Tag: ilimin tarihi

  • Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci

    Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci

    Ba shakka addinin Musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa dangane da waƙafi a matsayinsa na sadaka; wacce ladan ta yake ɗorewa har bayan rayuwar wanda ya yi ta. Kamar yadda ya zo a cikin faɗin Allah Maɗaukakin Sarki; “Kuma ku tsayar da sallah kuma ku bayar da zakka kuma abin da kuka gabatar; domin kanku daga alheri za ku same shi a wurin Allah, lalle ne Allah ga abin da kuke aikatawa mai gani ne”. (Baƙara aya ta 110).

    Haka kuma ya zo a hadisin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana cewa; a lokacin da ɗan Adam ya rasu dukkan ayyukansa sun tsaya in ban da abubuwa guda uku; sadaka mai gudana (waƙafi), ko wani ilmi da ake amfana da shi; ko ɗa nagari da yake yi masa addu’a.

    Haka nan fassarar abin da ake nufi da sadaka mai gudana ta zo a wani hadisi da Ibn Majah ya ruwaito; wanda a cikinsa ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa; “Lalle abin da kawai zai cigaba da iske mumuni na kyawawan ayyukansa bayan mutuwarsa. Shi ne wani ilimi da ya yaɗa ko ɗa na ƙwarai da ya bari ko wani Alƙur’ani da ya bar gadonsa; ko wani masallaci da ya gina ko kuma gida da ya gina don (amfani) matafiya.

    Ko wata ƙorama da ya tona take gudana ko kuma wata sadaka da ya fitar daga cikin dukiyarsa; a lokacin da yake da lafiya sanda yake raye wacce ladanta zai ci gaba da riskarsa har bayan rayuwarsa”.

    Haka nan kuma ya zo a cikin littattafan sirah cewa; a lokacin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi Hijira daga Makka ya sauka birnin Madina. A duk faɗin birnin, babu wata hanya ta samun ruwan sha mai daɗi, sai wata rijiya da ake kira rijiyar Rumah, wacce a wancan lokaci mallakar wani marowacin mutum ce; wanda yake tsawwalawa mutane wajen sayen ruwanta.

    Ganin haka sai Ma’aiki Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwaɗaitar da sahabbansa da cewa; “Wane ne zai sayi rijiyar Rumah (ya sadaukar da ita) Allah ya biya shi da mafiticinta a gidan Aljannah wanda nan take kuwa Sayyidina Uthman ya saye ta dirhami dubu talatin da biyar, kuma Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi “Ka sadaukar da ita ga musulmai, Allah zai ba ka lada, shi kuwa bai yi wata-wata ba ya aikata hakan.

    Haka nan Bukhari da Muslim sun ruwaito daga sayyidina Umar ɗan Khaɗɗab (Radiyallahu Anhu) cewa; ya ce da ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na sami wata gona a Khaibara; wacce ban taɓa samun wata dukiya da ta kai darajarta a tsawon rayuwata ba”.

    Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; “Idan ka ga dama kana iya riƙe asalinta ka sadaukar da amfaninta da Sayyidina Umar. Ya ji haka sai ya sadaukar da ita bisa sharaɗin cewa, ba za a sayar da ita kanta gonar ko a kyautar da ita ko a ci gadonta ba; tare da sadaukar da duk wani amfani nata ga talakawa, da ‘yan uwa, da bayi; da hanyoyin ɗaukaka addinin Allah, da baƙi, da kuma matafiya.

    Babu laifi ga masu kula da ita su ci ‘ya’yan itatuwanta; su kuma yi kyauta ga abokansu gwargwadon yadda aka sani a al’adance ba da sayarwa ba.

    Wannan al’amari na waƙafi ya watsu matuƙa a cikin sahabban Ma’aikin Allah; tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bayan kwaɗaitarwar da ya yi da aikata hakan. Domin kuwa sun yi waƙafi na abubuwa daban-daban da suka haɗa da masallatai da gonaki; da rijiyoyi da kayan jihadi don ɗaukaka kalmar Allah.

    Ya tabbata cewa adadi mai yawa na sahabban Ma’aikin Allah; tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun yi waƙafi. Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Khalid ɗan Walid, da Jabir ɗan Abdullah, da Sa’ad ɗan Ubadah; da Ukbat Abdullahi ɗan Zubair, da Sa’ad ɗan Abi Waƙƙas, da uwar muminai Sayyidatina A’isha; da kuma Asma’u yar Abubakar – Allah ya yarda da su gaba ɗayansu.

    Babu wani mai hali daga cikin sahabban Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; wanda bai yi waƙafi ba, Haka kuma an rawaito daga Imam ash-Shafi’iya na cewa; “Labari ya ishe ni cewa mutum tamanin daga cikin sahabban ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; ‘yan Madinah kowanne a cikin su ya yi waƙafi” .

