Tag: tatsuniya

  • Tatsuniyar Budurwa Mai Neman Ganyen Miya

    Tatsuniyar Budurwa Mai Neman Ganyen Miya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata budurwa mai suna Yakadi a wani ɗan ƙauye da ke nan kusa da bakin rafi. Wata rana sai mahaifanta suka aike ta lambu ta samo ganyen miya. Ta shirya ta kama hanya tare da ƙannenta, suka je, suka samo ganyen miya. A kan hanyarsu ta dawowa gida sai suka haɗu da wata tsohuwa ta ce da su: “Sannunku ’yanmata, don girman Allah ku taimake ni da ganyen ɗan kaɗan mana.”

    Sai ita Yakadi ta ce: “Ba za a bayar ba.” Suka ci gaba da tafiya, da suka kai kusa da wani dutse sai suka ce za su huta. Bayan sun zauna sun huta, sai ƙannenta suka tashi
    tsaye za a fara tafiya, amma ita Yakadi sai ta kasa tashi domin duwawunanta sun manne a jikin dutse.

    Suka yi ƙoƙarin ɓanɓare ta domin su tayar da ita amma suka kasa. Da iyayensu suka ji haka, sai suka nufi gida da gudu don su sanar har inda ’yarsu ta maƙale. Suna isa, suka yi ta ƙoƙarin ciro ta, amma abu ya gagara. Sai suka yanke shawarar gina ɗaki a kanta, haka kuwa aka yi. Tana nan, kullum suna kai mata abinci.

    Duk sanda mahaifiyarta ta je wurinta a ɗakinta, sai ta yi wata waƙa, in ta ji muryar mahaifiyarta ne sai ta buɗe mata ƙofar ɗaki ta shiga, in kuma ta ji wata murya ce daban, sai ta ƙi buɗewa. Haka ta ci gaba da rayuwa har zuwa wani lokaci da Kura ta garin yawo ta tarar da ɗakin da Yakadi ke ciki, ta yi ƙoƙarin shiga, amma ta kasa.

    Ana nan, wata rana Kura ta ɓuya, ta ji irin yadda uwar yarinya take yin waƙa a buɗe, ta shiga. Bayan uwar yarinyar ta tafi, sai Kura ta je ta yi waƙar, to amma da yake muryar ba irin ta uwar yarinyar ba ce, sai Kura ta ki buɗewa. Da Kura ta ga haka, sai ta tafi
    inda ake gyaran murya, aka gyara mata. A kan hanyar zuwa inda Yakadi take, sai yunwa ta kama Kura.

    Da ta ga kuda, sai ta kama shi ta haɗiye. Da Kura ta isa ƙofar ɗakin, ta fara waƙa sai muryarta ta shaƙe, ta koma kamar ba a gyara ba. Yarinya kuwa ta ƙi buɗe ƙofa, Kura kuwa ta sake komawa wajen gyaran murya, mai gyara ya ce mata in ta kama hanya kada ta ci komai, sai ta yi waƙar ta gama.

    Sai Kura ta yarda, ta kama hanya. Kura tana cikin tafiya, sai yunwa ta sake kama ta. Da taga sauro, sai ta kama shi, ta haɗiye. A nan ma muryar Kura ta sake gyara mata murya, suka haɗa ta da mai kula da ita har sai sun je bakin ɗakin da yarinya take. Da yake Kura ba ta ci komai a hanya ba da ta yi waƙa a ƙofar ɗakin Yakadi, sai ta ji murya kamar ta mahaifiyarta, ta ja ƙofa ta buɗe.

    Kura ta shiga ta cinye ta, amma ta bar kai da ƙafafu. Bayan Kura ta tafi, sai uwar yarinya ta je, ta tarar an cinye ’yarta, in ban da kai da ƙafafu. Sai ta fara kukan baƙin ciki. Tana cikin kuka sai tsohuwar nan ta zo ta rarrashe ta, kuma ta gaya mata idan ta je gida ta kona zuba sai ta rinƙa kiran sunayen gangar jikin Yakadi ɗaya bayan ɗaya, har sai ’yarta ta haɗu.

    Sai ta yi wa tsohuwa godiya, ta tattara kai da ƙafafun ’yarta, ta koma gida. Da ta koma gida sai ta yi yadda tsohuwa ta umarci ta yi. Da ta fara kiran sunayen ɓangarorin jikin ’yarta, sai duk ɓangaren da ta ambata ya faɗo, har dai ta gama kiran dukkan sauran sassan jikin yarinya, sai ta ga ’yarta ta dawo da rai kuma kyakkyawa kamar yadda take a da, ta ci gaba da rayuwa har lokacin da aka yi mata aure. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Rowa sanadin tsiya.
    • Alheri danko ne ba ya faɗuwa ƙasa banza.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Dagaci Da Malaminsa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Dagaci Da Malaminsa

    Tatsuniyar Dagaci Da Malaminsa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wani Dagaci a wani gari yana da matarsa, to amma matar ba ta taɓa haihuwa ba. Ba tare da saninsa ba, wata rana matar wani babban malami ta je wurin matar Dagaci hira a gidansa. Suna cikin hira sai matar Dagacin ta fara ba matar malamin labarinta shi ne halin da take ciki na rashin haihuwa.

    Kuma ga shi maigidanta, watau Dagacin, ya ce yana son ya sami ’ya’yan da za su zo su gaje shi. Kuma ya ba matar tasa wasu ’yan watanni, idan ba ta sami ciki ba zai kore ta, ya auro wata matar. Wannan barazana ce fa ta sa matar Dagaci ta fara kuka da baƙin ciki. Da matar malami ta ji yadda labarin yake, sai ta tausayawa matar Dagaci.

    Shi ke nan, sai matar malamin ta ce mata: “Kin gani yanzu ina da ciki wata biyu, sai ki fara dunƙula tsumma ki ɗaura a cikinki ki gaya wa mijinki cewa Allah ya ba ki juna biyu.” Abinda matar malami take son yi shi ne idan Allah ya sauke ta lafiya, za ta kawo wa matar Dagaci abin da ta haifa, domin ta nuna wa mai gidanta cewa ta haihu.

    Wannan hikima ta faranta wa matar Dagaci rai, kuma ta yarda aka yi alƙawari da matar malami, har matar Dagaci ta durƙusa tana yi mata godiya. Bayan ’yan kwanaki sai ta gaya wa Dagaci cewa ta yi ɓatan wata, kuma tana tsammani tana da ciki wata biyu. Da Dagaci ya ji wannan labari sai ya shiga murna.

    Ya fara faɗa wa fadawansa da mutanen gari cewa yanzu kam matarsa tana da juna biyu, kuma in Allah ya yarda ba da daɗewa ba za ta haifa masa ɗan da zai gaje shi. Saboda farin cikin da Dagaci yake yi, sai ya ba da umarni a kai matarsa wani gyararren gida. Yasa a riƙa yi mata duk abin da take so.

    Kuma ya ce kada ta taka ko ƙofar ɗaki don kada ta wahala a lokacin da take renon cikin har ranar haihuwarta. Ana nan sai mutane suka fara tsegumi a kan ai da ma matar
    Dagaci ba ta haihuwa, yaya kuma yanzu za a ce tana da ciki? Surutai suka yi yawa a gari, har wasu suka bugi ƙirji, suka sami Dagaci suka fara yi masa irin wannan magana.

    Wani daga cikin su ya ce, idan matar Dagacin nan ta haihu, to a ɗauki rumbun zuba amfanin gonar gidan Dagaci a ɗora masa a kansa. Wani kuma yace, in ta haihu a ɗaura masa igiya a kwankwaso a zagaya gari da shi har ya mutu. Can na ukunsu ya ce, in har ta haihu, to zai cinye buhun barkono goma shi kaɗai.

