Tag: ilimin tarihi

  • Tarihin Gwani Daudu (1920-2000)

    Tarihin Gwani Daudu (1920-2000)

    An haifi Alaramma Malam Abubakar Yunusa a shekarar 1920 a garin Tsakuwawa a ƙaramar Hukumar Miga da ke cikin Jihar Jigawa. Ana yi masa laƙabi da Gwani Daudu saboda sarautar kakanninsa ta Galadiman garinsu.

    Alaramma Malam Abubakar ya shahara da baiwar karatu na yankan shakku. Saboda irin kaifin ƙwaƙwalwar da Ubangiji Maɗaukaki Ya ba shi, an ce Gwani Daudu ba ya manta duk abin da ya yi ido biyu da shi tun daga ƙuruciyarsa. Zarton malami, ma’abocin karamci da son almajirai. Gwani Daudu ya yi fice cikin dattijawan alarammomi da wayewa a zamanance da kuma kutsuwa fannonin ilmi Fiƙhu da Tafsir da Lugga da Nahwu.

    Gwani ya fita neman karatu bayan ya zama matashi mai kimanin shekaru goma sha biyar kuma bai koma gida ba sai da ya samu Alƙur’ani kuma ya rubuta shi. Ya yi tafiye-tafiyen neman karatu cikin Birniwa da Kirikasamma da Gayan. Gwani Daudu ya kafa tsangayun AIƙur’ani a birane daban-daban kamar garuruwan Mai Tafari da Kirikasamma da Kuka Uku.

    Don haka ne ma a halin yanzu ake kiran wata kasaitacciyar makaranta a garin Damaturu da tsangayar Gwani Daudu.

    Bayan Gwani Daudu ya dawo birnin Kano kuwa ya zauna a wurare daban-daban da suka haɗa da Durumin Zungura da Kankarofi cikin ƙaramar Hukumar Birni. Daga bisani kuma ya koma Unguwar Gwale.

    Gwani Daudu ya shahara da kyakkyawar maƙwabtaka da saraki da sauran al’umma. Saboda haka ne ma Sarkin Kano Ado Bayero ya ba shi filin da ya faɗaɗa tsangayarsa da ke Unguwar Gwale.

    Malaman Gwani Daudu sun haɗa da:-

    • Malam Mai Ɗanbahar Mai Tafari
    • Malam Iliya Gayan
    • Gwani Ɗankwandarai

    Gwani Daudu ya rasu a ranar 22 Sha’aban 1421, dai-dai da 17 ga Nuwambu 2000. Ya rasu ya bar ‘ya’ya da almajirai masu yawa:-

    ‘Ya’ya:

    • Malam Muhammad Abubakar
    • Malam Ahmad Abubakar
    • Malam Susi Abubakar
    • Malam Tamimuddari
    • Malam Adisaru
    • Malam Arisu

    Manyan Almajiransa sun haɗa da:-

    • Malam Ali Basukkwace
    • Malam Umar Panshekara
    • Malam Ahmad Ɗantsadawa
    • Alh. Hamza Yusuf
    • Malam Garba Na’ibi
    • Malam Muhammad Ɗan Meram

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Malam Isa ƊanƘauranmata Bin Umar danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Misalan Waƙafi Ababen Koyi A Tarihin Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

     

  • Tarihin Alaramma Malam Isa Ɗan Ƙauranmata Bin Umar

    Tarihin Alaramma Malam Isa Ɗan Ƙauranmata Bin Umar

    An haifi Malam Isa Umaru a garin Ƙauranmata zamanin Sarkin Kano Usman. Mahaifinsa Malam Umar ya aika da shi garin Bunkure wajen Malam Adamu Gangaran a farko-farkon zamanin Sarki Abdullahi Bayero. Bayan Malam Isa ya data ne ya nemi a kai shi garin Rimi cikin yankin Sumaila wajen Malam Isuhu.

    Gwanin Alƙur’ani, ma’abocin tawaru’u da yawan karamci, Malam Isa ya yi tafiye-tafiyen neman AIƙur’ani cikin ƙasar Gumel; wajen Malam AbdulHamid da garin Ciromawa a ƙasar Haɗeja.

    Saboda irin baiwar da Ubangiji ya ba wa Malam Isa abokansa ne suka gabatar da shi a matsayin mai darasu bayan rasuwar Alaramma Malam AbdulHamid a katafariyar tsangayarsa da ke garin Ciromawa.

    Dawowar Sa Kano Da Zama Bayan gwagwarmayar neman karatu daga wannan gari zuwa wancan; Malan Isa ya koma mahaifarsa a garin Ƙauranmata a inda ya cigaba da hidima ga mahaifinsa Malan Umar. Don haka kullum yana tsankanin cikin birni da ƙauyensu, sai dai ya yi ‘yan kwanaki ya koma gida.

    Daga ƙarshe wasu daga cikin attajirai irin su Alhaji Hamidu Namudi da ke Unguwar Dala; suka nemi mahaifinsa da ya yi masa izinin dawowa Kano don koyar da Alƙur’ani.

    Bayan samun izini mahaifinsa ne ya dawo Kano ya zauna a Unguwar Dala; daga bisani ya koma Gwale a farkon mulkin Sarki Ado Bayero Manyan abokan karatunsa su ne:-

    • Malam Saleh Ɗangalinja Ƙarfi
    • Malam Umar Magasawa

    Malam Isa Ɗan Ƙauranmata bai gushe ba har zuwa yanzu yana karantarwa a tsangayarsa da ke gidansa a Gwale.

    Yana da ‘ya’ya kamar haka:-

    • Malam Umar Isa
    • Malam Usman Isa
    • Malam Abubakar
    • Malam Abdulhamid
    • Malam Garba
    • Malam Sabi’u
    • Malam Aminu
    • Malam Jamilu
    • Malam Kabiru

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Malam Salisu Ɗanruwantsa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Magabata da Haihuwar Ɗanƙwairo danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Gwani Ɗanbirni

    Tarihin Gwani Ɗanbirni

    An haifi Malam Muhammad ɗan Malam Ali a unguwar Zage da ke Birnin Kano a zamanin Sarkin Kano Usman. Gwani Ɗan birni ya sha bam-ban da ragowar takwarorinsa makaranta.

    Domin kuwa ya fara neman ilmi ne a fagen Fiƙhu da Hadisi cikin tsarin ilmin zaure; musamman ma wurin Malam Baƙo da Malam Habu da ke Unguwar Ciromawa.

    Tsananin sha’awarsa ga zurfafa neman karatun Alƙur’ani ya sa ya nemi izinin mahaifinsa don ya fita zuwa wasu wurare da ke wajen Kano. Koda Gwani Ɗanbirni ya samu izinin mahaifinsa sai ya yi niyya ya fita. A lokacin ba wanda ya san inda ya nufa, ballantana inda za a same shi. Bayan wani lokaci ne aka samu labarin yana wurin Gwani Abdullahi da Gwani Ahmadu.

    Koda Gwani Ɗanbirni ya samu labarin wani mashahurin masanin Alƙur’ani a garin Ubba sai ya tafi izuwa gare shi. Daga nan ya dawo gida Kano bayan ya tumbatsa kuma ya shahara wajen ƙarfin tilawa da baiwa a fagen karatun Alƙur’ani. Wannan ya zaburar da irin abokansa na ƙuruciya da ke Unguwar Zage, saboda ganin irin ɗimbin ilmin da Ubangiji Maɗaukaki Ya yi masa a wani lokaci taƙaitacce. Manyan abokan karatun Gwani Ɗanbirni sun haɗa da Gwani Saleh Ɗanzarga da Malam Abdu Ɗankankare da Malam Kafi-ɓari da Malam Musa jikan Shehu da Malam Sani Adam.

    Manyan malaman Gwani Ɗanbirni sun haɗa da mashahurin masanin Alƙur’anin nan Gwani Hamad da Gwani Abdullahi Ɗan Gwani Ahmadu da Gwani na Ubba da Malam Awaisu na Madabo da Malam Inuwa almajirin Malam Salga da Gwani Dubu da Gwani Hamidu.

    Game da yawan almajiran Gwani Ɗanbirni kuwa za mu iya cewa ɗaruruwan almajirai sun sami Alƙur’ani a hannunsa Fitattu; daga cikin Su sun haɗa da Malam Tijjani Rabi’u da Malam Idi da Malam Ahmadu Ɗanjajaye da Malam Isa ƙofar Mata da Sharu Bala da Sharu Ahmadu da Malam Ahmadu Mai Makarantar Dare Gabari da Alhaji Gagara da Na’ibin Masallacin Juma’a na Shehu Ahmadu Tijjani da Malam Inuwa Mai Gemu da Alhaji Ali Indabawa.

    Gwani Ɗanbirni ya shahara da kyawawan halaye da sabo da jama’a. A lokaci guda kuma yana da ƙima wurin Sarki da attajirai na Kano irin su marigayiya Mai Babban ɗaki; mahaifiyar mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Khalifa Sarki Sunusi (Murabus) da Alhaji Aminu Ɗantata. Gwani Ɗanbirni ya rasu a watan 10 na shekarar 2004. Ya bar ‘ya’ya maza da mata goma sha biyar (15).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Mahmud Manzo Arzai danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Sheikh Is’haƙ Rabi’u Khadimul Alƙur’ani

    Tarihin Sheikh Is’haƙ Rabi’u Khadimul Alƙur’ani

    Halifa Sheikh Is’haƙa Rabi’u mashahurin Mahaddacin Alƙur’ani ne da Ubangiji Ya yi wa baiwar ƙarfin tilawa a tsakanin sa’o’insa.

    Ma’abocin son makaranta da yi musu hidima Kamar yadda muka ga cewa Shehun Barno Muhammad Al’Kanemi shi ne Alaramma na farko da ya haɗa karatu da mulki tun a ƙarni na goma sha takwas a Daular Barno.

    Haka kuma a ƙarni na ashirin da ɗaya a Kanon Dabo, Halifa Is’haka Rabi’u shi ne farkon alaramman da ya zama gawurtaccen attajiri; sannan kuma Halifan Ɗarikar Tijjaniyya.

    Duk da nauyin jagoranci da al’amuran gudanar da kasuwanci; Halifa Is’haka Rabi’u bai gushe ba yana musharaka cikin tukuri da masaffa da ake gudanarwa a kodayaushe a Masallacinsa.

    Babban Misalin da rayuwar Sheikh Is’haƙa Rabi’u ta bayar ga raya tsangayun Alƙur’ani shi ne gina gidaje na hubusi da ya yi; ya sanya makaranta a ciki da iyalansu. Ubangiji Maɗaukaki Ya yi masa baiwar ‘ya’yaye maza da mata mahaddata Alƙur’ani.

    Har yanzu gidansa da ke Kano cibiya ce ta tsangaya. An ce Mahaifinsa Malam Rabi’u Ɗantinki ya taɓa mafarki ya ga tsangayarsa ta taso daga cikin gari; ta dawo gindin Gwauron Dutse; da gardawa da wutar gargari na ci ganga-ganga. Ashe kuwa abin zai tabbata a hannun magajinsa Halifa Sheikh Is’haƙa Rabi’u.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Gwani Daudu (1920-2000) danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan AL’ADAR BAHAUSHE danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi e daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Mahiru Sharif Bala

    Tarihin Mahiru Sharif Bala

    An haifi Gwani Sharif Bala ɗan Sharif Musɗafa ɗan Sharif Muhammad a shekarar 1345; wadda ta yi dai-dai da shekarar 1934 a Unguwar Gabari cikin garin Kano.