    Domin karanta cikakken bayani a kan Manufofin Waƙafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfani Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan

    Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmowar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma. Wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Magabata da Haihuwar Ɗanƙwairo

    Tarihin Magabata da Haihuwar Ɗanƙwairo

    Magabatan Musa Ɗanwaƙiro Maradun su ne; kakanninsa da mahaifinsa da mahaifiyarsa da yayansa da ‘ya’yansa da kuma sauran ‘yan’uwa na jininsa.

    Musa Ɗanƙwairo da magabatansa sun fito ne daga garin Ɗankadu ta cikin Gundumar Bakura ta jihar Zamfara ta yanzu.

    2.1 Usman Ɗankwanagga: Mahaifin Ɗanƙwairo

    Usman Ɗankwanagga shi ne ɗan Kaka Maiganga, kuma shi ne ya haifi Musa Ɗanƙwairo. Usman Ɗankwanagga da zuriyyarsa mutanen Ɗankadu ne da ke cikin Gundumar Bakura, kamar yadda bayanai suka gabata.

    Usmaan Ɗankwanagga manoni ne, mai jajircewa a ayyukan gona. Haka kuma makaɗi na noma ne wanda ya shahara sosai. Sannan ya gaji kiɗan noma daga mahaifinsa, Makaɗa Kaka Maiganga. Har wa yau kuma Usman Ɗankwanagga ya gwama kiɗan fada da kiɗan noma. A kiɗan fada ya kaɗa abin kiɗa na kotso ne.

    A wani ƙauli an nun a wajejen 1914 Usman Ɗankwanagga ya bar garinsa na asali; ya fita neman wani wuri da zai yi noma shi da iyalinsa. A wannan tafiya ce ya haɗu da Sarkin Maradun, Alhaji Ibrahim I (1903-1923) a wata gonarsa ta Bazamawa. A wannan haɗuwa ce Sarkin Maradun ya amince ya ɗauki nauyin Usman Ɗankwanagga da dukkan jama’arsa; shi kuma ya zama makaɗinsa. Daga nan ne Usman Ɗankwanagga ya zaɓi ya zauna Birnin Ƙaya gari mai dausayi da ƙasar noma mai albarka. Iyalin Usman Ɗankwanagga sun zauna a ƙasar Ƙaya a wani wuri da ake kira Tunga, mai yalwar ƙasar noma7.

    Bayan da Usman Ɗankwanagga ya tsufa, sai ya yi murabus; aka naɗa babban ɗansa Abdu Kurna Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun, mai amfani da kotso.

    2.2 ‘Yarnunu: Mahaifiyar Ɗanƙwairo

    ‘Yarnunu ita ce mahaifiyar Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Ita kuma ‘yar asalin Goran Namaye ce, Bazamfariya ce gaba da baya.

    2.3 Makaɗa Abdu kurna

    Shi makaɗa Abdu Kurna an haife shi ne a garin Ɗankadu, a cikin Gundumar Bakura; Ƙaramar Hukumar Bakura, Jihar Zamfara a yau a daidai shekara ta 1899 bisa ƙiyasi. Tare da Abdu Kurna ne Usman Ɗankwanagga ya baro Ɗankadu zuwa Tunga ta Birnin Ƙaya, Maradun. Makaɗa Abdu Kurna ya yi kiɗan noma da na masu Sarauta . Makaɗa Abdu Kurna ne ya gaji Halifar Mahaifinsa Usman Ɗankwanagga ta Sarkin Kiɗan Sarkin Muradun. An naɗa Abdu Kurna a matsayin makaɗa na Sarkin Maradun a yayin da mahaifin nasu Usman Ɗankwanagga ya tsufa; kuma ya roƙi a maye gurbinsa na sarautar kiɗa da babban ɗansa Abdu Kurna.

    2.4 Yanayin Haihuwar Musa Ɗanƙwairo (1909)

    Yanayin haihuwar Musa Ɗanƙwairo ya riski wani hali na ɓurɓushin tasirin da zai zo wa Hausawa da al’ummar Arewa na shigowar Turawan Mulkin Mallaka a ƙarƙashin jagorancin Sarauniyar Ingila. Duk da saɓanin tarihin haihuwa; an ɗauka an haifi Musa Ɗanƙwairo a 1909, jim kaɗan da tsayar da mulkin mallaka na Turawa a 1902.

    Haihuwar Musa Ɗanƙwairo ta wakana a garin Ɗankadu na gundumar Bakura a yau ta Jihar Zamfara; kafin iyayensa su koma Tunga, Birnin Ƙaya ta gundumar Maradun. An raɗa wa Ɗanƙwairo sunan yanka na Musa.

