Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani Kare da wata Kura a Dajin Saidawa. Suna ganin juna amma daga nesa, har dai yau da gobe suka saba, sai suka ƙulla abota. Kare yana da ’ya’ya bakwai, Kura kuma tana da’ya’ya biyar. Sai wata rana suka ce za su je daji dakan wake. Sai suka shirya suka fita.
Suka yi ta tafiya har suka isa wurin dakan wake, suka kama aiki. Can sai Kare ya ce wa Kura: “Gara ki jeki ɗora mana sanwar kalaci. Ina ganin wake da shinkafa ya kamata ki
dafa. ”Kura na jin haka ta ce: “Gaskiyarka, Kare.” Kura ta je ta kama ’ya’yan Kare, ta zuba su a tukunya, ta ɗora sanwa.
Daga nan ta koma wurin aiki. Da Kare ya ga ta koma, sai ya tambaye ta: “Kin ɗora sanwa ne?” Kura ta ce masa: “E, na ɗora. Ai yau fa za mu ci daɗi.” Daga nan sai
Kura ta kama waƙa tana cewa:
“Mu yi daka da wuri mu tafi,
’Ya’yan Kare suna shan wuta,
Hum tiri hum.”
Da Kare ya ji abin da take cewa, sai ya ce: “Kura bari inje in duba mana sanwa ko wuta tana ci.” Kura kuma ta ce wa Kare: “Idan ka je kar ka buɗe tukunyar; ka iza wutar kawai ka dawo.” Sai Kare ya ce: “To, na ji.” Kare na isa murhu ya tarar wutar ta mutu; ko zafi ma sanwar ba ta fara yi ba.
Sai ya buɗe tukunyar domin ya ga abin da Kura take dafa musu. Kare na buɗewa sai ya ga ’ya’yansa suna mutsulniya a cikin ruwa. Bai yi wani ɓata lokaci ba, sai ya fitar da su. Nan da nan ya kamo ’ya’yan Kura ya sa a cikin tukunyar nan, ya nemo guma-guman itace ya haɗa wuta; ya ɗora tukunya a kan murhu.
Sai ya kai ’ya’yansa ya ɓoye a kan wata bishiya. Da ya koma wurin aiki inda Kura ke jiransa, sai ta tambaye shi: “Ka gyara itacen dai ko?” Ba tare da ya nuna mata abin da ya yi ba, sai kawai ya ce da ita: “E, na gyara, ƙanwar Zaki, surukar Damisa, kanwar Giwa!” A cikin murnar kirarin da Kare ya yi wa Kura da kuma zaton za ta ci naman ’ya’yansa, sai ta ci gaba da rera wannan wakar:
“Mu yi daka da wuri,
Kafin rana ta kai tsakiya,
’Ya’yan Kare sun sha wuta,
Sun kusa nuna.
Hum tiri hum.”
Sai Kare ya fara tasa waƙar yana cewa:
“Ka juye nawa ’ya’yan
Ka bar na an’uwana.”
Sai Kura ta ce: “Wace irin waƙa ce haka Kare?” Sai Kare ya ce: “Sanda kike yin taki waƙar, na yi magana ne?” Da jin wannan tambaya tasa sai ta yi shiru. Suka ci gaba da gyaran wake, har suka gama. Bayan sun gama aiki, sai Kura ta ce wa Kare: “Je ka ka ɗebo wake da shinkafa daga cikin tukunya mu ci.”
Sai Kare ya je ya ɗebo musu; ita tana zaton naman ’ya’yan Kare ne. Kura ta ci nama, ci irin na ƙeta da haɗama, har ta rage da nufin za ta kai wa ’ya’yanta. Sai Kare shi ma ya ce zai kai wa ’ya’yansa abin da ya rage. Da ta ji maganar Kare, sai ta fashe da dariya, amma ba ta yi wa Kare bayanin dalilin dariyarta ba.
Shi kuma bai tambaya ba. Suka tafi, kowa da nufin ya kai wa ’ya’yansa nama. Lokacin da Kura ta isa raminta, sai ta tarar saura ɗanta ɗaya. Sai ta koma da gudu ta tambayi Kare, “Ina ’ya’yana?” Sai Kare ya ce: “Da kika ɗora ’ya’yana a kan wuta za ki dafa, na tambaye ki ne?”
