Tag: Ramadan

  • Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

    Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su

    Halayen mai Azumi – Akwai waɗansu muhimman halaye da ya kamata mai azumi ya siffanta da su; a gan su da gaske a tattare da shi. Cikin halayen akwai:

    1. Haƙuri, wato mai azumi ya siffantu da haƙuri wanda shi zai zama jagaba a cikin lamuransa; ya hana shi bin son zuciya da saɓa wa Allah. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce “Idan ɗayan ku yana azumi, kada ya yi maganganun fasiƙanci. Idan wani ya zage shi, ya ce Ni mai azumi ne” (Sahihul Bukhari 1894, Sahih Muslim 1151).

    2. Riƙon amana, yana da kyau mai azumi ya zama mai riƙon amana; domin tana daga cikin abar da za ta taimaka masa wajen kiyaye azuminsa.

    3. Rahama, ana son mai azumi ya siffantu da rahama, da sakin hannu da karamci, da kuma yalwar zuciya. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, yana da kwatankwacin ladan wanda ya ciyar ba tare da an rage ladan wanda aka ciyar ɗin ba” (Sunan al-Tirmizi 647, Sunan Ibn Majah 17).

    4. Nasiha, yana da kyau mai azumi ya kasance mai yin nasiha da kuma umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.

    5. Sulhu, mai azumi yana da kyau ya kasance mai yin sulhu da sasanta mutane; musamman la’akari da cewa ƙiyayya da gaba na kawo tsaiko wajen karɓar ibada da addu’a.

    6. Kame harshe, ya kamata mai azumi ya kame harshensa daga maganganu na shirme da shashanci, sannan ya nesanci giba, zagin mutane da yi musu ƙage ko sharri da ƙarya ko musu marar dalili; musamman abin da ya shafi siyasa ko wasan ƙwallo ko wanin waɗannan.

    An karbo hadisi daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Wanda duk bai bar faɗin magana ta zur da aiki da ita ba; to Allah ba shi da buƙatar ya bar cinsa da shansa”. (Bukhari 4/99).

    Haka nan wani hadisin dai daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) dake cewa; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ba azumi ba ne barin ci da sha, shi azumi shi ne na yasasshen zance da batsa; ko da wani ya zage ka, ko ya yi maka wauta, to ka ce; “Ni mai azumi ne”. (Ibn Khuzaima 1996). Ibnu Majah ya fitar da hadisi mai ɗauke da razani ga mai yin maganganun banza a yayin da yake azumi, ya ce; “Sau da yawa wani mai azumin ladansa shi ne yunwa da ƙishirwa”.

    7. Rintse ido da kame farji, yana da kyau mai azumi ya rintse idanuwansa daga kallon haramun; ya kuma kare farjinsa daga dukkanin haramtattun abubuwa. A nan muna jan hankalin waɗanda ke ganin kallon fina-finai ko tashoshi na gusar musu da yunwa; haƙiƙa wannan kuskure ne babba da kuma munana zato ga Allah, da kuma keta iyakokin Sa. Su ma masu sanya fina-finai a tashoshi wajibi su ji tsoron Allah; su sani ribar rayuwa da albarkar abin da suke so shi ne ginawa bisa tafarkin Musulunci.

    8. Iklasi, ya kamata mai azumi ya ƙudurce cewa lalle yana yin wannan azumin ne saboda Allah; kuma domin neman yardar Allah, ba domin mutane su yabe shi ba. A nan, ana jan hankalin yan’uwa masu yin sadaka ko ciyar da masu azumi da masu tafsirin Alkur’ani; da limamai masu rera tilawa, da masu zuwa Umarah, da sauran aiyuka nagari; wajibi su sanya iklasi kada shaiɗan ya lalata musu ayyukansu.

    9. Bin sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam); wajibi ne mai azumi ya nesanci bidi’o’i, ya tsaya kan sunna ka’in da na’in; domin kyakkyawan aiki yana cikin koyi da Fiyayyen Halitta (Sallallahu Alaihi Wasalam).

