Tag: tatsuniya

  • Tatsuniyar Kishiyoyi Biyu

    Tatsuniyar Kishiyoyi Biyu

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wasu kishiyoyi biyu masu zaman lafiya a tsakaninsu a wani gari. Ba su taɓa ɓata wa juna rai ba. Suna nan, sai wata rana ɗaya daga cikinsu ta kwanta jinya. To da ma kowaccensu tana da ’ya mace, ’ya’yan kuma sun yi kama da juna ainun, yadda ba kowa ne zai iya bambance su ba, tamkar dai ’yan biyu.

    Da mai jinyar nan ta ga alamun ciwon nata ba na tashi ba ne, sai ta kira kishiyarta, ta ba ta amanar ’yarta. Kishiyar ta karɓa, kuma ta yi alƙawari za ta kula da duka yaran biyu kamar ita ta haife su. Da mai jinyar ta rasu, sai kishiyar ta ci gaba da kula da yaran har suka girma, suka zama ’yan mata.

    To amma saboda tsabar so da adalci da take yi wa ’yar kishiyarta, sai ya zamanto ba ta iya gane ’yarta daga cikinsu, domin kamanninsu ɗaya. Sai wata tsohuwa ta ziyarce su da ta lura da yanayin matar ta hanyar adalcin da take nunawa a tsakanin yaran, sai ta rinƙa yi mata faɗa a kan yaya za ta riƙi ɗan wani kamar nata.

    Sannu a hankali, har dai ta fara karkata ga zancen tsohuwa, to amma sai tace ba za ta iya gane ɗiyarta daga cikin yaran ba. Sai tsohuwar nanta ba ta shawara da cewa in sun je ɗaukar ruwa kafin su dawo, ta dafa dambu, ta ajiye a bakin randa, in sun dawo suna jin yunwa za su fara ci.

    To sai ta bari sai sun fara cin dambun sai ta daka musu tsawa, tana cewa: “Kun san yadda yake ne, ba ku tambaya kafin ku fara ci? ”Tsohuwa ta ce mata ta lura da kyau, domin wadda ta fara cire hannunta daga akushin dambun to ita ce ’yar kishiyarta. Wadda taƙi cire hannunta, kuma ta ce suna jin yunwa ne, to ita ce ’yar cikinta.

    Sai kuwa matar nan ta yi hakan. Bayan yaran sun dawo daga ɗaukar ruwa sai suka hangi dambu a bakin randa, suka nufi bakin randa da gudu, suka fara cin dambu. Nan take sai ta daka musu tsawa, tana cewa: “Kun san yadda dambun yake ne, ba ku tambaya ba kafin ku fara ci? ”Nan da nan suka razana, sai ’yar kishiyarta ta cire hannunta daga cikin akushin dambu, ita kuma ’yarta ta cikinta, ta dubi uwarta ce: “Haba mama, muna jin yunwa ne fa.

    ”Daga nan sai ta kama ’yarta ta kai daki, kuma ta kama’yar kishiyarta ta yi mata tsaga a fuska. Daga nan fa sai ta fara gana wa ’yar kishiyar nan tata azaba iriiri, har ya kai ga in za su ci abinci, sai ta ƙi zuba wa ’yar kishiyarta nata abincin a akushi, sai ta zuba mata a ƙasa. Amma kuma maimakon ’yar kishiyar nan ta rame ko ta damu, sai ƙiba kurum take yi.

    Daga nan sai ta daina ba ta abincin sam-sam, har ma dai takore ta daga gidan, wai ta je can kabarin uwarta ta karbi abinci. Da yarinya ta ji haka, sai ta yi ta kuka, ta kama hanya ta tafi bakin kabarin uwarta tana kuka. Ana haka, ana haka, wata rana da ta je kabarin uwar tana kuka, sai uwar ta fito ta rarrashe ta, ta ba ta abinci, ta ci ta ƙoshi.

    Haka dai, kullum sai ta je bakin kabarin uwarta, ta fito ta ba ta abinci. Nan da nan ta sake yin ƙiba, ta yi kuma kyau, ta goge, abin gwanin ban sha’awa. Ita kuwa mai uwa a murhun, sai ramewa take yi. Uwarta ta rasa abin da za ta yi. Wata rana sai wasu samari suka je tambayar uwar cewa ɗaya daga cikinsu yana son ya shiga neman auren marainiyar.

    Maimakon ta yi abin da samarin suka nema, sai ta ce sai dai su auri ’yarta. Su kuma suka ce waccan mai tsaga a fuska suke so. Amma sai ta hana su, ta mare su, ta gaya musu kada su sake zuwa gidan neman aure in ba ’yarta suke so ba. Da marainiyar nan ta ga haka, sai ta gudu, ta shiga uwa duniya. Tana cikin tafiya a dokar daji, sai ta ga shinkafa da nama.

    Sai shinkafa ta yi wa budurwar nan magana, ta ce idan tana jin yunwa ta zauna ta ci. Amma sai yarinya ta ce ta ƙoshi, kuma ta ci gaba da tafiya. Can kuma sai ta ga naman kaza, sai naman ya yi mata tayi, amma sai ta ƙi ci, ta ci gaba da tafiya. Haka ta rinƙa haɗuwa da kayan daɗi iri-iri, amma ta ƙi amsa tayinsu, ta haƙura da yunwar da take ji, ga baƙin cikin da ke damunta.

    Tana cikin tafiya sai ta ga hadari ya haɗu, ita kuma babu inda za ta fake. Ta duba nan, ta duba can, sai ta hangi wata ’yar bukka, nan take ta nufe ta a guje, ta buɗe ta shiga. Bayan ta zauna sai ta ga wani babban kumurci a gefenta. Sai macijin nan ya sulalo ya nufo wurinta, amma ba ta ji tsoro ba sai kallon sa take yi.

    Da ya ji bayaninta, sai ya tambaye ta tana iya gane garin, sai tace ta sani. Ba tare da ɓata wani lokaci ba, sai ya ce ta shirya su je su kai musu ziyara. Jin haka ya sa ta shiga murna da shirye-shiryen tafiya. Ta tanadi kayan sutura da sauran kayan masarufi. Da ranar da suka sa ta zo, sai Sarki ya sa aka haɗa su da dawakai da ’yan rakiya masu yawa, sai ka ce ita ce matar Sarki, suka kama hanya.

    Da suka isa garin, sai ita da mijinta da ’yan rakiyarsu suka nufi gidan iyayenta, suka shiga gidan, mutanen gari kuma suna ta mamakin yadda wannan yarinyar da aka ba wuya a baya ta koma. Da ’yar’uwarta ta gan ta sai ta rungume ta, amma da kishiyar uwarta ta fito sai ta ce ba ita ce ta ɓata ba, to amma saboda tsagun fuska da ta yi mata, sai ta gane ta.

    Nan take suka rungume juna cikin murna. Bayan amarya ta huta sai suka fara hira, ta kwashe labari tun daga barinta gida har zuwa lokacin da ta auri ɗan Sarki. Data gama ganin dangi, sai ita da mijinta suka yi musu sallama, suka kama hanya tare da ’yan rakiyarsu, sai garin mijin.

