Tatsuniyar Ladi Da Dodo

0
1

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wata yarinya kyakkyawa tana tare da iyayenta waɗanda suke maƙwabtaka da surukan Gizo a wani ƙauye wai shi Yana. Sunan yarinyar Ladi. Wata rana sai ƙawayenta suka biya mata domin su tafi bayan gari cin kaɗanya. Da yayyenta suka ji inda za su, sai suka ce kada ta je saboda akwai wani mugun Dodo da yake kashe mazauna Yana in sun fita bayan gari.

Ladi ta ƙeƙasa ƙasa, ta kafe ita sai ta je. Sai ta sha ɗamara, ta ɗauki sanhon zuba kaɗanya, ta bi ƙawayenta, suka fita bayan gari. Ba su tsaya ba sai gindin wata babbar kaɗanya da ta yi ’ya’ya birjik, abin ban sha’awa da sa marmari. Sai ɗaya daga cikin ’yan matan nan ta ce: “Kowacce ta hau kaɗanya ta ɗebi rabonta.”

Kowacce ta hau, suna cikin kaɗar kaɗanya, sai Dodon nan ya zo gindin bishiyar ya tsuguna, ya ce: “Ku ’yan mata, ku sauko in cinye ku.” Sai ko suka fashe da kuka saboda tsoro, idanu suka raina fata, ciki ya ɗuri ruwa, kowacce sai kyarma take yi, duk sun ɗimauta. Can sai wata mai wayo daga cikinsu ta kama waƙa tana cewa:

“Dodo, Dodo,

ba ni ce Ladi ba,

Ladi fara ce, kyakkyawa,

In ta yi dariya, nono ne ke zuba,

In ta yi murmushi, madara ce ke zuba.”

Da Dodon ya ji wannan waƙa, sai ya yi wani irin gunji, ya yi miƙa da gyatsa ya ce: “Sauko ’yata ba da ke nake ba, Da Ladi nake, Zan kakkarya ta, In sha madararta da ke zuba.” Da ƙawayen Ladi suka ga yadda ɗayarsu ta ceci kanta daga sharrin Dodo da wannan waƙa, sai wata daban kuma ta ɗauka:

“Dodo, Dodo, ba ni ce Ladi ba,

Ladi fara ce, kyakkyawa.

In ta yi dariya, nono ne ke zuba,

In ta yi murmushi, madara ce ke zuba.”

Da ya ji wannan waƙar ma, sai ya mayar mata da cewa:“Sauko ’yata ba da ke nake ba, Da Ladi nake, Zan kakkarya ta, In sha madararta da ke zuba.” Sai ta sauko, ita ma ta kama hanya, ta gudu gida. Da haka da haka duk ’yan matan nan suka sauko, saura Ladi ita kaɗai ta rage a kan kaɗanya, ƙasa kuma ga Dodo yana jira ta sauko ya halaka ta.

Kamar dai dabara za ta ɓace mata, amma dai ita ma ta kama waƙa irin wadda sauran suka rera: “Dodo, Dodo, ba ni ce Ladi ba, Ladi fara ce, kyakkyawa, In ta yi dariya, nono ne yake zuba. In ta yi murmushi, madara ce ke zuba.” Sai Dodo ya ce: “Na ji ba ke ce Ladi ba, amma sauko in cinye ki, yunwa nake ji.”

Da Ladi ta ji lafazin Dodon, sai ta fashe da kuka. Tana cikin kuka sai wani tsuntsu ya sauka a kan kaɗanyar kusa da ita ya ce: “Me ya sa kike kuka?” Sai ta ba shi labarin yadda ƙawayenta suka yi suka gudu, amma Dodo ya ce sai ya cinye ta. Da tsuntsu ya ji halin da Ladi take ciki sai ya ce: “To, ina dabara?”

Sai Ladi ta yi masa kwatancen gidansu domin ya je ya gaya wa mahaifanta. Tsuntsu ko ya je ya gaya musu. Iyayen ko ba su ɓata lokaci ba, suka yi gayyar jama’a don a je a ceto ta. Da yake suna da farin jini a garin, nan da nan majiya ƙarfi suka ɗebo makamansu, aka zo inda Dodo yake aka yi sukuwar salla a kansa aka yi kaca-kaca da shi.

Ladi ta sauko, sai gida tare da jama’ar gari. Daga wannan rana Ladi ta daina zuwa ko da ƙofar gida, sai da yardar iyayenta ko yayyenta. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Rashin bin maganar magabata yana sa a faɗa cikin hatsari.
  • Zaman lafiya da jama’a yana kawo samun taimakon gaggawa a lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Talume

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Talume
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.