    Mahiru Sharif Bala ya taso a gidan ilimi da wadata da karamci a inda ya yi karatu a wurin mahaifinsa tare da ɗan uwansa Sharif Ahmad. Mahiru Sharif Bala ya rubuta Alƙur’ani sau uku tun yana ɗan shekara goma sha takwas; kuma a dai-dai wan nan lokaci ne aka yi masa auren fari. Mahiru Sharif Bala ya kutsa fannonin ilmi inda ya karanci tafsiri da Hadisi da Fiƙhu a Unguwar Makwarari.

    Wani abin mamaki game da rayuwar Mahiru Sharif Bala ya yin neman Alƙur’ani shi ne: bai taɓa zuwa ko’ina ba kamar yadda abin yake wajen mafi yawan makaranta. Babbar baiwar da Mahiru Sharif ya shahara da ita baya ga ƙarfin tilawar Alƙur’ani, shi ne gwanintar rubutunmu na Magribi.

    Kwanciyar baƙaƙen AIƙur’ani irinsu “Kaulasan” da Lam’ara da tsaiwar Bayala shaida ce ga ficen da Mahiru Sharif Bala ya yi a wannan fage. Saboda irin baiwar rubutunsa da irin karɓuwar da yake da ita tsakanin makaranta Alƙur’ani ba a ƙasar Kano ba kawai; har ma da wasu sassa na Afrika ta Yamma; ta sa Mahiru Sharif Bala ya juyi littattafai a sassan ilman Musulunci da hannunsa irinsu:-

    – Asshifa
    – Dala’ilul Khairati
    – Ishriniyya
    – Alburda
    – Hamziyya
    – Risatul Anwar
    – Igasatul ibad
    – Risala
    – Iziyya da sauransu

    Babu shakka wannan ya sauƙaƙawa makaranta tsangaya waɗanda ba su saba da rubutun sharƙiyya ba, damar kutsawa fannoni ilmi.

    A taƙaice za mu iya cewa hannun Mahiru Sharif Bala da tasirinsa a tsarin tsangaya ya zama “hantsi leƙa gidan kowa”; domin kuwa ya ratsa kowane loko da saƙo na makaranta.

    Ma’ana dai, in almajiri bai je gabansa ya yi karatu ba to kuwa ya kwaikwayi irin salon rubutun hannunsa; tun daga kan Juzi’i biyar ko goma har zuwa ashirin.

    Yaɗuwar da Alƙur’anin Mahiru Sharif Bala ya yi ya zarta yaɗuwar mafi yawan Alƙur’anan da aka rubuta da hannu; domin kuwa ya rubuta Alƙur’ani hamsin da hannunsa. An buga bakwai daga cikinsu, kuma an ɗabba’a su fiye da sau dubu ɗari biyu: waɗanda duk sun yi fice da fitar da harji da meram da falalar kowace sura.

    Game da taimakon yin magani da ayoyin Alƙur’ani kuwa, Mahiiru Sharif Bala ya rubuta Alƙur’ani don sha fiye da sau ɗari; Suratul Yusuf sau dubu ɗaya, Bisimilla da Wallahu ya ‘asimuka da Sanuƙ’ri’uka sama da miliyan guda.

    Farin jinin rubutunsa da baiwar da Ubangiji yai masa ta sa an buga:-

    i- Asshifar da ya rubuta da hannunsa sama da dubu talatin
    ii- Dala ilul khairati sama da dubu ɗari
    iii- Ishiriniya sama da dubu ɗari biyar
    iv- Alƙur’ani ɗan izu ashirin sama da dubu ɗari biyar
    v- Alƙur’ani ɗan izu goma sama da miliyan biyu
    vi- Alƙur ‘ani ɗan izu biyar sama da miliyan biyu
    vii- Ƙawa’idi sama da miliyan biyu
    viii- Ashmawi sama da dubu ɗari biyar
    ix- Risala sama da dubu goma
    x- Iziyya sama da dubu goma
    xi- Alburda sama da dubu goma
    xii- Ira’atul biladi sama da dubu goma.

    Har zuwa yanzu, Mahiru Sharif Bala bai gushe ba yana ba da karatu da ilimi a shahararriyar makarantarsa; tare da mataimaka sama da talatin da almajirai yara da manya, maza da mata sama da dubu biyar. Ubangiji Maɗaukaki Ya ƙara masa lafiya ya kuma sanya masa kyawawan ayyukansa a mizani.

    Tsokaci

    Akwai wasu malamai na Alƙur’ani fitattu a Kano da yawa – da ya kamata na gutsurawa mai karatu wani abu daga tarihin rayuwarsu, amma hakan ba ta samu ba.

    Cikinsu akwai Malam Na Mai Ganji da Malam Giwar Takwasa da Malam Husaini Ɗangurai da Malam Ɗangidimoni; da Malam Ɗayyabu Mai Saje da Malam Yahaya Malammadori da Gwani Tata Bunkure da Malam Ɗan Ringim; da Malam Mai Hafizai da ma waɗanda ban ambata ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wasu Daga Malamai a Katsina danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Haƙƙoƙin Mabiya A Kan Shugabanni

    Haƙƙoƙin Mabiya A Kan Shugabanni

    Su kuwa mabiya suna da waɗannan haƙƙoƙi a kan Shugabanninsu:

    1. Tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi da mutuncin mabiyansa. Wajibi ne ya kula da tsaron kan iyakoki, ya yi maganin ‘yan fashi da ɓarayi da ‘yan ta’adda. Ya kula sosai da jin daɗin jami’an tsaro da iyalansu ta yadda za su samu ƙarfin gwiwa da kishin kare ƙasa.

    2. Kulawa da addini da bunƙasa shi ta hanyar jan managartan malamai a jiki da neman shawarwarinsu da fatawoyinsu da sauraron karatuttukansu da wa’azin su.

    Kada ya bar kafirci ko bidi’a ko lalata da masu yinsu su samu sakewa har su kafu a inda yake da iko. Ya ƙarfafa koyar da ingantacce sahihin addini bisa koyarwar ƙur’ani da sunna da fahimtar magabata na ƙwarai.

    3. Wajibi ne shugaba ya kula da al’amarin musulunci, kada ya yi sakaci da salloli biyar a cikin jama’a ya ringa halartar sallolin juma’a da na idi, ya kula da yadda limamai suke gabatar da huɗubobi, da karatuttukansu, ya kula da ladanai da kiran salla daidai.

    4. Ya naɗa alƙalai masana masu adalci da tsoron Allah da kamewa, ya sanya idanu sosai a kansu, saboda sai an tuhume shi kan duk shari’un da suka yi, zai kuma samu lada kan adalci da taimako da suke yi wa mutane.

    5. Wajibi ne a kan shugaba musulmi ya ringa fita jihadi da kansa, sannan kuma ya tura mujahidai suna yi a ƙalla sau ɗaya duk shekara. Gwargwadon ikonsa. Koda kuma ya yi sakaci da sauran nau’o’in jihadin.

    6. Aiwatar da Shari’ar Allah da hukunta masu laifi ba sani ba sabo kamar yadda Allah ya shari’anta da manzonsa, kada ya kuskura ya yi wani hukunci da ya saɓawa shari’ar Allah Ta’ala.

    7. Ya kula da tattalin arziƙin mabiyansa da jin daɗinsu da walwalarsu. Ya tabbatar yana bin hanyoyin da shari’a ta yarda da su domin samun kuɗin shiga kamar zakka, ganima da jizya, ya kuma sarrafa su ta hanyoyin da shari’a ta yi izini a sarrafa su.

    8. Kafa hukumar kula da waƙafi da tsara al’amarinsa ta yadda kowa zai amfana da shi, mutane kuma su samu ƙarfin gwaiwar bayar da kafa waƙafin.

    9. Yin adalci wajen rabon arziƙin ƙasa da gudanar ayyukan ci gaban al’umma.

    10. Wajibi ne shugaba ya kasance mai gaskiya da riƙon amana ya guji zalunci da nuna son kai da bambanci tsakanin mabiyansa.

    Shahararren malamin nan masanin siyasar musulunci Abul Hassan Almawardi Rahimahullahu ya faɗa a cikin sanannen littafinsa ‘Al- Ahkamus sultaniyya cewa akwai haƙƙoƙi goma a kan shugabanni.

    A taƙaice su ne;

    1. Kiyaye addini daga gurɓata.
    2. Tabbatar da doka da oda da bai wa kowa haƙƙinsa.
    3. Tabbatar da tsaro a birane da ƙauyuka.
    4. Tabbatar da hukuncin Allah ba sani ba sabo.
    5. Tabbatar da tsaron kan iyakoki.
    6. Yin jihadi domin ɗaukaka addinin Allah Ta’ala.
    7. Tattara kuɗin shiga da sarrafa su ta hanyar da shari’a ta yarda da su.
    8. Rabon arziƙin ƙasa da biyan ma’aikata albashinsu.
    9. Naɗa amintattu mutanen kirki masu gaskiya a kan muƙamai.
    10. Sanya idanu a kan dukkanin al’amuran mabiyansa da wanda ya naɗa su kula da ɓangarorin gudanarwa kada ya bari kowa yake cin karensa ba babbaka.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau danna nan.

    Edita:@rumasau-kallamu

     

  • Iyalin Musa Ɗanƙwairo

    Iyalin Musa Ɗanƙwairo

    Iyali suturar mutum, iyali suturar gida. A bisa yanayin zamantakewar bil Adama da aljannu, cikar ɗa, mutum namiji ko ‘ya, mutum mace ita ce yadda Allah ya hore musu, ya ba su dama, suka assasa zuriya ta kankin kansu.

    Ta haka za su sami nutsuwa, da samun ayyukan yi a duniyarsu da lahirarsu, musamman ma idan suka yi aiki da hukunce-hukuncen addini da matakan zamantakewar rayuwa bisa kyakkyawan zaɓi da dacewa. Haka kuma aure yana a kan gaba wajen tsayar da usra ko iyali da za su iya zama ƙwarara, ina ma a ce an bi sharuɗɗa da kyawawan dangogi na yin sa.

    Alhaji Musa Ɗanƙwairo wanda aka fi sani kuma ake kira da Maradun, ya sami jagoranci na iyaye wajen yin matar farko 21. A yayin zaman Ɗanƙwairo a doron rayuwar duniya bayan matarsa ta fari, ya auri mata da yawa kuma wasu daga cikinsu ne suka haifa masa ‘ya’ya har goma sha bakwai (17).

    Matan Aure na Musa Ɗanƙwairo

    Mata waɗanda Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya aure a rayuwarsa ta duniya su ne:

    i) Hauwa Taladan
    ii) Hajiya Hadiza (Ikka/Tashikka)
    iii) Amina
    iv) Tumba
    v) Rabi (‘Yar Zuma)
    vi) Maryam (Amarya)
    vii) Hauwa
    viii) Maimuna

    ‘Ya’yan Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maza da Mata

    Ga tsarin sunayen ‘ya’yan Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ta bin ɗakunan iyayensu mata da suka haɗa da:

    i) Ɗakin Hauwa (Taladan)

    ii) Ɗakin Hajiya Ikka (Tashikka)
    a) Muhammadu Ɗanmakaɗa, Dauda na ɗaya (1)
    b) Alhaji Garba, Zwacin Kiɗi, Marafa, Daudu (2)
    c) Audu Adodo, Wakilin Kiɗa
    d) Zulaihat
    e) Habiba

    iii) Ɗakin Amina
    f) Ummaru Ka-ji-Dama (Makaɗin Noma)
    g) Amina (Kassu): Tana aure a Maradun

    iv) Ɗakin Tumba
    h) Sanin Ɗanƙwairo, Zakin Murya

    v) Ɗakin Maryam (Amarya)
    i) Sa’adatu
    j) Muhammadu Balarabe
    k) Umaru

    vi) Ɗakin Rabi’a (‘Yarzuma)
    l) A’ishatu (Indo)
    m) Malam Musa Tunau (Malamin Makarantar Allo)

    vii) Ɗakin Hauwa
    n) Abubakar, Ciroman Kiɗa
    o) Amina, Ige
    p) Ibrahim Ɗan’auta22

    viii) Ɗakin Maimuna
    Ba ta Haihu ba.

