    ‎Cinkalkal, cinkalkal kalaya,

    Turmin ’yan kale ya yi fure, ceɗiya.

    Tudu na korar Tudu, Marina.

    Tudu na korar tudu da ƙaho.

    Ban da kwatsa-kwatsan.

    Ban da ƙanƙan.

    Sai ’yan uwanta su zo su taru su ciccinye kuɓewa. Sa’an nan in sun gama sai su tafi gida. ‎Ita kuma sai ta yi birgima ta komo mutum ta ɗauki zanenta ta ɗaura. Sai ta koma gida ta dinga cewa, ‘Ni da gangan aka tura ni. Ga shi nan ban samo kome ba.’

    ‎To, ran nan sai mijinta ya bi ta gonar. Sai ya gan ta tana birgima. Da ta gama birgimar, sai ya ga ta rikiɗe ta zama barewa. Sai ya ga ta yi kiran ‘yan’ uwanta bareyi da waƙa. Bareyi suka taru a gonar jingim. Duk suka cinye kuɓewa.

    ‎Suna cikin ci sai ya fasa su. Sai ya ga matarsa, ta gan shi. Ya komo gida. Sai ta ɗauko kuɓewar ta biyo shi. Ta tarad da shi a gida. Ya ce, ‘Wace ce?’ Ta ce, ‘Ni ce.’ Ya ce, ‘Ina za ki?’ Ta ce, ‘Ɗaki za ni.’ Ya ce, ‘A a, koma daji.’ Sai ta ce ta ƙi. Sai ya biyo ta a guje ya kora ta daji.

    ‎Daga nan ba ta sake dawowa  ba. Shi ke nan. Kurunkus.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin tatsuniyoyi da wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Namun Daji

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ‎Gizo Da Namun Daji

    Tatsuniyar ‎Gizo Da Namun Daji

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Gizo ne dai yana son ya ci nama, amma ba shi da shi. Ya rasa yadda zai yi. Sai ya ce a ransa, ‘Bari dai in yi wata dabara. Sai ya sayo goro ya rarraba wa namun daji da tsuntsayen gida.

    ‎Sai ya fara kai wa kaza, ya ce, ‘Ga shi. Goron wasa ne wanda za a yi a cikin daji. Naki ne wannan. ‎Sai kaza ta ce, ‘To. Amma fa kada ka kai wa muzuru. Sai ya ce, ‘Haba, me zai sa in kai masa?’

    ‎Da gizo ya fita, sai ya shiga gidan muzuru, ya kai masa goro. Sai shi ma muzurun ya ce, ‘To, amma kada ka kai wa kare. ‎Sai gizo ya ce, ‘Haba me zai sa in kai masa? ‎Da dai gizo ya fita, sai ya shiga gidan kare ya ba shi nasa goron. Kare ya ce, ‘To, amma fa kada ka kai wa kura.’ Gizo ya ce, ‘Haba me zai sa in kai mata?’

    ‎Da ya fita, sai ya kai wa kura nata goron. Kura ta ce, ‘To, amma fa‎ kada ka kai wa Zaki.’ Ya ce, ‘Haba kura, me zai sa in kai wa Zaki? ‎Shi ke nan, sai ya kai wa Zaki nasa goron, ya ce, ‘Ranka ya daɗe. Wani ɗan wasa za a yi na kawo maka goro.’

    ‎Da Zaki ya karɓa, sai ya ce, ‘To Allah ya kai mu. ‎Shi ke nan. Da ya fita, sai ya shiga ya kai wa damisa. Damisa ta ce, ‘In ce ko dai ba ka kai wa Sarki Zaki ba? Sai Gizo ya ce, ‘Haba, haba. Wane ni da gayyatar Sarki? Sai damisa ta ce, ‘To, Allah ya kai mu.’

    ‎Da ya fito sai kuma ya shiga gidan giwa ya kai mata nata goron. Sai giwa ta ce, ‘To, in ce ko ba ka kai wa manyan dawa ba? ‎Ya ce, ‘Mhm. Yaya zan kai? Ko kai masa ne ma ai ke zan bai wa ki kai masa.’