    Shi kuwa Ɗanƙwairo wata alkunya ce ake gaya wa Musa bayan da ya kai shekaru bakwai da haihuwa; kuma ya fara sa hannu a harka ta kiɗa da waƙa a ƙarƙashin mahaifinsa Makaɗa Usman Ɗankwanagga. A cikin mataimakan kiɗa na Usman Ɗankwanagga akwai wani baransa, wani mutum mai murya wasai; mai zaƙi da shiga jiki wanda ake yi wa laƙabi da Ƙwairo. To sai Musa ya gaji irin wannan murya, shi ne mahaifinsa Usman Ɗankwanagga yake faɗin; ‘Ga Ɗanƙwairo an mayas (Gusau, 1996: sh. 104). Bishiyar Nasabar Kaka da Iyayen Musa Ɗankwairo.

    Makaɗa Kaka Maiganga

    Binta Amina Usman na Ɗankwanagga
    Sa’idu Shayi
    Mairana Naruwa Ɗantomi16
    Ali Sabon Kiɗi
    Abubakar Muh Maigayya Amadu Zuwaira Lawali Umaru17
    Lawali Shamsiyya Aliyu Musa Ibrahim Nasfatu
    (a) (b) (c)

    = Karima = Yarnunu = Ba’u (Mora)
    Abdullahi
    (Yawale) Ya Rasu a Ilorin
    Abdu Kurna Hauwa Musa Ɗanƙwairo Binta (Maryam)
    Galadima Maituwo Amina “Yardaudu Ƙauna
    (Indo A’isha)
    Ambaye Amina ‘Yaddaudu (Dosara)
    Garba Sambo Mani Ige Ibrahim
    (Ɗandarali) (Zuma) Usman (Kahiyo)
    Tamaidaji20 Umaru Karɓa Iro Abdu
    (Tsahara) ɗankutuɓe Maikano
    Tashayi (Inno) Safiya (‘Yarkwando)

    15 Makaɗa Usman Ɗankwanagga ya koma sabon mazauninsa na Tunga, Birnin Ƙaya; a Gundumar Maradun tare da dukkan wannan zuriyya ta mahaifinsa Makaɗa Kaka Maiganga.

    16 Sauran ‘ya’yan Amina su ne: Mustafa da Ibrahim da Mukhtari da Talatu da Rabi da kuma Saratu.

    17 Saruan ‘ya’yan Ali Sabon Kiɗi su ne: Abubakar da Zuwaira da Rumasa’u da Lawali.

    18 Sauran ‘ya’yan Muhammadu Maigayya su ne: Amadu da Ladidi da Hamida da Nomau Libiris (Namagarya).

    19 A dubi ‘ya’yan Musa Ɗanƙwairo a 3.3.2.

    20 ‘Ya’yan Tamaidaji (Tsahara) su ne: Ta’inna (A’isha) da Muhammadu Magaji (Sarkin Gida) da Sale da Hassi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Iyalin Musa Ɗanƙwairo danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Haƙƙoƙin Shugabanni A Kan Mabiyansu

    Haƙƙoƙin Shugabanni A Kan Mabiyansu

    Haƙƙoƙin Shugabanni – Kamar yadda iyaye suke da haƙƙoƙi a kan ‘ya’yansu; haka su ma Shugabanni suke da haƙƙi a kan mabiyansu; kai haƙƙoƙin shugabanni sun ma fi na iyaye nauyi da cancantar a kula da su, saboda su iyaye ‘ya’yansu kaɗai suke kula da su; amma su shugabanni gaba ɗayan al’umma suke kula da su.

    Illolin saɓa wa iyaye ba sa yin naso mai yawa ta yadda zai shafi kowa; amma musibar da take biyo bayan saɓa wa shugabanni da yi musu tawaye; babu wanda ba ta shafa ba.

    Haƙƙoƙin shugabanni a kan mabiya a taƙaice;

    1. Yi wa shugabanni biyayya a fili da ɓoye, sai dai in sun yi umarni da a saɓa wa Allah; ko kuma sun hana a bi Allah, to a nan ba za a bi su ba.

    2. Yi musu nasiha da ba su shawarwari na gari; a fili da ɓoye tare da girmamawa da tausasawa da kuma mutuntawa. Ba tare da aibatawa ko suka ko zagi ko gallazawa ba.

    3. Taimaka musu da ƙarfafar su da goya musu baya; saboda ƙarfinsu ƙarfin Musulunci ne; rauninsu rauni ne ga Musulunci da musulmai. Kada a soma mara wa ‘yan adawa baya don a cutar da shugaba. Ko a hana ko a lalata wani aikin alhairi da yake yi ko kuma yake yunƙurin aikatawa.