    Bishiyar Iyalin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun

    Kaka Maiganga
    Usman Ɗankwanagga = Yarnunu
    Musa Ɗanƙwairo23 Amina Binta (Maryam)

    = Hauwa = Haj. Hadiza =Amina = Tumba = Maryam =Rabi = Hauwa =Maimuna
    (Taladan) (Ikka Tashikka) (Amarya) (‘Yar Zuma)
    Malam Musa Ba ta
    Tunau haihu ba
    Umaru Amina (Kassu)
    (Ka-Ji-Dama) Tana Aure Sa’adatu Muh Umaru
    a Maradun (‘Yabbata) Balarabe
    Muhammadu Sani (Zaƙin Murya)
    Ciroma Amina Ibrahim Ɗan’auta
    Abubakar (Ige) (Harkokin
    Magaji na (2) Kasuwanci)
    Muhammadu Garban Audu Zainabu Habiba
    (Ɗanmakaɗa) Ɗanƙwairo (Adodo)
    Magaji na (1)

    = Salame = Baraka
    Muhammadu Muh Tamaikiɗi
    Ɗanjimma Basiru
    Magaji na (3)

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kiɗa da Waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Kiɗa da Makaɗi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Ranar Damokuraɗiyya A Najeriya

    Tarihin Ranar Damokuraɗiyya A Najeriya

    Alhamdulillah yau ranar damokuraɗiyya, tun lokacin da Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ayyana cewa duk ranar 12 ga Yuni ita ce ranar damokuraɗiyya a Najeriya, domin girmama gwagwarmayar da masu rajin tabbatar da tsarin damokuraɗiyya suka yi, na kawo wannan tsari har zuwa yanzu. Yana da kyau  a yi waiwaye kuma a duba menene ita kanta damokuraɗiyyar da kuma , me yasa muke cikin matsayin da muke ciki a Najeriya. Saboda maganar tattalin arziƙi da wasu abubuwa da suka shafi rayuwarmu. Da kuma ƙalubalen da muke ciki, har ya sa wasu suke ganin ai damokuraɗiyyar ba ma cin gajiyarta. 

    Za mu yi waiwaye a kan wannan mu duba mu wane yanayi ne ya fi dacewa da mu, sannan mu bibiyi ƙalubalen da fahimta ta wasu mutane irin su tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da yake cewa ai mutanen Afirka sun ƙirƙiro tasu damokuraɗiyyar. Duk wannan suna cikin abin da yake ƙalubale a kanmu, kuma a matsayin mu na masu bibiyar al’amura, ya kamata mu yi nazari a kan wannan.

    Na farko, kamar yadda muka sani damokuraɗiyya mutane daban-daban suna da fahimta iri-iri a kanta. Ba wai a nan ƙasar tamu ba har a faɗin duniya baki ɗaya. Ana da fahimta daban-daban da ta shafi damokuraɗiyya hatta a ƙasashen yamma da suke ganin su ne asalinta, kuma ita ce aƙidarsu. Haka kuma ƙasashen mu na Afirka da ƙasashen Musulmi, wasu na ganin damokuraɗiyya kafirci ce ba musulunci ba ne. Da dai maganganu daban-daban. Wannan abu ne mai zurfi, kuma mai faɗi amma za mu taƙaita a kan misalai ƙalilan; domin samun haske a kan ma’anar damokuraɗiyya.

    MA’ANAR DAMOKURAƊIYYA

    Ita dai damokuraɗiyya ana ganin cewa gwamnati ce wadda mutane suka zaɓe ta. Wannan ita ce fasasara mai sauƙi, amma wasu suna ƙalubalantar wannan. Damokuraɗiyya wani tsari ne da zai kawo gwamnati mai inganci, kuma wanda mutane suke da damar faɗin albarkacin bakinsu, domin nuna sakamakon abin da aka yi musu, su fitar da ra’ayinsu, kuma su yanke hukunci ba tare da an tilasta musu ba. 

    Mutane za su yi zaɓe, su yi abin a cikin lumana, kuma kowacce ƙasa da irin nau’in gwamnatin da ta ɗauka na tafiyar da gwamnati mai adalci ko da ba a yi zaɓe ba. Bisa haka ne ma mutane irin su Muhammad Gaddafi yake ganin shi damokuraɗiyya yake yi saboda ya ba wa al’ummarsa duk irin abinda suke bukata, shi ma damokuraɗiyya ce. Kamar ƙasar Rasha da suke yi abubuwansu mai inganci, su ma suna ganin damokuraɗiyya ce. Ita damokuraɗiyya ta banbanta da yanayin da mutane suka ɗauki kansu. 

    Misali kamar mutanen China, suna ganin ƙasarsu ma tana bin damokuraɗiyya duk da cewa ba zaɓe suke yi ba da za a ce duk gari mutum ɗaya a zaɓe shi, a a sai dai ‘yan jami’yya ne  kawai suke yin zaɓe tare da bin ƙa’idoji na tabbatar da tsarin gwamnati, saboda China sun fi shekara dubu uku(3000) sun yi gwamnati mai inganci, wadda kafin a ɗauke ka aiki, sai ka nuna ƙwarewa (meritocracy), sun daɗe suna irin waɗannan abubuwan tarihi da ya ba su damarsu fito da tsarin da zai amfane su. 

    Saboda haka a ko’ina za ka ga mutane suna da irin nasu tsarin na damokuraɗiyya ta yadda za su aiwatar da ita. Tun da haka kenan za a ce irin damokuraɗiyyarsu ba za ta zama irin ta ƙasashen turawa ba. A zaɓi shugaban ƙasa, da gwamna da ‘yan majalisa. In dai aka samu gwamnati mai inganci, mai adalci, mai kulawa da haƙƙin jama’a, shi kenan su wasu suna ganin cewa wannan damokuraɗiyya ce.

    Saboda haka, amana ce idan aka ɗauketa aka auna ta za a ga cewa wasu mutane ne suke damfarar jama’a su juya akalar gwamnati, duk da kana zaɓe amma ba ka da tasiri sai wasu mutane ƙayyadaddu da suke da kuɗi da ɗaurin gindi na wasu ƙungiyoyi, kamar yadda yake yanzu a Amurka take fuskantar barazanar yahudawa (Zionists) sun karɓe ƙasar sai yadda suke so, saboda suna da yadda za su yi, ba ka da damar cewa komai saboda suna da kuɗi da jaridu da abubuwa da za su iya hanaka samun wannan zaɓe, tun da ba kowa zai tsaya a zaɓe shi ya ci ba, sai ace damokuraɗiyya ce.

    Kuma akwai yawancin mutane da suke ganin cewa damokuraɗiyyar nan turawa ne suka ƙirƙireta kuma ya saɓa da tsarin musulunci. To amma shi fa tsarin musulunci nan ya danganta da wanda yake magana, misali, musulmin ƙasar India kimanin mutum miliyan ɗari biyu (200 miliyan) fiye da yawan musulmin ƙasashen Afirka, babu inda ya fi su yawan musulmi a duniya sai ƙasar Indonesia. 

      Shi wannan musulmin sai ya ce maka shi ya fi son tsarin damokuraɗiyya, saboda idan ba tsarin damokuraɗiyya ba, babu yadda zai iya gudanar da addininsa na musulunci. Saboda haka a ba wa kowa ‘yancin ya gudanar da addininsa yadda yake so shi musulmin India yake buƙata.  

    Amma kuma idan ka je ƙasar da musulmi ke da rinjaye, za su  ce mu a bar mu mu yi tsarin musulunci mu ɗabbaka shari’a, domin shi ne  zai yi mana dai-dai da yadda muke so. Don haka,  a nan an samu bambanci da damokuraɗiyya da yadda za a yi aiki da ita.

    Damokuraɗiyya kamar riga ce ko mota da za ka yi amfani da ita, ba lallai sai an bi tsarin yadda turawa suka kawo ba. Su turawan sun kawo wannan tsarin (liberal democracy) ne da a zo a yi zaɓe kuma duka abin da mutane suke so shi za ayi, kenan babu haƙƙin Allah. Tun da farko Kent ne ya zo da tsarin wayar da kai a kan babu Allah (enlightment) da suka ce kada mutum ya yarda da abin da ba ya ganinsa. 

    Tun daga nan turawa suka daina tunanin Allah cikin al’amuransu saboda waccan aƙidar ta (Enlightment philosophy). Allah da suke bauta masa shin “son zuciyarsu”, duk abin da zai tabbatar musu  da wannan son zuciyar da jin daɗi. Shi kuwa musulmi ai ba za su yarda da wannan ba. 

     Idan ka ba da zaɓi za a yi wannan, a misali ƙasar Misra, idan  ka zo ka ce za a yi damokuraɗiyya a yi zaɓe, mutanen Ikhwan su ne za su ci zaɓen, saboda haka turawa ba za su yarda a yi damokuraɗiyya a Egypt ba. Sun fi son a dinga mulki irin na soja ko sarakuna (mulukiyya) , wanda da wannan za su yi amfani su juya mutane yadda suke so. 

    Amma idan aka ce za ayi damokuraɗiyya to, tsari irin na Ikhwan ne zai tabbata. Musulmi da ‘yan ideology sun fito sun ce wai ‘yan Ikhwan ba mutanen kirki ba ne, saboda haka a nan za ka zaɓi Musulmi ‘yan Ikhwan ne ko maƙiya addinin Allah irin su Sise. Sai ka ga shugabannin larabawa suna goyon bayan Sise sun ƙi su goyi bayan Ikhwan, waɗanda za su tabbatar da adalci, su ba da dama a yi addinin gaskiya. Amma sai su goyi bayan Zionists don biyewa son zuciya, kawai.

     

    Ita damokuraɗiyya ba ya danganta da yadda ka ɗauketa, wanne tsari ka shigo da shi don ka tabbatar. Shi yasa ƙasar China da suka fi kowaɗanne mutane yawa, sun tafiyar da damokuraɗiyyarsu a kan tsari na tafiya da gwamnati mai kyau, kuma za a dauki mutane waɗanda suke da inganci su yi aiki. 

    Yanzu shi shugaban ƙasar China sai da ya yi shekara 30 yana aiki, tun daga kan matsayin Kansila ya fara, sai sun tabbatar da kai kwararre ne kafin ya zo kan shugaban ƙasa. To ka ga China da suka zo da ‘yan gurguzu (communist) ɗinsu dole ne ka ba su wannan matsayi na damokuraɗiyya, idan aka zo za a yi aiki ko na makaranta ne ko asibiti ko kwashe shara, sai sun fito da abubuwa an tambayi mutane domin a ji ra’ayinsu tare da bin diddigi a kan aiki. 

    Shi yasa masana ilimin kimiyyar siyasa suke cewa, ba za a ce China ba ta bin tsarin damokuraɗiyya ba, domin kowanne aikin gwamnati sai an tabbatar da ingancinsa, kuma sai an tambayi ra’ayin jama’a amma ba haka ba ne a ƙasar Amurka, ba ruwansu da wannan, kawai idan an yi zaɓe bayan shekara hudu an kori wannan an kawo wannan haka dai. To amma su China a tsarin damokuraɗiyyarsu da manufarsu shi ne ta yaya tattalin arziƙinsu zai juya ƙasar. Shi ya sa daga 1978 zuwa yanzu mutum sama da miliyan 500 sun fitar da su daga talauci. 

     Wane abu ne za su fito da shi da za su taimakawa mutane. Shi ya sa su a wurinsu duk wanda ya ce tsarinta ba ingantacce ba ne ya yaudari kansa. Domin sun ɗora sha’anin al’adunsu da tarihinsu. 