    Bayan tafiyarta sai kishiyar uwarta ta ce lallai ita ma ’yarta ta je ta auro ɗan Sarki. A kan dole yarinya ta amsa. Da ta kama hanyar tafiyar neman ɗan Sarkin da za ta aura, kamar dai yadda ’yar’uwarta ta yi, tana shiga daji sai ta ga shinkafa da nama. Tun kafin ma a yi mata magana sai ta tsuguna ta fara ci. Sai shinkafa ta ce da ita: “‘Yan mata zo ki ci shinkafa.

    ”Da budurwa ta ji haka sai ta dubi shinkafa ta mayar mata da jawabi: “Da ma ko ba ki yi magana ba, ai ina jin yunwa.” Sai ta ci gaba da cin shinkafa har ta ƙoshi. Daga nan sai ta kama hanyar ta fara tafiya. Ba ta yi nisa ba kuma sai ta haɗu da naman kaza. Nan ma ta zauna ta ci har ta ɗebi cinya da fukafukai da ƙirjin kaza a hannunta, ta yi guzuri. Ta sa kai ta fara ci gaba da tafiya tana lasar baki.

    Ba jimawa sai hadari ya taso, ta rasa yadda za ta yi. Gashi ba gari kusa a baya, kuma ba ta san inda ta dosa ba. Can sai ta hangi wata ’yar bukka, ta ruga a guje ta shiga, sai ta ga wani shirgegen maciji. Tana ganin macijin nan sai ta ƙwala ihu, tana neman hanyar gudu. Sai ɗan yaro ya ɓullo ɗauke da abinci, ya ce ta ba macijin abinci.

    Sai ta ce: “Tabɗi! Ta yaya ina jin yunwa in ga abinci in ba wani maciji?” Sai ta kama cin abinci, ta yi watsi da maciji. Jim kaɗan sai macijin ya fara rikiɗa. Tana ganin haka sai ta faɗi sumammiya, watau ba ta ga ɗan Sarki ba, balle ta san kamanninsa. Bayan ta farka sai ta gan ta a gidan wasu masu sarauta, amma talakawane da wani ɗan yaro ya zo ya gaya mata cewa za a zo a yi mata kitso, amma idan makitsiyar ta ba ta abin ƙwalama kada ta ci.

    Tana cikin haka da macijin nan, sai wani ƙaramin yaro yaɓbullo ɗauke da kayan abinci, ya gaya mata ta ba macijin nan abinci. Nan da nan ta ba shi ruwa ya sha, kuma ta ba shi abinci ya ci. Da ya ƙoshi sai ya rufe baki. Bayan ta kammala ciyar da macijin nan da shayar da shi ruwa, sai yaron ya tambaye ta ko ita ma za ta ci abincin ne.

    Sai tace ta ƙoshi. Sai macijin nan ya sake yin ƙoƙarin razana ta, amma sai tace ita komai ya ga dama ya yi mata, domin ba ta da wurin zuwa, kuma ta riga ta sadaukar da rayuwarta. Da jin haka, sai macijin ya shiga rikiɗa, yana zama namun daji daban-daban, amma duk da haka ba ta razana ba. Maimakon haka ma, sai ta gyara zama tana kallon ikon Allah, har dai macijn nan ya rikiɗa, ya koma yaro matashi kyakkyawa.

    Yarinyar ba ta sani ba, ashe macijin nan ɗan Sarki ne yake neman aure, amma sai ya bi wannan hanya don ya sami mace mai hankali, mai amana. Nan da nan ya sa aka ɗauke ta a kan doki, akakai ta gidan Sarki, aka ɗaura mata aure da shi, aka sha biki. Bayan an gama biki sai aka tura yaro ya gaya wa amarya za a zo a yi mata kitso, to amma matar da za ta yi mata kitson mayya ce, kuma za ta zo da kayan ciye-ciye a hannunta, idan ta ba ta kada ta ci.

    Yaron ya ce mata ta riƙe duk abin da za ta ba ta a hannunta, ko sau nawa ta ba ta kuwa kada ta sa a baki. Yaro ya ƙara bayyana mata cewa, bayan wannan mayya ta gama kitso za tayar da matsefata a gidan, amma kada ta gaya mata, ta kyale ta ta tafi. Bayan ta tafi kuma za ta dawo ta tambayi matsefatar, to sai ta miƙa mata haɗe da kayan ciye-ciyen da ta ba ta.

    Amaryar ta amince. Da makitsiya ta zo gidan, sai aka ce ta je ta yi wa amarya kitso. Da ta fara kitso sai ta miƙa wa amarya kayan ƙwalama, wai ta ɗan lashe bakinta da shi, sai amarya ta karɓa kamar za ta ci, amma sai ta riƙe a hannunta. Jim kaɗan kuma sai
    ta sake miƙa mata wani abincin, sai amarya ta karɓa ta haɗa su a hannunta. Haka dai har sai da suka gama kitso, makitsiyar ta tashi za ta tafi, sai ta yar da matsefin da ke hannunta a tsakar ɗakin amarya, amma amarya ta ƙi gaya mata.

    Makitsiya ta kaɗa kai ta yi tafiyarta. Bayan wasu ’yan sa’o’i da tafiyarta sai ta dawo, wai ta manta matsefinta a gidan, sai amaryata ɗauko mata, ta haɗa mata da kyautar da ta ba ta ta kayanƙkwalama a lokacin da take yi mata kitso. Da mayyar nan ta ga an dawo mata da tarkacenta, sai kawai ta fara zage-zage, ta kama hanya a fusace ta fita abinta. Amarya da mijinta ɗan Sarki suka ci gaba da zamansu cikin jin daɗi.

    Wata rana sai amarya ta kwanta a ɗaki ita kaɗai tana ta rusar kuka. Da mijinta ya shigo sai ya tambaye ta abin da ya faru, sai tace tana tunanin gidansu ne da mahaifinta da kuma kishiyar mahaifiyarta wadda ta riƙe ta. Ta kwashe labarinta gaba ɗaya ta gaya masa. Tana jin wannan ƙa’ida sai ta ce: “Tabdi! Ai ni in har na ga abin daɗi ba zan ƙyale shi ba sai na ci.

    …..”Da makitsiya ta zo ta fara kitso sai ta miƙa wa yarinyar abin ƙwalama, sai ta karɓa ta kai baki ta cinye. Da ta sake miƙa mata na biyu sai ta sake lanƙwamewa. Bayan sun gama kitso sai makitsiyarta yar da matsefinta, sai ta ce da ita: “Ai kin manta matsefinki.” Sai ta juya ta karɓa, ta tafi tana dariya. Bayan wasu ’yan kwanaki sai yarinyar nan, abin tsautsayi ta kamu da cuta, wadda ta zama ajalinta aka binne ta, ba tare da ta auri ɗan sarkin ba. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Munafunci dodo ne, yakan ci mai shi.
    • Mai rabon ganin baɗi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.
    • Hassada ga mai rabo taki ce.
    • Mahakurci mawadaci.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta  Tatsuniyar Ƙawancen Kyanwa Da Bera

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Na-Goma

    Tatsuniyar Na-Goma

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata rana, an yi wani mutum wanda ya ke da ‘ya’ya goma. Shi kuwa maharbi ne. Kullum ya je daji yawon harbi sai ya kamo tsuntsu guda ɗaya. Shi ke nan kullum ya kamo tsuntsun sai ɗansa Na-Goma ya gasa shi ya cinye shi kaɗai. Kullum haka, kullum haka.

