Mutuwa Da Rabon Gadon Bahaushe

1
77

Bahaushe yana kiran mutuwa da sunaye kusan 20, daga  cikin akwai rasuwa, fakuwa, ƙaura, tafiya,  rigaya/margayawa, kauwa da sauransu.

Bahaushe ya yi  imani da mutuwa, dole ce, ta sanadin tsufa, rashin lafiya,  hatsari, kisa, camfi, annoba, rantsuwa da sauransu.  Bahaushe na gane mutum ya mutu ta sanyin jiki, farin  ido, buɗewar baki, ƙafewar ido da sandarewar jiki  (Abdullahi, 2008). 

Kafin zuwan addinin Musulunci, Maguzanwan Hausawa  ba sa binne gawa sai bayan kwana 3 da mutuwa (Ibrahim  1982), a kan ɗorawa cikin mamaci dutse, ko takobi ko  wani abu mai nauyi da zai hana cikin kumbura kafin a je  a binne shi.

Domin karanta bayani akan Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe Danna nan 

Za a ɗebo ruwa ƙwarya a wanke mamaci, sai  a cika ƙwarya da hatsi da (wasu) kayan mamaci a ba wa  mai wankan gawa, dama can Bahaushe na haƙa rami ya  binne gawar mamaci, da warkinsa a gindi, za a shafa  masa shuni da nufin in ya je lahira ya ba wa mutuwa  tsoro don kar ta dawo ta ɗauki wani. 

Idan miji ya mutu, za a ba wa matar sanda tana yawo da  ita, saboda a da an yi imani da fatalwa, wai ko da zai dawo, sai ta doke shi. Za a zubar da ruwan cikin randar  gidan, a kife su, a sa wa yara toka ko baqin bayan tukunya a zagayen idonsu don zama makarin mafarki da matacce. 

Bayan binne mamaci, Bahaushe yana da tsarin zaman makoki, idan za a zo ana yi wa iyalan mamaci gaisuwar mutuwa (ta’aziyya), a wasu wuraren a kan ɗauki  kwanaki uku, wasu huɗu, wasu sati (kwana bakwai).  Bayan zuwan addini aka ce bidi’a ne, wasu suka daina,  amma har yau ana yi a wasu wuraren.

Domin karanta bayani akan Jinya Da Likitancin Bahaushe Danna nan

Ta ɓangaran gado kuwa, kafin zuwan Musulunci Bahaushe bai ba wa rabon gabo muhimmanci ba, idan ya Bahaushe ya tsufa ne, ya kan ƙoƙarin raba dukiyarsa ga  iyalansa sabo da gudun rigima, (Abdullahi, 2008), idan  kuma bai raba ba har ya rasu, akan ɗauki lokaci mai  tsayi ba a raba, wani lokacin kuma idan akwai babban ɗa  tsayayye, sai yadda ya yi da ita, babban wa uba ne. zai  raba gonaki wa maza, dabbobin kiwo kuma ga mata.

A wasu wuraren kuma, mace ba ta da gado, sai na mahaifiyyarta kawai. Musulunci ne da ya zo ya yi wa mace gata. Idan kuma ‘ya’ya ne suka rasu, za a raba  gadonsu har ga kishiyoyin gidan, da ‘ya’yansu.  Bahaushe yana alfahari da bajintar iyayensa da  kakaninsa. 

Domin karanta cikakken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceJinya Da Likitancin Bahaushe
Labarin na GabaTSUMAGIYA

SHARHI ƊAYA