    Da wannan za mu fahimci cewa ita damokuraɗiyya nan da ake magana ba tsarin da za a ce don kana da gwamnati da aka yi zaɓe wai ka yi damokuraɗiyya, haka ne  ka yi demokuraɗiyya, amma akwai abubuwa da yawa da suka shafi wannan. Kamar irin abin  da yake faruwa a India, ga shi nan Indian tun 1940 suka samu ‘yancin kai ba a taɓa gwamnatin soja ba, amma yanzu india ta lalace, saboda ‘yan Hindu masu aƙidar bambancin addini, waɗanda su ne mafi yawa suke tsangwamar musulmi saboda ƙiyayya. 

    Idan zaɓe ne , to an yi zaɓe a India, kuma abin da suke so masu rinjaye (majority) su kashe mara rinjaye (minority). Wannan bai shigo cikin tsarin damokuraɗiyya ba, domin yadda aka ce, amma ana amfani da dangwalen masu rinjaye domin a cutar da marasa rinjaye (musulmi). Ya nuna cewa India duk maganar da suka yin a damokuraɗiyya ba haka ba ne. 

    Bisa wannan, idan za ka yi maganar damokuraɗiyya, sai ka yi bibiya, menene ya shafi rayuwar al’umma, an samu ci gaba ko ba a samu ci gaba ba?

    DAMAKURAƊIYYA A NAGERIYA

    Lokacin da turawa suka zo sun tarar da mutane, suna da tsarin rayuwarsu da tsarin gudanar da mulkinsu a wuraren da ake da shi, sun samu Daular Usmaniyya (Shehu Ɗan Fodio) duk suna da tsarin rayuwarsu da ƙabilu ma da ba su da tsarin shugabanci, amma suna da irin tsarinsu, na zaman lafiya da na rashin zaman lafiya da na tattalin arziƙi da zamantakewa.

    Daular Usmaniyya ta ƙasar Sokoto ta haɗa gaba ɗaya ƙasar Hausa da Nupe da Ilori da can ɓangaren Adamawa da wasu a Kamaru da Benin da Nijar da Burkina Faso. Ƙasa ce amma da sarakuna a kowanne garuruwa. Bayan jihadi aka kafa Daula mai ƙarfin tattalin arziƙi a nahiyar Afirka ta baƙar fata a ƙarni na goma sha tara (Q-19).

    Turawa da suka zo sai suka haɗe mu da yankunan Arewa da Kudu, a shekara ta 1914, domin samun dunƙulalliyar Najeriya. Bayan kowanne yanki da irin al’adunsa da addininsa daban, ta yaya za a yi wannan zamantakewar? Wannan dai bature ya haɗa ne saboda ya yi cinikayya ya samu kuɗi saboda a wannan nahiya ta savannah har zuwa kurmi akwai arziƙi ta yadda zai dinga fitar da amfanin gona, ya gyara sannan ya dawo da shi don ya samu kuɗi, wato dai saboda ƙarfafa arziƙin turawa. 

    Saboda haka suka haɗe waɗannan ɓangarori, don ya yi amfani da su wajen mulkinsa bisa samar da umarni ta ƙarƙashin sarakuna (indirect rule). Da bature ya zo zai tafi bayan shekara 60, babu wani abu da ya sani sai tsarin mulkinsa irin na nasara, wanda suka ɗora kansu a kai tun bayan da suka yi Industrial revolution a ƙasashen yammacin turai, da ƙasasahen da suka kafa.

    Wannan ya dogara da irin tsarinsu da zamantakewarsu da suka zo da su. A nan sai suka lura da cewa tun da kuɗi suka zo nema, sai su yi amfani da irin tsarin mulkinsu amma su hana waɗannan sarakuna wani iko, sai abin da suka ga dama za su yi da su, cewa haraji idan za ka biya sai da kuɗin nasara. Shi kuma kuɗin nasara ba a samunsa sai an yi aikin leburanci , ko a yi noma irin nau’in abin da za su saya. Wannan ya jefa ƙashin bayan tattali arziƙinmu cikin talauci, kuma har yanzu ana cikin wannan yanayin talauci. 

    Saboda haka aka kawo ilimin Boko wanda idan babu shi babu wani abin da za ka yi. Ya zama dole ta sa, sarakuna da mutanensu suka shiga wannan karatu, daga bisani suka ce sai an kafa jam’iyyu da tsarin siyasa. Aka yi jam’iyyu a Arewa da jam’iyyu a Kudu. Wannan shi ne ya samar da jamhuriyya ta farko kowanne larduna yana da nasa tsarin da yadda za a tafiyar da su.

    Akwai babbar matsala a wannan lokaci na wasu rukunin ƙabilu da aka rufe su ba a ma jin labarinsu, misali kamar a jihar yamma an samu matsala da tashe-tashen hankali, sai jihar Arewa suka haɗa baki da jihar Gabas suka rinjayi ‘yan majalisa na jihar Yamma domin samar da  jihar  Yamma ta Tsakiya (Mid west). 

    Abubuwa suka yi ta faruwa ana ta rikici wanda da ma tsarin ƙarfin iko daga majalisa (parliament), inda shugaban gwamnati za a zaɓo shi daga mazaɓarsa ba duk ƙasa ce take zaɓarsa ba, kuma jami’yya ce take gaba da shi, da jam’iyya za a yi amfani da jam’iyya za a yi mulki da jam’iyya ake haɗa kai da wasu aka yi wannan wake- da- shinkafar aka yi zaɓe, zaɓenma an samu maguɗi da kashe-kashe da rigingimu, har manyan kudu( waɗanda sun san abin da suke yi) suka yi ta ba da matsala a majalisa (parliament)

    Sir Abubakar Tafawa Balewa ya yi fama da ita wajen neman haɗin kan mutane. Har Antony Enahoro yake cewa; idan babu wannan mutumin ƙasar nan ba za ta zauna lafiya ba, haka Tafawa Balewa ya sha wahala. ‘Yan kudu da suka ga idan zaɓe za a yi ba za su iya kai labari ba. 

    Sai sojoji suka zo suka kifar da wannan gwamnati, suka kashe Tafawa Balewa da Sardauna da Akintola da sauransu. Domin sun ce idan ba su da yawan mutane a majalisa, to su  bi ta hanyar maguɗi a  ƙidayar jama’a (Census) wanda aka yi a shekara ta 1963 har aka sake a 1964, suka ga maguɗinsu bai ci ba. Sun fahimci zaɓe, ƙato-bayan- ƙato da ƙuri’a bayan ƙuri’a, to ɗan kudu ba zai yi mulki ba. Sai suka ce maganin wannan shi ne su zuga sojoji su yi juyin mulki.

    A wannan lokacin mafi yawan sojoji ‘yan ƙabilar igbo ne, amma ainihin jam’iyyar AG ta Awolowo ita ce ta saka su. Duk waɗannan abubuwan saboda rashin kyakkyawan nazari da ba mu da shi a ƙasar nan sai aka dinga cewa ai Inyamurai ne  suka shirya juyin mulki da wannan kisan gillar. Amma dai babbar manufar an yi shi ne don a hana mutanen Arewa mulkin Najeriya.

     Don haka akwai maganar ƙabilanci , akwai maganar bambancin addini, saboda  Sardauna mai riƙo da addininsa ne kuma yana son ƙabilarsa da addininsa su fi kowacce al’umma a Najeriya. Lallai akwai wannan amma ba shi kaɗai ba ne, abubuwa suna wuce haka. ‘Yan kudu abin da suke so a wannan lokaci shi ne, yadda zasu karɓi mulki, tun da ba su samu ta hanyar dangwale ba sai suka ƙaro rigima, inda suka kawo soja ya ƙwace mulki.

      Wannan yana da muhimmanci mu fahimce shi. Kuma Mr. SG Ikoku ya faɗa a wani taro (conference), ya ce sun yi magana da sojoji domin su fahimtar da su maganar siyasa. Shi ya ce ‘yan siyasa ne suka zuga soja aka yi juyin mulki a Najeriya.Tun bayan mutuwar Tafawa Balewa ƙasar nan ta kasa zama lafiya, kamar yadda Tony Enahoro ya faɗa cewa, idan babu Tafawa Balewa ƙasa ba za ta zauna lafiya ba.

     Haka kuwa aka yi da aka yi wannan, abin da ya biyo baya shi ne yaƙin Biafra aka zo aka kashe mutane, abubuwa da yawa  a ƙasa , aka shiga rigingimu. A daidai wannan lokaci sojojin Arewa suka hamɓarar da gwamnatin Ironsi, suka saka Gowon ya zama shugaban ƙasa. A dalilin haka da sauran abubuwa suka  ce za su yi ƙasar Biafra, wannan ya haifar da yaƙi domin tsare ƙasa daga masu ƙoƙarin ɓallewa. 

    Shi Yakubu Gowon yana tare da mutanen Arewa aka zo  yin yaƙi na Ojukwu aka shafe kusan shekaru uku ana yaƙi (1967-1970).  Gowon ya yi shekaru tara yana mulki, a lokacin manyan ‘yan siyasa, suna nan  waɗanda ba a kashe su ba, irin su Awolowo da Azikwe da malam Aminu Kano da Shagari da sauransu. Su ma waɗannan ‘yan siyasar  suka yi ta ƙoƙarin a basu mulki.

     Gowon ya yi ta yaudararsu, yau ya ce wannan gobe ya ce ya canja. Saboda ya ga irin yadda aka yi a ƙasashen Afirka, sojoji suna ta yin mulki. Kuma babu maganar yin zaɓe. Saboda haka  daga cikin sojoji Kanal  Shehu Musa ‘Yar Adua ya jagorance su , suka yi juyin mulki  suka kawo Janar Murtala Muhammad wanda dama shi ne shugabansu tun bayan da aka yi yaƙin Basasa.

     Wanda yake tsayyaye ne a kan batun rashin cin hanci da rashawa. Nan da nan suka ce za su mayar da mulki a hannun farar hula domin ƙasa ta zama ɗaya. Za a yi mulki damokuraɗiyya, wanda za a kawo tsarin shugaba mai cikakkken iko ba irin na jamhuriyya ta farko ba wato parliamentary.

    Yanzu Allah ya kawo zamani wanda mutane ba wani nazari suke yi ba da har suke kawo maganar wai a koma wancan tsari na ƙarfin iko daga majalisa (parliament). Saboda ba ma yin ƙoƙarin fuskantar abubuwa bisa nazari. 

    Shin menene matsalar Najeriya? Ta ƙarfin iko daga majalisa (parliament) ne ko kuma ta shugaba mai cikakken iko (presidential), ko ta wani abun ce daban? Sai suke ganin cewa wai a koma baya. Wannan jamhuriyar fa ita ce ta wahalar da mutane da rarrabuwar kai, wadda ta haddasa yaƙin basasa. Ita ce suke son ta dawo kawai a nan ma suna ganin idan ba haka suka yi ba, ba za su samu mulki ba daga hannun ɗan Arewa. Shi kuma ɗan Arewa gani yake, idan babu mulki ba zai cigaba ba.  Wannan matsala ce da take fuskantar ‘yan Najeriya.

    Da aka zo gwamnatin Murtala, suka kashe shi. Sannnan Obasanjo ya zo a matsayin shugaban ƙasa, gwamnatin ta yi ƙoƙari waje shirya zaɓe domin mayar da mulki a hannun farar hula, aka zaɓi Alhaji Shehu Shagari daga Jam’iyyar NPN.

    Sun zo da tsarin shugaba mai cikakken iko saɓanin tsarin jamhuriya ta farko na ƙarfi daga majalisa (parliament), wanda ba duk ƙasa ce take zaɓen shugaban ƙasa ba. Shi kuwa wannan tsari na shugaba mai cikkaken iko, duk ƙasa ce take zaɓen shugaban ƙasa da mataimakinsa. Idan za a duba magana ta hankali, ya kamata a ce wanda zai jagoranci mutane gabaki ɗaya suka zaɓe shi da hannunsu da amincewarsu ya zama shugaban ƙasa, sauran jama’a suna da ta-cewa a kansa.