    ‎Ran nan sai ubansu ya ce a tafi kogin rantsuwa a yi rantsuwa a ga wanda ya ke cinye tsuntsun da ya ke kamowa kullum. ‎Shi ke nan. Sai suka ce, ‘To.’ Suka bi shi zuwa kogi. Da suka je kogin, sai na farkon, watau Na-Ɗaya, ya shiga ya ce:

    Ni Na-Ɗaya, na ɗayan Babaye.

    ‎In ni na ci tsuntsun Babaye,

    ‎Ruwa tafi da ni kar ka dawo da ni.

    ‎Sai ruwa ya ƙi tafiya da shi. Sai ya fito. Na-Biyu kuma ya shiga ya ce:

    Ni Na-Biyu, na biyun babaye.

    ‎In ni na ci tsuntsun babaye,

    ‎Ruwa tafi da ni kar ka dawo da ni.”

    ‎Sai ruwa ya ki tafiya da shi shi ma, ya fito. Duk sauran suka yi ba su nutse ba har aka zo kan Na-Goma wanda ya ce:

    Ni Na-Goma, na goman babaye.

    ‎In ni na ci tsuntsun babaye,

    ‎Ruwa tafi da ni kar ka dawo da ni.”

    ‎Shi ke nan. Sai kuwa ruwa ya tafi da Na-Goma.

    ‎Sai ‘yan uwansa suka ce, “To, baba, ka ga wanda ya ke cinye maka tsuntsu.” Uban kuma ya ce, “Na gani. Ku mu tafi gida. ‎Da suka je gida, suka shaida wa uwarsu wannan labari, sai ta fashe da kuka. Ta yi kukanta ta gaji ta share hawaye ta ce, ‘Ba kome. Allah ya ji kansa.’

    ‎Shi ke nan. Ruwa yana cikin tafiya da Na-Goma, sai ya zo gaɓar kogi. A nan ne fa ya ga wata dodonniya tana ta cin kwaɗi. Sai ta kama shi ta ce, ‘Kai yaro mutum ne, ko dodo irina?’ Sai yaro ya ce, ‘Ni mutum ne. ‘Sai ta ce, ‘Kai kuwa me ya kawo ka nan? ‎Sai ya ce, ‘Abin da ya sa na zo nan, shi ne, kullum kullum ubana ya kamo tsuntsu ya kawo gida, sai in ɗauka in gasa in cinye ni kaɗai, ba wanda ya sani.

    Shi ke nan, sai ran nan ya gaji ya ce mu je kogin rantsuwa tare da ‘yan uwana a gwada a ga wanda ya ke cinye tsuntsun da baba ya ke kamowa. Da muka je muka yi rantsuwar, shi ne kogin ya cinye ni ya kawo ni nan. ‘Sai ta ce, ‘To, yanzu ka ga ni dodonniya ce. In cinye ka ko in ƙyale ka?’

    ‎Sai ya ce, ‘Ni dai ina so ki yi mini arziƙi in zama ɗanki. ‘‎Shi ke nan, sai ta ce, ‘To, tashi mu tafi gida. Sai suka tafi gida. Da suka isa gidan, sai ta soma yi masa abubuwa yana sayarwa. Tana yi masa ƙosai yana talla. Kullum haka har yaro ya girma. Sai ta sai masa doki da kayan doki yana hawa yana tallan ƙosai a kai.

    In lokacin cin abinci ya yi, sai ta samo masa irin nasa na mutane. Ita kuma ta samo irin nasu na dodonni. ‎Shi ke nan. Kullum haka, kullum haka, sai rannan ‘yan’uwan Na-Goma suka gan shi yana tallan ƙosai a kan doki. Suka ce, ‘Wannan kamar Na-Goma,’ a zuciyar su. Shi ma kuma ya shaida su. Sai suka ce, ‘Kai mai ƙosai!’

    ‎Sai ya waigo. Suka ce, ‘Ko kai ne Na-Goma? ‎Sai ya ce, ‘I. Ni ne. ‘‎Sai suka rungume juna suna ta kuka. Shi ke nan, sai suka ce, ‘To, mu tafi gidan da ka ke. ‘Sai ya ce, ‘To, ai ni babata dodonniya ce. ‘‎Sai suka ce, ‘Mu tafi haka. Ba kome.’

    ‎Sai suka je suka yi sallama. Suka gaisa da dodonniya, suka ce ‘Mun zo ne mu tafi da ɗan’uwanmu Na-Goma.’

    ‎Sai ta ce, ‘Ni ba zan ba ku shi ba.’

    ‎Sai suka ce, ‘Ki yi haƙuri ki ba mu shi.’

    ‎Sai ta ce, ‘To, ku gaya min dalilin da ya sa ya zo ya same ni a nan.’

    ‎Sai suka gaya mata kamar yadda Na-Goma ya gaya mata, tun farkon haɗuwarsu a bakin kogi. Sai ta ce, ‘To na ji. Amma yanzu sai ku je ku kawo duk irin abin da za ku iya na dangin abincina. ‘Sai suka ce, ‘To.’ Suka tafi gida suka ce wa babansu, ‘Baba, yau dai mun ga Na-Goma yana tallan ƙosai a kan doki.’

    ‎Sai babansu ya ce, ‘Kai ku tafi can masu ƙarya, wanda ruwa ya cinye ina za ku gan shi? ‘Sai suka ce, ‘Ai gaskiya mu ke faɗa. Har ma wadda ta ke riƙonsa ta ce sai mun kai mata kayan abinci, sannan za ta ba mu shi. ‘‎Shi ke nan sai uban ya ce, ‘To a kai mata taikin gero ɗari da gomiya bakwai.

    Taikin dawa ɗari da gomiya bakwai. Taikin shinkafa ɗari da gomiya bakwai. Kai da duk dai irin abincin da mutane su ke ci a yi mata ɗari da gomiya bakwai-bakwai.’‎Da aka kai mata, sai ta ce:

    Ba cina ba, Na-Goma Ba cina ba.

    Je ka ka dawo, Na-Goma Je ka ka dawo.

    ‎Shi ke nan sai suka koma suka ce, ‘Baba, ta ƙi karɓa. Ta ce ba ta cin irin wannan abincin. ‘Sai ya sa aka yi mata taikin ƙuda ɗari da gomiya bakwai. Taikin tsutsa ɗari da gomiya bakwai. ‎Taikin kyankyaso ɗari da gomiya bakwai. Haka kuma taikin su gwano, da na tururuwa, da kiyashi, da jaba, da gafiya, da ɓera, da ƙadangare ɗari da gomiya bakwai-bakwai.

    Sai aka kai mata su. Da ta ga wannan gara zango-zango, tsibi-tsibi na irin abincinta, sai ta ce:

    Ga cinan nan, Na-Goma,

    ‎Ga cinan nan.

    ‎Ga shanu nan, Na-Goma,

    ‎Ga shanu nan.

    ‎Madalladai, Na-Goma,

    ‎Madalladai.

    ‎Dau wandonka, Na-Goma,

    ‎Dau wandonka.

    ‎Sa rigarka, Na-Goma,

    ‎Sa rigarka.

    ‎Sa hularka, Na-Goma,

    ‎Sa hularka.

