Tag: Ibada

  • Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam)

    Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam)

    Azumin Annabi Dawud (Alaihis salam) shi ne, yau a yi, gobe a huta. Iya tsawon rayuwar mutum.

    Falalarsa.

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Sallar da Allah ya fi so,, ita ce sallar Annabi Dawud (Alaihis salam) Kuma azumin da Allah ya fi so, shi ne azumin Annabi Dawuud (Alaihis salam)”

    (Bukhari 1976. Muslim 1159).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Raya Daren Lailatul Ƙadari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Raya Daren Lailatul Ƙadari danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Falalar Dasa Bishiya danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

    Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

    Zahabaz zama’u wabtallatil uruƙu, wa sabatal ajru in sha’allaahu”.

    {Ƙishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah ya so}.

    Abdullah bin Amr bin Al- As ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “Mai azumi yana da addu’a da ba a mayar da ita idan ya zo buɗe baki”. Abdullahi bin Amr ya kasance idan ya zo buɗa baki sai ya ce:

    Allaahumma innii as’aluka bi rahmatikal latii wasi’atu kulla shai’in an tagfiralii“.

    {Ya Allah! Ina roƙon ka saboda rahamarka da ta yalwaci komai, ka gafarta mini}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Gaggauta Buɗa Baki danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Shugaban Istigfari

    Shugaban Istigfari

    An karɓo daga Shaddad Ɗan Aus (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: shugaban Istigfari shi ne ka ce :

    Allahumma anta Rabbi, laa ilaha illa anta, khalaƙatani, wa ana abduka; wa ana ala ahdika, wawa’adika mastaɗ’atu, abu’u laka, bini’imatika alayya; wa abu’u laka, bi zanbi fagfir lii, fa innahu laa yagfiruz zunuba illa anta”

    Ya ce: wanda ya faɗi wannan da safe yana mai cikakken imani sai ya mutu a wannan yinin kafin yamma; to shi ɗan Aljanna ne, idan da daddare ne yana mai cikakken imani, sai ya mutum kafin safiya; to shi ɗan Aljanna ne” (Bukhari 6306).

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Haƙiƙa ni kaina ina yin istigfari ina tuba fiye da sau saba’in a yini ɗaya”. (Bukhari 6307, 3259).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Salati Ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Bayan Tahiyya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Ramuwar Azumin Ramadan

    Ramuwar Azumin Ramadan

    Ramuwar Azumin Ramadan – Dukkanin wanda Azumin watan Ramadana ya kubce masa bisa dalilai na Shari’a, ramuwa ta wajaba a kansa. Game da ramuwar kuwa, ga yadda abin yake:

    1. Ka sani ɗan’uwana, ramuwar azumin da ya kubce na Ramadan ba wajibi ba ne ramawa nan take, babu laifi a jinkirta; saboda abin da ya zo daga Nana A’isha (Radiyallahu Anha) cewa: “Yana kasancewa akwai ramuwar azumin Ramadan a kaina, ba na samun damar ramawa sai a watan Sha’aban”. (Bukhari 4/166, Muslim 1146).

    Alhafiz Ibn Hajar yana cewa: “A cikin wannan hadisi akwai dalili a kan halaccin jinkirta ramuwar azumin Ramadan kai tsaye ko da uzuri ko babu”.

    Abu ne sananne, babu shakka a kai cewa ramawa take ya fi ramawa da jinkiri, saboda shigar hakan ƙarƙashin ayoyin da suke nuna gaggawa zuwa ga ayyukan alheri da rashin nawa wajen gabatar da su. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: “Ku yi gaggawa zuwa ga gafarar Ubangijinku”. (Aali Imram 133). Da fadin sa: “Waɗannan su ne masu gaggawa cikin alherai kuma masu rige-rige”. (Mu’uminun: 61).

    Ba wajibi ba ne a yi ramuwa a jere, saboda Allah ya ce: “A yi ramuwa cikin wasu kwanaki daban”. Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Babu laifi idan an rarraba”. Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Ya dinga yin sa mara idan ya ga dama”.

    2. Malamai sun yi ijma’i kan cewa wanda ya mutu ana bin sa salloli; waliyyinsa ba zai rama masa ba, haka ma waninsa. Haka ma wanda ya kasa azumi babu wanda zai yi masa; matuƙar yana raye sai ya ciyar kowacce rana miskini ɗaya kamar yadda Anas Bin Malik (Radiyallahu Anhu) ya aikata. Sai dai wanda ya mutu ana bin sa azumin bakance; to waliyyinsa zai rama masa dalilin faɗin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) inda ya ce; “Wanda ya mutu ana bin sa azumi, to waliyyinsa ya yi masa”. (Bukhari 4/168, Muslim 1147).