    4. Girmama shi da mutunta shi, da ba shi matsayinsa a fili da ɓoye

    5. Faɗakar da shi da sanar da shi duk abinda zai kawo gyara da maslahar al’umma; ka da a yi ƙwauron magana; amma a iya a cikin ladabi da girmamawa. Haka zalika da nusar da shi kurakuransa, domin ya gyara duk wannan a yi a cikin girmamawa da tausayawa.

    6. Ba shi kariya gwargwadon ikon daga sharrin maƙiyansa; da masu yi masa hassada da sanar da shi ƙulle-ƙulle da makirce-makircen da suke shiryawa.

    7. Taimaka masa da goya masa baya domin ya sauke nauyin da yake kansa.

    8. Wayar da kan ‘yan adawa da maƙiyansa da fanɗararru domin su fahimce shi; su daina adawar da kangarar da suke yi masa.

    9. Taimakon sa da dukiyarka da harshenka da matsayin ka da jikinka; da duk abin da za ka iya a fili da ɓoye.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Ƙasar Hausa danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Za su Taimaka wa Mutum Wajen Tsara Lokacinsa danna nan

  • Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari

    Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari

    Shugaba Nagari – Ya kamata kowane Shugaba daga sama har ƙasa ya sifantu da waɗannan halaye:

    1) Adalci shine tushen samun nasarar kowane Shugabanci adalcin Allah Ta’ala shi ne yake riƙe da sammai da ƙassai; da duk wanda yake ƙarƙashinsa yake bai wa kowa haƙƙinsa babu nuna wani bambanci.

    Amr ibnul As Radiyallahu anhu yana cewa; mulki ba ya yiwu wa sai da tsayayyun jami’ai, su kuma ba za su samu ba sai da kuɗi, kuɗi kuma ba ya samuwa sai ana raya ƙasa, raya ƙasa ba ya yiwuwa sai da adalci.
    Yana daga adalci shugaba ya hana azzalumai zalunci yana hana maɓarnata ɓarna, kada ma ya bari sai talakawa sun fara kokawa, saboda in har aka kai matsayin da suka fara kokawa to za su iya ɗaukar doka a hannunsu.

    2) Lallai ne shugaba ya kasance mai nisantar zubar da jinin mutane kada ya yi kada ya bari a yi.

    3) ya kasance mai magana ɗaya babu ƙarya babu yaudara.

    4) ya zauna lafiya da mutanen kirki masu tsoron Allah; kada ya saki fuska ga azzalumai da ashararai kada su samu sakewa a ƙarƙashin ikonsa.

    5) Shugaba ya kasance mai cika alƙawari mai faɗar gaskiya in ya san ba zai yi ba; kada ya ce zaiyi, kada kuma bai yi ba ya ce ya yi.

    6) Kada ya raina abokin gaba komai rauninsa ya yi masa maka ido.

    7) Lallai ne ya sami likita na musamman ƙwararre mai amana masoyi na haƙiƙa; kuma kada ya dogara da likita guda ɗaya, a’a ya sami wadatattun likitoci waɗanda in wani gagarumin ciwo ya same shi za su haɗu a kansa in bakinsu ya zo ɗaya akan irin maganin da za’ayi masa to sai a yi bayan shawartar waɗansu amintattunsa keɓaɓɓu.

    8) ya bai wa mataimakinsa muhimmanci sosai, kada ya ture shi gefe guda ta yadda zai zama kamar ɗan kallo a harkar mulki; amma kuma kada ya bari ya sake ya miƙe ƙafa har ya fi shi ƙarfi ya zama kamar shine shugaban shi kuma ya zama hoto.

    9) Haka kuma ya samar da kyakkyawar jituwa tsakaninsa da ‘yan majalisarsa ya ringa zama dasu akai – akai yana shawartarsu kowa ya ji cewa ana yi da shi; babu ɗan mowa a cikinsu, babu kuma waɗansu fulogai waɗanda su kaɗai ne suke jan mai kuma in babu su babu inda za a je. Wannan zai haifarwa da shugaba babbar matsala.

    10) Shugaba ya kula da tattalin arziƙi sosai musamman sana’o’i da harkokin kasuwanci ya buɗawa mutane hanyoyin samun arziƙi da ayyukan yi musamman ga matasa; ya ringa tallafawa ‘yan kasuwa, kada ya ɗora musu haraji mai yawa ko ya basu bashi da kuɗin ruwa. Lalle ne shugaba ya kiyayi abin hannun mabiyansa. Ya guji karɓe- karɓe da cin hanci da rashawa.