     Don haka wannan fa ya fi wancan. Wancan kawai, mazaɓar shugaba ce za ta zabo shi sannan ya zo zauren majalisa, su kuma ‘yan majalisa su zaɓe shi shugaban gwamnati. Domin jam’iyyar da ta fi kowacce karɓuwa a Najeriya baki ɗaya NPC ita ce ta ci zaɓe. Tana da mutane daban-daban daga kowanne sashe na ƙasa, ba wai kawai mutanen Arewa ba ne a cikinta, da mutanen kudu da mutanen tsakiyar Najeriya.

     Wannan ce ta sa jamiyyar ta samu karɓuwa ta kafa gwamnatin tarayya. A dalilin wannan ya sa, ana tafiya har wannan gwamnati ta lalace, ana ta rigima daga baya soja ya sake dawowa ya karɓe mulki ta hanyar juyin mulki a 1983. Matsalar da gwamnatin Shagari ta fuskanta shi ne na ‘yan jaridar kudu da suka saka shi a gaba. Wannan suka da jaridun kudu suka dinga yi wa gwamnatin har mutane suka karɓa suna ganin gwamnatin babu inganci ga cin hanci da rashawa a tsakanin ministoci da sauran laifuffuka, ‘yan kudu sun sa su a gaba, saboda su suke da bakin magana. Allah dai ya kawo qarshen gwamnatin, to ita ma ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba sojoji a tsakaninsu suka tumɓuke Muhammadu Buhari, sai Babangida ya hau.

    Daga nan ne aka fara tunanin ranar damokuraɗiyyar nan, menene ya kawo 12 ga watan Yuni? Shi Janar Babangida ya kawo sauye-sauye da yawa a cikin harkar Najeriya, kuma duk da cewa soja ne shi amma yana da ra’ayin ba wa mutane dama su yi Magana da kuma ra’ayi tattalin arziƙi da cewa ba wai lallai sai gwamnati ce zata riƙe ba, wato abubuwa za su koma hannun ‘yan ƙasa da ‘yan kasuwa.

     Wannan ya sa ya bambanta da sauran sojoji, kuma ya ba wa mutane dama su yi magana. Ya gabatar da tsare-tsare na siyasa da suka haɗa da taron makomar siyasa da cibiyar tattauna batutuwan siyasa. Da farko ya ba wa mutane damar su yi jam’iyyu suka kasa, ya zo ya yi jam’iyya guda SDP wadda ta karkata ga hagu, masu ra’ayin ci gaba da sauri da NRC wadda ta karkata dama, mai ra’ayin cigaban ‘yan mazan jiya (jari hujja). 

    Bayan da aka yi zaɓe na cikin gida a jam’iyyun sai aka ga duk ‘yan Arewa ne za su fito takara, domin Janar Shehu Musa Yar Adua shi ne ya ci a SDP sannan Malam Adamu Ciroma ya ci a NRC, wanda duk daga Arewa suka fito, aka ce wannan zaɓen fitar da gwanin yana da matsala domin an yi magudi , Babangida ya soke.

    Bayan gwamnatin Babangida ta soke zaɓen, sai ta sake ba da dama a zo a sake. Bayan sun gudanar da zaɓe, sai SDP ta fitar Chif MKO Abiola, ita kuma NRC ta fito da Alh. Bashir Othman Tofa, abokin Babangida, ɗan Arewa kuma ɗan Kano ne. Aka yi ta rigima, zaɓen ba a kammala shi ba, amma mutanen Abiola suka ce shi ya ci.

     Gwamnatin Babangida ta soke zaɓen a ranar 12 ga watan Yuni 1993. Wannan ya sa a ka cigaba da rigima daga ƙarshe dai Babangida, ya ce ya tafi (ya zakuɗa) daga shugabanci Najeriya. Ya sauka ya ba wa wata gwamnatin riƙon ƙwarya ta Chif Earnest Shoniken. 

    Sai gwagwarmayar sai an dawo damokuraɗiyya, sai an dawo da zaɓen da aka soke a Yuni tare da nuna cewa Abiola ne ya ci zaɓe aka hana shi saboda ba ɗan Arewa ba ne. Wannan rana aka mayar da ita kamar ranar sallah. Bayan da aka ba wa Shoniken shi kuma ya kasa, saboda tsangwamar mutane NADECO, sai Janar Sani Abacha ya karɓe mulkin ya shekara biyar, ya yi abin da zai yi, har Allah ya karɓi ransa yana shugaban ƙasa a 1998.

    Daga nan sai Janar Abubakar Abdussalam, ya karɓa, ana tunanin yadda za a saki Abiola bayan an tsare shi saboda ya ayyana kansa shugaban ƙasa. 

    Abdussalam ya sako shi. Ya yi ta ƙoƙari ganin an rantsar da shi ta hanyoyi daban-dabani, ya  haɗu da mutane  a wata tattaunawa da wani jami’in gwamnatin ƙasar Amurka (mataimakin minister) da wata jakadiyar majalisar ɗinkin duniya da wasu ‘yan fadarsa, Ya sha shayi a gabansu, Allah ya yi ikonsa rai ya yi halinsa. Daga nan wutar rigima ta cigaba, inda suke cewa dole mulki sai ya koma kudu. Abdussalam ya ga cewa abin da zai yi shi ne, ya miƙa mulki a hannun farar hula, inda ya shirya yin zaɓe tare gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa. 

    Ya tuntuɓi manyan ƙasa irinsu Babangida, suka shawarta cewa, idan za a ba da mulki, sai a ƙyale mutane su yi jam’iyyu, kuma lallai a saka ‘yan kudu guda biyu su fito takara. Don haka tun da Shehu Musa ya mutu yana gidan kurkuku tun lokacin da Abacha ya tsare shi, sannan Abiola shi kuma yana raye, sai a fito da shi a ba shi tikitin takara a jam’iyyar PDP. 

    Sannan jam’iyyar APP da kuma AD wanda yarabawa ne mafi yawancinsu aka ce su haɗe wuri ɗaya, su fito da ɗan takara guda ɗaya, suka fito da Chif Olu Falaye. Aka yi zaɓe domin a ba wa ‘yan kudu damar shugabanci, ‘yan arewa suka marawa jam’iyyar PDP ta Olusegun Obasanjo baya ya zama shugaban qasa a shekara ta 1999. 

    Obasanjo ya yi mulkinsa amma kullum tunanin June 12 suke yi, a yi ta nanatawa, duk shekara sai sun yi taro na nuna goyon baya a Lagos da sauran jihohin Yarabawa a ƙarƙashin ƙungiyarsu ta NADECO, wasu kuma sun shiga jam’iyyar AD har suka ci zaɓe kamar Bola Ahmed Tinubu a jihar Lagos. Wannan shi ne asalin gwagwarmayar June 12 da ta kawo har aka mayar da ita ranar biki mulkin damokuraɗiyya a Najeriya. Shugaba Muhammadu Buhari yace ya mayar da ranar demokuradiyya ta koma sha biyu ga watan Yuni.

    RIBAR DAMOKURAƊIYYA GA ‘YAN NAJERIYA 

    Yau an samu kimanin shekaru ashirin da biyar ana bikin ranar damokuraɗiyya a Najeriya tun daga 1999-2024, amma mutanen Najeriya suna cewa su har yanzu ba su ci gaba ba. Me yasa kuma har yanzu wasu suna ganin tsarin da ake tafiya bai kamata a yi shi ba? Tsarin baya a dawo da shi, kwan-gaba-kwan baya, waɗannan abubuwa su ya kamata mu yi nazari a kansu.

    Akwai abubuwa da yawa da suka kawo rashin cin ribar damokuraɗiyya a Najeriya. Zamu kalli abu biyu zuwa uku, da farko tushe, cewa Najeriya ta samu matsaloli na siyasa, wato ko ta soja ko ta farar hula. 

    Ba ta samu dama ta kafa tattalin arziƙi a lokutan farar hula ba, haka kuma a lokutan soja, da ya zauna da gindinsa ba. Idan ba a samu kafuwar tsarin tattalin arziƙi da ya kafu da gindinsa ba, duk abin da aka ɗora masa ba zai zauna ba. Mutane kawai abin da suke hanƙoro shi ne su shiga gwamnati su samu kuɗi. 

    Idan muka duba daga 1960 tun lokacin da Najeriya ta samu ‘yanci, mutane suna ganin Najeriya zata zama wani abu a duniya, saboda duk abin da ake tunani da akwai shi a ƙasar; akwai mutane da albarkar ƙasa. Ya kamata a ce an samu cigaba.

      A jamhuriya ta farko ‘yan siyasa babu abin da ke gabansu sai yaya za a cigaba da mulki, kowanne sashi yana hanƙoro sai ya riƙe mulki, kuma sai sashin ya samu kaso mafi yawa na madafan iko a mulkin Najeriya. Wannan ne yasa a wannan jamhuriyar ba a iya assasar da wani abu ba, da ma sojojin da suka biyo baya.

    Idan ka dubi duk waɗannan ƙasashen masu hanƙoron cigaba, a wancan lokaci Najeriya ta fi su, hatta China ballantana ka yi maganar irin su Korea da Indonesia da Malaysia amma rashin shugabanci nagari ya haifar da koma baya. Shi kuma shugabanci nagari ya gagara ne saboda ‘yan siyasa ba su ɗauki za su jagoranci mutane da adalci a tsakaninsu ba.

     Kowa kallo yake yi, yaya zai samu abin da zai samu ko ƙabilarsa su samu. Duk ƙasar da ta zama tana da irin wannan ba za ta samu cigaba ba. Muddin ‘yan siyasa ba su yi hakurin cewa za su yi mulki ba tare da cin dunduniyar wani ba, to ba za a samu cigaba ba. Kamar yadda muka faɗa Sir Abubuakar Tafawa Balewa yana ta wannan ƙoƙari amma abu ya gagara.

    A lokacin da duk ƙasashen duniya suke samun cigaba, mu kuma ‘yan Najeriya muna faɗa a tsakanin mu. A shekara ta 1968 ƙasar South Korea ta fara yin masana’antar ƙarfe (steel industry), wanda a sannan suna fama da yunwa babu abinci. Amma saboda suna da jagoranci ga abin da suka sa a gaba, cewa idan ba su da ƙarfe ba za su samu cigaba a duniya ba. Suka mayar da hankali suka yi. Duk wanda ya je ƙasar aka kai shi kamfanin mulmula ƙarfensu zai ga irin abin da suka yi.

    Mutanen Malaysia suna da matsala ta ƙabilanci a cikin tsarin zamantakewarsu, amma sun yi tunani a tsakaninsu cewa ku Malay tun da ku ne kuka fi yawa zamu bar muku shugabanci a ƙasar nan amma yaya za a yi kowa ya samu ‘yanci a yi kasuwanci don kowa ya amfana. Haka suka hakura suka yi, saɓanin Najeriya sai yaƙar juna ake yi, ba a samu wannan dacewar ba.

     Idan ba a samu wannan yarjejeniyar ba, ba za a samu zaman lafiya ba. Shi ya sa duk abin da waɗannan ƙasashen suka yi mu mutanen Najeriya muka kasa yi. Yanzu Malaysia suna fitar da kaya na sama da Dala biliyan 200-300, yayin da Najeriya muna fita da kaya ne kawai na Dala biliyan 63, South Korea wajen Dala biliyan Dari biyar ($500Billion). 