    ‎Hau dokinka, Na-Goma,

    ‎Hau dokinka.

    ‎Sai wata rana, Na-Goma.

    ‎Sai wata rana.

    ‎Sai wata rana, Na-Goma,

    ‎Sai ka dawo.

    ‎Shi ke nan, sai suka rabu, dodanniya tana kuka, Na-Goma yana kuka. Aka kai Na-Goma gida, ya yi zamansa. Bai sake cinye wa babansa tsuntsu ba. ‎Shi ke nan.

    ‎Kurunƙus kan ɗan ɓera. Ba don Gizo ba da nai ƙarya. Ba don ƙarya ƙarya ce ba, wa zai ci tuntuɓe da tuwon shinkafa, ya dauje baki da tsokar nama, ya faɗa rijiyar zuma, a ciro shi da nakiya da alkaki?

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai taken TATSUNIYOYI DA WASANNI wadda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa

    Danna nan don karanta Tatsuniya Mai Taken Marainiya

  • Tatsuniya Mai Taken Wani Sarki Da Matansa

    Tatsuniya Mai Taken Wani Sarki Da Matansa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wani Sarki ne mai mata uku, amma Allah bai taɓa ba shi haihuwa ba. Ana nan, ana nan wata rana sai ya nemi shawarar fadawansa a kan abin da ya kamata ya yi saboda wannan rashin haihuwa. Sai suka ce ya kamata ya ƙara aure. Shi ko ya ɗauki shawararsu, ya sa aka nema masa budurwa kyakkyawa ya aure ta.

    Bayan wasu ‘yan watanni sai Allah ya ba ta ciki, labari kuma ya gama ko ina, matar Sarki tana da ciki. Su kuwa kishiyoyinta sai suka shiga baƙin ciki, don sun daɗe a gidan Sarki ba tare da ko ɗaya daga cikinsu ta sami ko da ɓatan wata ba. Daga nan sai suka shiga neman hanyar da za su bi su zubar da cikin, amma abu ya gagara, har lokacin haihuwa ya zo.

    Lokacin da suka tabbatar ta kusa haihuwa, sai suka je wurin Sarki suka nemi izini su je shan iska da saran itace a jeji tare da bayinsu. Ba tare da wani mugun zato ba, sai Sarki ya ba su izini, amma da sharaɗi, ba za su je da amaryarsa mai juna biyu ba. Sai suka ce ai za su kula da ita, kuma babu abin da zai same ta.

    Da suka nace, sai Sarki ya bar su suka tafi jeji da ita. A dajin nan naƙuda ta kamata, suka kai ta gindin bishiya, suka kwantar da ita, ta haihu. Da suka ga ta haifi ‘ya kyakkyawa, kuma ba ta cikin hayyacinta, sai suka ɗauki jaririyar suka jefa a kan bishiya. Can da rana ta yi sanyi, sai su da bayinsu suka kama hanyar gida, tare da mai jego.

    Lokacin da suka isa gida, sai matan Sarki suka je turakarsa, suka gaya masa wai matarsa ta haifi wani ɗan itace ne, ba mutum ta haifa ba. Da jin wannan bayani sai ya fusata, domin ya ɗauka gaskiya suka gaya masa, ya sa aka kai amaryarsa wani gida ita kaɗai inda ba kowa, sai abin tsoratarwa, aka bar ta a can.

    Bayan wasu ‘yan watanni sai bayin Sarki suka je daji yankowa dawakin Sarki ciyawa. Suna cikin yankan ciyawa sai wata ‘yar tsuntsuwa ta zo ta sauka a kan bishiya, ta tarar da ‘yar yarinya. Sai ta fara waƙa tana cewa: “Ɗan tsuntsu kar ka faɗa kan ‘yar Sarki, Wadda kishiyoyi suka ce, Wai ɗan itace uwarta ta haifa, Suka jefa ta kan bishiya, Ba ɗan itace ba ne, ‘Yar Sarki ce.

    “Ta rinƙa maimaita wannan waƙa, har bayin Sarki suka ji wakar ‘yar yarinya ta kan bishiya. Wannan ya sa suka fita da gudu, suka koma gari. Washe-gari ma da suka koma yankan ciyawa sai suka ji waƙar. Da suka kasa kunnuwansu da kyau, suka kuma saurari waƙar ‘yar yarinya, sai suka koma gida suka gayyaci mutanen gari masu yawa, domin su ma su je jejin su ji.

    Mutanen gari suka saurari waƙar da tsuntsuwa ke yi wa yarinya. Daga nan fa suka koma gari, suka je suka sanar da Sarki abin da suka ji. Sarki ya tashi da kansa ya nufi jeji inda yarinyar take, yasa aka hau bishiya a ga ko me yake yin wannan waƙa. Da aka hau bishiya sai ga yarinya kyakkyawa mai kama da Sarki, sai ka ce kakinta ya yi.

    Bayan an sauko da ita Sarki ya gan ta, nan da nan ya rungumi ‘yarsa, yana ta salati irin na godiya ga Allah, yana sumbatar yarinyar nan, don ƙauna irin ta ‘ya da mahaifi. Bayan wannan nuna murna ta Sarki da amsar barka da arziki daga jama’arsa da ke wurin, sai ya sa aka kawo masa doki ya hau, aka miƙa masa ɗiyarsa, suka hau doki tare, shi da ɗimbin jama’a suka kama hanyar gari.

    Da suka isa gida sai ya aika aka kawo masa uwar yarinyar da aka kai can wani gida da ke bayan gari, yana cike da nadama, amma kuma a cikin muryar bayyana farin ciki, ya ba amaryar haƙuri, ya nemi ta yafe masa horon da ya yi mata ba tare da laifin ta ba, a sakamakon makircin kishiyoyinta.

    Bayan fada ta cika ta batse da mutanen gari, sai aka bayyana musu miyagun halaye da makircin sauran matan Sarki, da yadda suka sa Sarki ya hori matarsa ba tare da ta yi masa laifi ba, da kuma yadda suka jefa da ‘yar Sarki a daji. Nan take Sarki ya umarci
    Hauni da ya fille musu kawuna, aka je aka zuba su a rami, aka binne. Sarki kuma ya ci gaba da sabuwar rayuwa shi da amaryarsa da’yarsa. Da ba domin Gizo ba da na shara muku ƙarya. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mugun nufi ba ya kashe ɗan kurciya.
    • Ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Ƙawancen Kyanwa Da Bera

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ƙawancen Kyanwa Da Bera

    Tatsuniyar Ƙawancen Kyanwa Da Bera

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Kyanwa da Bera dai ne suka yi ƙawance, suka kuma yi shawarar cewa ya kamata su tara kayan abinci da za su rinƙa ci idan lokacin hunturu ya zo. Suka kuwa zartar da wannan shawarar.

    Suna nan, sai rannan Ɓera ya ce da Kyanwa zai je bikin ƙanwarsa. Da ya fita sai ya nufi rumbun abincin da suka tara, ya ci har sai da ya ƙoshi. Da ya dawo gida sai Kyanwa ta yi masa maraba, ta tambaye shi, “Me aka samu ne?” Ɓera ya dubi Kyanwa ya ce: “Abin da aka samu shi ne, wuyar aiki ba a fara ba!” Aka yi murna aka watse.