    ‎Shi ke nan. Ana nan ana nan, sai ranar wasa ta zo. Gizo ya bayyana musu wurin da za su haɗu a yi wasan. Ya ce musu, ‘To, ku tafi zan same ku. Ni daga baya zan taho tare da makaɗa. Shi ke nan. Sai kaza ta fara tafiya. Ashe ba su sani ba, gizo ya riga su isa can. Sai kaza ta isa can. Gizo ya yi mata maraba. Ya ce, ‘To shiga wannan bukkar kafin su zo.’

    ‎Shi ke nan. Kaza ta shiga, ta zauna. Daga can sai ga muzuru ya taho. Sai Gizo ya gaya wa muzuru cikin raɗa, ‘Maraba. Shiga tana nan a ciki. Shi ke nan sai muzuru ya shiga ya tasar wa kaza zai cinye ta. Ya cinye ta.

    ‎Can kuma sai ga kare ya taho. Shi ma dai Gizo ya gaya masa kamar yadda ya gaya wa muzuru. Sai shi ma karen ya cinye muzuru. Daga nan kuma sai ga kura. Ita ma ya gaya mata kamar yadda ya‎ gaya wa kare da muzuru. Sai kura ta shiga ta cinye kare.

    ‎Kura kuma tana zaune a cikin rumfa. Sai ga Zaki ya taho. Shi ma Gizo ya gaya masa haka. Ya shiga ya cinye kura. ‎Daga nan sai ga giwa da damisa sun jero sun taho. Sai Gizo ya ce, ‘To. Ku shiga nan bukkar mana.’

    ‎Daga shigarsu, sai suka kaure da faɗa. Suka yi ta faɗa tun daga cikin rumfa har suka yiwo waje. Idonsu duk ya rufe, suna ta faɗa. Sai Gizo ya samo ganga, ya soma kiɗa yana waƙa:

    ‎Zaki bari, damisa bari.

    ‎Giwa bari.

    ‎Faɗanku na manya,

    ‎Wa yake shiga?

    ‎Sai wawa, sai mahaukaci.

    ‎Sai ko ni da ba ni da hankali.

    ‎Suna ta faɗa, can da giwa ta ga abin ba dama, sai ta fito ta yi‎ tafiyarta gida, ta bar zaki da damisa suna karawa. Sai Gizo ya ci gaba da yi musu waƙa. Ya yi ta yi, su kuma suna ta faɗa. Ashe Gizo da ma ya zo da yaji a ƙunshe. Sai ya ɗauko yajin nan ya barbada musu a idanunsu. Sai fa faɗa ya rincabe, idanunsu suka rufe ruf.

    ‎Daga can sai Gizo ya ɗauko wuƙa ya ce, ” ‘Yan banza. Ana so a ci nama an rasa yadda za a yi.” Sai ya kama yankan naman jikinsu yana tarawa, har ya kashe su duka. Sai ya jide naman ya kai gida aka soya masa, ya ci ya  ƙoshi, ya ajiye sauran, yana ci lokaci-lokaci.

    ‎Shi ke nan. Ƙurunƙus.

    ‎Wannan rubutu an ciro shi ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Edita@rumasau-kallamu

  • ‎Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni

    ‎Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata yarinya ce dai mai tsananin kyau, duk garinsu babu mai kyanta, ta ce ba ta son kowa sai maras tabo. Sai dodanni suka ji labari. Sai suka yi wanka a gidan tururuwa. Sai suka zama samari kyawawa da su.

    ‎Da ta gan su, sai ta ce ta sami mazan aure. Sai duk ta dube jikinsu, sai ta ga jikin wannan da ɗan tabo ɗan mitsitsi, sai ta ce ba ta son sa. Da ta duba jikin ɗayan ta gan shi‎ sumul ba ko ɗigon tabo a jikinsa, sai ta ce shi ta ke so.