    Yanzu ƙasar da take fitar kaya na dala biliyan 63 ina take da ƙarfin tattalin arziƙi da zai kai ta har a samu cigaba, har a haɗ a su da irin waɗancan ƙasashe. Saboda haka ko ance za a yi zaɓe, ko za a yi damokuraɗiyya ko mulkin soja, idan ba a lalubo hanyar tattalin arziƙi da zai riƙe ƙasar ba, ba za a samu cigaba ba.

    Duba da yanayi tattalin arziƙinmu , yanzu duniya ta canja, baka da wani siddabaru da zaka yi, idan ba za ka yi abubuwa ba a kasarka, na kamfanoni da za a yi amfani da su a cikin gidanka. Ba ka da sinadari (chemicals) ko sumunti, ko tama da ƙarafa. To yanzu a Najeriya babu ɗaya da ake da shi. 

    Sai yanzu da ance za a samar da sumunti da fetur. Maganar gaskiya ba ka da wani siddabaru idan ba ka da waɗannan kayayyaki, sannan ka ce za ka cigaba. Tattalin arziƙinmu ba zai gyaru ba saboda ‘yan siyasa abin da ke gabansu mulki, ba sa tunanin su haɗa kai don mutanen ƙasarsu. 

     Saboda rashin haɗin kai ya zama babu wata jam’iyya a Najeriya, yanzu abin da muke da shi, taron mutane kowa yana son ya yi mulki ko ya haɗa kai da wasu ya yi damfara, ya yi cuta a zaɓe ya zama shugaban ƙasa. 

    Shi yasa zaka ga wani ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyu daban- daban, ya yi PDP, ya yi ACN, ya yi a APC, ya sake dawowa PDP, wani ya yi takara a jam’iyya wani ya fito takara sosai. Duk irin wannan babu aƙida ta siyasa da manufa da tsayawa a kan kyakkyawan ƙudiri na tsari ko na shekara takwas, ko shida ko ma hudu duk babu.

    Yanzu jam’iyyar PDP ta yi mulki a Najeriya tsawon shekara goma sha shida, amma babu abin da ta aiwatar, saboda ba ta da tsari maje-gaba, na maganar tattalin arziƙi, wanda zai fitar da ‘yan Najeriya.  Tun lokacin Obasanjo daga 1999-2015 ba a yi wani abu na tattalin arziƙi mai dogaro da abincin da zamu iya ciyar da kanmu, za mu samu lantarki, za mu samu wasu abubuwan more rayuwa dasu ba. 

    Jam’iyyar PDP ba ta samar ba haka suka gama mulkinsu. APC ta zo a 2015, ita ma ta ƙare baragadarta, sai ya zamo ‘yan siyasa, wani ne zai fito ya ce zai yi takara yana son zai zama shugaban ƙasa, ya zo ya yi abin da zai yi ya ci shugaban ƙasa, ya debo mutanensa su yi abinda suka ga dama, ta yaya zaka ce zaka ci ribar damokuraɗiyya a nan. 

    Wai wannan ma ya zama labari, shi yasa za mu yi ta zama a wuri ɗaya, idan wasu ƙasashen suna yin ƙere-ƙeren nan dole a samu mota, dole a samu jirgin sama. Wane irin tunani ne za ka haɗa Najeriya da Malaysia da ba su wuce mutum miliyan talatin ba. Amma suna fitar da kaya na sama da dala biliyan dari biyu, mu kuma muna fitar da kaya na dala biliyan sittin. Ka ga daga ji ka san wannan ƙasar ba a ɗora ta a kan gaskiya ba. Idan za a shekara dubu a Najeriya ba za a samu damar ɗora tattalin arziƙi ba, ba za a samu cigaba ba. 

    An raba kan mutane, an ce wannan ƙabilarsa daban, wannan addininsa daban , wannan sashensa daban. Ana amfani da wannan don su karɓi mulki su yi abin da suka ga dama. Ya zama cewa babu inganci a yadda rayuwa take. Duk tsarin da ake bi na tabbatar da abubuwa, haka ne. 

    idan kana maganar jam’iyya haka suke, idan kana maganar ƙungiyoyi haka suke. Mutane sun kasa ganewa cewa abin da ya kamata mu yi a Najeriya, mu haɗa kanmu, mu yi maganin matsalolin da suke damunmu, ba tare da maganar ɓangaranci ba.

    Ya kamata ko mu mutanen Arewa, ɓangaranci a siyasa ba zai kaimu ko ina ba, an yi amfani da ɓangarancin nan an kawo gwamnati ta shekara takwas, me ta yi wa mutanen arewan? Kuma a arewan nan babu wasu da za su ce idan an zo siyasa ga abu kaza da abu kaza da muke so, a matsayinka da kake takara ko ɗan Arewa ne ko ɗan kudu, mu sai ka yi mana wannan zamu zaɓeka.

     

    Babu wannan, mutane ma ba su damu da hakan ba, waɗanda suke da ikon yi ba su da damar da za su iya. Saboda ga yadda jam’iyyun suke, idan kana maganar sadarwa da kafofin yaɗa labarai, duk ba mu da su. Yanzu ko kafofin sadarwa na zamani (social media) har sai sun samu labarai daga kafofin sadarwa na ainihi, sannan suke yin wani tasiri. 

    Yanzu a gidajen talabijin guda shida da su ka yi fice a Najeriya, AIT, Arise, Channels, TVC, Trust TV , a cikinsu idan ban da Trust duk na ‘yan kudu ne. Haka idan ka zo ka ɗauki jarida, ana yin jaridu guda goma sha shida kullum, guda biyu ne kawai na ‘yan Arewa kawai na Arewa. 

    Saboda haka Arewa ba su da kafafen yaɗa labarai da za su dogara da su wajen nemowa Arewan ‘yanci da neman goyon bayan da suke buƙata. Kuma ‘yan siyasa wannan ba shi ne a gabansu ba, kowa hanƙoro yake yi a ba shi takarar gwamna ko ɗan majalisa, ya je ya yi ya dawo kuma da ma mutanensa duk yunwa suke yi. 

    Tunda yanzu, gwamnati ba ta ba da ilimi kyauta, ta yaya za a yi mutane kansu ya waye, tun da babu ilimi. Sun cutar da al’umma, sun mayar da su almajirai da ‘yan ta’adda da ‘yan banga saboda rashin ilimi. Ga shi kuma babu aikin yi, haka kuma dama idan siyasa ba ta zama daidai ba, ba yadda za a yi ta tabbatar da tattalin arziƙi, ya zama daidai. 

    Ana ta zagayawa a wuri ɗaya (cycling) idan wannan zagaye ba a dakatar da shi ba babu maganar cewa za a zo a yi zaɓe, ko za a yi damokuraɗiyya dai-dai ko za a samu shugabanni nagari. Duk wannan sai dai ya zama labari, kuma duk abin da da zai faru a duniya, mu ne koma-baya, sai dai a bar mu muna suɗi.

     Idan motoci sun mutu a kawo mana daga Korea, daga Amurka, daga inane? Tun da lantarki ma mun kasa samu, balle har ace za mu yi masana’antu, ɗan Arewa ma ya riƙe ya ƙasa. 

    Saboda haka, dole mutane su ce ai damokuraɗiyya ba ta zamar mana alheri ba! Duk da cewa mutane sun samu ‘yanci da sauran abubuwa amma tun da babu tsayayyen tattalin arziƙi, damokuraɗiyya ba ta samar musu ba. kuma ba za ta samar musu ba, a dai wannan tsari da ake yi saboda ‘yan siyasar nan suna yin siyasa ne saboda biyan buƙatunsu.

     Idan za ka tsaya takara ko na jiha ko ɗan majalisa, sai kana da ubangida nasu amma yanzu har sun fara caccanza su. Sai dai kuma wani yanayi daga Allah Ya kawo juyinsa, ko wani juyi ya zo a wani zamani, a samu mutane nagari, ya zama abin ya tabbata.

     Mu daina tunanin cewa Najeriya ko tsarin gudanar da mulki ne, wato ko ƙarfin iko daga majalisa (parliament) ko na shugaba mai cikakken iko (presidential) duk ba haka ba ne, mutane ne da matsalar. Idan an samu wasu da zasu maye gurbinsu ba, wanda hakan yana da wahala.

    Mun gani a ƙasar Turkiyya zuwan Erdugon, duk wahalar da ƙasar ta sha, sai da aka samu wasu suka kutsa, amma idan ba haka aka yi ba, waɗannan mutanen ko suna PDP ko suna APC, jam’iyyu haruffa ne kawai ya banbanta su. 

    Shi ya sa za ka ji  mutum yau APC gobe kuma ka ji shi a PDP jibi ya koma Labour, haka dai za ka ga suna ta yi. Kuma abubuwan nan da suke faruwa a duniya ba wai maganar tafiya sama ba ce. 

    Ya gagara a ce gwamnatin Najeriya shekara sittin ba za ta iya ciyar da kanta ba, shekara sittin an samu ‘yancin mulki kai, amma Najeriya ba za ta iya fitar da kaya ba, kai ko da zama muke muna ciyar da kanmu da sauran abubuwa kamar yadda China take yi da yanzu mun cigaba.

    Ɗan siyasar Najeriya abin da ke gabansa, ya samu mulki amma ba yadda zai ciyar da ƙasar gaba ba. Waɗanda suke zama suke magana a kafofin yaɗa labarai ko a ina ne, sai ka yi ta shan mamaki, su kuma ‘yan siyasar sun fi son waɗanda za su fito suna zagin wane ko su ce wane ɓarawo ne, ko wanda zai zo bambaɗanci. 

     To wannan shi ne ya sa muke da matsala. Idan ba mu canja siyasar mu ‘yan arewa ba, ba za mu samu cigaba ba. Dama su ‘yan kudu tafiya suke bisa tsari, don haka za su yi ta samun cigaba. Saboda mu ba mu fahimci inda duniya ta sa gaba ba. Muna fatan Allah ya bamu zaman lafiya a ƙasa, ya magance mana fitintinun da suka addabe mu, amin, Subuhanakallahumma… 

     

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

     

                                

  • Wasu Birane Da Garuruwa Da Makarantu Da KumaTsangayu A Arewacin Najeriya

    Wasu Birane Da Garuruwa Da Makarantu Da KumaTsangayu A Arewacin Najeriya

    Akwai wasu al’amura da ke jawo karkatar makaranta ko masu neman karatun Alƙur’ani zuwa wasu larduna ko biranen fiye da karkatarsu ga wasu lardunan ko biranen.

    Ƙaura daga wuri zuwu wani Wurin daban, abu ne da aka san makarantan tsangaya da shi, tun kaka da kakanni. Da yawa za ka ga Wata tsangaya cike da gardawa ko almajirai a lokacin rani; amma da zarar damina ta sauka sai ka neme su ka rasa. Irin wannan na faruwa ne saboda noma da aikin gona don samun ishasshen abinci.

    A wani lokaci kuma, makaranci kan yi ƙaura da almajiransa ko kuma gardi a karan kansa, idan ya sami labarin wata tsangaya mai tashen tara makaranta; ko kuma labarin wani mashahurin alaramma mai baiwa don ya fa’idanta daga baiwar da yake da ita. Yanayin wuri da ni’imarsa ko yalwar ruwa da wadatar ƙasar noma shi ma wani dalili ne da ke jawo taruwar makaranta.

    Irin wannan al’ada ita ake kira yawon bundi a wasu sassa na Arewacin Najeriya, musamman ma Sakkwato da kewayenta. Don ƙarin haske game da asalin wannan al’ada, sai a duba Babi na Huɗu cikin Sashe na Biyu kan ɗabi’un makaranta da halayensu cikin zamantakewar tsangaya.