    Wani kuma ya ce, shi idan ta haihu to zai cinye dutsen da yake bayan gari. Haka dai suka ci gaba da maganganu, shi kuwa Dagaci bai ce komai ba, aka ci gaba da renon ciki har ya kai lokacin haihuwa. A ranar da matar malami ta haihu sai aka ce ai matar Dagaci ta haihu. Kamar yadda aka yi alƙawari, sai matar malami ta ɗauki jaririnta ta kai wa matar Dagaci ba tare da wani ya san an yi haka ba.

    Bayan labari ya bazu a gari sai masu rantsuwa suka dawo gaban Dagaci suka ce har idan an fito da yaro aka yi masa aski ranar suna, to za su cika alƙawarinsu da suka ɗauka, amma idan kuma zancen ƙarya ne, to za a kashe matar Dagaci. Dagaci ya yarda da haka. Matar Dagaci ta ci gaba da renon jaririn matar malami har ranar suna ta zo.

    Ana gobe suna sai matar malami ta dawo ta ce mijinta ya ce shi ba zai ba da ɗansa ba, saboda haka a dawo masa da ɗansa. Matar Dagaci na jin haka, sai ta ce: “Haba matar malam, bayan mungama magana da ke kuma kin ɗauki alƙawari yanzu ki ce in dawo ki ce ba zai yiwu ba, ai wannan cin amana ne.

    Idan Dagaci ya ce ina jariri bayan kowa ya ji na haihu, to me zan gaya wa Sarki? Kuma an ce idan ba a fita da yaro ba gobe ranar suna, za a kashe ni. Ki yi min rai mana!” Haka dai ta yi, ta yi, amma matar malami ta ƙi yarda, daga ƙarshe ta karɓi ɗanta ta tafi gida, matar Dagaci ta rasa yadda za ta yi. Da ta ga ba mafita sai ita da ƙanwarta suka shirya za su gudu cikin dare.

    Da dare ya yi suka kama hanyar daji suna cikin tafiya, sai suka ji wata tsawa a gabansu sai suka ga ƙasa ta tsage, sai ga wani jariri a cikin tsumma yana kuka. Sai matar Dagaci ta yi godiya ga Allah, ta ɗauki yaro suka kama hanyar gida. Ba su jima da komawa gida ba gari yawaye.

    Fada kuwa ta cika fal da mutanen gari da maƙada da mawaƙa da wanzamai za a yi wa ɗan Dagaci aski, kuma a raɗa suna. Su kuma masu alƙawari suna gefe suna jiran burinsu ya cika a ce babu yaro. Sai Dagaci ya tura a kawo jariri. Aka shiga cikin gida aka fito da yaro kyakkyawa mai kama da Dagaci. Nan take waɗanda suka ɗauki alkawari idanu suka raina fata.

    Shi kuma malami mamaki ya kama shi, aka dai yi wa yaro aski, aka raɗa masa suna. Sarki ya sa aka kamo waɗanda suka ɗauki alƙawari aka fara hukunta su, ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, har suka mutu. Shi kuma malami ya kama hanyar gida ya kwashe labari ya gaya wa matarsa yadda aka yi. Sai malami ya ce da matarsa ta ɗauko yaron su ma su raɗa masa suna.

    Da ta je ta ɗauko yaro, sai ta tarar ya mutu. Matar malami kuma baƙin ciki ya kama ta, ta kama hanyar gidan Dagaci. Da ta shiga ta sami matarsa sai ta yi ta ba ta haƙuri game da laifin da ta yi mata. Ita ko matar Dagaci ta ce ba komai, zance ya wuce, ta ci gaba da zaman daɗi da mijinta har lokacin da mai rabawa ta raba. Ga ɓera nan, ga ɓera nan, duk wanda ya ji tsoro alhaki a kansa. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Da kyautar Allah.
    • Alheri ya fi mugunta

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta

    Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    An yi wani mutum a wani ɗan ƙauye yana da mata da ’ya’ya. Ana nan, sai ɗaya daga cikin matansa ta haifa masa yarinya kyakkyawa. Bayan kwana bakwai sai ya raɗa mata suna Kwambal. Sannu a hankali, kwanci-tashi, yarinyar ta girma, kyanta ya ƙara bayyana, har ya kasance duk garin ba mai kyau kamar nata.

    Da ta isa aure sai mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa neman aurenta, wancan ya zo, amma sai ta ƙi, haka aka yi ta fama amma babu wanda ya yi nasarar samunta. Kwatsam sai wani yayanta, wanda suke ’yan turaka, mai suna Dawi ya ce zai aure ta. Da Kwambal ta ji niyyarsa, sai ta ƙi ta ce yaya za ta auri wanda suke ubansu ɗaya da shi?

    Shi ko Dawi da man ɗan baiwa ne. Wata rana sai ya ɗauke ta a kan raƙumi suka tafi cikin wani ƙungurmin daji ihunka banza, inda babu mutane. Ashe da man ya ja ta dajin ne domin ya nuna mata hatsabibancinsa ko ta ji tsoro ta aure shi. Da fari ya rikiɗa, ya zama wani babban baƙin maciji, mai gemu da jajayen idanu da ’yan kunne.

    Sai ya fasa kai, ya ƙura mata jajayen idanunsa masu kama da garwashi, ya ce ta yarda ya aure ta, ko kuma ya cinye ta. Ita ko da kafewa, sai ta ƙeƙasa ƙasa ta ƙi. Da ya ga haka, sai ya zama wani dodo mai haƙora gatso-gatso da farata masu tsawo da kaifi da kofatai a ƙafafunsa. Yana cikin wannan hali ya sake cewa ta yarda ta aure shi, ko kuma a bakin ranta.

    Ita kuma ta sake kafewa faufau, ta ƙi. Haka dai ya rinƙa rikiɗa, yana fito mata a kamanni da halittu daban-daban masu ban tsoro don ta ji tsoro, amma ta ƙi yarda, har ya gaji. Sai ya dube ta ya sanar mata da aniyarsa ta komawa gida ba tare da ita ba, watau zai bar ta a dokar dajin nan tun da ta ƙi yarda.

    Yana gama gaya mata haka, sai ya kwantar da raƙuminsa, ya ɗare, ya karya akala, raƙumi kuwa ya kama tafiya. Da ta ga ya bar ta, sai ta gyara muryarta tattausa, mai daɗin sauti da ratsa rai, ta kamawaƙa tana cewa:

    “Dawi ɗan’uwana,

    Ɗora ni a kan raƙuminka.”

    Da ya ji wannan waƙa, sai ya mayar da waƙa yana cewa:
    “Ki ce ni mijinki ne,
    In ɗora ki a kan raƙumi.”

    Sai ta mayar masa a cikin wannan baitin:
    “Ba ni iya faɗa, Kai dai ka ɗora ni a kan raƙumi.”

    Duk da waƙoƙin da suke yi, bai tsaya ba, ita kuwa ta rinƙa binsa tana yi masa waƙa da magiya ko ya ɗauke ta ya kai ta gida, amma sai ya ƙi, ya yi tafiyarsa shi kaɗai. Da ta gaji, sai ta zauna a gindin wata bishiya tana kuka. Can sai wani dodo ya ɓullo. Tana ganin dodo ta razana, ta yunƙura za ta tashi ta gudu.

    Da dodo ya ga haka sai ya buɗe bakinsa mai feshin wuta da hayaƙi ya ce da ita: “Idan kika gudu zan cinye ki yanzun nan.” Tana jin haka sai ta tsaya. Da dodo ya ga kyawunta sai yace mata: “Idan kin amince kika aure ni, zan kai ki gidanku, amma idan kika ƙi zan cinye ki.” Da ta ga ba mafita, sai ta yarda ya aure ta.

    Suka tafi gidan dodo, ta dangana, ta zauna da shi. Suna nan, har dodo ya tambaye ta irin abincin da takan ci, sai ta ce nama ta fi so. Duk yayin da ya fita farauta sai ya kaso namun daji ya kawo mata nama da yawa. Duk dare ’ya’yan dodon sai su fara cewa suna jin warin mutum, kuma suna so su ci naman mutum.