    Bayan ’yan makwanni kuma Ɓera ya je wani sunan, ya bi ta rumbu ya ci har ya ƙoshi. Da dawowa gida sai Kyanwa ta tambaye shi: “Yau kuma wa aka samu?” Sai Bera ya dubi Kyanwa yana murmushi ya ce: “Yau kuma an sami kwanci-tashi ba ta bar komai ba.” Duk abin da Ɓera ke yi dai Kyanwa ba ta sani ba.

    Da Ɓera ya je gidan suna na uku ya dawo, sai Kyanwa ta nemi sanin abin da aka samu. Sai ya harare ta ya ce: “An sami ta-faru-ta-ƙare.” A tafiyar suna na huɗu Ɓera ya dawo da fuska a murtuke. Ita ko Kyanwa ta tambayi sunan jariri da goron suna. Maimakon Ɓera ya ba ta jawabi kamar yadda ya saba, sai ya fara yi mata wani kallon raini, kuma ga shi tana jin yunwa, tana jiran ya kawo mata abincin suna.

    Da ta ga alamun babu abincin nan, kuma Ɓera yana yi mata kallon raini, sai haushi ya kama ta ta fusata ta ce: “Kai ka cika surutu da fitina.” Kafin a ce haka, ta yi carab ta far masa, ta kama shi ta cinye. Ƙarya daɗin ji, amma ba na yi tun da Gizo yana nan. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Ruwa ba sa’an kwando ba ne.
    • Duk wanda ya ci amana, sai amana ta ci shi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kaza Da Muzuru

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kaza Da Muzuru

    Tatsuniyar Kaza Da Muzuru

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Kaza ce dai ta ce ba ta son kowa a cikin duk ‘yan uwanta zakaru masu nemanta. Ta dage ita sai muzuru kawai ta ke so da aure. Iyayenta ma suka ce ba za su ba ta shi ba. Ita kuma ta ce shi take so.

    ‎Da suka ga ta dage, sai suka ce, ‘To, mu dai babu ruwammu. Kada ki je ki jawo mana abin da zai hallaka mu baki ɗaya. Kaza kuwa ta ce ita dai shi ta ke so, ba za ta sake ba.

    ‎Sai aka kirawo ƙawayenta suka rarraba goron biki. ‎Shi ke nan, aka yi biki. ‎Sai ‘yammatan amarya suka je suna waka suna cewa:

    ‎Ke kaza kar ki jawo mana tserereninya da muzuru.’ Sai kaza ta ce: ‘Shi ba ya cin kaji, mhn. Shi ba zai ci kaji ba, mhn. In ji dai ni na kai kaina, mhn.’

    ‎Shi ke nan, sai suka ce da makaɗin ya sauya musu kiɗa. Shi kuwa makaɗin zakara ne, saboda a dangin amarya ya ke. Sannan ga kuma angwaye muzurai sun jeru, suna jin waƙa.

    ‎Shi ke nan, sai ‘yar ƙaramar kaza ta shiga fage ta ce:

    ‘Ni auta, autar kaza,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ji kiɗan da daɗi.’

    ‎Sai ta fita. Wata kuma ta shiga ta ce:

    ‘Ni wake-waken kaza,

    Kazar da ba a duka,

    Kazar da ba a zagi,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ji kiɗan da daɗi.’

    ‎Shi kuma makaɗin zakara, yana cewa:

    ‎’Daga baya-baya nake tsaya, In na ji kaya-kaya in naƙe.’

    ‎Sai kuma kaza ta uku ta shiga ta ce:

    ‘Ni ja-ja ja-jar kaza,

    Kazar da ba a duka,

    Kazar da ba a zagi,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ga idon muzuru!’

    ‎Daga nan fa sai angwaye muzurai suka yiwo kan ‘yan biki kaji radadada. Muzurai suka fara ciran su kai, su fafa, su fukafiki na kaji. Ita kuwa amarya sai cewa ta ke yi, ‘Kar ka cire mini fukafiki. Kar ka cire mini kai.’ Suka isa gida da ƙyar, suna cewa: Ga shi ta jawo mana tsiya. Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho. An ce ta bari ta  ƙi.

    ‎Kurunkus kan ɗan kusu.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin Tatsuniyoyi Da Wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya Ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can cikin wani ƙungurmin daji akwai wata Zomanya mai ciki, wadda gidanta yake kusa da na wata Kura, ita ma mai juna biyu. Suna zaman lafiya da junansu irin na maƙwabta. Wata rana sai Zomanyar nan ta je wurin Kura ta ce mata: “Kin ga ni da ke mun kusa haihuwa, ya kamata mu nemi wurin da za mu rinƙa  ɓoye ‘ya’yanmu.

    “Sai Kura tace: “E, gaskiya ne, to amma bari mu tona rami babba domin mu saka ‘ya’yanmu a ciki.” Da suka tona rami sai suka zauna tare, har lokacin haihuwarsu ya yi. Da suka haihu, sai suka tara ‘ya’yansu a rami ɗaya, kuma suka yi alƙawari cewa Kura za ta rinƙa samo musu abinci, ita kuma Zomanya za ta rinƙa renon ‘ya’yansu.

    Suka zauna, in Kura ta tafi neman abinci ta dawo, sai ta miƙa wa Zomanya ta ci, kuma ta raba wa ‘ya’yansu. Kullum haka. Amma ita kuwa Zomanya, in an kawo mata abinci sai ta ba ‘ya’yanta su ci, in sun ƙoshi sai ta cinye sauran, ta hana ‘ya’yan Kura. Kullum haka, kuma in Kura ta zo ta ce za ta duba lafiyar ‘ya’yanta sai Zomanya ta ce ai sun ci abinci sun ƙoshi, suna barci.

    Haka suka yi ta yi, har dai wata rana Kura ta ce sai ta ga ‘ya’yanta. Da ta leƙa ramin ta jawo ‘ya’yanta sai ta ga duk sun rame. Sai ta tambayi ‘ya’yanta abin da ya same su, suka rame haka. Sai ‘ya’yan suka ce ai ba a ba su abinci, in an kawo abinci sai Zomanya ta hana su, ta bai wa ‘ya’yanta, su kuwa sai ta sa su yi barcin dole kullum.

    Da jin haka sai ran Kura ya ɓaci, ta yi kuka, ta yi gumani da ƙaraji mai tsanani, ta ce tun da Zomanya ta ci amanarta, to ita da ‘ya’yanta za su cinye Zomanya da ‘ya’yanta gaba ɗaya. Ko da Zomanya ta ji abin da Kura ta faɗa, sai ta rasa abin da za ta yi, idanunta suka raina fata.

    Tsoro ya kama ta. Sai ta dubi Kura ta ce: “To shi ke nan, tunda kin ce ni da ‘ya’yana mun zama nama, to ki yi haƙuri mu fito daga rami tukunna.” Zomanya ta shiga rami ta gaya wa ‘ya’yanta idan ta fita Kura ta bi ta, to su fita da gudu su yi nasu wuri. Da Kura ta sake magana, sai Zomanya ta haɗa manyan kunnuwanta biyu, ta ɗan miƙo su waje ta ce da Kura: “Don Allah ki riƙe mini takalmana kafin in fito.

