Falalar Ƙulhuwallahu Ahad

0
567

Falalar Ƙulhuwallahu Ahad – An karɓo hadisi daga Abu Sa’idil Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce: Ɗan ‘uwana Ƙatada ɗan Nu’uman ya ce:

Haƙiƙa wani mutum ya yi tsayuwar dare a lokacin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya yi ta karanta ƙulhuwallahu Ahad (Bayan Fatiha), bai ƙara wata sura ba.

Da gari ya waye sai ya zo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ambata masa tsayuwar daren da ya yi da ƙulhuwallahu Ahad, yana ganin kamar surar ta yi kaɗan. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunsa tabbas tana daidai da ɗaya bisa uku (1/3) na Alƙaur’ani”. (Wato wajen samun lada). Bukhari ne ya rawaito shi.

Kuma an Karɓo daga Anas ɗan Malik, Allah ya yarda da shi ya ce; Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ina matuƙar son wannan sura: “Ƙulhuwallahu Ahad”. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Son da kake yi mata ya shigar da kai Aljanna”. Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi.

Sannan an karɓo wani hadisin daga Buraida ɗan Husayyib Allah ya yarda da shi ya ce; “Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa:

“Ya Allah ina roƙon ka, ina mai tabbatar da na shaida tabbas kai kaɗai ne abin bauta; babu wani abin bautawa bisa cancanta (na gaskiya) sai kai kaɗai; ɗayan da ake nufa da buƙata, wanda bai haifa ba; kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani wanda ya yi daidai da shi”.

Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Tabbas ka roƙi Allah da sunansa wanda in har aka roƙe shi, to zai bayar da abin da aka roƙa; kuma idan aka kira shi da shi, to zai amsa”. Imam Ahmad, Abu Dawud, Tirmizi da wasunsu ne suka rawaito shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad danna nan

Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Surah A Cikin Sallah danna nan

labarin da ya wuceSahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad
Labarin na GabaHaƙƙoƙin Shugabanni A Kan Mabiyansu