    10. Tarbiyya, wajibi ne mai azumi ya tsaya wajen ƙoƙarin tarbiyyantar da kansa da ‘ya’yansa; ko ‘yan’uwansa ko waɗanda yake da iko a kansu. Kuma iyaye su ɗauki wannan wata a matsayin lokacin roƙarwa ‘ya’yansu shiriya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Aiyukan Mai Azumi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Niyyar Ɗaukan Azumi

    Niyyar Ɗaukan Azumi

    Ana ɗaukar niyyar azumi ne kafin fitowar alfijir; saboda hadisin da Nana Hafsat (R.A) ta rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa: “Wanda bai ɗauki niyyar azumi da dare ba (kafin fitowar alfijir) ba shi da azumi”.

    (Sheikh Nasiruddeen Albani ya yi tahƙiƙinsa a cikin Sahih Jami’ al-Saghir, 6536).

    Sannan a yayin niyya, ba a ƙulla ta da lafazin cewa, na yi niyyar yin azumi, a’a ana ƙulla ta ne a zuci, da zimmar gobe zan tashi da azumi idan Allah ya kai mu rai da lafiya.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Ayyukan Mai Azumi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Rashin Yin Sallah A Cikin Jama’a Na Lalata Azumi? danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Watan Ramadan (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Mafifitan Ayyukan Mai Azumi

    Mafifitan Ayyukan Mai Azumi

    Ayyukan Mai Azumi – Akwai ayyuka mafifita da ya kamata mai azumi ya kusance su; daga ciki akwai:

    1. Karatun Alƙur’ani Mai Girma, wato mai azumi ya lazimci karatun Alƙur’ani da kuma fahimtar saƙon da yake cikinsa, amma idan ba za a iya karatun ba, to babu laifi a lazimci majalasin karatun, wato wajen da ake karantawa tare da fassara Alƙur’ani.

    Nana A’isha, Abu Huraira da Ibn Abbas (Radiyallahu Anhuma), sun faɗa cikin hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa, “Mala’ika Jibrilu ya kasance yana karanta wa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) Alƙur’ani a kowane dare na watan Ramadana, sau ɗaya a kowacce shekara, sai ya karanta masa sau biyu a shekarar da zai yi wafati”. (Sahihul Bukhari 4997 – 4998, Sahihu Muslim 2450).

    Wannan hadisi ya nuna cewa karatun Alƙur’ani shi ne mafificin aikin ibada ga mai yin azumi a watan Ramadana, don haka, sai a himmatu da karatunsa.

    2. Kyauta, ana son mai azumi ya yawaita kyauta ta hanyar ciyar da jama’a da kuma sakin hannu gare su, da taimakon gajiyayyu da makusanta. An karɓo hadisi daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fi kowa kyauta, kuma ya fi yawaita kyautarSa a cikin watan Ramadan, musamman a lokacin da yake ganawa da Mala’ika Jibrilu. (Bukhari 4997).

    Haka nan Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce, “Alherin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fi sakakkiyar iska”. (Bukhari 1902).

    3. Sallar Nafila, ana so mai azumi ya yawaita nafila, musamman Ƙiyamul Laili (wato sallar dare); saboda kwaɗaitarwar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya yi cikin hadisin Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa, “Duk wanda ya tsaya yin sallar Ƙiyamul Laili, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa da suka gabata”. (Bukhari 2009).

    Haka nan cikin hadisin Abu Dharrin Alghiffariy (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Wanda ya yi sallar asham tare da liman, har ya idar, za a rubuta masa ladan ƙiyamul laili”. (Sunan Tirmizi 646, Ibnu Majah 1327).

    4. Yawaita zikiri, ana son mai azumi ya yawaita yin zikiri da salatin Fiyayyen Halitta (Sallallahu Alaihi Wasalam); domin akwai gwaggwaɓan lada ga yin zikiri da salatin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam).

    5. Ciyar da mai azumi abin buɗa-baki, yana daga cikin mafificiyar ibada ciyar da masu azumi abin buɗa-baki. Hadisi ya tabbata daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa; “Duk wanda ya ciyar da mai azumi abin da zai yi buɗa-baki, yana da kwatankwacin ladan mai azumin, ba tare da an rage ladan wanda ya ciyar ba”. (Sunan Tirmizi 647, Ibnu Majah 1746).

