Sharuɗan Wajabcin Azumin Watan Ramadan

0
482

Azumin watan Ramadan yana sauka a kan wasu, sakamakon waɗansu dalilai da Shari’a ta aminta da su; shi ya sa wajen ci gaba da ayar da ta gabata, malamai suka bayyana ire-iren waɗannan mutane, tare da dalilan. Ci gaba da bayani, sai Allah ya ce; “Waɗansu kwanaki ne ababan ƙidayawa.

To wanda ya kasance mara lafiya a cikinku, ko a kan wata tafiya; to (idan ya sha ruwa) sai ya rama a waɗansu kwanakin na daban, har ma waɗanda za su iya yin azumin; su ba da fansa ta ciyar da abinci ga miskini guda ɗaya, to dukkan wanda ya ƙara (a kan abincin miskini), to wannan ya ƙara wa kansa alheri.

Amma ku riƙa yin azumin shi ne ya fi alheri a gare ku, in har kun kasance kuna sani”. Watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa, shiriya ce ga mutane, kuma ayoyi bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa tsakanin ƙarya da gaskiya. Don haka dukkan wanda ya halarci watan cikin ku, to ya azumce shi. Kuma wanda ya kasance marar lafiya, ko a kan tafiya, (to idan ya sha ruwa) sai ya rama a waɗansu kwanaki na daban.

Allah yana nufin sauƙi a gare ku, kuma ba ya nufin tsanani a gare ku. Don haka ku cika adadin (kwanakin Ramadan); kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da ya yi, kuma ku zamo masu godiya gare shi. Kuma idan bayina suka tambaye ka game da ni, to ni kusa nake (da su); ina amsa kiran mai kira, da zarar ya kiraye ni. To su nemi amsawata, kuma su yi imani da ni, domin su shiryu.

An halatta muku saduwa da matayenku a daren watan Azumi, su sutura ce gare ku, ku ma suturu ce a gare su. Allah ya san ku kun kasance kuna ha’intar kawunanku, sai ya dawo da ku, kuma ya yi muku afuwa. To a yanzu ɗin ku sadu da su (da daddare), kuma ku nemi abin da Allah ya rubuta muku; kuma ku ci, kuma ku sha har farin zare ya bayyana daga baƙin zare na alfijir; sannan ku cika azumi zuwa dare, kuma kar ku sadu da su alhali kuna i’itikafi a masallaci.

Waɗannan iyakoki ne na Allah, kada ku kusance su! Kamar haka ne, Allah yake bayyana ayoyinsa ga mutane; don su zamo masu taƙawa” (Bakara: 184 – 187).

Waɗannan ayoyi a dunƙule sun yi bayanin waɗanda shari’a ta dauƙe musu azumin watan Ramadan; sakamakon wasu dalilai da karɓaɓɓu ne a Shari’a da sharaɗin bayan waraka daga waɗannan al’amura; sawa’un rashin lafiyar da za ta hana yin azumin ne, ko mace mai shayarwa ko juna (kamar yadda wasu malamai irin su Ibn Taimiyya da almajiransa; Auza’i, Hasanul Basri da Ibrahimul Nakha’i suka tafi a kan su ma marasa lafiya ne), ko matafiya ne; to za su rama waɗannan azumi da suka sha bayan kwanakin azumin, ma’ana bayan Ramadan.

Sannan a cikin su, akwai bayanin waɗanda za su ciyar da miskinai abinci, sakamakon rashin lafiya; ko tsufa da mai ciki ko shayarwa bisa fatawar Abdullahi Ibn Umar, Abdullahi Ibn Abbas da Ishaq Ibn Rahawaihi; kamar yadda Sheikh Nasiruddeen Albani ya fitar a cikin littafinsa Irwa’ Alghalil 4/18 – 24).

Shahid dai, waɗannan ayoyi ƙunshe suke da cikakkun bayanai game da wajabcin azumin Ramadana; da kuma nuni a kan waɗanda azumin ya wajaba a kansu, misali dukkanin musulmi, baligi, mai hankali; kuma wanda yake da ikon yi, mazaunin gida. Sannan an bayyana matakan da aka bi wajen shar’anta shi, da kuma waɗanda azumin ya zama wajibi a kansu. Domin neman cikakken bayani, sai a tuntuɓi malamai a majalisunsu domin jin yadda abin yake.
A gefe guda kuma, akwai waɗanda azumin Ramadana ya sauka a kan su, ma’ana, su azumin Ramadana bai wajaba a kan su ba.

Cikin irin waɗannan akwai:

i. Kafiri.

ii. Yaro, amma za a iya umartar sa da yin azumin domin ya saba.

iii. Mahaukaci, wannan kuwa koda balagagge ne, domin ba ya cikin hankalinsa. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ya ce, “An ɗauke alƙalami a kan mutum uku: mai barci har sai ya farka, yaro har sai ya balaga, da mahaukaci har sai ya warke”. (Sahihul Jami’ al-Saghir (3513).

iv. Tsoho, amma zai bayar da mudun-nabi guda biyu, ko ya ciyar da miskini dafaffen abinci a madadin kowacce rana.

v. Marar lafiya, sai dai akwai ramuwa a kansa bayan ya warke, wannan kuwa ko da bayan shekara nawa ne. Amma cutar da ƙwararrun likitoci suka tabbatar ba za a warke ba, sai dai kawai a ciyar a madadin kowacce rana.

vi. Matafiyi, zai yi ramako bayan Ramadana.

vii. Mai jinin haila ko jinin biƙi, amma ita ma akwai ramuwa a kanta.

viii. Mace mai ciki ko shayarwa, ita ma za ta iya ajiye azumi idan tana tsoron cutuwarta ko cutuwar abin dake cikinta, ko abin da take shayarwa idan ta ci gaba da azumin.

An rawaito hadisi daga Anas Ibn Malik Al-Ka’abi (Radiyallahu Anhu) cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce, “Haƙiƙa Allah ya ɗauke wa matafiyi rabin sallah, kuma ya ɗauke azumi ga matafiyi da mai ciki da mai shayarwa”. (Sunan Ibn Majah, (1667).

A nan malamai suka yi bayanin cewa, idan matuƙar dai matafiyi da mara lafiya za su rama azumi, to babu abin da zai sa a ce mai ciki ba za ta rama ba.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tsayuwar Watan Ramadan danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Dake Cikin Yin Sahur danna nan.

Wannan bayanin anciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Sa Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceTsayuwar Watan Ramadan
Labarin na GabaFalalar Watan Ramadana 1