    Ita tana can inda babansu ya ɓoye ta. Da zarar ta ji irin wannan magana ta ’ya’yan dodo, sai ta wurga musu irin naman da ubansu ya kawo, sai su ɗauka su tafi. Kullum haka take fama da su. A can gidan su Kwambal kuwa, baƙin cikin duniya ya dami mahaifiyarta, kuma tuni ta shiga cigiyarta, har wata rana ta haɗu da tattabara.

    Bayan sun gaisa da tattabara, sai ta tambaye ta ko ta ga ’yarta Kwambal? Da tattabara ta ji wannan tambaya, sai ta kaɗa fuffuke, ta dubi gyatumar Kwambal ta kaɗa baki ta ce: “E, na ganta amma tana gidan dodo suna zaman aure.” Jin wannan labari ya ƙara tayar da hankalin uwar, nan take ta ɓarke da kuka.

    Can dai ta daina kukan, ta share hawaye ta dubi tattabara ta ce da ita: “Akwai kuwa yadda za a yi a kuɓutar da ita daga hannun dodo?” Tattabara ta ce: “E, akwai wata dabara. Tun da dodon yana da gashi, a aika wa Kwambal cewa ta gaya masa za ta yi masa kitso a gindin kuka.

    ”A cikin ƙagara uwar Kwambal ta ce: “To daga nan fa?” Sai tattabara ta ci gaba da bayani: “Idan ta yi ƙananan tsoraye sai ta nuna masa daga nan kuma sai ta ɗebi gashinsa mai yawa ta ɗaure shi da shi a jikin kuka. Idan ta ɗaure shi bajau, sai ta tashi ta kama hanyar gari da gudu”

    Da uwar Kwambal ta ji wannan shawara sai ta ji daɗi, ta yi wa tattabara alƙawari idan ’yarta ta kuɓuta za ta ba ta tukuici mai yawa. Sai tattabara ta tashi sama ta kama hanya har gidan dodo, ta sauka a kan ɗakin Kwambal, ta fara waƙa tana kiran sunan Kwambal tana cewa:
    “Kin yi tagumi ’yar auta,

    Ki daina kuka ’yar autar iya,

    Idan ya dawo ’yar auta,

    Ki kai shi gindin kuka ’yar auta,

    Ki yi masa kitso ’yar auta,

    Ki kitsa ƙanana ’yar auta,

    Ki nuna masa ’yar auta,

    Ki ɗebi mai yawa ’yar auta,

    Ki ɗaura a jikin bishiyar kuka ’yar auta,

    In ya ɗauru ki kama hanyar gida.”

    Ta rinƙa maimaita waƙa har Kwambal ta fara jin waƙa sai ta fita. Ta saurari waƙar tattabara da kyau sai ta fahimci bayanin tattabara. Washegari da dodo ya zo ɗakinta sai ta ce za ta yi masa kitso amma a gindin kuka, sai ya yarda ya fara jin daɗi matarsa za ta yi masa kitso.

    Suka tafi gindin bishiyar kuka ta fara yi masa kitso, idan ta kitsa ɗan siriri sai ta nuna masa sai ya ji daɗi, idan ta ɗebi gashi mai yawa sai ta ɗaura a jikin bishiya har ta gama yi masa kitso. Da ta ga daɗin kitso ya sa ya fara gyangyaɗi, sai ta yi sanɗa ta janye jikinta ta fara gudu ta kama hanyar gari.

    Da ya farka sai ya hangi matarsa na gudu, idan ya yunƙura zai tashi sai ya ji kansa a ɗaure a jikin bishiya. Ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kuɓuce amma sai abu ya gagara. Ita kuwa Kwambal tana ta sheƙa gudu ba ta tsaya ba har ta isa gida. Haka ta bar dodo ɗaure a gindin bishiyar kuka yana ta birgima. Da ba domin Gizo ba da na yi muku ƙarya. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • So amanar zuciya.
    • Sabo da maza jari.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Cin Kasuwar Sama

    Tatsuniyar Cin Kasuwar Sama

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Da Zanzaro da Barangunda suka ƙulla abota. Wata rana suka je cin kasuwar sararin sama, da nufin su dawo da yamma. Da suka je suka dawo sai suka tarar Gizo ya fito ya zauna ya kame a kan kujera, yana shan iska. Da man hanyar ta bi ta ƙofar gidan Gizon ne.

    Da Gizo ya gan su sai ya tashi ya yi musu maraba, suka amsa masa, har suka ba shi tsarabar kasuwa. Gizo da matarsa Koƙi suka ji daɗin tsarabar, sai Koƙi ta shawarci Gizo da ya bi su ko shi ma ya samo kayan daɗi. Gizo ya je da dare ya roƙe su, su taimake shi, su je tare.

    Zanzaro yace: “Kai Gizo al’amarinka fa da wuya, ka cika fallasa.” Gizo ya tsaya da rantse-rantse, yana cewa: “Ai na bar halin da kuka san ni da shi a da.” Da ƙyar dai suka amince, suka ce gobe ya shirya za sutafi tare. Da tsakar dare Gizo ya je wurinsu, ya nemi ya tashe su daga barci, wai asuba ta yi. Suka far masa da faɗa cewa yaya zai zo musu da tsakar dare haka?

    To idan haka zai yi musu su ba za su je tare da shi ba, domin ya fara halinsa na zumuɗi. Ya dai haƙura ya koma gida, amma ya kasa barci, ya laɓe a hanya har asuba ta yi. Sai suka ji ana kuwwa, ana cewa: “Wayyo Allah, na halaka.” Suka fito suka same shi, suka tambaye shi: “Gizo me ya faru?” Gizo yace: “Yunwa za ta halaka ni. “Sai Barangunda ta ce da shi, “Shiga hancina ka ci abinci”.

    Da ya shiga sai ya tarar da wata babbar kasuwa, ya ci abinci har ya ƙoshi. Can bayan wani ɗan lokacin sai Barangunda ta ce da Gizo: “Fita mana, ai yanzu ka ƙoshi.” Sai Gizo ya ce: “Tukuna.” Ashe har Gizo ya ɗauki ƙosai, yana talla. Can dai Barangunda ya harzuƙa, ya yi atishawa sai Gizo ya faɗo tare da faifan tallar ƙosan. Sai Barangunda ya ce masa ya koma cikin hancin ya mayar da ƙosan.

    Nan da nan Gizo ya shiga ya mayar, suka ci gaba da tafiya. Can kuma sai suka ji ihu, da aka tambayi Gizo ya ce ƙishirwa ke damun sa. Zanzaro ya ce ya shiga mararsa ya sha ruwa, ya shiga ya sha. Da ya ji sanyin wurin sai ya ƙi fitowa, ya ce sai ya yi wanka tukuna. Zanzaro kuwa bai ɓata lokaci ba, sai kawai ya matsa mararsa Gizo ya faɗo tim!

    Haka dai suka yi ta tafiya. Da suka isa bakin kasuwar sama sai suka sami wani wuri suka ajiye kayansu, suka shiga kasuwa. Da Gizo ya ga sun ɓace masa cikin kasuwa sai ya tashi ya shiga kasuwa yana tara yara, yana gaya musu, su zo zai koya musu irin wasan garinsu.

    Yara suka taru ya ce musu zai yi waƙa su kuma su amsa. Ya ƙara da cewa: “In kun ji na ce marmaron Zanzaro na sha ruwa, sai ku ce hancin Barangunda da kasuwa.

    “Sai ya fara:

    “Marmaron Zanzaro na sha ruwa,

    hancinBarangunda da kasuwa”

    Suka shiga tsakiyar kasuwa, Gizo yana ta rawa, yana tsalle. Zanzaro da Barangunda suka sami labari sai suka zo, suka saurari duk abin da Gizo yake faɗi, suka yi baƙinciki, suka rasa yadda za su yi, suka ma kasa isa wurin Gizo. Shi kuwa da ya gaji sai ya zo ya kwanta, barci ya kwashe shi. Da Zanzaro da Barangunda suka zo suka ga yana barci, sai suka ce madalla, abin nema ya samu, suka ciccire fukafukan da suka ba shi aro, suka sauƙo suka bar shi a sama.

