Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana wata yarinya wai ita Talume sun je daji cin ɓaure ita da kawayenta da sauran ’yan matan garinsu, tare kuma da yayyensu mata. Bayan sun gama shan ɓaure, sai yayyen yaran nan suka ce da su: “Kowacce ta share hannunta, ta goge bakinta, kuma kada a ce za a ɓoye a kai gida.”
Ashe Talume ta ɓoye wani ɓauren domin ta kai wa mahaifiyarta, ga kuma danƙonsa da ta bari a hannunta ba ta share ba domin ta riƙa lasa a hanya. Suna cikin tafiya sai ta riƙa tanɗar hannunta, tana jin zaƙin ɓaure, har suka isa gida. Da ta kawo ɓauren ta ba mahaifiyarta, sai ta tambaye ta da cewa:
“Kai wannan ɓaure da zaƙi yake, a ina kika samo shi?” Sai ta ce da ita: “Ni da su yaya muka samo shi a daji.” Ana nan, ana nan, rannan Talume da ƙawayenta sun shirya za su je biki, sai ta roƙi mahaifiyarta ta ba ta aron zannuwanta ta ɗaura. Da uwar ta ji haka, sai ta ce mata: “Zan ba ki, to amma sai kin kawo mini irin ɓauren nan na kwanakin baya.”
Sai Talume ta ce: “To bari in je daji ko zan samo shi.” Ta kama hanya tana tafiya har ta kai gindin ɓaure, ta rasa yadda za ta yi. Sai ta kama waƙa, tana yi ɓaure yana mayar mata suna cewa:
Talume: “ɓaure, ɓaure ka ba ni ɓaure.”
Baure: “Yarinya, in ba ki Baure? In ba ki Baure ki kai wa wa?”
Talume: “In kai wa babata.”
Baure: “Ta ba ki me?”
Talume: “Ta ba ni kaya.”
Baure: “Ki je ina?”
Talume: “In je biki, ’Yan mata duk sun tafi, Samari duk sun tafi.”
Sai Baure ya ce mata ta iya waƙa, kuma ta je ta nemo kashin shanu ta kawo masa kafin ya ba ta ’ya’yansa. Ta kama hanya ta sami shanu suna kiwo. Kamar yadda suka yi da ɓaure, ga waƙar da ta fara suka amsa mata:
Talume: “Shanu, shanu ku ba ni kashi.”
Shanu: “Mu ba ki kashi, ki kai ina?”
Talume: “In kai wa ɓaure.”
Shanu: “Ki kai wa Baure ya ba ki me?”
Talume: “Ya ba ni ’ya’ya.”
Shanu: “Ya ba ki ’ya’ya ki kai ina?”
Talume: “In kai wa babata.”
Shanu: “Ki kai wa inna ta ba ki me?”
Talume: “Ta ba ni kaya.”
Shanu: “Ta ba ni kaya, ki je ina?”
Talume: “Ta ba ni kaya in je biki, ’Yan mata duk sun tafi, Samari duk sun tafi.”
Sai ɗaya daga cikin shanun ta ce: “Ki je ki kawo mana ciyawa mu ci, sai mu yi kashi ki kwasa.” Sai ta ce: “To.” Ta doshi inda ciyawa ta fito ta yi lif-lif, koriya shar gwanin ban sha’awa ta ce:
“Ciyawa, Ciyawa ki ba ni ciyawa.”
Ciyawa: “In ba ki ciyawa ki kai ina?”
Talume: “In kai wa shanu.”
Ciyawa: “Ki kai wa shanu su ba ki me?”
Talume: “Su ba ni kashi.”
Ciyawa: “Ki kai wa wa?”
Talume: “In kai wa Baure.”
Ciyawa: “Ki kai wa Baure ya ba ki me?”
Talume: “Ya ba ni ’ya’ya.”
Ciyawa: “Ya ba ki ’ya’ya ki kai wa wa?”
Talume: “In kai wa babata.”
Ciyawa: “Ta ba ki me?”
Talume: “Ta ba ni kaya in je biki, ’Yan mata duk sun tafi, Samari duk sun tafi.”
Sai Ciyawa ta ce: “Hanzarta ki ɗebo ruwa ki kawo. Ki zuba mini, in ya so ki yanke ni ki kai wa shanun.” Yarinya ta ce: “To, ciyawa, na gode.” Da ta isa bakin wani babban gulbi mai ruwa garai-garai, sai ta ce: “
Gulbi, Gulbi, ka ba ni ruwa.”
Gulbi: “In ba ki ruwa ki kai wa wa?”
Talume: “Ka ba ni ruwa in kai wa ciyawa.”
Gulbi: “Ta ba ki me?”
Talume: “Ta ba ni ciyawa.”
Gulbi: “Ki kai wa wa?”
Talume: “In kai wa shanu.”
Gulbi: “Su ba ki me?”
Talume: “Su ba ni kashi.”
Gulbi: “Ki kai wa wa?”
Talume: “In kai wa Baure.”
Gulbi: “Ya ba ki me?”
Talume: “Ya ba ni ’ya’ya.”
Gulbi: “Ki kai wa wa?”
Talume: “In kai wa babata.”
Gulbi: “Ta ba ki me?”