    ‎Shi kenan, sai aka shirya aka yi biki. Sai suka ce za su tafi da ita garinsu, su ba mazauna ba ne, Sai aka ce to za a ba ta ƙanwarta ta taya ta zaman ɗaki. Sai ta ce ita ba ta so, ta zauna ita kaɗai. Shi kenan, aka yi aka yi su tafi da ƙanwarta ta ƙi. Sai ƙanwar ta zama ƙuda ta maƙale mata.

    ‎Shi ke nan, da suka je gidan dodanni, sai dare ya yi suka shiga ɗaka suka rufe ƙofa. Sai ta ga ƙanwarta, sai ta rufe ta da faɗa, ta ce, ‘Ke wa ya kawo ki nan? ‎Ita kuwa ƙanwar sai ta yi shiru. ‎Shi ke nan sai yar ta ƙyale ta.

    ‎Ita yar kamar sokuwa ta ke. In dare ya yi, sai ta yi ta shirga barci. Ita kuwa ƙanwar sai ta zauna tangar har gari ya waye. Sai uwar mijinta ta zo da tsakar dare ta ce:

    ‎Sarma-sarma duf-duf.

    ‎Sai ƙanwar ta ce:

    ‎Wane ne nan ya ke mana Sarma-sarma duf-duf?

    ‎Sai uwar mijin ta ce:

    ‎Uwar miji ce ta ke mu ku Sarma-sarma duf-duf.

    Sai yarinya ta ce:

    Me ki ke so ki ke mu ku Sarma-sarma duf-duf?

    Sai ta ce:

    Wuta na ke so na ke muku Sarma-sarma duf-duf.

    Sai yarinya ta ce: Iya ga wuta nan.

    ‎Ki bar mana Sarma-sarma duf-duf.

    ‎Sai yarinya ta watso mata wutar. Tsohuwa ta je ta kashe wutar ta kuma dawo musu. Nan kuwa ashe ba wuta ta ke so ba. So ta ke yi ta cinye su idan ta tarar sun yi barci. Kullum haka, kullum haka. Duk sa’ad da yarinyar ta gaya wa yarta game da uwar mijin mai zuwa ɗiban wuta da daddare, sai yar ta ce ƙarya ta ke yi.

    ‎Ana nan a haka sak, ran nan yarinya ta ce da yarta, ‘To, yau dai ki zauna kada ki yi barci don ki ji yadda mu ke yi da tsohuwar da kunnenki. Shi ke nan, ya ta zauna. ‎Sai ita uwar mijin ta zo ta yi musu irin yadda ta ke yi kullum. ‎Shi ke nan, sai ya ta ji da kunnenta.

    ‎Shi kuma mijin nata yana wani ɗaki suna kwance tare da abokansa. Idan an yi abinci na aikin gona an kai musu, sai su yi haka su bunne. Sai su yi ta cin kwaɗi. Ita kuwa ƙanwar, wadda ta kai musu abincin, sai ta ce da su:

    ‎Mijin yata, ci kwaɗi.

    Mijin yata, ci kwaɗi.

    Mazan-wazata, ci kwaɗi.

    Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.

    Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.

    Su kuma idan sun ji wannan waƙar, sai su yi ta rawa suna cin kwaɗi. Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, ‘Ga kwanukanki nan.

    Ki ce muna yi mata sannu da aiki. Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, ‘Ga kwanukanki nan. Ki ce muna yi mata sannu da aiki. Shi ke nan, sai yarinya ta ɗebi kwanuka ta tafi da su gida. Kullum haka, kullum haka.

    ‎Sai rannan yar ta yi shawara da ƙanwarta don su gudu gida. Sai suka yi ta haƙa rami, tun daga nan gidan har ya zuwa hanyar ƙofar garinsu. Suna ta bin rami da ita da ƙanwarta har suka je gida.

    ‎Iyayenta suka ce da ita, ‘Lafiya?’ Sai ta ce wa iyayenta, ‘Ashe dodanni ne? Ni ca na ke mutane ne.’ Shi ke nan. ƘurunƘus kan ɗan ɓera. Ba don ƙarya ƙarya ce ba, wa zai zuba  ruwa a jallo, jallo ya fashe kuma ruwan bai zube ba?

    ‎Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Labarin Kalala Da Kalalatu

    Edita@rumasau-kallamu