Ba Kowane Ciwon Ƙirji Bane Ulcer

0
24

Mutanen mu sun lamincewa kansu cewa; duk ciwon kirji kurum ulcer ce,shi yasa ciwon zuciya ya aika mutane da yawa lahira ta farat ɗaya… da sunan ulcer, domin ba’a son zuwa asibiti ai gwaje-gwajen da suka dace, asalin uwar hanji bama a kirji take ba,saide eh munji ana iya jin ciwon kirji sanadiyyar refer pain amma ba dole ulcer ba ko yaushe. 

Shifa gwajin nan baka da buƙatar sai likita yace ma gashi yi kaza… A’ah inkaga baida niyyar baka matuƙar da hali roƙa zakai kace kana so ya baka gwaji iri kaza kayo don kurum ka ƙara sanin matsayin ka.

Ciwon kirji abin tsoro ne musamman in mutum nada hawan jini,matsalar zuciya,ballantana wasu sun gado matsalar da basusan suna da ita ba a family,haka wasu suna da matsalolin hawan jini amma basu sani ba,gani suke ciwo kaza sai a tsoffi ko masu aure,wa ya gayama haka? 

Idan kunaso ku karanta Bayani Akan Gyambon Baki {Canker Sore} Danna nan

Saidai ina! Duk maimakon haka kun gwammace zama kuyita ɗibar maganin ulcer har sai yakai ga fara saku gudawa,gashi fa saboda wauta ana jin ana shan maganin amma ba canji, kuma koda anji relief zai dawo,amma mutum ya share duwawu ya zauna,ulcer dinnan fa ana warketa…. 

Ya kamata Musani duniya ta wuce wannan zamanin, indai ka iya neman kudi Toh dole kuma ka koyi neman lafiya tare da tattalin ta,dole ne kaiwa rashin lafiya tanadi tun kan tazo. 

A yanzu dai baka da buƙatar sai kaji ciwo sannan kaje asibiti,masu dabara duk shekara sukan je sau 1 su nemi a basu mahimman gwaji da suka dace da masu shekaru irin nasu saboda in ma jikin su ta fara shiga wani lokon to ai ƙoƙarin tsamo shi.

Domin karanta bayani akan Samiha-Borin Jini {Hives,Urticaria,Neetle Rash} Danna nan

labarin da ya wuceSamiha-Borin Jini {Hives,Urticaria,Neetle Rash}
Labarin na GabaSanƙaran Nono Wato {Breast Cancer}