    Bukhari da Muslim sun fitar da wani hadisi daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) cewa; wani mutum ya zo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ya Manzon Allah, Mahaifiyata ta rasu alhali ana bin ta bashin azumin wata guda, zan iya rama mata? Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Eh, bashin Allah shi ya fi cancanta da a biya”.

    Waɗannan hadisan gamammu ne a zahiri wajen halaccin waliyyi ya yi wa mamaci azumi gaba ɗayan nau’o’in azumin; kuma da wannan wasu malamai cikin Shafi’iyya da Ibn Hazm suka yi fatawa. Sai dai waɗannan hadisan za su iya shiga gamammen da ake keɓancewa; saboda waliyyi ba zai yi wa mamaci azumi ba sai na bakance. Da wannan Imam Ahmad Ibn Hambal ya ce; “Ba za a iya wa mamaci azumi ba sai na bakance”. Sai na ce masa; “To ya ya azumin Ramadan? Sai ya ce; “Sai ya ciyar kawai”. (Masa’il na Abu Dawud 96).

    Aiki da wannan fatawa shi ne daidai, kuma a nan dalili ke rinjaya; saboda cikinta akwai amfani da gaba ɗaya hadisan da suka zo ba tare da an ki karɓar ko ɗaya daga cikinsu ba, tare da fahimta ingantacciya, musamman hadisin farko; Nana A’isha (Radiyallahu Anha) ba ta fahimci cewa wannan izlaƙin ya game azumin Ramadan da waninsa ba, ita dai ta tafi kan cewa za a ciyar ne. Domin ita ce ta rawaito shi saboda abin da Amrata ta rawaito cewa; “Mahaifiyata ta rasu kuma ana bin ta azumin Ramadan, zan iya rama mata? Sai Nana A’isha ta ce; “A’a, kawai ki yi sadaka muhallin kowanne yini rabin sa’i ga kowane miskini”. (Mushkili Aathar na Zahawiy 3/142).

    Abdullahi Ibn Abbas shi ya rarrabe tsakanin azumin bakance da na Ramadan, domin yana ganin idan na bakance ne; za a rama, amma idan na Ramadan ne ciyarwa ta wadatar, kamar yadda ya ce; “Idan mutum ya yi rahin lafiya a watan Ramadan; sannan ya mutu ba tare da ya yi azumi ba, sai a ciyar masa ba sai an rama masa ba”. Amma idan bakance ne sai a rama masa.

    Abu ne a zahiri cewa Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu); shi ne ya rawaito hadisin da ya gabata, musamman ma kuma ya rawaito wani hadisi wanda a cikinsa akwai nassin cewa waliyyi ya yi wa mamaci azumin bakance, ya ce; “Sa’ad Bn Ubadata (Radiyallahu Anhu) ya tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) cewa: “Mahaifiyata ta rasu ana bin ta azumin bakance? Sai ya ce: “Ka rama mata shi”. (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).

    Wannan rarrabawar shi ne ya fi dacewa da ƙa’idojin shari’a da asalanta kamar yadda Babban Malami Ibn Ƙayyim ya bayyana cikin littafinsa “I’ilaamul Mauƙi’eena”; sannan ya ƙara bayani sosai a cikin littafinsa “Tahzeebi Sunani Abee Daawud”, mujalladi na 3, shafi na 279 – 282.

    3. Sannan wanda ya mutu ana bin sa bashin azumin bakance; to ya halasta mutane adadin kwanakin da ake bin sa su yi masa azumin. Hasanul Basri ya ce; “Idan mutane talatin suka yi wa mutum, kowane mutum ya yi na kwana ɗaya, ya isar masa”. Amma ciyarwa idan waliyyinsa ya tattara miskinai adadin kwanakin da ake bin sa ya ciyar da su ya halasta. Haka Anas Bn Malaik (Radiyallahu Anhu) ya aikata. Wallahu a’alam.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kaffarar Azumin Ramadan danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ƙara Yawaita Ibadu Da Alhairi A Goman Ƙarshe Na Ramadan danna nan.

    Wannan bayanin anciro shine daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Ake Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Bayan Tahiyya

    Yadda Ake Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Bayan Tahiyya

    “Allaahumma salli alaa Muhammadin wa alaa aali Muhammadin; kamaa sallaita alaa Ibrahima innaka hamiidun majiidun; Allaahumma baarik alaa Muhammadin wa alaa Muhammadin; kamaa baarakta alaa Ibrahima wa alaa aali Ibrahima innaka hamidun majiidun”.