    11) Ya kasance mai tattali da tsimi da tanadi da shirin ko- ta- kwana; musamman tanadin abinci da kayan masarufi saboda ba da agajin gaggawa a lokacin da wata musiba ta afko kwatsam ta; yadda ba sai an fita waje da ƙoƙon bara ba.

    12) Ya kasance mai alƙawari ya yi kyakkyawan sakamako ga duk wanda ya taimaka masa; musamman a lokacin da yake neman mulki. Kada su tura mota ta tashi ta bar su da hayaƙi.

    13) Kada ya bari wani talaka ya san wurin hutunsa da shaƙatawarsa ballantana ya je wurin; wannan zai janyo raini manyan mutane kaɗai zai bari su ringa halartar irin wannan wurin; in ya buƙaci zuwansu domin tattauna muhimman al’amari cikin nutsuwa.

    14) Ya yi ƙoƙarin aikata duk abinda zai jawo masa baƙin jini da maƙiya.

    15) Kada ya naɗa ‘yan uwansa a manyan muƙamai saboda gudun hassadar ‘yan uwa. Amma ya kai matuƙa wajen kyautata musu da mutunta su; sannan kuma ya sa ido a kansu ya yi kaffa – kaffa da su, ya yi haƙuri kan cutarwarsu.

    16) Lallai ne shugaba ya riƙe halaye guda uku;
    1. kyauta 2. Haƙuri 3. Da tabbatar da gaskiyar komai kafin ya ɗau mataki akansa.

    17) Ya ringa yabo da zargi daidai ƙurji daidai ruwa. Wato kada ya yi yabo fiye da ƙima kada ya yi ta zargi, faɗa, ko mita fiye da ƙima. Haka kuma ya daidaita tsakanin alƙawarurrukansa da barazanarsa. Kada barazana ta fi yawa, kada kuma alƙawari yafi rinjaye.

    18) Ya kasance mai halin ba-sani-ba- sabo duk wanda ya taka doka, doka ta taka shi.
    A dunƙule dai abubuwa uku ne suke tabbatar da nagartar mulki;
    1- Ɗaukaka da inganta addinin mutane
    2- Tabbatar da tsaro da zaman lafiya
    3- Inganta rayuwar al’umma.

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan 

  • Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Hanyoyin Tabbatar Da Adalci – Majaddid shaihuna Usman ɗan Fodiyo Allah ya ƙara rahama a gare shi; ya rubuta littafi mai suna; “Usulul adli liwalatil umuri wa ahlil fadli” – wato Ginshiƙan kafuwar adalci domin shugabanni da manyan mutane.

    A cikin wannan littafi, ya yi bayanin hanyoyi goma waɗanda in dai shugabanni daga sama har ƙasa za su yi bi su; babu makawa za su kasance masu adalci a shugabancinsu.

    A taƙaice ga waɗannan ginshiƙai na hanyoyin tabbatar da adalci;

    Tushe Na Ɗaya

    Shugaba ya san matsayi da darajar shugabanci da yake yi. Ya sani cewa shugabanci ni’ima ce babba; wacce in ya yi gaskiya da adalci za ta kai shi ga samun ni’ima madawwamiya a lahira da kyakkyawan suna a duniya. Idan kuwa aka samu akasi to zai gamu da matsananciyar azaba a duniya da lahira; saboda haka kada ya yi wasarere da shugabanci ya riƙe shi ƙam ƙam ya yi da gaske ba wasa.

    Tushe Na Biyu

    Lallai ne shugaba ya ja malamai masu tsoron Allah da aiki da iliminsu masu son alhairi ga al’umma masu faɗar gaskiya marasa tsoro marasa kwaɗayi, ya ja su a jikinsa ya rinƙa neman shawarwarinsu da fatawa akan al’amuran shugabancinsa; ya kuma rinƙa amfani da shawarwari da nasihohi da suke yi masa.

    Haka kuma ya nemi masana ƙwararru a kowane fanni na rayuwa kamar manyan ‘yan kasuwa; tsofaffin shugabanni, da ma’aikata na kowane ɓangare dattawan gari har ma da matasa maza da mata masu tsoron Allah da kishin ƙasa domin ya amfana da iliminsu da ƙwarewarsu a fannonin rayuwa da sauransu.

    Tushe Na Uku

    Kasancewarka mai gaskiya da riƙon amana da adalci ba zai kuɓutar da kai ba a wurin Allah; sai ka tabbatar mai ma’aikatanka da jami’an gwamnatinka suna da hali irin naka. Amma idan kana ganin ɓarna ka yi shiru; to haƙiƙa sai ka ba da amsa akan wannan ɓarnar; kuma sai an tuhume ka akan duk ɓarnar da akayi kana sane ka yi shiru ayi maka azaba a kanta ranar ƙiyama.