    Da Gizo ya farƙa ya ga ba fukafukai, sai ya fita ya yi ta yawace- yawace ko zai gan su, amma bai gan su ba, ya rasa yadda zai komo gidansa, sai ya fashe da kuka. Da yaran gari suka gan shi, sai suka tambaye shi abin da ya faru, ya yi musu bayani, suka ce za su taimake shi. Suka sami doguwar igiya da ganga da abin kiɗa. Suka ɗaura wa gangar igiyar suka ce da shi ya hau saman gangar.

    Ya hau suka ba shi abin kiɗa, suka ce idan ya isa ƙasa sai ya kaɗa gangar don idan sun ji
    muryarta sun san ya isa kenan, sai su saki shi. Suka fara zura shi. Da ya zo rabi sai ya tambaye su irin muryar da gangar take da ita wadda za su ji ta daga sama. Sai ya ce bari ma ya ji muryar, sai ya kaɗa gangar da abin kiɗa.

    Da yaran suka ji muryar sai suka saki igiyar, Gizo ya surmiyo ƙasa, ya faɗi ya yi rugu-rugu. Da ƙyar aka tattara tarkacensa aka kai wa matarsa Koƙi ta shiga jinyarsa. Ya daɗe yana jinya kafin ya warke. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kowa ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Gizo Da Matarsa Ƙoƙi

    Tatsuniyar Gizo Da Matarsa Ƙoƙi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Koƙi matar Gizo ta fito fili ta matsa masa a kan zancen gona da amfanin yin noma. Gizo ya yi fushi, amma duk da haka ya je kasuwa ya auno tiya biyu ta irin gujiya ta shukawa. Da damina ta faɗi aka yi isasshen ruwa, sai ya ce da Koƙi ta je ta soya irin. Ta so ta yi masa musu, amma sai ta kanne, watau ta danne zuciyarta, ta je ta soya da gishiri
    kaɗan.

    Kamar da gaske, tun da asubar fari Gizo ya ɗauki sunguminsa da goransa cike da fura, sai gona. Yana isa gona sai ya je ya sami itaciya babba, mai cikakkiyar inuwa sansanya, ya zauna, ya buɗe burgamin irin gujiya da aka soya masa, ya dumbuzo, ya sa abinsa a gaba ya ci har ya yi nak.

    Sai ya ɗauki goran fura ya kaɗa, ya kwankwaɗi abinsa, ya yi gyatsa, ya yi rigingine, sai barci. Yana ta sharar barci har la’asar sakaliya ta yi. Da ya farka daga barcinsa, sai ya je kogi ya yi wanka, ya koma gida. Haka ya yi ta yi har gujiyata ƙare, matar tana ta yi masa sannu da aiki.

    Da kaka ta yi, kowa ya fara kai amfanin gona gida, amma Gizo bai kawo ko da ƙwaya ɗaya ba, sai matar ta tambaye shi zancen amfanin gona. Sai ya fara zuwa gonar Sarki yana ta labto gyaɗa yana kawowa gida suna ta tsinke ’ya’yan shi da matarsa Koƙi. Kowa a gari ana ta yin mamakin amfanin gonar da ya samu.

    Ana nan, sai rannan Sarki ya hau ya je gonarsa gewaya, amma sai ya ga gona kusan ba komai a cikinta. Da ya tambayi bayin da ke kula da gonar da maƙwabtansa na gona wane ne ya farɗe masa gyaɗa, sai suka ce ba su ga kowa ba. Sai ya nemi shawararsu a kan yadda za a gane mai ɗibar amfanin gonar Sarki ba izininsa.

    Kowa ya kawo shawara da dabararsa, amma Sarki ya ga duk ba wadda ta dace. Sai ya kawo tasa dabarar, suka amsa. Shawarar kuwa ita ce, ya sa aka tara ɗanƙo mai yawa, kuma aka yi masa mutum-mutumi irin ta kyakkyawar budurwa, kamar ka ce tashi mu tafi. Aka je aka sa mutum-mutumin nan a tsakiyar gona. Da safe Gizo ya je gona kamar yadda ya saba, ya ɗebi gyaɗa, ya tsaya yana gyaran gammo, can sai ya hangi mutum-mutumin.

    Sai ya jefar da gammo ya je wurinta, ya ga budurwa tana yin murmushi, zato yake tana yi masa ne. Cikin murmushi ya matsa kusa da ita ya yi mata magana, ba ta kula ba. Gizo dai sai ya ga kamar araha ta samu, sai ya matsa ya kai hannu ya taɓa mamanta. Nan take hannunsa ya maƙale, ya kai mari da na hagun, sai shi ma ya maƙale.

    Ya kai shuri da ƙafa, ita ma ta maƙale, ya rungume ta da ƙirji ya maƙale, suka faɗi rigingine ba damar tashi, ga shi ba a fara zafi ba, balle ɗanƙo ya narke. Can sai ga Biri ya iso, sai ya ce: “Yaya ne Gizo?” To, ga shi nan dai, Biri ya ga halin da Gizo yake ciki, tarko ya kama shi sai ya ce: “Tsiyarka Gizo, na san halinka in an yi maka rana, sai ka yi wa mutum dare.”

    Gizo ya yi ’yan rantse-rantsensa na ba zai cuci Biri ba, sai Biri ya kuɓutar da shi ya ɓalle shi amma shi ya manna kansa a jikin budurwar ɗanƙo. Da Gizo ya sami kansa sai gidan Sarki, ya durƙusa yace da shi, “Ranka ya daɗe, na kama maka ɓarawo”. Aka je aka kama Biri. Shi
    kuma ya yi ya yi, ya faɗi yadda aka yi, amma ina, an hana shi damar yin magana.

    Amma da yake Allah yana bayan mai gaskiya, sai wani Zagodo ya zo ya gaya wa Sarki yadda aka yi domin a gaban idonsa aka yi komai. Sarki ya ce Zagodo ya je ya kira Gizo. Zagodo ya je gidan Gizo ya tarar yana cin abinci, sai ya yi masa tayi, ya zauna kuma sai da ya yi ƙat, aka ƙara masa har ba ya iya magana. Gizo ya yi masa magana, sai kaɗa kai kurum yake iyayi.

    Da Gizo ya tabbatar ba ya iya magana sai ya ce su tafi wajen Sarkin. Da suka isa, sai Sarki ya ce wa Zagodo, ya faɗi maganarsa. Zagodo ya kasa magana, sai kaɗa kai yake yi kurum. Sarki ya yi fushi ya sa a je a yanka Zagodo da Biri. Gizo kuwa ya ci bulus, sai kawai ya yi ban kwana da Sarki, ya koma gidansa, inda shi da matarsa Koƙi suka yi ta amfani da gyaɗarsu. Duniya ke nan. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Duk wanda ya daka ta Gizo sai ya kwan ciki.
    • Illar yin katsalandan ga abin da bai shafi mutum ba.
    • Ƙarancin bincike kan jawo rashin adalci a shari’a.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Zomo Da Damo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Zomo Da Damo

    Tatsuniyar Zomo Da Damo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Zomo da Damo suka yi abota, kowa na zuwa gidan abokinsa ya yini ko su yi hira. Rannan Zomo ya je gidan Damo ya tarar yana cin doya, suka ci tare suka ƙoshi. Bayan ‘yan kwanaki sai Zomo ya shirya tasa doyar, ya sa matarsa ta shirya manya-manyan, ya kira Damo cin doya.

    Damo ya zo ya ga irin doyar Zomo manya ba ƙanana, ga kuma gari. Da suka gama cin doyar, sai Damo ya tambayi Zomo yadda ya yi doyarsa ta zama manya haka? Zomo ya ce idan lokacin shuka ya yi, ya zo zai gaya masa yadda zai yi. Da lokacin shukar ya yi, sai Zomo ya gaya wa Damo ya kawo irin doyar da zai shuka gidansa duka, kada ya bar ko daya.