    A nan, muna jan hankalin masu hali a kan su taimaka wa mabuƙata, musamman makusantansu. Domin za ka iske mutumin da yake da hali a unguwa; amma kaso mafi yawa suna rasa abin da za su yi buɗa-baki, a wani lokacin kuma, masu ƙoƙarin yin sadakar ma, za ka iske suna yi ne cikin rashin kyautatawa, face kaɗan. Yana da kyau masu hali da shugabanni su gane, taimakawa a irin wannan lokaci; cikin iklasi da neman yardar Allah, wallahi rabautuwarsu ce. Amma ina tausayi da rahama, kai ka ci mai kyau, amma maƙwabtanka suna fama da yunwa!

    Yana da kyau ku ciyar daga mafi kyawun dukiyarku; kuma cikin abu mai kyau; tare da sakin zuciya da jin dadi da walwala.

    6. Umarah, yin Umarah cikin watan Ramadana na daga cikin mafifitan ayyuka; don haka, mutumin da yake da iko sai ya ɗauki azama. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Yin Umarah a cikin watan Ramadan daidai yake da aikin Hajji”. A wata ruwayar kuma Ya ce, “Wanda ya yi Umarah a watan Ramadan; tamkar ya yi aikin Hajji ne tare da Ni”. (Sahihul Bukhari 863).

    A nan ma, muna ƙara jan hankali, musamman ga waɗanda sun yi Umara; amma suna ta ƙara maimaitawa, alhali maƙwabtansu na fama da yunwa, da baƙin talauci. Ku sani, duk da wannan falala ta Umara ta nafila; duk da wannan lada, ciyarwa ita ta fi sama da Umarar da za ka tafi, alhali ga maƙwabtanka; ko danginka na fama da yunwa, da wahala ta rashin abin da za su ci, idan za su yi sahur; ko za su ci, idan za su yi buɗa-baki.

    Kuskure ne alhazan ke yi, sun je, ba sau ɗaya ba; ba sau biyu ba, su ƙara niƙar gari su tafi, alhali ga mabuƙata nan a kewaye da su.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Suke Ɓata Azumi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Idan Nayi Haɓo Da Azumi A Bakina, Yaya Azumina Zai Kasance?

    Idan Nayi Haɓo Da Azumi A Bakina, Yaya Azumina Zai Kasance?

    Idan Nayi Haɓo Da Azumi A Bakina Kafina Sha Ruwa, Yaya Azumina Zai Kasance?

    Amsa: Duk wanda haɓo ya same shi, kuma da azumi abakinsa, babu komai, azuminsa na nan daram.

    Hujja: (Daarul Ifata’i Almisiriya). (Alajnatu da’ima lilbuhusul ilmiya wal ifta’i 10/264).

    Domin karanta cikakken bayani akan Ina Alwala, Na Haɗiye Ruwa Garin Kurkure Baki, Yaya Lafiyar Azumina? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Na Ɗanɗana Miya, Na Tofar Ban Haɗiye Ba, Ya Batun Azumina? danna nan.

  • Idan Na Shaƙi Hayaƙin Turaren Wuta Ko Turaren Ƙamshi Na Ruwa, Ko Na Sakawa A Ɗaki, Yaya Azumina?

    Idan Na Shaƙi Hayaƙin Turaren Wuta Ko Turaren Ƙamshi Na Ruwa, Ko Na Sakawa A Ɗaki, Yaya Azumina?

    Amsa: Idan mutum ya shaƙi hayaƙin turaren wuta, ko turaren ƙamshi na ruwa, babu komai, azuminsa na nan daram.

    Hujja: (littafin Fatawa 55455, littafin Farawa 107799).

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Nayi Haɓo Da Azumi A Bakina Kafina Sha Ruwa, Yaya Azumina Zai Kasance? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ina Alwala, Na Haɗiye Ruwa Garin Kurkure Baki, Yaya Lafiyar Azumina? danna nan.

  • Idan Na Shaƙi Mantaleta Ko Rob Ko Na Saka Aleɓe, Shin Yaya Makomar Azumina?

