Sallar Tahiyyatul Masjid

0
809

Duk mutumin da ya shiga masallaci, ana so ya yi salla raka’a biyu kafin ya zauna, in ya manta ya zauna, sai ya tashi ya yi in ya tuna.

Saboda umarnin da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi kan yin wannan salla. Waɗansu malamai suka ce wajibi ce ba mustahabi ba, kuma ana iya yin ta ko da a lokacin da aka hana sallar nafila ne.
Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: “Idan ɗayanku ya shiga masallaci kada ya zauna har sai ya yi salla raka’a biyu” (Bukhari 444, muslim 714).

Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Alwala Da Falalar sa danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Sallatut Tasbihi
Labarin na GabaSallar Alwala Da Falalarta