    Kuma ya tabbatar an dafa doyar duka, kuma ya ɗauki babba daga ciki ya ci. Kada ya ba kowa sai ya je ya shuka. Damo ya yi yadda Zomo ya shawarce shi. Da kaka ta yi kowa yana kawo doya gida, amma Damo in ya je ya haƙa sai ƙasa. Ya rasa yadda zai yi da ƙyar ya nemo musu abincin da zai kai su shekara shi da matarsa.

    Damo ya rantse sai ya sha fansar abin da Zomo ya yi masa. Sai ya shirya da uwarsa cewa zai haƙa ƙabari ya sa uwar a ciki kamar ta mutu, kuma za a binne ta, a bar ‘yar ƙofa inda za ta rinƙa miƙa wa ɗanta Damo kayan daɗi irin na lahira. Aka shirya kaf, bayan kamar sati biyu, sai Damo ya je ya gaya wa Zomo yau gyatumarsa za ta kawo masa kayan daɗi daga lahira, saboda haka yana gayyatar sa domin a yi komai tare da shi.

    Suka zo wajen ƙabarin uwar Damo, sai ya ce: “Iya ina soki aiko mini babbar riga mai aska takwas da rawani ɗan Kura da dara mai tunta da takalmi ɗan Zariya don za mu biki.” Sai ga dukkan kayan da ya ambata sun fito. Zomo ya yi ta al’ajabi, ya tambayi Damo yaya ake irin wannan abu.

    Sai Damo yace da shi, ai da man duk wanda uwarsa take lahira za ta riƙa aiko masa duk irin abin da ya nema. Da Zomo ya ji haka, sai ya fara tunani shi ma me yake jira tunda ga tasa uwar ta tsufa, ba ta yin amfanin komai a nan duniya, gara ta je ta dinga aiko masa da duk abubuwan da yake so daga lahira.

    Tun a hanyar komowa gida ya sami kulkin da zai kashe uwarsa. Da Zomo ya je gida ba ko sallama sai kawai ya sami uwarsa ya dinga kwaɗa mata kulkin nan. Nan take ta faɗi ta mutu. Yasa aka yi jana’iza. Bayan an yi bakwai sai ya aika wa Damo ya zo su je wurin gyatumarsa domin ya ga abin da za ta aiko masa daga lahira. Damo ya zo suka je wajen ƙabari.

    Zomo ya ce: “Mama, ina so ki aiko mini riguna shuɗiya da fara masu aska shida-shida.” Shiru ba wani abu da ya fito daga ƙabari. Sai Damo ya dubi Zomo ya ce, “In ba hauka ba, wa ya taɓa gani an mutu an dawo?” Ya ƙara da cewa: “Ka manta da abin da ka sa na yi da doyata? “To a cikinsu wa ya fi ƙwaruwa? Zomo ko Damo?
    Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    * Ramuwar gayya, ta fi gayya ciwo

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Wata Mata Mai ’Ya’ya Biyu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Wata Mata Mai ’Ya’ya Biyu

    Tatsuniyar Wata Mata Mai ’Ya’ya Biyu

    Ga ta nan, gata nanku.

    Akwai wata mata tana da ’ya’ya biyu, ɗaya mace, ɗaya kuma namiji. Macen ce babba, namijin kuma shi ne ƙarami. Tana nan, tana nan sai wata rana ta kamu da rashin lafiya. Tana cikin rashin lafiyar ta kira ’ya’yanta, tana yi wa macen wasiyya cewa, ko da bayan ranta yaron ya ce zai yi wani abu to kada ta hana shi, ta bar shi.

    Bayan uwar ta rasu sai suka bar gidan, suka kama hanya suka nufi wani gari daban. Suna tafiya a cikin daji kwana da kwanaki, rannan sai wata babbar tsuntsuwa ta ɗauke su ta tashi sama da su, ta yi ta tafiya har suka isa daidai wani babban gari. Sai yaron ya ɗauki tsinke ya ce da yayarsa zai tsokale zumɓutun tsuntsuwar, amma sai ta ce idan ya tsokale tsuntsuwar ai za ta yar da su.

    Da ya ji haka sai ya ce mata ba uwarsu ta ce ta bar shi ya yi duk abinda yake so ya yi ba? Da yarsa ta ji haka sai ta yi shiru. Ya samo tsinke ya tsokali zumɓutun tsuntsuwar nan. Ita kuwa sai ta zubar da su a wannan gari.Can sai suka ga wani gida suka shiga, to ashe na wata tsohuwa ne. Da ta gan su sai ta yi maraba da su, ta ba su ruwa suka sha, ta tambaye su daga inda suke, sai suka kwashe labari suka ba ta.

    Sai ta ce da su za ta riƙe su, amma kuma akwai wani dodo da yakan zo da dare yana cinye mutane kullum a garin. Da dare ya yi aka kulle gida, sai yaron nan ya ce a ba shi ƙarafa guda uku, waɗanda zai yi amfani da su ya soke dodon, kowa ya huta a garin. Da tsohuwa ta ji abin da yaro ya faɗa, sai ta ce da shi ba zai iya ba, amma sai ya dage a kan shi dai a ba shi.

    Tsohuwa ta yi masa yadda ya nema amma ba da son ranta ba. Yaro ya hura wuta, ya zuba ƙarafan a ciki. Da suka yi ja, sai ya ji waƙar dodon yana cewa:

    “Wane ne ya isa ya ja da ni, a garin nan?

    Wane ne ya isa ya ja da ni, ni dodo?

    ”Sai can yaron nan ya ce: “Ni ne na isa na ja da kai a garin nan. Ni ne na isa na ja da kai, Ni Auta, har ma na fi ka.” Da dodo ya ji haka sai ya buɗe bakinsa ya yi wani irin ƙaraji. Sai Ɗan auta ya yi wuf, ya jefa masa ƙarfe ɗaya da ya yi jajir a cikin bakin. Sai dodon ya cafe ya haɗiye ƙarfen, yaron ya jefa masa ƙarfe na biyu, dodo ya cafe ya ƙara haɗiyewa.

    Da yaron ya jefa masa na uku ya haɗiye, sai dodon nan ya faɗi rigija. Nan take ya mutu a ƙofar masallaci, ko shurawa bai yi ba. Ganin haka sai Ɗan auta ya bar takalminsa a wajen mushen dodo. Da asuba ladan ya je ƙofar masallaci domin ya shirya ya kira salla, amma sai ya ga mushen dodon nan shim. Sai ya je ya gayawa Sarki abin da ya gani.

    A cikin murna Sarki ya je ya ga mushen dodo, kuma ya tambaya ko wane ne ya kashe shi, domin an ga takalmin wanda ya kashe dodo, amma ba a san ko na wane ne ba. Abu kamar wasa, sai Sarki ya ce duk wanda ya sa takalmin nan ya yi masa daidai, to shi ne ya kashe dodon, kuma Sarki ya yi alkawari zai ba wanda ya kashe dodon ladan rabin garin nan.

    Masu kwaɗayin wannan kyauta suka ta zuwa suna gwada takalmi, amma bai zauna musu daidai ba. Can sai aka ba Sarki labarin wata tsohuwa da ta yi baƙi, sai Sarki ya sa aka kira ta ta sa takalmi bai yi mata daidai ba. Daga ƙarshe dai Ɗan’auta ya sa takalami, kuma ya yi masa daidai. Da dai aka tabbatar shi Ɗan’auta ne ya kashe dodo, sai Sarki ya cika alƙawarin da ya yi, watau na ba shi rabin garin.