    Idan Na Shaƙi Mantaleta Ko Rob Ko Na Saka Aleɓe, Shin Yaya Makomar Azumina?

    Amsa: Idan mutum ya shaƙi Mantaleta ko Rob, ko kuma ya shafa aleɓe, babu komai; azuminsa na nan daram.

    Hujja: (Littafin fatawa lamba 55455, littafin fatawa lamba 107799).

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Na Shaƙi Hayaƙin Turaren Wuta, Yaya Azumina? danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane danna nan.

  • Idan Na Ɗanɗana Miya, Na Tofar Ban Haɗiye Ba, Ya Batun Azumina?

    Idan Na Ɗanɗana Miya, Na Tofar Ban Haɗiye Ba, Ya Batun Azumina?

    Idan na ɗanɗana miya domin naji fitowar gishiri, amma na tofar ban haɗiye ba, yaya batun azumina?

    Amsa: Idan mutum ya ɗanɗana miya, gishiri, suga, zuma, zobo, juicy, azuminsa na nan matsawar bai haɗiye ba.

    Hujja: “Wanda yaci ko ya sha, bisa mantuwa, azuminsa yana nan”.

    Marawaici Abu Huraira, littafi Sahihul Bukhari Sahihu Muslim.

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Na Shaƙi Mantaleta, Rob Ko Na Saka Aleɓe, Ya Makomar Azumina? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Watan Ramadana 1 danna nan.

  • Ina Alwala, Na Haɗiye Ruwa Garin Kurkure Baki, Yaya Lafiyar Azumina?

    Ina Alwala, Na Haɗiye Ruwa Garin Kurkure Baki, Yaya Lafiyar Azumina?

    Amsa: Mutumba zai rama azumi ba, idan ya haɗiye ruwa lokacin kurkurar baki, bada ganganci ba; a cikin alwala ko ba acikin alwala ba.

    Hujja: “Allah ya yafewa al’ummata abubuwa guda uku, kuskure da mantuwa da kuma abinda aka tilasta su a kai”.

    Marawaici Ibn Abbas, Sunan Ibn Maajah, Sahihu Ibnu Hibban, Mu’ujamu Ɗabara’ni.”Ba ku da laifin abinda kuka yi bisa kuskure, sai abinda zuciyarku tayi da gangan”. Suratul Ahzab aya 5.

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Na Ɗanɗana Miya, Na Tofar Ban Haɗiye Ba, Ya Batun Azumina? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Ranar Arfa danna nan.

  • Shin Rashin Yin Sallah A Cikin Jama’a Na Lalata Azumi?

    Shin Rashin Yin Sallah A Cikin Jama’a Na Lalata Azumi?

    Amsa: Rashin yin sallar jam’i baya lalata azumi, matsawar mutum yana yin sallar a kan lokaci; kawai dai yana tabka asarar lada mai yawa.

    Hujja: “Sallar mutum acikin jama’a, tafi sallarsa shi ɗaya a kasuwa ko gida da lada ashirin da biyar ko lada ashirin da bakwai”. marawaici Abu Huraira, Ibn Umar, littafi Sahihul Bukhari.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ina Alwala, Na Haɗiye Ruwa Garin Kurkure Baki, Yaya Lafiyar Azumina? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Abubuwan Da Ba Sa Ɓata Azumi danna nan.

  • Abubuwan Da Ba Sa Ɓata Azumi

    Abubuwan Da Ba Sa Ɓata Azumi

    Ɓata Azumi – Kasancewar azumi ibada ce, ibada ce da ake kusantar Mahalicci da ita. Sanin kowane ɗaya cikin ɗaiɗaikun mutanen dake karatu kuma suna fahimtar karatun cewa; ba manufar Ubangiji ba ce ƙuntata musu a cikin rayuwa, ba sauƙi ake nufin su da shi.

    Hakan ya sanya, aka halattawa mai yin azumi wasu al’amura, ko kuma idan mai azumi ya tsinci kansa cikin wasu, to ba komai a kansa. Cikin waɗannan abubuwa akwai:

    1. Idan alfijir ko safiya ta riski mai azumi da janaba ta kusantar iyalinsa a cikin wannan dare, to babu komai na ramuwa a kansa, kuma azuminsa yana nan, abin da ke kansa kawai shi ne wanka.

