Rashin Lafiyar Bayin Allah

0
591

Rashin lafiyar bayin Allah wata jarrabawa ce daga Allah Maɗaukakin Sarki. Jarrabar bayi da rashin lafiya wani tsari ne daga cikin tsare-tsaren Allah, game da gudanar da al’amuran bayinsa.

Saboda haka, Allah ne kaɗai yake da ikon ɗora wa bawa cuta, kuma shi kaɗai ne mai iya yaye wa bawa cuta. Kamar yadda ya ambata haka da kansa cikin Alƙur’ani inda ya ce,
“Idan Allah ya ɗora maka wata cuta to fa babu mai iya yaye maka ita sai shi….”.

Bayan haka, Allah (Subhanahu wata’ala) ya labarta mana cewa a kan wannan fahimta Annabawansa da Manzanninsa da Mabiyansu suke a kai.

1. Ga abinda Annabi Ibrahim (A.S) ya ce,
“Idan na yi rashin lafiya to shi yake warkar da ni (wato Allah)”.
2. Ga kuma abin da Annabi Ayyuba (A.S) ya ce lokacin da ba shi da lafiya,
“Kuma ka tuna Annabi Ayyuba lokacin da ya roƙi Ubangijinsa ya ce:
“Haƙiƙa cuta ta same ni, kuma kai ne mafi jinƙan masu jinƙai. (83) sai muka amsa masa roƙonsa; muka yaye masa cutar dake tare da shi… (84)”.

An karɓo Hadisi daga A’isha Allah ya yarda da ita ta ce: “Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance idan ya je gaida mara lafiya yana cewa: “Ya Ubangijin mutane ka tafiyar da wannan ciwo, kuma ka warkar, kai ne mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarka, warakar da ba ta barin wani (sauran ciwo)”.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Don haka a duk lokacin da mara lafiya ya fahimci cewa, cuta da waraka daga Allah suke, to ya sami mabuɗin samun sauƙi da waraka daga ciwonsa wannan kenan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin A KULA DA LAFIYA wanda Abubakar Abbas Ibrahim ya wallafa domin karanta ——————- danna koren rubutun nan

labarin da ya wuceAbubuwan Dake Jawo Asarar Lokaci A Rayuwar Ɗan Adam
Labarin na GabaAbubuwan Da Za su Taimaka wa Mutum Wajen Tsara Lokacinsa