    Yaron kuwa ya karɓi rabin gari ya ci gaba da mulki cikin nasara, shi da yayarsa. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mai biyayya lamarinsa ba ya ɓaci.
    • Kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa a wannan duniya.
    • Duk mai mugunta sai ya gamu da wanda ya fi shi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar ’Yan Mata Masu Kamun Kifi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ’Yan Mata Masu Kamun Kifi

    Tatsuniyar ’Yan Mata Masu Kamun Kifi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana wasu ’yan matan ƙauye suka tafi rafi su, watau kamun kifi. Suka kuma yi sa’a suka kamo kifaye, suka kama hanya suka koma gida. A kan hanyarsu ta zuwa gida sai suka haɗu da wata tsohuwa sai ta tsayar da su, ta roƙi su sammata kifin da suka kamo, ko da mai ƙaya ne.

    Sai suka hana ta. Amma sai wata budurwa daga cikinsu ta ɗeba mata kifin. Ta karɓa, ta gode mata suka tafi. Washe-gari da suka koma rafi don kamun kifi, da yawa daga cikin ’yan matan kuma sun kamo kifin mai yawa, ƙoransu cike maƙil. Da tsohuwar nan ta roƙe su, suka hana ta sai waccan budurwa da ta bai wa tsohuwa kifin jiya ta gaya mata cewa yau ba ta samu ba sai wasu ’yan ƙanana guda biyu kawai.

    Ga shi kuma tana jin tausayin ’yar tsohuwar. Saboda haka sai ta ba ta ɗaya, ita kuma ta riƙe ɗaya. Kafin su rabu, sai tsohuwar ta gaya mata in ta je gida da wannan kifi guda ɗaya da ya rage a hannunta, kada ta dafa shi ta sanya shi a cikin randar gidansu. Bayan ta isa gida sai ta saka kifin a cikin randar kamar yadda tsohuwa ta ce ta yi. Sai ta shiga ɗaki ta kwanta.

    Da gari ya waye sai ta buɗe randa don ta ɗauki ɗan kifinta, amma sai ta ga randa ta cika maƙil da manya- manyan kifaye. Ta yi ta ɗiba, amma kifayen nan ba sa ƙarewa. Bayan ’yan kwanaki ’yan mata suka koma rafi don su kamo kifi, amma wannan ranar ba su sami komai ba, sai suka koma gida babu kifi.

    Washe-gari sai aka yi shela a gari cewa Sarki yana son ya ci kifi, kuma duk budurwar da ta kamo kifi ta dafa wa Sarki ta kai masa zai aure ta. Gaba ɗayan ’yan matan ƙauyen suka fita kamun kifi, amma ba wadda ta samo sai wannan budurwa da ta taimakawa tsohuwa da kifi. Yadda aka yi ta samo kifin nan kuwa shi ne, da ta kama hanyar rafi
    sai ta haɗu da wannan tsohuwar.

    Sai tsohuwa ta ce mata kada ta je babban rafi, ta nuna mata wata hanya da za ta kai ta har bakin wani ƙaramin gulbi. Sai tsohuwa ta ce ta yashe ruwan. Da budurwa marainiya ta fara yashewa sai ta fara ganin manyan kifaye, ta yi ta ɗiba har ƙwaryarta ta cika, ta koma gida. A duk faɗin garin budurwar nan kaɗai ce ta kamo kifi a wannan rana. Bayan ta dafa kifi ta sa a cikin akushi ta kai fada, mutanen gari da Sarki suka yi mamaki.

    Nan take Sarki ya amince zai aure ta. Bayan ta koma gida sai aka gaya mata ta sanar da iyayenta, za a yi bikinta da Sarki. To da yake iyayenta duk sun rasu marainiya ce, ba ta da kowa, da ta koma gida dare ya yi ta kwanta, sai ta tashi tsakar dare tana kuka domin tana tunanin ba wanda zai yi mata kayan gara. Tana cikin wannan hali na damuwa, sai ta ga kwatsam tsohuwar nan ta ɓullo mata a tsakar ɗaki, kuma ta tambaye ta ko mene ne yake damun ta.

    Sai marainiya ta yi mata bayanin dukkan abin da yake damun ta, har ya zamanto ba ta iya yin barci. Da’yar tsohuwa ta lallashe ta sai kuma ta gaya mata za ta iya yin dukkan abin da take buƙata. Yarinya ta yi ajiyar zuciya cikin murna, ta yi wa tsohuwa godiya. Tun kafin gari ya waye, sai ta ga ɗakinta cike da kayan gara fiye da yadda take zato za ta samu, ta yi ta murna.

    Ta godewa Allah. Ana nan, ana nan, ranar bikinta ta zo, aka ɗaura musu aure ta yi ta murna. Tagode wa Allah aka yi gagarumin biki, aka kai amarya gidan Sarki. Da kayan gara ya ƙare sai tsohuwa ta sake ɓullo mata a ɗakinta, ta kuma kawo mata kayan alatu da na marmari. Tace mata kullum za ta rinka kawo mata kayan ɗadi ta rinka ba Sarki, amma kada ta gaya wa kowa.

    Yarinya ta ce ba za ta gaya wakowa ba. Suka yi sallama tsohuwa ta tafi. Bayan ’yan kwanaki sai matan Sarki suka fara tsegumi cewa amarya ba ta da kowa, amma kullum Sarki yana ƙara son ta fiye da sauran matansa, kuma kayan alatu da take ba Sarki wa yake ba ta? Suka yi ta bincike, amma ba su gano bakin zaren ba, sai suka haƙura, suka bar ta.

    To shi Sarkin bai taɓa haihuwa ba, duk sanda matansa suka ɗauki ciki, sai ya zube. Rannan bayan ’yan shekaru da auren marainiya da Sarki, sai ya tara matansa, bayan ya tabbatar kowacce tana da ciki. Ya ce da su kowacce ta tafi gidan iyayenta, kuma kada ta dawo sai ta haihu. Bayan kowacce ta kama hanyar gidansu, sai ita kuma amaryar
    Sarki marainiya ta tafi gindin wata tsamiya ta zauna, ta kama kuka, tana waƙa tana cewa:

    “Wa zai ba ni yaro a yau?
    Wa zai amshi haihuwa a yau?
    Ni ba ni da uwa, ni ba ni da uba?”

    Tana cikin wannan hali sai tsohuwa ta zo ta sake tambayar ta abin da yake damun ta. Sai ta kwashe labarin yadda suka yi da Sarki ta gaya mata. Sai tsohuwa ta ɗauke ta, ta kai ta gidanta, ta cigaba da kula da ita, tana yi mata albishirin cewa in Allah ya yarda, za ta haihu, cikin ba zai zube ba.

    Suna nan tare da tsohuwahar ranar haihuwa ta zo, ta haifi ɗanta lafiyayye, kowa ya gan shi ya ga ubansa. Amma sauran matan Sarki kuwa ba su sami haihuwa ba, sai ɗaya daga cikin kishiyoyinta ta sami labarin haihuwar amaryar Sarki marainiya. Sai ta fara bin ta a sace, har ranar da aka sa za su koma gidan Sarki. Rannan sai amaryar Sarki ta tafi bakin rafi donta yi wanka tare da ɗanta.

    Da ta je bakin rafin sai ta ajiye jaririn, ta shiga wanka. Sai kishiyar nan tata ta zo ta sace yaron, ta gudu da shi.Da suka koma fada sai amaryar Sarki marainiya ta je ta gayawa Sarki cewa ta haihu, amma an sace abin da ta haifa. Sai aka ƙi yarda da wannan magana. Da kishiyarta wadda ta sace yaron ta zo, sai suka ce ita ce ta haifi yaron.

    Ita kuwa matar Sarki marainiya sai aka sa fadawa da yaran Sarki suka kafa mata ɗaki irin na dawaki, aka ajiye ta a can, bisa cewa ta yi wa Sarki ƙarya. Da kishiyarta ta ba yaron nono sai ya ƙi kamawa. Aka yi juyin duniyar nan, jaririn nan ya ƙi shan nono, sai aka rinƙa ba shi madarar shanu, har ya girma. Ana nan, ana nan, wata rana sai ɗan duba watau Sarkin bokayen Sarki, ya gaya wa Sarki cewa wannan ɗan nasa matar da ta rene shi ba ita ce uwarsa ba.

    Mamaki ya kama Sarki, sai ya nemi Sarkin bokaye da ya gaya masa ta yadda zai gane uwar yaron. Sai mai duba ya ce ya tara matansa ranar kasuwar garin, kuma a tara mutane a fada, sannan duk matansa su yi abinci, su kawo shi bainar jama’a, kuma su jeru a fada. Idan an yi haka, sai a ce da yaron ya zaɓi abincin da matan Sarki suka kai wurin, to duk abincin da yaron ya zo ya ci, tabbas mai wannan abinci ita ce uwarsa.

    Ba tare da nuna wata shakka ba, Sarki ya ce a yi haka ɗin. Sarki ya umarci matansa a kan abin da ake so kowacce ta yi. Duk matan suka yi dafe-dafen kayan daɗi. Ranar kasuwa ta zo, mutane suka taru, fada ta cika ta batse. Amma ita amaryar Sarki marainiya, kuma uwar yaron ta gaskiya, ba ta da abin da za ta dafa.

    Hasali ma tun ranar da aka kai ta ɗakin dawaki ba ta cin komai sai in an zuba wa doki dusa ta ɗiba, ta dama ta sha, ko ta yi tuwo da ita. Da aka ce har ita ma sai ta yi abinci, sai ta ɗebi dusar da aka kai wa dawaki kamar yadda ta saba, ta kama gafiya ta yanka, ta gyara ta da kyau, ta ɗauka ta kai fada.

    Da ta isa fada sai ta tarar duk sauran matan Sarki sun jeru, suka shiga yi mata kallon reni da nuna mata ƙyama. Can da ɗan Sarki ya zo a kan doki aka ce ya zaɓi abincin wadda zai ci daga cikin matan Sarki, sai kawai ya ƙarya linzami ya doshi inda mahaifiyarsa marainiya take. Da zuwa sai ya kama cin abincin dusar nan da ke gabanta.

    Da mutanen da suka yi cincirindo a fada suka ga haka, sai mamakin yadda al’amarin ya kasance ya kama su.Da Sarki ya ga alama lallai gaskiya ce ta yi halinta, sai yasa aka kama matar da ta sace yaron ta ce nata ne, aka fille mata kai. Ita kuwa mahaifiyar yaron ta gaskiya sai Sarki ya ba ta haƙuri, ya nemi ta gafarta masa.

    Ba a daɗe da yin wannan abu ba, Sarki ya kamu da rashin lafiya, wadda ta zama ta ajalinsa. Bayan an gama zaman makokin rasuwar Sarki, sai aka naɗa shi ɗan marainiya a matsayin sabon Sarki. A cikin ikon Allah yaro ya hau karagar mulki. Ya ci gaba da tafiyar da harkar mulki kuma ’yar tsohuwar nan da uwarsa zumuncin da yake tsakaninsu ya ƙara ƙarfi. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Alheri danko ne ba ya faɗuwa ƙasa banza.
    • In Allah ya rufa maka asiri, ba mai tonawa.
    • Karya fure take ba ta ’ya’ya.

    Wannan tatsunya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Biyu)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Biyu)

    Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Biyu)

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana ’ya’yan Kura sun je yawo gidan Kurege sai suka tarar an yi farfesun Biri. Sai aka ba su suka ci. Da babban cikinsu ya ji daɗin farfesu sai ya ɗebi romon ya shafa a kan gashin kansa ya tafi gida. Da suka koma gida, sai ya je wurin babansa Kure ya ce: “Baba ka dafa kaina mana. ”Da uban ya ji haka sai ya dube shi ya ce: “Ka taɓa jin an cewa uba ya dafa kan dansa ne?

    ”Sai ɗan ya nace shi dai uban ya dafa kansa. Sai ya dafa kan, ya ji danshin romo, ya sa harshe ya lashe. Da ya ji zaƙin romo, a nan take ya tambaye su a inda suka sami wannan abu mai daɗi. Suka amsa masa da cewa a gidan abokinsa Kurege aka ba su. Sai Kure ya sa takalminsa ya tafi gidan Kurege ƙwalama. Da ya isa gidan Kurege sai ya tarar saura kaɗan a tukunya.

    Kurege ya zuba masa ya ci. Da ya ji daɗi sai ya ce da Kurege: “Ina kake samo wannan nama mai daɗi haka?” Sai Kurege ya amsa masa da cewa: “Muna wasa ne a ruwa kullum tare da birrai, sai in daura tarko a ƙafata. Idan mun shiga mun fara kurme a ruwa sai in kama ƙarami a cikinsu, in danne a ruwa har sai ya sha ruwa sosai ya mutu. In sun tafi sun bar shi, sai in ɗauka in yanka mu yi farfesu a gidana.

    ”Da Kure sarkin kwaɗayi ya ji haka sai ya ce: “To in gari ya waye gobe zan bi ka.” Sai Kurege ya amince. Da Kure ya tafi gidansa sai ya kasa barci, ya ƙagara gari ya waye. Can dai da ya ga kamar gari ya ƙi wayewa, sai ya hura wuta ta haske ko ina. Daga nan ya je ya faɗa wa Kurege wai gari ya waye, sai Kurege ya ce: “Haba Kure, ka hura wuta a kan dakinka ka ce gari ya waye?

    Ai gara ka koma gida sai gari ya waye.” Bayan ya koma gida ya ɗan jima gari bai waye ba, sai ya kama zakara ya rinƙa matsa shi har ya rinƙa yin cara. Da Kurege ya fito sai ya ce: “Haba Kure yaya kake damun kanka haka ne? Na gaya maka sai gari ya waye.” Haka dai Kure ya haƙura ala tilas har sai da gari ya waye. Da sassafe ya shirya ya nufi ƙofar gidan Kurege.

    Suka kama hanyar rafi har suka isa, suka tarar da birrai a bakin rafi. Sai Kure da Kurege suka yanke shawarar su shiga cikin ruwa su yi wasan kurme. Da suka shiga tare da birrai sai Kurege ya faki ƙarami daga cikinsu ya danne a ruwa. Shi kuma Kure maimakon ya faki ɗan ƙarami, sai ya nufi kan babba, ya sa masa igiya ya danne shi. Da ya ji Kure zai halaka shi, sai ya yi ƙara, har sauran suka ji, suka watse da gudu.

    Kure da Kurege dai kowa ya kaso Biri daya, amma sai Kuregeya ce: “Kai kuma Kure da muka yi da kai za ka kama karami donkada su gane, sai ka kama babban cikinsu?” Sai Kure ya dubi Kurege ya ce masa ai ƙarami ba zai ƙosar da shi ba, shi ya sa ya kama babba wanda idan ya yi farfesu da shi zai sha ya ƙoshi ya more.

    Washe-gari da suka koma tun safe har yamma suna jira a bakin rafi babu Birin da ya fito bakin rafi. Sai Kurege ya dubi Kure yace da shi: “Kai ka yi mana wannan ɗanyen aiki.” Rannan dai haka suka koma gida, ba su sami nama ba. Sai Kurege ya gaya wa Kure gobe da safe za su je unguwar birrai su gaishe su domin rashin da suka yi na babbansu.

    Da ma birrai sun aika wa Kurege da Kure za su yi taro domin ba su sani ba cewa ko Kure da abokinsa Kurege ne suka kashe musu’yan’uwa. Da gari ya waye suka shirya, sai Kurege ya ce zai hau doki, shi kuma Kure ya hau ɓera. Sai Kure ya ƙi, ya ce tun da shi ne babba shi zai hau doki shi kuma Kurege ya hau ɓeran.