    Tushe Na Huɗu

    Lallai ne shugaba ya kasance mai yawan haƙuri; afuwa da kau da kai ya guji saurin fushi da yanke hukunci cikin ɓacin rai.

    Tushe Na Biyar

    A duk lokacin da za ka ɗauki wani matakai ko yanke hukunci ko shawara ko sanya hannu akan wani ƙudiri; waɗanda suke ƙarƙashinka ka ɗauki kanka a matsayin ɗaya daga cikin talakawa duk abinda ba za ka so a yi maka ba to kada ka yi wa waninka, duk abinda za ka so ayi maka to ka zartar da shi.

    Tushe Na Shida

    Kada ka wulaƙanta talaka da sauran mutane masu kawo buƙatunsu gare ka da koke – kokensu; saboda babban amfanin shugabanci shine sharewa mabiya hawayensu da sauran buƙatunsu da yin abinda ya kamata akansu.

    Tushe Na Bakwai

    Ka yi rayuwa matsakaiciya tare d tsantseni da wadatar zuci kada ka sabawa kanka da zurfafawa da al’mubazzaranci; a wajen jin daɗi da kece raini wannan zai sa ka mance da wahalhalun da talakawa suke ciki zuciyar ka ta bushe; in suna kuka ka rinƙa jin kamar kukan daɗi suke yi. Kana sheƙa dariya abinka.

    Tushe Na Takwas

    Dukannin abinda zai yiwu cikin sauƙi da lumana, kada ka bi hanyar tsanani ne da tursasawa wajen tabbatar da shi. Ana amfani da tsanani kawai a lokacin da sauƙi ba zai yi amfani ba.

    Tushe Na Tara

    A kowane lokaci ka rinƙa tunanin mutuwarka da kwanciyar ƙabari da tashin alƙiyama da musiba da azabobin da suke cikinta; da kuma ni’ima da rahamar da Allah ya tanada ga masu binsa. Ka rinƙa tunanin shin kai a wane ɓangare za ka kasance idan Allah ya tashi alƙiyama.

    Tushe Na Goma

    Ka sanya tsarin shugabanci na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance madubinka, ma’aunin shugabancinka ka rinƙa kwaikwayonsa gwargwadon ikonka.

    Bayan waɗannan tuwassa goma waɗanda Shaihu Usman ɗan Fodiyo; ya ambata ya kuma ce imamul Gazzali ne ya faɗe su a cikin wani littafinsa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Raka’a Biyu Kafin Magariba danna nan

  • Yabo A Waƙoƙin Baka

    Yabo A Waƙoƙin Baka

    Ba wannan aikin ba ne farau da yake ɗauke da yabo a cikin waƙoƙin baka na da ko na zamani; an yi ayyuka da dama da suke da kamanceceniya da wannan nazari.

    Misali: Yakawada (Babu shekara) ya yi wani aiki mai taken “Nazarin Jigon Yabo da Zuga A Kirarin Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina”. 

    Inda a wannan aiki nasa, ya yi ƙoƙarin hakaito wasu cikin yabon da aka yi wa Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina.

    Shi ma Bello (1976) ya yi makamancin wannan rubutu; inda ya bibiyi waƙoƙin Hausa ya zaƙulo yabo da zuga da kuma zambo.

    Yakawada (2001:68-85) ya maimaita wani aiki, amma a aikin, ya kalli tubalan ginin yabo ne inda ya kevanci nazarin ga waƙoƙin iko (sarauta) ne kawai.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi; Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan

    Domin karanta Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa danna nan

  • Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

    Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

    An haifi Sa’idu Muhammad Gusau a ranar 24 ga watan Maris 1952 a shiyyar Madawaki, bakin Masallacin Juma’a; unguwar Bube Attajiri da ke garin Gusau, Jihar Zamfara.

    Farfesa Gusau ya fara karatun allon a gaban Mahaifinsa Malam Muhammadu Ɗankullum da Malam Husaini Kanoma da Malam Labbo Haruna Gummi da sauransu; inda har Allah ya sanya ya sauƙe Alƙur’ani mai tsarki tun yana da shekaru goma sha huɗu (14) a duniya.

    Dagan aka sanya shi a makarantar Nizamiyya Islamiyya; a ƙofar gidan Ɗangaladiman Waziri Malam Attahiru daga 1965 zuwa Disamba 1969.

    Ya zarce zuwa Kwalejin Sarkin Musulmi Abubakar, Sashen Koyar da Larabci da Addinin Musulunci (H.M.S) Sakkwato daga Janairu; 1970 zuwa Yuni, 1973.

    A watan Oktoba na shekarar 1974 ya sami gurbin karatun Difloma a fannin Hausa da Larabci da Addinin Musulunci a Kwalejin Abdullahi Bayero Kano, kuma ya kammala a watan Yuni shekarar 1977.

