Abubuwan Da Suke Ɓata Azumi

0
408

Akwai abubuwan da suke ɓata azumi matuƙar mutum ya aikata su; to azuminsa ya lalace, cikin waɗannan abubuwa, akwai:

1. Ci ko sha da gangan, idan mai azumi ya ci abinci ko ya sha wani abin sha da gangan, to ya sani azuminsa ya lalace.

2. Jawo amai da gangan, wanda ya janyo amai da gangan shi ma azuminsa ya lalace. Domin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ambata cikin hadisi cewa, “………… amma wanda ya jawo amai da gangan, to ya yi ramuwa”. (Abu Dawud 2/310, Tirmizi 3/79).

3. Haila ko nifasi, idan mace ta yi jinin haila ko nifasi cikin wani yanki na yini sawa’un farko ne ko ƙarshe, to azuminta ya warware kuma ramuwa na kanta, idan kuma ta ƙarasa, to bai halatta ba, kuma ba ta da lada. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam ya faɗa cikin hadisai da suka zo daga Ibn Umar da Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa, “Ashe ba idan mace ta yi haila ba ta sallah, ba ta azumi ba? Suka ce “Haka ne”. Sai ya ce, “Wannan shi ne naƙasu a cikin addininta”. A wata ruwayar ya ce, “Tana zaman kwanaki ba ta sallah, tana shan azumi a Ramadan, to wannan shi ne naƙasu a cikin addininta”. (Muslim 79 – 80).

Game da umarnin ramuwa kuwa, ya zo cikin hadisin Mu’azat da take cewa; “Na tambayi Nana A’isha na ce mata: “Me ya sa mai haila take rama azumi amma ba ta rama sallah?” Sai ta ce; “Baharuriya ce ke?” Sai na ce “A’a, ni dai ina tambaya ne”. Sai ta ce: “Ya kasance hakan yana samun mu, sai a umarce mu da rama azumi, amma ba a umartar mu da rama sallah”. (Bukhari 4/429, Muslim 335).

4. Allurar ƙoshi, shi ne shigar da wasu sinadarai masu ƙosar da mutum cikin uwar hanji da nufin ƙosar da maras lafiya, to wannan yana karya azumi, saboda yana shiga ciki ne. Haka zalika idan uwar jini take bi, to ita ma tana karya azumi muddin tana zuwa ne a madadin abinci ko abin sha.

5. Jima’i, Imam Asshaukani ya ce: “Jima’i babu saɓani kan cewa yana lalata azumi idan ya faru bisa mantuwa, to wasu daga cikin malamai sun haɗa shi da wanda ya ci ko ya sha alhalin ya manta”. Ibnul Ƙayyim ya ce; “Alƙur’ani ya yi nuni cewa jima’i yana karya azumi, kamar ci da sha babu sabani kan hakan”.

Hadisi ya tabbata daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) cewa; wani mutim ya zo gun Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; “Ya Manzon Allah na halaka! Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce masa; “Me ya halakar da kai?”

Sai mutumin ya ce; “Na sadu da matata cikin Ramadan!” Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce masa; “Za ka iya azumin wata biyu a jere?” Sai ya ce: “A’a”. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce masa; “Za ka iya ciyar da miskinai sittin?”. Sai ya ce “A’a”. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce masa “Zauna”.

Sannan ya zauna; zuwa wani lokaci sai aka zo wa da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) da dabino, sai ya ce; “To ga shi nan, ɗauki ka yi sadaka da shi”. Sai mutumin ya ce; “A tsakanin unguwannin Madina kaf, ba wanda ya kai mu buƙata”. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya yi murmushi har haƙoransa suka bayyana; sannan ya ce masa “Ɗauki ka ciyar da iyalanka”.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ba Sa Ɓata Azumi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Laccocin Ramadan Na Mumbarin Jawabi Daga Malamai danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Guziri Ga Mai Azumin Ramadana (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah); wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi; Don karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceShin Idan Hakan Ya Halatta, Mene ne Sakamakon Kallon Takardar Alƙur’anin?
Labarin na GabaYadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi