Ga ta nan, ga ta nanku.
An yi wata tsohuwa mai ‘ya’ya uku mata. Sannu a hankali suka girma, har suka kai munzalin aure. Saboda haka ta ce da kowaccensu ta fid da mijin aure. Nan da nan Allah ya ba kowacce wanda za ta aura. Suka yi aurensu, kowacce ta tare a gidan mijinta a garuruwa daban-daban.
Bayan ‘yan kwanaki kaɗan, sai tsohuwa ta ce ya kamata ta ziyarci kowacce a gidanta a garuruwan da suke. Ta fara da zuwa garin ‘yarta ta fari ta tarar kusan dukkan mutanen garin kowa maye ne. Ga shi kuma suna da jela da kunnuwa dogaye, kamar dodanni. Ta tambayi inda gidan ‘yarta yake. Mutane suka kwatanta mata.
Da ta je gidan ‘yarta ta karɓe ta a cikin murna matuƙa. Ita ma ‘yar ta zama mayya, tana kuma da wutsiya da dogayen kunnuwa. Sai uwar ta tsorata. Ko da yake an karɓe ta da fara’a, ta yi tunanin cewa ya kamata ta koma garinsu da wuri. Ba da sanin uwar ba ashe ‘yar da mijinta sun shirya a kan za su cinye ta cikin daren.
Da dare ya yi sai suka saɗaɗa cikin ɗakin da suka saukar da ita a ɓoye, amma suka tarar ba ta yi barci ba. Sai suka koma a kan cewa washe-gari za su ƙara yin ƙoƙari ko za
su same ta ta yi barci. Ita kuma ganin haka sai ta shirya da sassafe za ta gudu ta bar garin. Gari yana wayewa, ko ban kwana ma ba ta yi da su ba, ta kama hanya.
Ta shiga dajin Allah tana ta hanzari ba ta tsaya ba sai gidan ‘yarta ta biyu. Ita ma wannan ‘yar ta karɓe ta da murna ƙwarai, sai dai ta gaya wa uwar cewa a ƙauyen idan dare ya yi sukan rikiɗa su zama fari, su je su kwana a kan wata bishiya. Uwar ta ce ba ta damu ba, za ta bi su.
Da dare ya yi dukkan mutane suka koma bayan gari suka rikiɗa, suka zama fari. Suka ɗunguma gaba ɗaya sai kan itacen da suka saba kwana. Tsohuwa dai ba ta bi su ba, ta zauna ita kaɗai a gida. Ba a daɗe ba hadari ya taso, aka yi ruwan sama mai yawa, ta jiƙe sarai. Da gari ya waye sai ta bar wannan garin ta nufi ‘yarta ta uku.
Da ta je garin sai ta tarar mutanen suna soya naman shanu. ‘Yarta ta karɓe ta da hannu bibbiyu. Sun ɗan sammata naman amma da gargaɗin cewa kar ta cika cikinta domin a garin ba a ƙashi da fitsari. ‘Yar ta ce in fa ta karya dokar to Sarkinsu zai sa a kashe ta. Uwar ta yi banza da gargaɗin; ta ci naman sai da ta ƙoshi.
Can cikin dare ta ta-da ‘yarta a kan cewa tana so ta je bayan gari. ‘Yar ta ce: “To, ba ga abin da na gaya miki ba. Daman na gaya miki abin da ke faruwa a garin.” Ba da ɓata lokaci ba ta ɗauki uwar ta kai ta bayan gari. Da gari ya waye sai mutanen garin suka dinga jin wari ta ko’ina, suka je suka shaida wa Sarki.
Sarki ya ce lalle akwai wani baƙo da ya shigo garin. Da ‘yar ta ji haka sai ta yi maza ta ɗauke mahaifiyarta, ta raka ta har sai da ta bar garin. Sarki ya aika a nemo ta, amma ba su gan ta ba. Ta riga ta gudu. Tsohuwa tana kan hanyar komawa gida ne ta gamu da wani mutum. Bayan sun gaisa sai ta tambaye shi ko zai ci naman da ta yo guzurinsa.
Ta ce da mutumin idan ya ci naman ya je garin ya yi kashi, zai sami wata kyauta. Mutumin kuwa ya karɓi naman ya ci. Da ya je garin ya yi kashi sai aka kama shi. A maimakon a ba shi wani abin arziki sai suka kashe shi a zaton shi ne ya yi kashin nan na kwanan baya. Ita kuma tsohuwa ta koma ƙauyenta lami lafiya. Ta ɗauki
alƙawari cewa ba za ta ƙara karambanin zuwa ziyarar ‘ya’yanta ba. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
- Kwaɗayi mabuɗin wahala.
- Wajibi ne ga baƙo ya saurari gargaɗin masu masaukinsa.
- Kowane tsuntsu, kukan gidansu yake yi.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Dogarawa Uku
Edita@rumasau-kallamu