    “Jin haka sai ya sa ran Kura ya ɓaci, ita a tsummaninta yaya za a yi kamar Zomanya ta ce ta riƙe mata takalmanta, bayan ta zama nama a wurinta. Sai ta kama kunnuwan Zomanya da ƙarfi ta finciko su ta jefar, wai ita a nufinta takalma ne. Sai kunnuwa suka sulluɓe, Zomanya da ‘ya’yanta suka ranta a na kare.

    Kamar wasa, Kura ta kasa kama ko ɗaya daga cikinsu. Da ba domin Gizo ba da na shara muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    •  Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.
    • Ƙarshen maci amana jin kunya.
    • Kowa ya ci zomo, ya ci gudu

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana wata mata mai juna biyu ta je ɗibar ruwa a bakin rafi. Bayan ta cika tulunta da ruwa, sai ta kasa ɗauka saboda cikinta ya girma sai nishi take yi, abin tausayi. Kuma ga shi ita kaɗai ce ƙwal a wurin.

    Haka ta haƙura ta zauna. Can sai ga wani mutum ya taho, sai ta dube shi ta ce: “Malam don girman Allah ka ɗora ni mana.” Sai yace shi ba zai ɗora ta ba sai dai idan za ta yi masa wani alkawari. Mai ciki ta dube shi ta ce: “Na mene ne?” Shi ko ya kaɗa baki yace: “Idan kin haihu, in namiji ne to abokina ne, idan kuma mace ce, to matar ɗana ce.

    ” Da jin wannan sharaɗi sai ta yarda. Ya ɗauki tulu ya ɗora mata ta kama hanya ta tafi gida. Da ta je gida sai ta yi wa mijinta bayanin yadda suka yi da mutumin. Da yake mijinta mai sauƙin kai ne, sai ya ce: “To shi ke nan, Allah ya sauke ki lafiya.

    ”Bayan ’yan kwanaki sai mutumin ya zagayo gidan matar, suka gaisa. Ya nuna mata ɗansa suka yi sallama ya koma gida. Bayan wata ɗaya sai matar ta haifi ’ya mace, amma jikinta na jaki ne. Da mutumin ya ga haka sai ya yi halin dattaku ya ce: “To shi kenan tun da an yi alƙawari ai sai an cika.

    ”Sai ya kira ɗansa aka ɗaura musu aure da yarinyar ya kai ta gidansu. Yaro ya zauna da mace mai jikin jaki, ya ɗaure ta a gida. Amma duk sanda ya tafi gona idan ya dawo gida sai ya tarar an yi masa shara, an dafa masa abinci an kuma kai masa ruwan wanka bayan ɗaki.

    Kullum haka, sai abin ya fara ba shi tsoro tun da ba kowa a gidan. Rannan sai ya je ya sami babansa ya gaya masa, amma sai baban ya ƙi kula shi sai ya kore shi. To da ma yaron yana mutunci da wata tsohuwa maƙwabciyarsa dangarsu ɗaya. Sai wata rana ya zauna a gindin bishiya, yana tunanin abin mamakin da ke samunsa.

    Da tsohuwar ta gan shi a zaune haka, sai ta kira shi ta ce: “Ɗanyaro me ke damunka ne?” Shi ko sai ya kwashe labari ya bai wa wannan tsohuwa. To da ma ashe tsohuwa tana ganin duk abin da yarinya take yi idan ya tafi gona. Watau rikiɗa take yi ta koma kyakkyawar budurwa, ta shiga yi masa waƙa, ta yi shara, ta yi wanke-wanke, ta dafa abinci, ta ɗebo ruwa a rijiya ta kai masa banɗaki.

    Duk bayanta gama kafin ya dawo sai ta mayar da jikinta na jaka, ta ɗaure kanta a turke.
    Da tsohuwa ta gama bai wa yaron labarin abin da take gani sai ta shawarce shi da cewa gobe ya kwashi kayan aiki kamar zai tafi gona, idan ya kama hanya sai ya ratse a hanya, ya zagayo gidanta.

    Bayan sun gama shirya zancensu, sai ya koma gida yana mamaki, ya shiga ɗaki ya kwanta. Da gari ya waye sai ya saka kayan aiki ya ɗauki fartanyarsa ya kama hanyar gona. Bayan ya tafi ya yi nisa sai ya ratse cikin ciyawa, ya zagayo ta gidan tsohuwa, ya same ta a ɗaki.

    Daga nan sai suka ɓuya suka shiga leƙen yarinyar. Jim kaɗan sai suka ga ta rikiɗa ta koma kyakkyawar mace, ta fara waƙa ta kama shara da sauran ayyukan gida, ta shirya miya, ta dafa abinci, ta zuba nasa, ta kai masa ruwan wanka banɗaki. A daidai lokacin da ta fito daga bayan gida sai mijinta ya tsallaka danga ya dira a gabanta.

    Sai kawai ta razana za ta rikiɗa sai ya kama hannunta ya fara yi mata waƙa yana roƙon ta. Da ta ji waƙarsa sai ta fara kuka tana roƙon ya yafe mata. Shi kenan suka yi zamansu cikin daɗi suka ci gaba da more rayuwarsu cikin ƙauna da farin ciki. Dan kan ɓarya, ba domin Gizo ba da na sheƙa muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Alkawari kaya ne, in an sauke sai a huta.
    • Tsintar dami a kala.
    • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wasu tsuntsaye biyu a wani baƙin daji da ke ƙasashen Gabas. Ɗaya sunanta Cilakowa, ɗayar kuma Kodokodo. Ita Cilakowa tana da dogon baki, ita kuma ’yar Sarkin tsuntsaye ce.

    To tana so ta yi aure, amma saboda dogon bakin nan nata, ba wanda ya fito domin ya aure ta. Ana nan, sai rannan ta yi tunanin cewa bari ta je wurin Kodokodo ta yi mata dabara, ta ce za ta biki ta ba ta aron bakinta, idan ta gama harkar bikin za ta dawo mata da shi.

    Sai ta yanke shawarar haka, ta je ta yi bayani sai Kodokodo ta ba ta. To ashe daga bikin nan aure za ta yi. Sai ta gama biki, ita ma ta yi aure. Ana nan, ana nan sai Kodokodo ta ji shiru, ko labarin Cilakowa babu. Ga shi kuma bakin Cilakowa da ta karɓa ta ba ta aron nata, ya yi mata tsawo, ta yadda ma ba ta iya magana ko cin abinci da shi.

    Sai ta fara ramewa saboda ƙishirwa da yunwa, abin ya dame ta. Da ta ga ba dama, watau ba za ta iya ci gaba da jurewa ba, sai wata rana ta yanke shawarar cewa gara ta je ko ina ne neman Cilakowa.

    Duk inda ta je sai a riƙa cewa ai sunan Cilakowa Sheba. Kodokodo dai ta mai da hankalinta wajen neman bakinta. Tana cikin tafiya sai ta tarar da wasu mutane suna daka. Da ta ƙarasa kusa da su, sai ta durƙusa ta gaishe su, da waƙa kamar haka: –

    “Masu dakan nan, masu dakan nan;
    Ba ku gane min Sheba ba?
    ’Yar gidan su Dalailu.
    ’Yar Sarkin tsuntsaye. Ta karɓi aron bakina. Daga biki sai aure. Wutsiyata ta shinge. Bakina na talaka talak.”