    Haka aka yi; suka kama hanya, kafin su isa sai Kurege yace in sun je shi zai ɗaure abin hawansa a jikin bishiya, sai Kure yace shi ne zai ɗaure a jikin bishiya, domin shi ne babba. Sai Kurege yace to shi zai ɗaure nasa a jikin ciyawa. Da suka isa garin birrai aka yi musu maraba, aka ba su masauki, shi Kure ya ɗaure abin hawansa a gindin bishiya, shi kuma Kuregeya ɗaure nasa abin hawan a jikin ciyawa.

    Suna zaune a masauki aka ce za a kawo musu giya don liyafar baƙunta. Kafin a kawo sai Kurege ya ce ya kamata su yi waƙa. Suka fara waƙa. Kurege yana rerawa yana cewa: “Ni da ƙananan nake wasa, Da ƙananan nake abota.” Shi kuma Kure yana waƙa yana cewa: “Ni da babban nake wasa, Babba na kama, A wasan ruwa mai daɗi” Sai manyan birrai suka ji abin da Kure yake faɗa, sai suka kawo musu giya a ƙwarya.

    Kure yana ta sha, Kurege kuma ya yi kamar tare suke sha amma in ya zuba a ƙoƙo sai ya kwara a jikin shinge, shi kuma Kure ya yi ta shan giya har ya yi tilis. Su kuma manyan birrai suna ta shiri don su rama abinda Kure da Kurege suka yi musu. Nan take birrai suka ƙwala ihu, suka ce a kawo sanduna za su ɗauki fansa. Suka ɗebo sanduna suka nufi kan Kurege da Kure.

    Shi kuma Kure ya riga ya yi tilis da giya ta yadda ba ya jin abinda ake faɗa. Sai ya tambayi Kurege ko me suke cewa a waje? Sai Kurege ya gaya masa cewa an ce a kawo musu farfesun ƙashi da nama. Da Kure ya ji haka sai ya gyara zama, yana dariya da murna wai za a kawo musu nama da ƙashi. A daidai lokacin da birrai suka shigo da sanduna za a fara ma Kurege da Kure, sai Kurege ya kutsa ta jikin shinge, inda yake kwarar da giya, ya gudu.

    Kure kuwa ba zai iya gudu ba, saboda haka suka yi ta jibgar sa. Bayan Kurege ya fita ta baya, kafin su biyo shi har ya hau kan ɓera. Yana taɓa shi sai ya fara gudu. Shi kuma Kure kafin ya fito ya kwance dokinsa daga jikin bishiya, ya rigaya ya sha sanduna har ya faɗi ya suma. Suka ɗauke shi, suka ɗora shi a kan dokinsa, suka kora shi gida. Ya isa gida a galabaice, ya yi ta jinya da kyar ya warke. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Son zuciya, ɓacin zuciya

    Wannan tatsunya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Daya)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Daya)

    Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Daya)

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Kurege da Kura suna yawo, sai suka tsinci ƙyallen fatari. Sai Kurege ya ce, bari ya je ya ɗinka musu riguna da shi. Ya je ya ɗinko riguna biyu, amma girmansu ɗaya. Ya bai wa Kura ɗaya. Da Kura ta saka sai rigar ta matse ta, ta shaƙe mata wuya saboda ta yi mata kaɗan.

    Sai Kurege ya ce da Kura tun da rigar nan ta yi mata kaɗan, sai ta bar masa ita. Da Kura ta ji haka sai ta ce masa: “Daman ka cuce ni ne tun da ka ɗinka rigata daidai da taka, sai ka ɗauka.” Kurege ya haɗa duka biyun, suka shiga jeji don su farauto abinda za su ci. Da suka kamo namun daji da yawa sai suka dawo gindin wata bishiya, suna hutawa.

    Kurege yana so ya cinye namanshi kaɗai, amma ya rasa yadda zai yi. Can sai ya hango wasu ‘yanmata a bakin rafi, sai ya dubi Kura ya ce: “Ga ‘yan mata can, mu je mu yi musu magana. “Sai Kura ta yarda, suka je suka tarar da ‘yan matan suna hira. Suka zauna suna sauraron hirar.

    Da Kurege ya ga hira ta fara yin daɗi sai ya ce da Kura su je su dafa naman nasu. Sai Kura tace ita tana nan a wurin hira, ba za ta je ba. Shi kuwa Kurege sai ya je domin ya dafa musu naman. Ashe ya sami abin da yake so, wato sai ya zaɓi nama mai kyau ya zuba a jakarsa, ya ɓoye. Sai ya samo naman mushe ya dafa, ya ajiye wa Kura. Bayan ta dawo sai ya miƙa mata nama.

    Kura ta hau ci ba ta san mushe ya dafa mata ba. Ta ci nama, irin cin haɗama, amma ta ɗan rage ta ɓoye a jakarta. Kura ba ta da masaniyar cewa Kurege ya ɓoye nama mai kyau, ya ba ta mushe. Saboda wayo irin na Kurege, sai ya dubi Kura ya ce: “Kura ki rage mini naman mana. Saboda haɗama irin ta Kura ita ma sai ta harari Kurege tace:
    Ni ba zan ba ka ba tun da kai ne ka dafa, na san sai da ka zaɓi inda ya fi ko ina daɗi ka ci ka ƙoshi, ba zan ƙara maka ba.

    Da rana ta faɗi, kuma dare ya yi sai suka samu wata bukka suka kwanta, can cikin dare sai zawayi ya kama Kura. Ta nemi Kurege ya raka ta, sai da rana ta faɗi, kuma dare ya yi sai suka sami wata bukka suka kwanta ki, ya ce in zawayin yana damunta, to ta fita waje. Ya ƙara da cewa: “Idan ma abin ya dame ki ai sai ki yi shi a kwance ba sai kin tashi ba.

    Amma idan na ji ihu to babu lafiya, idan kuma abin ya yi tsanani, idan kuma kin yi shiru to lafiya kenan. Sai Kura ta fita waje ta yi kwanciyarta. Jim kaɗan sai kunama ta harbe ta. Kura da raki sai ta ƙwala ƙara, haka dai ta kwana tana zawo. Wayewar gari ke da wuya, sai ta je ta faɗa wa Kurege cewa jiya da daddare kunama ta harbe ta.

    Sai Kurege ya ce: “Ai dama mun yi da ke idan na ji shiru lafiya ta samu, idan kuma na Ji ihu to ta yi tsanani sai in fita in taimaka miki. “Bayan Kura ta ji bayanin Kurege, sai ta ce: “To shi ke nan.” Da suka gama maganganunsu, sai Kurege ya rasa yadda zai yi ya ɗauki naman da ya ɓoye ya kai gida, domin ya sani idan Kura ta gani za ta ƙwace. Sai ya yi dabara ya ba Kura shawara ta je ta sha ruwa, ta wanke jikinta kafin su tafi gida.

    Ba tare da zaton wani abu ba, sai ta kama hanyar rafi. Da Kurege ya ga ta tafi rafi, sai ya ɗauko namansa a inda ya ɓoye, ya saka shi a jakar Kura, shi ma ya shiga cikin jakar. Da ta dawo daga wanka, sai ta ɗauki jakarta ta rataya. Ba ta san Kurege yana cikin jakar ba, sai ta kama hanya. Daɗin waƙa ya sa ta kama hanyar gida ta fara tafiya, ta manta da Kurege.

    Tana cikin tafiya sai ta fara yi wa Jakarta waƙa tana cewa. “Sai ni Kura durungu, Na yi farauta, Na cika jakata da nama, Nama sai mun ture, Ga shi a cikin jakata.” Haka ta rinƙa yi wa jakar waƙa. Sai da ta isa gida ta tuna ta bar cikin jakar Kura, riƙe da namansa ya gudu zuwa gidansa. Shi ya sa duk wanda ya je daji zai ga Kura tana ta yawon nema nai. Shi kuma da za ku je gidansa, za ku tarar da gidan cike yake da nama mai kyau, wanda yake ci ya more. Da babu Gizo da na yi muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Karamin mai hankali ya fi babba mai wauta.
    • Wauta mai janyo wuya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kishiyoyi Biyu

    Edita@rumasau-kallamu