    Wata tsohuwar al’ada tsakanin makarantan Arewacin Najeriya ita ce, tafiya Gabas, ma’ana ƙasar Barno don samun karatu. Don haka ne ma zai yi wuya ka sami wani makaranci a faɗin wannan nahiya ta Arewa; wanda bai dangana da Barno ko kewayenta ba ya yin neman karatu. Wannan na komawa ga irin rigayen da Kanem Barno ke da shi wajen karɓar Musulunci da tsohowar alaƙar wannan daula; da ƙasshen Larabawa, ƙarnuka masu yawa da suka shuɗe.

    Ƙasar Barno ta zamo tamkar wata Ka’aba ce ga manema Alƙur’ani. Makaranta, a bisa ɗabi’arsu, sun fi son wurin da za su keɓance kansu nesa da jama’a; kodayake buƙatun rayuwa na yau da kullum musamman buƙatar abinci ya jawo yawaitar almajirai da makaranta cikin birane da garuruwa masu cigaban kasuwanci da tashoshin mota da kasuwanni.

    Za mu iya ayyana wasu garuruwa da suka yi fice tuntuni da tara makaranata a Arewacin Najeriya kamar haka:

    – Ngazargamu
    – Gaidam
    – Gashuwa
    – Gubuci
    – NGuru
    – Damaturu
    – Takai
    – Bama
    – Ganjarma
    – Birniwa
    – Kebberi
    – Hadejiya
    – Kondiga
    – Paki
    – Kahutu
    – Hunƙuyi
    – Matazu
    – Tsakuwa
    – Maƙarfi
    – Kura
    – Zangon Daura
    – Ningi
    – Bunkure
    – Illela a Nijar
    – Kance a Nijar
    – Mutame a Nijar
    – Insharuwa da dai sauransu.

    Abu ne mai matuƙar muhimmanci sanin yawan tsangayunmu na Alƙur’ani, da yawan malamansu da almajiransu. Wannan ya sa tsohowar gwamnatin jihohin Arewa ƙarƙashin jagorancin Marigayi Sir Ahmadu Bello; Sardaunan Sakkwato ta aiwatar da wannan ƙididdiga a Makarantun Alƙur’ani Bisa ƙididdigar Gwamnatin Arewacin Najeriya (1960)

    Domin karanta cikakken bayani a kan Gudunmawar Tsangayun Alƙur’ani Wajen Cigaban Al’umma danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Misalan Waƙafi Ababen Koyi A Tarihin Musulunci

    Misalan Waƙafi Ababen Koyi A Tarihin Musulunci

    1. Zamanin Halifofi Shiryayyu ba shakka an samiu nau’o’i daban-daban a wannan lokaci, kaɗan daga cikin misalan su sun haɗa da:

    Waƙafin da sayyidina Umar ya yi da kasonsa guda ɗari dake Khaibar, wanda ya rubuta wasiyya da kansa da cewa:- “Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai, wannan takarda sheda ce ta wasiyyar da bawan Allah Umar shugaban muminai ya yi ko wani abu zai faru da shi (yana wasiyya da cewa) Samgah da Sirmata bn Al-Akwa (gonaki biyu) da dukkan bayin da suke cikinsu da kasona guda ɗari dake Khaibara da dukkan bayin da suke cikinsu”..

    Waƙafin da Sayyidina Ali Bn Abi-Ɗalib Allah Ya yarda da shi ya yi, wanda ya rubuta shi kamar haka:- “Wannan takardar sheda ce bisa abin da Ali bn Abi-Ɗalib ya yi, ya kuma hukunta da dukiyarsa cewa; na sadaukar da (amfanin gonakinsa) na Yanbu da Wadil-Kura da Azinah da Ra’ah a cikin hanyar Allah; kuma ga ‘yan uwa na kusa da na nesa, kamar yadda ba za a yi kyauta da su ba, kuma ba za a gaje su ba, a lokacin rayuwa ko bayan raina”.

    Ba shakka wannan kaɗan ne daga cikin misalai da yawa na waƙafi; a lokacin halifofi shiryayyu, Allah ya yarda da su.

    2. Zamanin Mulkin Banu Umayya

    Ba shakka akwai misalai masu ƙayatarwa matuƙa na irin nau’o’i daban-daban na waƙafi da aka yi a wancan lokaci. Ga kaɗan daga cikinsu:-

    Gina babban masallacin nan na birnin Dimashk wanda har zuwa wannan zamani namu yana nan daram, wanda kuma muka ambata a baya cewa an gina shi a zamanin Halifa Walid ɗan Abdul – Malik wanda aka ruwaito cewa; a lokacin da zai gina wannan masallaci, sai da ya sa aka kawo masa ƙwararru daga ko’ina; waɗanda yawan su da sauran ma’aikatansu ya kai kimanin mutum dubu goma sha biyu.

    Ya kuma kashe kuɗi kimanin akwati ɗari huɗu; kowane akwati yana ɗauke da kwabbunan tataccen zinare guda dubu ashirin da takwas. Sai da ya shafe tsawon shekaru ashirin yana ginin wannan masallaci.

    Gina Asibitoci Da Hanyoyi Da Rijiyoyi

    Haka nan kuma shi dai wannan bawan Allah; shi ne mutum na farko da ya gina asibitoci na musamman don amfanin mutane.

    Haka kuma ya gina waɗansu na musamman da ya keɓance su ga masu ciwon kuturta; waɗanda a lokacinsa ya killace su, ya hana su bara; ya kuma ware maƙudan kuɗaɗe don yi musu magani da ba su cikakkiyar kulawa. Haka kuma, ya bayar da umarni ga gwamnansa mai kula da Madinah a wancan lokaci Umar ɗan Abdul-Aziz cewa ya gyara unguwanninta ya kuma gina rijiyoyi, ya kuma ɗauki ma’aikatan da za su rinƙa janyo ruwa don amfanin jama’a.

    Haka nan, ya aikawa dukkan jami’ansa a ko’ina kuɗaɗena suke cewa; su ware musamman ga mabuƙata tare da shimfiɗa hanyoyi da gidaje domin saukar baƙi kyauta. Bugu da ƙari kuma, wani kyakkyawan misali na waƙafi don amfanin al’umma shi ne ; yadda halifofin Banu Umayyah na wancan zamani suka bayar da muhimmanci matuƙa wajen gina madatsan ruwa, alal misali, a lokacin halifancin Umar ɗan Abdul- Aziz haka madatsan ruwa a wurare masu ɗumbin yawa kamar su Basra, da Arnmenia, da Dimashk da sauransu.

    3. Zamanin mulkin Abbasiyyawa

    Ba shakka halifofin zamanin Abbasiyya sun bayar da muhimmanci ga waƙafi a fannin gina asibitoci; da samar da littattafai don horar da ƙananan likitoci, tare da hayar ƙwararru da za su koyar da su duk ta hanyar waƙafi. Kaɗan daga cikin misalan asibitoci da aka gina a wancan lokaci; sun haɗa da asibitocin nan da ake kira Almustashfà Al-adudiy (wanda muka ambata a baya) wanda Haifa Adudud – Daulah al-Buwaihiy ya gina a birnin Bagdad a shekara ta (366 Hijiriyyah /976 Miladiyya) ya kuma ɗauki ƙwararrun likitoci a fannoni daban-daban waɗanda kimanin yawansu ya kai 24.

    Komai na asibitin kyauta ne, ga kulawa da marasa lafiya wajen abinci; da abin sha; da ɗinka musu sababbin tufafi, baya ga tsarin bayar da guzurin komawa gida ga duk wani marasa lafiya da aka sallama. Kamar yadda kuma ya zo a littattafan tarihi cewa, waɗansu daga cikin gwamnoni na wannan daula, sukan kashe kuɗaɗe maƙudai wajen yin irin waɗannan nau’o’i na waƙafi kamar yadda aka samu cewa, Ahmad ɗan Dolon gwamnan Masar a wancan lokaci, ya gina asibiti a lokacin da ya kammala, sai ya sadaukar masa da kuɗaɗen shigar da ake samu daga dar addiwan da kasuwar bayi da waɗansu gidaje nasa.

    Haka kuma ya kafa ƙa’idar cewa; a cikin waɗanda za su amfana da wannan asibiti ban da manyan hafsoshinsa da fadawansa da ‘ya’yan sarauta; haka kuma duk wanda za a kwantar a asibitin, sai an ba shi sababbin kaya ya sa, tsofaffin kuma za a adana masa su ne har zuwa lokacin da Allah ya ba shi sauƙi sai a damƙa masa kayansa.

    Haka kuma akan yi masa sabuwar shimfiɗa a kula da cin sa da shan sa, da yi masa magani, kuma ba za a sallame shi ba, har sai ya warke sarai; ya dawo yana cin duk wani abinci da ya saba ci kafin rashin lafiyarsa.

    Haka kuma a waɗansu lokuta akan gayyato likitoci daga wurare daban-daban don bayar da kulawa ga marasa lafiya, wato kamar dai abin nan da muka sani a wannan zamani da ake kira “medical tour”; (wato likitoci ‘yan sha-ka- tafi tare da biyansu haƙƙoƙinsu da ɗaukar ɗawainiyar duk wata buƙata ta su).

    Misalai na waƙafi da aka yi wancan zamani ba wai ya tsaya ne kawai ga gina asibitoci ba; haka kuma bai tsaya ga ɓangaren hukuma kawai ba. Wani ɗan ƙaramin misali da zai tabbatar mana da hakan shi ne, wani waƙafi da wani attajiri ya yi mai suna Fakhruddaula bn Almuddalib a birnin Bagdad (ya rasu a shekara ta 578 bayan Hijira ); ya gina wata katafariyar makaranta mai suna Dar Adhdhahab, ya damƙa ta a hannun wani mashahurin malami mai suna Jamaluddin bn Fadlan Ash- Shafi’i ya kuma sadaukar mata da wata dukiya tasa da abin da take samarwa kowace shekara, ya kai kimanin dinare dubu ɗaya da ɗari biyar.

    Bugu da ƙari, su kansu mata ba a bar su a baya ba; wajen wannan ayyuka na alheri, domin kuwa ya zo a littattafan tarıhi cewa Sayyida Zubaidah bnt Ja’afar bn Mansur; matar Halifa Harun Ar-Rashid ta haƙa rijiya da ake kira da “ainul mashash a Hijaz” ta kuma sa aka yi wa ruwanta hanya a tudu da gangare; har tsawon tafiyar mil goma sha biyu zuwa garin Makkah; wanda wannan aiki ya lashe kuɗi kimanin dinare miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai; (wanda ƙiyasin kowanne dinare ɗaya a zamaninmu shi ne nauyin giram 4.25 na tataccen zinare).

    A ɓangare na makarantu kuwa, tarihi ba zai taɓa mantawa da jerin gwanon makarantun nan da ake yiwa laƙabi da makarantun Nizamiyya ba; waɗanda waziri Nizamul Mulk Addardusi (ya rasu shekara ta 485 Hijiriyya) ya kafa, waɗanda da yawa daga cikinsu suka zamo a sahun farko a tarihin jami’o’i a duniya baki ɗaya. Haka nan ya ci gaba da gina irin waɗannan makarantu a ko’ina a cikin daular Musulunci, kamar yadda aka sami mashahuran malamai da suka koyar a waɗannan makarantu. Alal misali, a daidai lokacin da Imam Al-Ghazali yake koyarwa a reshenta na Bagdad, shi kuwa shahararren malamin nan mai suna Imam Al-Haramain Abu Al-Ma’ali Al-Juwaini yana koyarwa a reshenta na Naisabur.

    4. Daular Musulunci Ta Andalus

    A haƙiƙanin gaskiya ana iya cewa waƙafi na ɗaya daga cikin alamomin wuraren da daulolin Musulunci; suka kafu a ko’ina a faɗin duniya; domin kuwa shi ne kamar wata alama da ta zama ruwan dare a waɗannan dauloli a tsawon tarihinsu; duk da kasancewar sun kafu ne a wurare daban-daban kuma a lokuta mabambanta. Dalilin faɗin hakan kuwa shi ne, duk da cewa daular Musulunci da ta kafu a Andalus(Spain) ta yi nisa matuƙa; daga ƙasashen Larabawa waɗanda suke gabashin duniya.