    Suka ce: “A a, ba mu gan ta ba, ki yi gaba.” Da ta yi gaba sai ta ga wasu mutanen, su ma ta sake yi musu irin wannan waƙar. Sai suka ce da ita ta je ta shiga wani gidan, sai
    ta shiga.

    Tana shiga sai suka yi arba da Sheba, ta dube ta tace: “Na biyo bakina, daga aro sai aure?” Kafin ma Cilakowa ta yi wata magana sai fut, ta cire bakinta, ta ba ta nata, ta tafi. Da mijin Cilakowa ya dawo sai ya ga Sheba da dogon baki.

    Ganinta haka ya ba shi mamaki, sai ya dube ta yace, “Sheba ɗauke karan nan.” A cikin murya tattausa ta mayar masa da jawabi cewa: “Ba kara ba ne, bakina ne.” Sai ya dube ta ya ce: “To in haka ne ba zan iya zama da ke ba, bakinki ya yi tsawo da yawa.” Shi ke nan ya kore ta, ta koma gida. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • In ba ki da gashin wance kada ki ce za ki yi kitson wance.
    • Kayan aro ba ya rufe ƙwauri.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    Da gero da dawa da maiwa da duk dai kayan abinci haka, su shinkafa, acca, iburu, alkama da burtuntuna, sai suka shirya za su tafi gun wani saurayi wanda ya ce duk wata wadda ta faɗi sunansa, ita zai aura.

    ‎Shi ke nan. Ko wacce ta ci kwalliya. Ita kuwa burtuntuna ba ta yi kwalliya ba don ba ta da kayan ado. Suka kama hanya suna tafiya. A kan hanyar da su ke wucewa sai suka ga wata ‘yar tsohuwa a tsugunne da ruwan wankanta.

    ‎Sai tsohuwa ta ce da dawa, ‘Don Allah yarinya, zo ki cuɗa ni mana? ‎Sai dawa ta ce, ‘A, don Allah ku ji ‎tsohuwa? In yi kwalliyar tawa haka sannan ki ce in zo in cuɗa ki? Sai ta wuce ta ki cuɗa ta.

    ‎Sai kuma shinkafa ta zo, tsohuwa ta ce da ita, ‘Don Allah yarinya zo ki cuɗa ni mana? Sai shinkafa ta ce, ‘Duk wannan kwalliyar tawa in tsaya in cuɗa ki?’ Sai ta ki cuɗa tsohuwa, ta shige abinta.

    ‎Sai su maiwa, su gero, su alkama suka zo da dai dai, kowacce tsohuwa ta tambaya ta cuɗa ta sai ta ki, ta yi wucewarta. Daga nan sai ga burtuntuna ta zo. Sai tsohuwa ta ce da ita, ‘Yarinya don Allah zo ki cuɗa ni mana?’

    ‎Sai burtuntuna ta ce da ita, ‘To.’ Ta shiga cuɗa ta. Tana cikin cuɗa ta, sai bayan ‘yar tsohuwa ya burme Yarinya ta ce, ‘Yau na shiga uku, na lalace. Sai ‘yar tsohuwa ta ce, ‘Mene ne?’ Burtuntuna ta ce, ‘Bayanki ne ya ɓurme.’

    ‎Sai ‘yar tsohuwa ta ce, ‘Me kika gani a ciki?’ Ta ce, ‘Na ga kwatashi guda biyu, babba da ƙarami. ‎Ta ce, ‘To, ɗauko ƙaramin.’ Burtuntuna ta ɗauko ƙaramin kwatashi. ‎Sai tsohuwa ta ce, ‘To, ajiye nan.’ Burtuntuna ta ajiye.

    ‎Can sai tsohuwa ta haɗiye burtuntuna. Ta mai da ita fara, ta fito da ita waje, ta duba ta ta ce, ‘Kai, ba haka na ke son ki ba. Sai ta sake haɗiye ta, ta mai da ita ja zur kamar tsada, ta fito da ita waje ta duba ta ta ce, ‘Yauwa, haka na ke son ki.’

    ‎Sai ta buɗe ɗan kwatashin nan, ta ba burtuntuna kayan ado irin na mata kamar su zannuwa, su fatala, su yari, su awarwaro. Burtuntuna ta ci ado da su. Da ta gama adon, sai tsohuwar ta ce, ‘To, ga shi na shirya ki. Kin san sunan yaron da za ku wurin sa?’ Ta ce, ‘A a, ban sani ba.’

    ‎Sai tsohuwa ta ce, ‘Sunansa Daskin-da-riɗi.’ Sai ta ce, ‘To. ‎Sai ta yi godiya, suka yi sallama. Shi ke nan. Sai burtuntuna ta tafi ta sami sauran ‘yan’uwanta a hanya. Da suka gan ta sai suka dinga cewa, ‘Kun ga waccan shegiyar.

    Wa ya ba ta aron kaya ta ɗaura?’ Sai kuma su ce, ‘Wa ya sani ne? Mu yi maza mu je kada ta riga mu. Ko da ya ke ma ko ta je me zai yi da ita? ‎Shi ke nan. Da suka je, sai suka jajjeru. Dawa ta fara zuwa kofar gidan saurayin. Ta ce:

    ‘Assalam alam ɗan yaro.

    Assalam alam.’

    ‎Sai ya ce:

    Wane ne nan ya ke mana,

    Assalam alam?

    Sai ta ce:

    ‎Dawarku ce ta ke maka Assalam alam.

    Mai tuwo da daɗi, ni dawa Mai tuwo da daɗi

    ‎Sai ya ce:

    Na ji naki suna yarinya, Ba ni nawa suna.

    ‎Sai ta ce:

    Ban san ka ba, ɗan yaro. Ban san ka ba.

    ‎Sai ya ce:

    Da ba ki san ni ba, yarinya, Koma da baya ki sha kuka.

    ‎Dawa sai ta koma da baya ta yi ta kuka saboda ba ta san sunan saurayin ba, kuma babu damar ta aure shi ke nan.

    ‎Sai kuma ga su maiwa, da gero, da iburu, duk dai suka zozzo. Kowacce ya ce ta faɗi sunansa, sai ta ce ba ta san shi ba. Suka yi ta kuka. Shi kuma ya ce sai wadda ta san sunansa zai aura.”

    ‎Shi ke nan, nan sai ga burtuntuna ta zo: Sai suka ce da ita; ‘Ke don Allah, mu ma ba mu san sunansa ba, balle ke! ‎Sai ta rabu da su. Sannan sai ta je kofar gidan saurayin ta ce:

    Assalam alam, dan yaro.

    Assalam alam.

    ‎Sai ya ce:

    Wace ce nan ta ke mini Assalam alam?

    ‎Sai ta ce:

    Burtuntunarku ce ta ke maka Assalam alam.

    Burtuntuna, ai ni ce, Mai ɓata kaya.

    ‎Sai ya ce:

    Na ji naki suna, yarinya. Ba ni nawa suna.

    ‎Sai ta ce:

    Daskin-da-riɗi dan yaro Daskin-da-riɗi.”

    ‎Sai ya ce:

    “Buɗe ki shigo, yarinya, Buɗe ki shigo.”

    ‎Shi ke nan sai ta buɗe ta shiga. Sai kuma sauran su dawa, su gero, su iburu su ke cewa, ‘Ni zan yi miki wanka.’