Talume: “Ta ba ni kaya.”
Gulbi: “Ki je ina?”
Talume: “In je biki, ’Yan mata duk sun tafi, Samari duk sun tafi.”
Sai Gulbi ya ce: “Kai wannan yarinya da ƙoƙari kike, zo ki ɗebi ruwan da zai kashe wa Ciyawa ƙishirwarta domin ta yarda ki yanke ta.” Yarinyar ta ɗebi ruwa mai yawa salka-salka ta je ta zuba wa Ciyawa. Ciyawa ta ƙara kyau, abin sai wanda ya gani, sai ta ce da Talume:
“Yanki yadda za ta ƙosar da shanun nan domin su yi kashi da yawa.” Sai ta yanka ta kai wa shanu, suka ci suka yi kashi mai yawa, kuma subul-subul mai kyau. Nan da nan Talume ta lafci kashin nan ta kai wa ɓaure ya yi murna da wannan kashin shanu da bai taɓa cin mai daɗi irinsa ba.
Sai shi kuma ya zubo mata da ’ya’ya masu yawa, waɗanda suka nuna lugub ta ɗiba ta kai wa mahaifiyarta,ita kuma ta yi godiya, ta kawo kayan da ta nema ta ba ta. Talume ta sa kaya, ta je wurin biki ta tarar an gama biki, amma Kuraye suna yin nasu. Da Kurayen nan suka ga Talume, sai suka yi kanta za su cinye ta, sai ta gudu, suka bi ta, har gida.
A gidansu kuma, sai ta tarar an rufe ƙofar kowane ɗaki. Sai ta doshi ƙofar ɗakin mahaifiyarta ta ce: “Iya buɗe mini ɗaki.” Sai mahaifiyarta ta ce: “Abin da ya biyo ki, ya cinye ki.” Haka ta yi ta bi ɗaki-ɗaki, ba wanda ya buɗe mata. Amma da ta je ɗakin kakarta ta buga, sai ta buɗe mata.
Da Kuraye suka ga Talume ta shiga ɗaki, sai suka haƙura saboda tsoron ko tarko aka yi musu suka gudu, ita kuma ta tsira. Washe-gari bayan kowa ya tafi gona sai Talume ta tattara kayanta, ta bar garinsu; ta je wani gari ta sami miji ta yi aure, ta ƙi zuwa ko da ganin gida shekara da shekaru. Mahaifanta sun so ganin ta, amma ta ƙi zuwa gida.
Ana nan sai mahaifan Talume suka ji labarin garin da ta yi aure, sai mahaifinta ya ce a je a gaya mata mahaifiyarta ta rasu. Aka kuwa same ta, aka gaya mata, amma ta ƙi zuwa. Bayan wasu watanni kuma ya ce a je a ce mata mahaifinta ya rasu. Aka je, aka gaya mata, amma ta ƙi zuwa.
Daga ƙarshe dai sai aka tashi wani tsuntsu Goraje aka aike shi don ya gaya mata yayyenta da ƙannenta duk sun mutu. Goraje ya tashi fir, bai tsaya ba sai a ƙofar ɗakinta ya ce:
Goraje: “Salamu alaikum Talume.”
Talume: “Wa alekumus-salam Goraje.”
Goraje: “Mahaifiyarki ta mutu Talume. Bariki ba gida ba.”
Talume: “Bariki ba gida ba, Goraje, Uwata ƙi ni, Goraje, Baba ya ƙi ni, Goraje, Yaya ta ƙi ni, Goraje, Kaka ta so ni, Bariki ba gida ba, Goraje, Ku je ku binne, Goraje.”
Sai tsuntsun ya koma ya shaida wa waɗanda suka aike shi, cewa Talume ta ƙi zuwa. Can sai wani maƙwabcin babanta da ya san tarihin abin da ya faru ranar da Kuraye suka bi ta za su kashe ta ya ce: “Idan kuna so ta zo, ku aika mata cewa kakarta ta rasu.” Jin haka ke da wuya sai aka sa tsuntsu Goraje ya je ya gaya mata kakarta ta rasu, ana can za a rufe ta.
Sai ta ce da tsuntsu: “Ga ni nan, kada a rufe ta sai na gan ta.” Talume ta shirya kayanta ta je garinsu, ta isa har gida. Sai ta tarar duk mutanen gidan ba wanda ya mutu, amma duk sun tafi gonakinsu aiki, in ban da kakar nan tata. Ta gayar da ita, suka yi hira. Jim kaɗan ta ce za ta komagarin mijinta.
Sai kakar ta ce da ita: “Kina da gaskiya, kama hanya, aure ba abin wasa ba ne.” Talume ta shirya ta ɗauki kayanta, ta kama hanya. Da iyayenta da yayyenta da ƙannenta suka dawo suka ji ta zo, amma ta ƙi jiran su, sai suka ce: “Kai wani hali sai su Talume.” Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
- Shan wahala a rayuwa ba ya hana a ƙarshe a sami kyautatawar hali.
- Motsi ya fi zama
- Mai nema yana tare da samu
- Mahaƙurci, mawadaci.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Sarki, Gizo Da Kwarkwata
Edita@rumasau-kallamu