    Sannan ya ci gaba da karatun digirin farko (B.A Combined Honors) a Jami’ar Bayero Kano, daga Oktoba, 1977 zuwa Yuni 1980.

    Bayan nan, sai ya sake komawa karatun digiri na biyu (M.A) a fannin Hausa daga Oktoba, 1982 zuwa Oktoba, 1983; A watan Mayu na shekarar 1989 ce ya kammala karatun digirinnsa na uku (Ph.D) a fannin Hausa; a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.

    Farfesa Gusau:

    Ya koyar a Makarantar Firamare ta cikin garin Talatar Mafara, wato Township daga Satumba 1973 zuwa Satumba, 1974. Ya koyar a Makarantar Horon Malamai ta U.P.E Wasugu, a shekarar 1977.

    Sannan ya yi karantarwa a Kwalejin Larabci (S.A.S) daga Agusta, 1980 zuwa Yuli, 1981.
    Farfesa Gusau ya riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban Makarantar Horon Malamai (G.T.C) Zuru daga 1981 zuwa Satumba, 1982. Ya taɓa zama Shugaban Sashen Hausa (H.O.D Hausa) a Babbar Kwalejin Horon Malamai (A.T.C), Maru daga 1984 zuwa Satumba, 1985.

    Daga watan Yuni na shekarar 1990 ya juya aikinsa na koyarwa zuwa Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami’ar Bayero Kano, a matsayin Malami mai daraja ta ɗaya.

    A shekarar 1991, ya zama Babban Malamin Jami’a, sai a shekarar 1995 aka ɗaga shi gaba ya zama Mataimakin Farfesa. A ranar ɗaya ga watan Oktoba, 2000 ya zama Farfesa.

    Farfesa Gusau ya yi rubuce-rubuce da dama a cikin muƙalu da rubuta littattafai da dama waɗanda suka shafi Hausa da kuma na Addinin Musulunci. Ya kuma halarci tarukan ƙara wa juna sani da dama, kuma ya gabatar da muƙalu da dama a tarukan.

    Yanzu haka yana zaune a Kano tare da iyalansa (matansa da ‘ya’yansa da jikokinsa) (Gusau, 2020:91-92).

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi: Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Yabo danna nan

  • Yabo Daga Waƙar Aminu Alan Waƙa

    Yabo Daga Waƙar Aminu Alan Waƙa

    Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa) ya yi wa Farfesa Gusau waƙoƙin yabo da dama; amma a wannan takarda an ɗauki waƙa ɗaya mai taken “Ga ka Farfesa” ; wadda a cikinta aka zaƙulo yabon da ya yi masa. 

    Ga wasu ɗiya da Alan waƙa ya yi yabo a cikin su:

    G/Waƙa: Ga ka Farfesa,
    Ga ka Farfesa ga ka katibi kan adabi,
    Sannu Farfesa Sa’idu ɗan Muhammadu na Gusau.
    Jagora: Yau akala na karkata na tunkari Gusau,
    Zan yabon masani mutafannunin nan na Gusau,
    Wanda yai harsasai kala-kala yam maye sau,
    A fagen ilmi yau da gobe ya zamma da sau.
    Jagora: Adabin Hausa na yabon ka Farfesa Gusau,
    Manazarta ma ka yi tubali sun ɗara sau,
    Littafan tarke da dabarbarun Hausa ka sau,
    Har da talifin tarke na siya da dama a Gusau.
    Jagora: Alan waƙa ke yabon ka don ka ɗara sau.

    Sanannen makaɗi ne a ƙasar Hausa wanda ya yi waƙoƙi da dama a ɓangarori da dama, cikin su har da waƙoƙin yabon Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau.

    An haifi Aminu Ala a ranar 11 ga watan Fabrairu, 1973 a unguwar Yakasai ta Kano. Ya yi haddar Alqur’ani da karatun littattafai; sannan ya yi karatun boko inda ya kai matsayin Difloma. Yanzu haka yana zaune a Birnin Kano, yana tare da iyalansa, sannan yana da muƙaman sarautu a wasu ƙasashen Hausa kamar: Ƙaraye, Bichi, Dutse da Gobir. (Gusau, 2016:229 – 234).

    Taƙaitaccen Tarihin Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa)

    Wannan suna an samar da shi ne ta hanyar haɗa farkon sunayensa, wato Aminuddeen Ladan Abubakar, sai aka sanya masa mahaɗin ‘n’, sannan aka yi ƙari da kalmar ‘Waƙa’ a gaba.

    Ya yi wannan waƙa rerawa ta farko a yammacin ranar Laraba 10 ga Maris, 2021, wadda ta dace da ranar bikin auren Hindatu Sa’idu Muhammad Gusau.