    Domin hadisi ya tabbata daga Nana A’isha Radiyallahu Anha cewa, “Lalle Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance alfijir yana samunSa alhali da janabar saduwa da iyalinsa da dare, sannan ya yi wanka ya ci gaba da azuminSa”. (Bukhari 4/123, Muslim 1109).

    2. Asuwaki, yin asuwaki ga mai azumi halattaccen abu ne, domin a kansa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa ya yi, “Da ba don kada na tsaurarawa al’ummata ba, da na umarce su da yin aswaki a yayin kowacce alwala”. (Bukhari 2/311, Muslim 252).

    A nan, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) bai keɓance mai azumi da waninsa ba; da wannan sai ya zamto dalili ne dake nuni a kan halaccin yin aswaki ga mai azumi. Haka zalika, wannan hukuncin ya game kowane lokaci; kafin faɗuwar rana ko bayanta.

    Game da irin asuwakin da za a yi amfani da shi; babu bambanci tsakanin ɗanye ko busasshe; domin a kan haka ne Imamul Bukhari ya yi babi a cikin ingantaccen Littafinsa a kan yin amfani da ɗanye ko busasshen asuwaki. Ibn Sirin ya ce; “Babu laifi ga mai yin azumi ya yi amfani da ɗanye ko busasshen asuwaki”. Sai aka ce masa; ai ɗanye yana da ɗanɗano. Sai ya ce; “Shin ruwa ba shi da ɗanɗano amma kuke kurkure baki da shi?”.

    Wannan kuma ita ce magana mafi rinjaye a wurin malamai; domin da aka ambaci Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) na yin asuwaki, ba a bambance ɗanye ko busasshe ba; ga mai azumi ko maras azumi ba. Bisa haka, mai azumi zai iya goge baki da man goge haƙora na zamani; kasancewar yadda ɗanyen asuwaki yake da shi. Sai dai kuma ya kamata a yi hattara kada a haɗiye”.

    3. Shaƙa ruwa da kurkurar baki, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance yana shaƙa ruwa tare da kurkure bakinsa, alhali yana azumi; sai dai ya hana wuce gona da iri wajen yin hakan da cewa; “………ka kai matuƙa wajen shaƙa ruwa sai idan kana azumi”. (Tirmizi 3/146, Abu Dawud 2/308).

    4. Runguma da sumbata ga mai yin azumi, Nana A’isha (Radiyallahu Anha) ta ce; “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance yana sumbata, kuma yana runguma alhalin yana azumi, sai dai shi ya kasance ya fi ku mallakar kansa daga sha’awa”. (Bukhari 4/131, Muslim 1106).

    Amma an karhanta yin hakan ga saurayi ban da tsoho, dogaro da hadisin Abdullahi Ibn Amru Bn Ass (Radiyallahu Anhu) wanda ya ce; “Mun kasance wajen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) sai wani matashi ya zo, sai ya ce; “Ya Manzon Allah, zan iya sumbata alhali ina azumi?”. Sai Ya ce masa “A’a”. Sai wani dattijo ya zo, ya ce; “Zan iya sumbata alhali ina azumi?”. Sai Ya ce masa “Eh”. Sai muka dinga kallon junanmu, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Shi dattijo yana iya mallakar kansa”.
    Da wannan hadisin malamai suka kafa hujja wajen rungumar mace, amma ba kowa ba, dattijo kaɗai ke iya yi.

    5. Ƙarin jini ko allura idan ba ta ƙoshi ba ce, ko sanya maganin ciwon idanu, Imam Hasanul Basri ya ce; “Babu laifi mutum ya ɗiga magani a hancinsa idan bai kai zuwa ga maƙoshinsa ba……”.

    6. Ƙaho, ya zo cikin hadisin Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa, “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya yi ƙaho alhalin yana azumi”. (Bukhari 4/155).