    {Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga Ibrahimu da alayen Ibrahimu; lallai kai abin godewa ne, mai girma. Ya Allah! Ka yi albarka ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu; da alayen Ibrahimu, lallai kai abin godewa ne, Mai girma}.

    Allaahumma salli alaa Muhammadin wa alaa azwaajihi wa zurriyyatihi kamaa sallaita alaa aali Ibrahima. Wa baarik alaa Muhammadin wa alaa azwaajihi wa zuriyyatihi kamaa baarakta alaa aali Ibrahima, innaka hamiidun majiidun”.

    {Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa; kamar yadda ka yi salati ga alayen Ibrahim, kuma ka yi albarka ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa; kamar yadda ka yi albarka ga alayen Ibrahimu, lallai kai abin godewa ne,mai girma}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tahiyya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Tahiyyatul Masjid danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal (Sitta Shawwal)

    Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal (Sitta Shawwal)

    Watan Shawwal shi ne watan Karamar Sallah. Ana so mutum ya yi azumi shida (6) a cikinsa.

    Shi wannan azumi ana iya yinsa a jere, ana kuma iya rarraba shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Azumin Ranar Arfa

    Azumin Ranar Arfa

    Ranar Arfa ita ce ranar tara ga watan Zul- Hajji, rana ce mai cike da darajoji, ana son yin azumi da yawaita ibada a wannan rana. Sai dai an hana yin wannan azumin ga wanda yake aikin Hajji.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Azumin Ranar Arfa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Kwanaki Shida A Watan Shawwal (Sitta Shawwal) danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Kar Harshe Ya Gushe Ba Tare Da Ambaton Ubangiji Maɗaukaki Ba.

    Kar Harshe Ya Gushe Ba Tare Da Ambaton Ubangiji Maɗaukaki Ba.

    Ambaton Allah

    Kada Harshe Ya Gushe Ba Tare Da Ambaton Ubangiji Maɗaukaki Ba,domin ambaton Allah yana da muhimmanci ga duniya da kuma lahirar ɗan-Adam.

    An karɓo hadisi daga Abdullahi bn Busrin cewa, wani mutum ya ce “Ya Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) sharuɗan Musulunci sun yawaita daga gare ni don haka ka ba ni labarin wani abu da zan yi riƙo da shi”. Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) ya ce, “Kar harshenka ya gushe ɗanye daga ambaton Allah (Subahanuhu wata ala)”.
    Babbar hanyar ribatar lokutan rayuwa ita ce, lazimtar ambaton Ubangiji.

    Ambaton Ubangiji Kuwa ,ya ƙunshi karatun Alkur’ani da hailala da tasbihi da salatin Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) da yawan istigifari a aji ko a ma’aikata ko a kwance ko a tafe.
    Na tabbata da ma’aikaci ko ɗan makaranta ko ɗan kasuwar da ma’aikatarsa ko makarantarsa ko kasuwarsa ke nisan mita (meter) dubu (1000) ko mita ɗari biyar (500), zai lazimta wa kansa wani zikiri tun daga fitowar sa daga gida, har ya kai inda za shi, to ba shakka zai iya samun adadi mai yawa na ladan zikiri, wanda mutane da yawa ba za su iya riskarsa a wata guda ba.

    Babu shakka, Ubangiji Maɗaukaki na kwaɗaitar da mu yawan ambatonsa a zaune ko a kwance, ta yadda ɗan-Adam zai ci moriyar rayuwarsa. Ubangiji Maɗaukaki ya siffanta masu hankali cikin Alkur’ani da cewa su ne, “Waɗanda ke ambaton Allah (Maɗaukaki) a halin suna tsaye ko suna zaune ko kuma (kwance) bisa kuyabunsu”. Sura-Al’Imra aya ta 191

    Ambaton Ubangiji mafi tsari shi ne wadda ake halarto da girmansa tare da jin tsoronsa cikin gaɓɓai da zuciya tamkar ana ganin sa.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ɗabi’ar lokaci saurin wucewa danna wannan koren rubutun.

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna Nan 

  • Falalar Salati Ga Manzon Allah (S.A.W)

    Falalar Salati Ga Manzon Allah (S.A.W)

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Mas’ud (RA) haƙiƙa Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “Haƙiƙa mutane da za su fi kusanci da ni rana alƙiyama su ne, waɗanda suka fi yawaita salati a gare ni” (Tirmizi 446).

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Malik (RA) ya ce: Manzon Allah (S. A. W.) ya ce: “Wanda ya yi min salati guda ɗaya, Allah zai yi masa salati goma, kuma za a kankare masa zunubi goma, kuma za a ɗaga darajojinsa” (Nisa’I 1280).

