Abubuwan Da Za su Taimaka wa Mutum Wajen Tsara Lokacinsa

0
447

Abubuwan da za su taimakawa mutum wajen tsara lokacinsa suna da yawa waɗanda za ka iya ribata da yin su cikin minti ɗaya rak:

 • Cewa subhanallah ko salatin Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da sauran zikiri
 • Sallama ga abokinka koda ta yin saƙon “text” cikin wayar tafi-da-gidanka (G.S.M).
 • Sake jaddada alwala.
 • Amsawa mai tambaya.
 • Sakin fuska ga mutane.
 • Kawar da abu mai cutarwa daga kan hanya.
 • Tsallakar da makaho ko wani rarrauna titi.
 • Tura wa mutum motarsa da ta mutu.
 • Miƙawa wanda yake a kan dabba abinsa da ya faɗo.
 • Maimaita wata aya daga ayoyin Alqur’ani.
 • Yiwa yara tsawa kan wata ɗabi’a mara kyau. Da sauransu.
Yin Jadawalin Ayyukan Rana Da Yini A Rubuce

Yin jadawali (Time-table) ga masulmi ya sha bamban da yadda ‘yan duniya ke tsara jadawalinsu. Musulmi zai yi jadawalinsa ne, yana mai rinjayar da abubuwan da za su jawo masa ribar lahira da yardar Ubangiji. ‘Yan duniya kan tsara lokutansu, ta yadda za su sami damar yin wasanni, kamar shaƙatawa a bakin ruwa, ko don yin guje-guje da tsalle-tsalle, ba tare da ba wa mahaliccinsu wani kaso ba.

Shi kuwa musulmi, zai tsara mafi yawan lokacinsa ga Ubangiji Maɗaukaki ta yadda barcinsa da shaƙatawarsa duk za su zamo ibada. Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya nuna mana cewa hatta mutum in ya biya buƙatarsa da iyalinsa ma lada ne, matuƙar ya bi koyarwar Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam).

Da mutum zai tsara ranarsa da ayyukansa ta yadda zai  ware sa’a guda a kowacce ranar aiki daga Litinin zuwa Juma’a, da zai samu kimanin awoyi 260 a shekara. Wanda wannan ya yi daidai da kwana talatin, ma’ana wata guda cur.

A lokacin kuwa, na tabbata mutum zai iya abubuwa masu amfani ga rayuwarsa misali, zai iya:

 • Haddace wasu sassa na Alqur’ani.
 • Sauke wani littafi na fikhu ko hadisi.
 • Koyon wata kwarewa (kamar kwamfuta).
 • Koyon wani harshe kamar Larabci ko Ingilishi ko kuma Faransanci.
 • Rubuta babin littafi mai amfani ga musulmi.
 • Yin kos din diploma a tsarin karatu daga gida(Distance learning).
Yi wa Kai Hisabi A Kowace Rana (SELF ASSESSMENT)

Wannan wata hanya ce dake taimaka wa mutum mai himma, wajen tabbatar da mutum ya ribaci lokutan rayuwarsa, kuma ya yi zikirin safiya da yammaci da sauransu. Don haka sai mutum ya zana wani jadawali na yi wa kai hisabi. Ya bibiyi wuraren daidai, ya kuma sanya alama (√) sannan wuraren kuskure kuma, ya sanya alamar (×).

Ta haka mutum zai san sau nawa ya rasa sallar jam’i ko kuma shin yayi sadaƙa a wannan ranar? Shin ranaku nawa ne suka wuce shi bai yi karatun Alƙur’ani ba? Idan ya ga adadin alamar (√) daidai bai kai na kuskure ba (×). To ya ƙara himma.

Akwai iyaye maza da ke da himma har sukan yiwa matansu da ‘ya’yansu irin wannan jadawali don taimakawa rayuwarsu.

Taswirar Jadawalin Yi Wa Kai Hisabi

Rana¬¬¬¬………………. Kwanan wata……………….

Sallah    Zikiri   Karatun Alkur’ani   sadaqa   zumunci    Umarni da kyakkyawa

Safe            Yamma X X
A B X X
A Z
L S
M G
I S

Hanyoyin Da Ke Taimakawa Wajen Kaucewa Asarar Lokaci Sun Haɗa Da:
 1. Tsara duk abinda kake son yi a safiyar kowace rana a rubuce.
 2. Da ka samu rarar lokaci sai ka shigar da shi wajen haddar alkur’ani da karatun Littafi mai amfani da zikiri da dai sauransu.
 3. In ku ka yi alƙawari ka tabbata an tsaida tsayayyen lokaci.
 4. Ka/ki tabbata ka/kin tanadi kayan aiki, kafin fara aiki, girki, tsara lacca, gini da sauransu.
 5. Kar ka fara tafiya zuwa wurin da wasiƙa ko waya za ta iya biyan buƙatar.
 6. Ka tabbata kana da mai motarka ko babur ɗinka a kowane lokaci.
 7. Kar ka yi tafiya, ba tare da safayar taya ba.
 8. Da ka ga za ka makara wurin alƙawarin da ka yi, yi saƙo da “text message.”

Domin karanta cikakken bayani akan Ƙa’idoji Goma Sha Ɗaya Na Samun Nasara A Rayuwa danna koren rubutun nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Lokaci A Rayuwar Musulmi Tsakanin Riba Da Asara wanda Sunusi Iguda Ƙofar Nasarawa ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceRashin Lafiyar Bayin Allah
Labarin na GabaHalittar Lokaci Da Ƙarewarsa