    A fagen waƙa kai rubutuka sun fice sau,
    Haka labaran ƙage kai nazar sun fice sau,
    Binciken Ala da yawan su taskarka Gusau.

    Idan aka lura da waɗannan baituka da suka gabata, za a ga tsantsar yabo ta fuska guda; amma sai aka rarraba shi zuwa wasu rassa amma duk a ɓangaren ilmi.

    Makaɗin, ya yi ƙoƙarin yabon Farfesa ta fuskar yalwatar iliminsa, inda ya zamana ilimin ba a ɓangare guda ba, wato fanni ne da dama. A kalmar ‘Mutafannun’ wadda ya yi amfani da ita wajen nuna Farfesa Gusau yana da ilimi a vangarori biyu ko uku, wato Hausa da Turanci da kuma Larabci. Har wa yau, a wajen yin yabo ga yalwar ilmin nasa, sai ya yabi yadda ya kasance ya yi tarke a ayyukan marubuta littattafan Hausa na ƙagaggun labarai, haka zalika a fagen waƙa ma ya yi irin wannan tarke da rubuce-rubuce da dama.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi: Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabo Daga Waƙar Maryam Fantimoti danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Muhallan Da Ake Waƙoƙin Fiyano Na Hausa danna nan

  • Ma’anar Yabo

    Ma’anar Yabo

    Yabo na nufin ba da shaida mai kyau game da mutum bayan ya yi wani abin a yaba; na burgewa ko kuma ana so ya aikata abin na burgewa ko na a yaba.

    Misalin Yabo:

    Jagora: Ka ji waƙa tana fita,
    Gurin ɗan Bafillatana,
    Abu kamar harsashi,
    In na yi hushi harsashin ɗin me?
    In dai waƙa ce,
    Allah ya yarda. (Gusau, 2009:350).

    A nan, za mu fahimci yabo da cewa wasu kalmomi ne da ake amfani da su wajen bayyana zahirin yadda mutum yake, shin waɗannan kalmomin da aka ambata ƙarya ce ko kuma gaskiya ce.

    Domin akan yabi mutum ta hanyar faɗar abin da yake ba gaskiya ba ne, an dai yi ne kawai domin a faranta masa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Yabo Gonar Makaɗi: Nazarin Yabon Farfesa Sa’idu Muhammd Gusau A Cikin Wasu Waƙoƙin Baka Na Situdiyo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabo A Waƙoƙin Baka danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yabon Gusau A Waƙoƙin Baka danna nan

  • Asalin Kiɗan Fiyano

    Asalin Kiɗan Fiyano

    Encyclopedia Americana (2003), ta bayyana cewa, a shekarar 1709;

    Fiyano – Bartolommeo Cristofori ya ƙirƙiri wani abin kiɗa da ake kira gravicembalo col piona e forte. Wanda yake samar da sautin piano (soft) da forte (loud). Daga haka aka samu sunan pianoforte ko fortepiano. Daga haka aka gajerce sunan zuwa piano.

    Binta (2011:76) ta bayyana cewa “Ana jin mutumin da ya fara ƙirƙiro fiyano, shi ne Bartolemo Cristofori ɗan ƙasar Italiya. Mawaƙi kuma ƙwararre a kan sanin kayan kiɗa wanda kuma iyalan Medici suka riƙe shi.

    Amma zuwa ƙarshen 1700, kiɗa da fiyano ya zamo abin zaɓi ga masu haɗa kiɗa da kuma su kansu mawaƙan”.

    Zainab (2009:83) ta bayyana asalin fiyano daga ƙasar Italy aka ƙirƙire shi, tun a ƙarni na sha tara (19), kuma Pianoforte shi ne cikakken sunanta, kuma sunan asali. Pianoforte ita ce nau’in fiyano na farko da aka fara samu. Mawaƙi mai amfani da fiyano ana kiransa pianist. Akwai wasu abubuwa da suka haɗu, suka tayar da fiyanon kamar strings da keys da pedal da pianostool.

    Enclyclopedia Americana (2003) da Concise English Dictionary (2006), sun ƙara bayyana cewa, fiyanon na da nau’o’i biyu cikinsu akwai: Grand Piano da Upright Piano.

    Grand piano ita ce wadda take da madannai guda tamanin da takwas (88), hamsin da biyar (55) farare ne, su kuma baƙaƙe talatin da shidda (36) ne. Ana latsa madannan tsawon inci 3/8 (9.6 mm). Ita Upright piano tana da wasu ɓangarori na grand piano, sai dai akwai ‘yan bambance bambance a tsarinsu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wuraren da Ake Kiɗan Fiyano (Situdiyo)