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Amr Ibnul As (RA) haƙiƙa ya ji Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: “Idan kuka ji mai kiran salla, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, sabo da duk wanda ya yi min salati ɗaya, Allah zai yi masa goma, sannan ku roƙa min Allah ya ba ni matsayin wasila, saboda wasila wani matsayin ne da mutum ɗaya ne kaɗai a cikin bayin Allah zai cancance shi, ina fatan na kasance ni ne wannan bawan, Kuma duk wanda ya roƙa min wasila, cetona ya tabbata a gare shi” (Muslim 577).

    Falala da fa’idodin salati ga Annabi (S.A.W.) suna da yawan gaske, yana haskaka zuciya da da kaifafa ƙwaƙwalwa, yana sanya a gafarta zunuban mutum, addu’ar da ake fara da shi karɓaɓɓiya ce, yana yaye baƙin ciki da ɓacin rai da suran fa’idoji masu yawa.
    Haka kuma akwai wurare da ake son a yi wa Annabi (S.A.W.) salati kamar a ƙarshen kiran salla da tahiyar farko da ta biyu, a lokacin addu’a da duk lokacin da aka ambaci sunansa da sauransu.

    Faɗakarwa

    Ya kamata ‘yan uwa mu sai cewa babu wani salati mai falala da daraja in ba salatin da ya fito daga bakin fiyayyen haitta ba (S. A. W.) a ingantattun hadisansa. Saboda haka, mu riƙi irin waɗanna salalatai mu bar kame-kame.

    Sigogin salati da suke da inganci da Manzon Allah (S.A.W.) za su kai goma sha bakwai, sai a tuntuɓi malaman sunna domin ƙarin bayani. Allah ya sa mu dace.

  • Yadda Za A Ci Jarrabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauƙi

    Yadda Za A Ci Jarrabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauƙi

    A duk lokacin da ka samu kanka cikin wani hali na matsi a rayuwa, to ka tuna daman can Allah yana jarrabar bayinsa da masifu daban-daban.

    Allah Ya ce:

    “Wallahi sai mun jarraba ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da tawayar dukiya, da asarar rayuka da na kayan marmari, kuma albishir ga masu haƙuri”.
    (Baqara:115).

    Ka ga tunda mun fahimci kowane irin tsanani daga Allah ne; To, ka ga mun san babu mai yaye mana, sai Allah Maɗaukakin Sarki.

    Mene ne abin yi kenan?

    Abin yi shi ne mu rungumi wannan ƙaddara, da yin haƙuri, da koyi da yadda Annabi (S.A.W) ya ce mu yi.

    Jarrabawa na iya zama mabambanta a tsakaninmu. Wani rashin iyaye, wani cuta, wani talauci, wani rashin ‘ya’ya da dai sauransu.

    Wani lokacin kuma, ya zama Annoba ce da Allah ya jarrabi dukkanin al’umma. Wato kamar ciwon sarƙewar numfashi (Corona).

    Shi Musulmi duk abin da ya same shi na sharri da wahala ba za ka same shi yana raki ba. Kuma yai ta mita ko laƙanawa wani shi ya ja masa. Koda yake rauni irin na ɗan Adam ba a hana mutum baƙin ciki ba. Amma dai zai zama mai dogaro ga Allah.

    Matakan cin jarrabawar bala’in da yayi tsanani

    • Mu ƙasƙantar da kawunanmu. Mu tuba, mu yi nadama. Mu yawaita istigfari.
    • Mu yawaita karatun Ƙur’ani.
    • Mu bincika tsakaninmu da iyayenmu mu gyara. Mu dinga kyautata musu.
    • Ma’aurata su gyara tsakaninsu.
    • Mu yawaita sadaka.
    • Mu yawaita addu’a Allah Ya yaye mana. Ya kawo mana mafita.
    • Mu yawaita: Hasbunallahu wa ni’imal wakeel.
      Lahaula wala quwwata illa billah.
      La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimn.

    A ƙarshe mu sani, mai sauƙi ne a wajen Allah ya yaye mana kowanne irin bala’i. Saboda haka, mu gaggauta gyara tsakaninmu da Mahaliccinmu. Sannan kuma ga dukkanin jarrabawa irin ta Annoba; Mu bi shawarar malamai, da shugabanni, da ma’aikatan lafiya.

    Da bin waɗannan in sha Allahu sai ka ga mun yi nasara. Mun ci jarrabawar bala’in da ya tsananta cikin sauƙi.

    Wallahu A’alam.

    Duba Yadda Ake Tsaftace Baki