    7. Ɗanɗana abinci, ya halatta mai azumi ya ɗanɗana abinci amma kar ya wuce maƙogwaro, domin ya zo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa: “Babu laifi da ɗanɗana ruwan khal ko wani abu matuƙar dai bai shiga maƙogwaronsa ba alhalin yana azumi”. (Bukhari 4/154).

    8. Zuba ruwan sanyi a kai ko a jiki, Imam Bukhari ya yi babi a cikin ingantaccen Littafinsa mai taken “Babin wanka ga mai azumi”, inda ya kafa hujja da dalilai kamar haka: Ibn Umar ya jiƙa kaya da ruwa ya sanya alhali yana azumi. Haka Imamu Sha’abiy ya shiga banɗaki alhali yana azumi. Hasanul Basri ya ce: “Babu laifi, da kurkurar baki da jiƙa jiki ga mai azumi”.
    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance yana zuba ruwa a kayansa saboda ƙishirwa ko zafin rana alhali yana azumi.

    9. Haɗiye yawu ma ba ya ɓata azumi.

    10. Mutumin da yake azumi, sai ya kalli matarsa ba tare da ya taɓa ta ba, sai ya fitar da maniyyi, to azuminsa na nan. Dalili kan wannan shi ne hadisin Jabir Ibn Zaid (Radiyallahu Anhu) a inda ya ce: “Wanda ya kalli mace, ya fitar da maniyyi, ya ci gaba da azuminsa, babu komai a kansa”.

    Imamus Shafi’i, da Imamus Thauri, da Imamul Auza’i duk sun tafi a kan cewa; babu wani dalili da ya zo cewar fitar da maniyyi kaɗai yana karya azumi, ba tare da jima’i ba. Amma idan jima’i ne ko an fitar da maniyyi ko ba a fitar ba; to yana karya azumi, kuma sai an yi kaffara. Haka kuma wanda ya sumbaci matarsa, sai ya fitar da maniyyi; shi ma azuminsa na nan, wannan shi ne zance mafi rinjaye.

    Sai dai wasu daga cikin malaman Malikiyya suna ganin fitar da maniyyi ta hanyar kallo ko runguma yana karya azumi; kuma akwai ramuwa da kaffara a kai. Amma idan maniyyi ne kawai, akwai ramuwa ba tare da kaffara ba. Sun kafa hujjar cewa abin da ake buƙata a jima’i shi ne fitar maniyyi; saboda haka fitar maniyyi ta wannan hanyar daidai yake da jima’i.

    Amma sauran malamai sun yi musu raddi da cewar hukuncin da nassin ya zo da shi; ya ambaci jima’i ne kawai, ba fitar da maniyyi ba. Sannan suka ƙara da cewar idan mutum ya yi jima’i ba tare da fitar da maniyyi ba; ai zai rama azumi kuma ya yi kaffara. Haka kuma, da a ce fitar da maniyyi ne kawai, da sai a ce mai barci ma idan ya yi mafarki; ya fitar da maniyyi, sai ya yi kaffara. Wallahu a’alam.

    11. Shafa mai ko turare ba sa karya azumi, kamar yadda ya zo daga fatawar Abdullahi Ibn Mas’ud (Radiyallahu Anhu) cewa; “Idan ɗayanku yana azumi, zai iya shafa mai, kuma ya taje kansa”. Haka kuma Abu Ƙatada Al’ansari (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Mustahabbi ne mutum ya shafa mai domin ya kawar da kura daga jikinsa”.

    Cikin malaman Mazhabar Malikiyya kuwa, Mutraf, da Abdulhakam, da Asbag duk sun ce ya halatta a shafa mai; kuma ba su bambance tsakanin mai ƙamshi da marar ƙamshi ba.

    Haka kuma sanya kwalli shi ma ba ya karya azumi; kamar yadda Imam Alzuhri, Ibn Majishun; da Mutraf, da Asbag, da Laith da Ibn Habib duk sun ce babu laifi.

    12. Shaƙar maganin asma ma ba ya karya azumi; kamar yadda Ibn Taimiyya da sauran malamai kamar sa Ibn Baz da Uthaimin da sauransu suka faɗa game da mai asma, zai iya shaƙa

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ramuwar Azumin Ramadan danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.