Tag: Falalar Sallar

  • Falalar Suratul Baƙara

    Falalar Suratul Baƙara

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “kada ku mayar da gidajenku kamar maƙabarta; Haƙiƙa Shaiɗan yana gudu daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara a cikinsa”. (Muslim 708).

    An karɓo daga Abu Umamah (Radiyallahu Anhu) haƙiƙa ya ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yana cewa; “ku riƙa karanta suratul Baƙara saboda riƙo da ita albarka ne, barinta nadama ne; kuma matsafa ba sa iyawa da ita”. (Muslim 804).

    Wato karanta suratul baraƙa yana maganin sihiri da tsafi da kuma sharrin shaiɗanu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Falalar Karanta Ayatul Kursiyyi Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Wajibcin Karatun Fatiha A Cikin Sallah danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Ƙulhuwallahu Ahad

    Falalar Ƙulhuwallahu Ahad

    Falalar Ƙulhuwallahu Ahad – An karɓo hadisi daga Abu Sa’idil Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce: Ɗan ‘uwana Ƙatada ɗan Nu’uman ya ce:

    Haƙiƙa wani mutum ya yi tsayuwar dare a lokacin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya yi ta karanta ƙulhuwallahu Ahad (Bayan Fatiha), bai ƙara wata sura ba.

    Da gari ya waye sai ya zo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ambata masa tsayuwar daren da ya yi da ƙulhuwallahu Ahad, yana ganin kamar surar ta yi kaɗan. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunsa tabbas tana daidai da ɗaya bisa uku (1/3) na Alƙaur’ani”. (Wato wajen samun lada). Bukhari ne ya rawaito shi.

    Kuma an Karɓo daga Anas ɗan Malik, Allah ya yarda da shi ya ce; Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ina matuƙar son wannan sura: “Ƙulhuwallahu Ahad”. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Son da kake yi mata ya shigar da kai Aljanna”. Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi.

    Sannan an karɓo wani hadisin daga Buraida ɗan Husayyib Allah ya yarda da shi ya ce; “Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa:

    “Ya Allah ina roƙon ka, ina mai tabbatar da na shaida tabbas kai kaɗai ne abin bauta; babu wani abin bautawa bisa cancanta (na gaskiya) sai kai kaɗai; ɗayan da ake nufa da buƙata, wanda bai haifa ba; kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani wanda ya yi daidai da shi”.

    Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Tabbas ka roƙi Allah da sunansa wanda in har aka roƙe shi, to zai bayar da abin da aka roƙa; kuma idan aka kira shi da shi, to zai amsa”. Imam Ahmad, Abu Dawud, Tirmizi da wasunsu ne suka rawaito shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Surah A Cikin Sallah danna nan

  • Falalar Tafiya Masallaci

    Falalar Tafiya Masallaci

    Tafiya masallaci domin yin ɗaya daga cikin salloli biyar bayan alwala. A lokacin da mutum ya ƙare alwala, idan namiji ne, duk takun da zai yi ko ɗaga ƙafa yayin tafiyar; sai an ɗaga darajarsa, an yafe masa zunubansa; haka ma kuma mace lokacin da take tafiya wajen da za ta yi sallah, ita nan ne masallacinta.

    Ana so mutum ya yi tafiya cikin nutsuwa domin tara lada mai yawa. Isowar sa masallaci ko kuma isowar ta wajen da take yin sallah, idan da dama, ana so a yi nafila raka’a 2 kafin sallar farilla.

    Ga sunayen nafilfilin salloli biyar da yadda ake gabatar da su.

    Ana kiran su da Larabci (Assunanur rawaatibi, Assunanun attabi’atu lil fara’idi). Ma’anar su a harshen Hausa ita ce, jerarrun sunnoni.

    Idan da Asuba ne ana yin raka’a biyu, wacce ake kiranta da Larabci (raka’ataanil fajri) ma’ana raka’a biyu lokacin fitowar alfijir, in Azahar ne ana yin raka’a biyu ko huɗu kafin sallar Azahar, sannan kuma raka’a biyu bayan sallar azahar.

    Idan da La’asar ne kuma raka’a biyu kafin sallar La’asar; in Magriba ce raka’a biyu bayan sallar Magriba, da isha’i kuma raka’a biyu bayan sallar Isha’i.

    Shi ne yawan su ya kai raka’a 14 idan mutum ya yi huɗu kafin Azahar, idan kuma biyu ya yi, sun tashi raka’a 12 kenan.

    Idan mutum ya yi sallama, yana zaune inda yake bayan nafila kafin sallar farilla; mala’iku za su dinga masa addu’a suna cewa Allah ya masa rahama; ya masa gafara, ya yi sallah masa afuwa matsawar bai yi hadasi ba kuma bai cuci wani a lokacin;wannan falalar duk ɗaya ne ga mace ko na miji.

    Domin karanta bayani a kan Fa’idojin Da Sallar Nafila Ta Ƙunsa danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Sallar Tahajjudi danna nan

  • Falalar Sallar Tahajjudi

    Falalar Sallar Tahajjudi

    1) Allah Ta’ala ya ce: “Kuma bayin Allah su ne waɗanda suke tafiya cikin nutsuwa a bayan ƙasa, in wawaye sun yi musu magana sai su ce, “Aminci ya tabbata a gare ku”. (Wato Allah ya ba ku haƙuri). Su ne waɗanda suke kwana suna sujjada suke tsayawa ga Ubangijinsu” (Suratul Furƙan: 63 – 64).

    2) Allaha (Subahanahu wata’ala) ya ce: “Haƙiƙa masu tsoron Allah suna cikin Aljannata da ƙoramu. Suna masu karɓar abin da Ubangijinsu ya ba su, haƙiƙa sun kansance masu kyautatawa kafin wannan. Sun kansance suna yin barci kaɗan a cikin dare, kuma a lokacin sahur suna istigfari”.

    3) Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam)ya ce: “Ya ku mutane, ku yaɗa Sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku rinƙa sallah da daddare a lokacin da mutane suke barci; za ku shiga Aljanna cikin aminci”. (Tirmizi 1855, Ibn Majah 1334 Ahmad 751).

    Ana iya yin ƙiyamul laili a farkon dare ko a tsakiyar dare ko a ƙarshen dare; ƙarshin daren shi ne mafificin lokaci.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Adadin Raka’o’in Sallar Asham danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.