    Domin kuwa Andalus tana cikin nahiyar Turai ne, to amma duk da haka, nau’o’i daban-daban na waƙafi da aka yi a cikinta, ko kaɗan bai gaza ga waɗanda aka yi a ƙasasshen gabas ɗin ba, a Alal misali, an samu Waƙafi a fannoni da dama a zamanin sarakuna irin su sarki Alhakam ɗan Abdur-Rahman An-Nasir wanda a lokacinsa ne wannan al’amari ya kai ƙololuwar bunƙasarsa, domin kuwa a zamaninsa ne ya sa aka jawo ruwa daga wurare masu matuƙar nisa zuwa ga wuraren buƙatar jama’a, waɗanda suka haɗa da masallacin Ƙurdubah.

    Kamar yadda ya yi waƙafi a fannin bunƙasa ilmi tun daga matakin koyon karatu da rubutu; har zuwa ga matakin ƙwarewa a fannonin haddar Alƙur’ani da Hadisi da Fiƙhu da sauransu.

    Hakazalika, an sami malamai da yawa waɗanda suka yi waƙafin litattafansu ga manyan cibiyoyin ilmi mai zurfi, kaɗan daga cikinsu sun haɗa da; Al Imam Abul-Ƙasim Abdul-Khaliƙ bn Abdil- Warith as-Sayuri (ya rasu a shekara ta 462 Hijiriyya) da al-Imam Kasim bn Isa bn Naji (ya rasu a shekara ta 839 Hijiriyya).

    Wani abin al’ajabi shi ne, ganin cewa yankin Andalus yanki ne mai yawan rafuka; wanda hakan yakan daƙile walwalar mutane matuƙa, sai musulmai na wancan lokaci suka yawaita yin waƙafi wajen gina gadoji. Littattafan tarihi sun ruwaito cewa gadar da ta fi kowacce girma da shahara a wancan lokaci ita ce gadar da sarki Hisham ɗan Abdur-Rahman ɗan Mu’awiya (ya rasu a shekara ta 180 hijiriyya) ya gina wacce ya kashe kuɗi matuƙa wajen gina ta.

    Kamar yadda ya ɗauki nauyin sa ido a kan aikin gina ta shi da kansa, wanda saboda da ganin haka har sai da waɗansu mutane suka fara gunagunin cewa; ya gina ta ne don amfanin kansa, a lokacin da labari ya kai gare shi, sai ya yi rantsuwa da cewa, “Ba zai yi taɓa bi ta kan wannan katafariyar gada ba, har sai idan tafiya yaƙi ko wani dalili ne ya tilasta masa yin hakan”.

    Kamar yadda kuma waɗansu daga cikin irin waɗannan gadoji sun yi ƙarƙo matuƙa; har zuwa wannan zamani namu, misali gadar da Mansur ɗan Abi Amir ya gina a shekara ta 389 Hijiriyya; wacce ya kashe mata kimanin kuɗi dinare dubu ɗari da arba’in.

    Wani abin mamaki dangane da yawaitar nau’o’in waƙafi a daular Musulunci ta Andalus; shi ne wani waƙafi da aka yi na musamman don sayen wani irin nau’i na kifi wanda ake kawowa a wani lokaci na shekara don raba shi ga matalauta; waɗanda ‘ya’yansu ƙanana na iya shiga cikin damuwa ganin yadda ‘ya’yan attajirai suke wadata da shi.

    5. Daular Uthmaniyyah

    Daular Musulunci ta Usmaniyya wacce Turkawa suka kafa, ita ce daula ta ƙarshe da ta faɗi. Ba shakka tarihin wannan daula cike yake da nau’o’i daban-daban na waƙafi; waɗanda lokaci ba zai ba mu dama mu yi bayanin su a wannnan ɗan ƙaramin littafi ba, to amma a taƙaice duk wani nau’i na waƙafi da muka ambata a baya, to su ma Turkawa ba a bar su a baya ba.

    Sannan kuma bugu da ƙari, muhimmancin da suka ba al’amarin waƙafi kai an samu cewa; akwai nau’o’i’ da dama a waƙafi da aka yi a lokacin mulkin wannan daula, kula da dabbobi marasa lafiya.

    6. Daulolin Musulunci na Nahiyar Afirka

    A haƙiƙanin gaskiya, abu ne mai matuƙar wahala a ce za a ƙididdige irin rawar da daulolin Musulunci na nahiyar Afirka; suka taka wajen bunƙasar al’ummarsu ta hanyar waƙafi. To amma hakan ba zai hana mu ɗan bayar da misalai na kaɗan daga cikinsu ba. Daga cikin mafiya muhimmancin irin waɗannan nau’o’i daban-daban na waƙafi sun haɗa da:

    Daular Musulunci ta Songhai

    An yi wani shahararren sarki na wannan daula mai suna Mansa Musa wanda ya yi gine-gine masu yawa da suka shafi na makarantu; domin bunƙasa harkar ilmi, ya gayyato tawaga ta musamman ta manyan masana a lokacin da ya je aikin Hajji da kuma gina masallatai guda biyu; na Gao da na Tumbuktu bisa taswirar da ɗaya daga cikin ƙwararru da ya zo da su a fannin gini mai suna Ishak el-Teudjin ya zana masa. Wannan masallaci ne daga baya ya zama shahararriyar jami’ar nan ta Sankore, duk a zamanin wannan sarki, a farkon ƙarni na goma sha huɗu na Miladiyya.

    Kamar yadda kuma an samo a tarihi cewa; a shekara ta 988 Miladiyya, an sami wani malami mai suna Al-Kadi Aƙib ɗan Mahmud ɗan Umar; wanda ya lashi takobin cewa; sai wannan gari na Tumbuktu ya tafi kafaɗa da kafaɗa da sauran manyan garuruwa na duniya a fagen bunƙasar ilmi mai zurfi. Domin aiwatar da wannan aniya tasa, sai ya nemi masu hannu da shuni da su taimaka da kuɗaɗe; don katafaren aikin faɗaɗa masallacin Tumbuktu da muka ambata a baya, ta yadda zai ɗauki malamai da almajirai masu yawa.

    Wani abin mamaki da ban sha’awa shi ne, sai aka sami wata mata mai dukiya; ta ɗauki nauyin gudanar da aikin ita kaɗai, a cikin dukiyarta a matsayin waƙafi.

    Daga baya wannan jami’a ta yi matuƙar shahara; har sai da ta zamo ɗaya daga cikin manyan jami’o’i na duniya a wancan lokaci; wanda har sai da yawan ɗalibanta ya kai kimanin dubu ashirin da biyar (25,000); haka nan katafaren ɗakin karatu da wannan jami’a take da shi daga littattafan da suka kama daga; dubu ɗari huɗu zuwa dubu ɗari bakwai (400,000 – 700,000). Nagartar karatunta ya zarce da yawa daga cikin manyan jami’o’in duniya na wancan lokaci.

    Dangane da al’amarin bunƙasa rayuwar al’umma kuwa, wannan daula ta bar wannan abin alfahari da dama; domin kuwa an samo cewa a lokacin wani sarki mai suna Muhammad Askiya, ya yi abubuwa a fannoni daban-daban da suka haɗa da kulawa; da jin daɗin matafiya masu keta hanyoyin sahara da suka gifta ta waccan ƙasa.

    7. Tsohuwar Daular Ghana

    Wani abin ban sha’awa dangane da ayyukan waƙafi a wannan daula shi ne; bayan Musulunci ya shiga wannan daula ba da daɗewa ba, al’umomin wannnan yanki suka fara aiwatar da abubuwa daban-daban da suka shafi; jin daɗin al’umma ta hanyar waƙafi.

    Alal misali addinin Musulunci ya shiga wannan daula ne a kashi na farko na ƙarni na ɗaya bayan Hijira; to amma sai ga shi a cikin shekaru goma da shigarsa; wato a shekara ta 60 bayan Hijira an samu cewa; yawan masallatai dake babban birnin wannan daula; waɗanda aka gina a ɓangarorin da musulmai suke; sun kai kimanin masallatai goma sha biyu; kowannen su cike yake da manyan malamai da ɗalībai a fannonin ilmi da dama.

    8. Zamanin Da Muke Ciki

    Kamar yadda muka ambata a baya cewa waƙafi wata babbar alama ce ta samuwar al’ummar musulmai a duk inda suke; ba shakka za mu iya ganin hakan har a wannan zamani da muke ciki; domin kuwa an sami mutane masu son aikin alheri da ƙungiyoyi waɗanda suka bayar da misalai ababan koyi na waƙafi. Ƙadan daga cikin waɗannnan misalai sun haɗa da:

    Tsarin Hannun Jarin Waƙafi Na Annur

    Wannan wani tsari ne da waɗansu bayin Allah suka yi. Reshen wannan gidauniya yana ƙasar Malaysia, to amma tana aiwatar da ayyukan waƙafinta a ko’ina a faɗin duniya. Ta hanyar da wannan gidauniya kuwa take gudanar da ayyukanta shi ne, ta tsattsara ayyukan da take son aiwatarwa; sannan sai ta rarraba shi a sigar hannun jari kowanne da farashinsa; wato abin nufi, iyaka yawan hannayen jarin da mutum ya saya, su ne gudunmawar da ya bayar wajen aiwatar da waɗannan ayyuka; waɗanda ake fatan ladansu zai ɗore har bayan rayuwar wanda ya bayar da taimakon.

    Wani misali na irin waɗannan ayyuka shi ne, wani tsari na juya kuɗaɗen taimakon da aka tara a cikin gidauniyar, ta hanyoyi masu sauƙin asara; idan ƙarshen shekara ta yi, sai a buga Alƙur’anai a raba da sunan wanda ya zuba jarin don yin haka kowacce shekara.

    Gidauniyar mai Martaba Muhammad Rashid Al Makhtum.

    Wanda ya kafa wannan cibiya shi ne sarkin Dubai wanda sunansa ne take ɗauke da shi. Manufar wannan cibiya shi ne, bunƙasa fannonin ilmi na Musulunci da fannonin ilmin kimiyya da fasaha; ta hanyar bayar da tallafi ga ‘ya’yan talakawa ‘yan baiwa, don su sami ilmi da horo a waɗannan fannoni. Wani abu da zai ba mai karatu sha’awa dangane da wannan gidauniya shi ne, irin maƙudan kuɗaɗe da ake ware mata; waɗanda sun kai dubunnan miliyoyi a kowacce shekara.

    Hubusin al Rajhi ɗan ƙasar Saudıyya, a inda kafin rasuwarsa ya yi wasicin dukkan dukiyarsa, a matsayin waƙafi ga talakawa da ayyukan alheri, bayan fitar da haƙƙin magada. Ubangiji Maɗaukaki kaɗai ne Ya san adadin talakawan dake rayuwa da iyalinsu cikin wannan dukiya mai albarka.

    Waƙaful Umm:

    Wannan wani sabon tsarin waƙafi ne na zamani kamar Annur na Malaysia. Da farko akan shata wata kadara mai nauyi, sannan a kasa ƙimarta zuwa ƙananan kaso na mai ƙaramin ƙarfi; don ‘ya’ya masu albarka su saya wa mahaifansu rayayyu ko marigaya. Jimillar kuɗin ita ce za a sai waccan kadara a bayar da hayar ta ga kamfanonin kasuwanci. Ribar ita za ake aiwatar da ayyukan alheri da ita. A halin yanzu wannan tsari na gudana a wasu daga ƙasashen Larabawa; Don ƙarin haske sai a duba littafinmu Jagorar ayyukan Cigaban Al’umma Mai Ɗorewa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfani Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmowar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.