    ‘Ni zan yi miki wanke-wanke.’

    ‘Ni zan yi miki alwala.’

    ‘Ni zan yi miki shara.’

    Da sauran abubuwa dai na barance. Sai  burtuntuna ta yarda suka zama barorinta. Shi ke nan. Ƙurunƙus.

    Wannan tatsuniyar an ciro ta ne daga littafin Tatsuniyoyi da Wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    ‎Danna nan don karanta Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniya Mai Taken Marainiya

    Tatsuniya Mai Taken Marainiya

    TASKAR TATSUNIYOYI”. Babi Na Daya: Marainiya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata yarinya marainiya, watau wadda take ba uwa ba uba; kuma ita kaɗai ce a wurin mahaifiyarta, lokacin da mahaifanta suka rasu suka bar ta. Ta sha wulaƙanci a wurin kishiyar uwarta, wadda take da ‘ya’ya maza da mata, waɗanda duka suka taru a kanta suka rika yi mata wulaƙanci.

    A cikin wannan yanayin kullum da sassafe takan je gindin wata bishiyar kurna ta zauna, ta yi ta kuka. Wannan kurna tana yin ‘ya’ya masu yawa, ga kuma zaƙi zaƙwai. Abincinta ke nan daga safe har yamma, kuma idan za ta koma gida sai ta ɗebo waɗanda za ta ci da dare.

    To akwai wani dan sarki kyakkyawa, mai suna Aminu, wanda ‘yar kishiyar uwarta take so, to amma shi kuma ba ya son ta. Shi ma kuma yakan je shan iska, ya hau kan wannan bishiyar kurna da marainiyar take zama a gindinta, ta sha ‘ya’yanta, yana kallon kowa, amma babu wanda zai gan shi don ganyen bishiyar ya ɓoye shi.

    Shi ke nan, wata rana marainiya tana zaune sai ɗan sarki ya sauko daga bishiya sai ya ce: “Sannunki ‘yan mata.” Sai ta ce: “Yauwa samari.” Aminu ya ce: “Me ke damun ki ne? Kullum sai in zo in gan ki a gindin wannan bishiya, har ma domin tunanin da kike yi ba ki sanin zuwana, kuma ga shi kikan riga ni zuwa don ni sai da la’asar nake zuwa, har in hau bishiya ba ki gan ni ba.”

    “To yaya kake zama a kan bishiyar kurna mai ƙaya?” Ta tambaye shi. Sai ya ce: “Ni na san dabarar da nake yi.” Haka dai suka ci gaba da hirarsu har ya kawo ga maganar aure, sai ta ce: “Ni dai marainiya ce, ba ni da uwa, ba ni da uba.” Sai ɗan sarki Aminu ya ce: “Yau na zama uwa da uba a wurinki.” Suna nan yana kiran ta, har ya fara zuwa gidansu marainiya.

    Da ‘yar kishiyar ta gane dan sarki ne yake zuwa wurinta, sai ta ce ta san makircin da za ta yi. Sai ta sayo allurai da yawa ta je ta sossoka a inda Aminu yake zama idan ya zo wurin marainiya. Da zuwansa sai ya zauna a kan alluran nan, kuma gaba ɗaya alluran suka shiga jikinsa.

    Nan da nan ya fara jin zazzaɓi, ya tashi ya tafi gida. Ciwonɗan sarki dai ya gagara warkewa, babu irin maganin da ba a yi ba. Wata rana marainiya ta tafi ɗiban ruwa a rafi, sai ta ji aljanu suna maganar ɗan sarki ba shi da lafiya, amma da an samo kashin tsutsotsi masu cin mutane a bayan wani gari mai nisa, aka jiƙa masa ya sha to zai warke.

    Da marainiya ta ji sai ta yi maza ta ɗauki goranta, ta je gida, ta aske kanta ta shafe jikinta da baƙin tukunya, ta sa kayan maza, ta ɗauki kwano, kamar almajiri zai je bara. Ta kama hanyar wancan gari mai nisa, inda za ta samo kashin tsutsa mai cin mutum, har sai da ta yi tafiyar shekara biyu kafin ta isa wurin tsutsotsin.

    Sai ta je wurinsu a hankali, ta kwanta don in sun ji motsin tafiyarta za su cinye ta. A hankali ta yi ta lulubawa dai -dai. Bayan ta sami abin da ta je nema, sai ta kama hanyar garinsu, ta isa lafiya. Bayan ta ɗan huta, sai ta kama hanyar gidan Sarki, ta tarar
    mutane maƙil sun cika fada suna jiran mutuwar Aminu.

    Da zuwa fada sai ta fara bara, mutane sun ɗauka namiji ne, suka ce: “Kai kana ganin ɗan sarki babu lafiya amma sai ka zo ka yi mana bara don ba ka da kunya?” Sai ta ce: “Ku bar ni in duba shi ko zai warke. Akwai wani magani da nake tafe da shi.” Sai suka daka wa ɗan almajiri tsawa, suka ce: “Duk duniyar nan babu wanda zai warkar da shi sai kai?”

    Sai ta ce: “Abar ni mana in ɗan gwada.” Da ƙyar aka bar shi ya shiga. Da shiga sai ta ciro wannan kashin tsutsa, ta jiƙa, ta ba ɗan sarki, ya sha. Cikin ikon Allah nan take sai ya fara amai, duk ya amayar da ciwon da ke damunsa, ya warke sarai. Kowa yana mamakin ɗan almajiri. A cikin farin ciki Sarki ya ce: “Zan ba ka gida da dawakai da dukiya mai yawa.” Shi ma Sarki bai san da mace yake magana ba.

    Sai ta ce: “A a ba na son wannan.” Sai Sarki ya ce: “To me kake so?” Ba tare da ɓata lokaci ba, marainiyar da ake zato namiji ce tace: “Ni dai babu abin da nake so kamar zoben hannunsa.”Ɗan sarki Aminu bai taɓa zaton zai rabu da wannan zobe ba, amma sai ya cire ya ba ta.

    Ta karɓa ta tafi. Bayan kwana biyu sai ya je gidan su marainiya a cikin fushi, yace da ita: “A duk garin nan babu wanda bai san da rashin lafiyata ba, amma ke ba ki taɓa zuwa gani na ba.” A cikin tattausar murya ta kalle shi ta ce: “Zauna ka ji labari.” Ya zauna ta fara gaya masa yadda ta yi.

    Da ta gama sai ya ce: “Ƙarya ne, idan maganarki gaskiya ce, to me aka bai wa ɗan almajirin?” Ya ce: “Zobe.” Sai ta ce: “To idan ke ce, nuna min zoben. Ya duba zobe, ya tabbatar zobensa ne. Daga nan ya fara mamaki. Ya ɗauke ta suka je gaban babansa, suka gaya masa labarin kome.

    Ya sa aka ɗaura musu aure, aka yi gagaruimin biki, kuma aka basu kyautar gari guda da dukiya mai tarin yawa, suka ci gaba da cin duniyarsu da tsinke. Kurunkus.

    > Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama
    • Mai nema yana tare da samu
    • Mai rabon ganin baɗi ko ana ha-maza ha-mata sai ya gani.
    • Hassada ga mai rabo taki ce.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    Edita@rumasau-kallamu