Sai Kura ta bi Kare da gudu za ta kashe. Da Kare ya ga haka sai ya ce da ’ya’yansa: “Ku miƙo mini igiya.”Suka jeho masa, ya kama, ya haye bishiyar. Da Kura ta kasa hawa bishiyar, sai ta ce wa Kare: “Za mu haɗu da kai.” Sai Kare ya ce: “Gobe ma zan je ɗaukar itace.” Sai Kura ta tafi abinta.
Washe-gari sai Kare ya ɗauki damin itace. Yana cikin tafiya sai ya hangi Kura tana zuwa. Sai ya shiga cikin itacen, yana mirginawa. Da Kura ta je kusa da itacen sai ta ce:
“Itace mai mirginawa!
Itace mai mirginawa!!
Ba ni hanya, ina neman Kare.”
Sai itace ya mirgina ya kauce, Kura ta wuce. Da Kura ta yi nisa, sai Kare ya fito ya ɗauki itace ya tafi zarafinsa. Da Kura ta komo sai ta sami Kare a kan bishiya, sai tace: “Kare jiya ka yi mini ƙarya, ka ce min za ka je ɗaukar itace, amma ban gan ka ba.” Sai Kare ya ce: “Jiya ba ki haɗu da wani itace yana murginawa ba?
”Kura ta ce: “Na haɗu da shi mana.” Sai Kare ya ce: “A garinku kin taba jin an ga itace yana murginawa shi kaɗai?” Sai Kura ta ce: “To, gobe ina za ka?” Sai Kare ya ce: “Gobe zan je in ɗebo ruwa.” Kura ta tafi, tana tunanin yadda za ta gama da Kare idan gari ya waye. Washe-gari sai Kare ya ɗauki tulunsa, ya je ɗaukar ruwa.
Sai ya hango Kura ta doshi rafin da yake. Sai ya shiga cikin tulunsa yana murginawa. Da Kura ta je kusa da tulun sai ta ce:
“Tulu mai mirginawa,
Tulu mai mirginawa.
Matsa mini in wuce, Domin ina neman Kare.”
Sai Tulun ya mirgina, Kura ta wuce. Da Kare ya auna, ya san Kura ta yi nisa, sai ya fito ya ɗauki ruwansa ya tafi. Daga baya kuma Kare da Kura suka haɗu, yana baya-baya da ita. Sai Kura ta ce: “Kare, ka yi min ƙarya.” Shi kuwa sai ya mayar mata da jawabi cewa, “Ba ki haɗu da wani tulu mai mirginawa ba?
Ai ni ne a cikin tulun.” Kura ta ce ta gamu da shi, ta sake tambayar sa cewa: “To gaya mini inda za ka gobe domin in sami damar gamawa da kai kowa ya huta.” Sai Kare ya harari Kura, ya yi mata kallon raini, ya ce: “Zan je su, watau kamun kifi a gulbin yamma da Dajin Saidawa.”
Washe-gari Kare da ’ya’yansa suka je su. Can sai suka ga Kura ta tunkari inda suke. Sai Kare ya ce wa ’ya’yansa duk su faɗa ruwa su buɗe haƙoransu. Har shi ma suka faɗa suka buɗe haƙoransu. Kura tana isa a gaɓar gulbi, sai ta ga haƙoran Kare da ’ya’yansa, sai tsoro ya kama ta. Sai ta ce wa ’yarta:
“Kilatanda! kilatanda!!
Baya baya ba ta.” Duk ta yi ’yan dube-dubenta ba ta ga Kare ba. Haka Kura ta gaji ta tafi. Da Kare ya ga lallai Kura ta tafi ba ta da nufin komawa bakin gulbi nemansa, sai ya fito da ’ya’yansa. Daga nan suka bar dajin nan domin kada wata rana tsautsayi ya sa Kura ta halaka shi da ’ya’yansa. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- In za ka gina ramin mugunta ka gina gajere, ba ka sani ba ko kai ne za ka faɗa.
- Rama cuta ga macuci ibada ce.
- Duk inda ka kai da wayo wani ya fi ka.
- Cin dare ɗaya kumburin ciki.
- Wankan wuta sau ɗaya a kan yafa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Naƙuda A Daji
Edita@rumasau-kallamu










