Tatsuniyar Marowata

0
5

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani mutum a wata ruga da ke gefen Dajin Ganji. Yana zaune tare da matarsa da ’ya’yansu biyu. Suna da matashin sa ɗaya. Wata rana mai gidan da matar suka yanke shawarar cewa ya kamata su yanka san nan su ci nama. To amma su marowata ne na ƙin ƙarawa.

Sai suka shirya cewa za su je dawa su yanka san inda ko ƙuda ba za su bari ya taɓa naman ba. Da zuwansu dajin sai suka tsuguna, suka yi kashi. Nan da nan ƙudaje suka rufe kashin; sai suka bar wurin wannan kashi, suka je wani wurin daban suka yi wani kashin. Nan ma ƙudaje suka yi cincirindo a kan kashin.

Da haka da haka har suka yi kashin da ba wani ƙudan da ya bi. Sai mai gidan ya ce: “To, a nan za mu yanka san nan.” Bayan sun yanka san tun kafin su feɗe shi, sai ga wani ƙaton Zaki ya zo, sai ya ce da su: “Kai, me kuke yi a nan?” Mai gida na jin haka sai ya ce da shi: “Mun yanka sa ne, to amma ba wutar da za mu gasa shi.”

Da Zaki ya ji haka sai ya ce: “To ku sam mini naman.” Duk da irin zafin rowarsu, sai suka yankar wa Zaki naman suka ba shi. Amma maimakon Zakin nan ya yi musu godiya sai ya ce: “Ku ƙara mini zan yi muku wata waƙa mai daɗin gaske.” Tun ma kafin su ƙara masa, sai ya fara rera waƙa yana cewa:

“Ɗan ƙanƙanen abin nan, dungum,

Waburga-burga ne, dungum,

Naburga a ɗanɗane ni, dungum.

Aboki yana kiran aboki, dungum,

Aboki yana kiran aboki, dungum.”

Da Zaki ya gama waƙar, sai suka sake yankar masa nama suka ba shi. Sai suka ce ya sake yin waƙar su ƙara masa. Da haka da haka, har naman ya ƙare. Sai suka ce da shi: “Ka ƙara yi mana waƙa mu ba ka ɗanmu.” Ba ko tare da Zaki ya yi gardama ba, sai ya rera musu waƙa, suka miƙa masa ɗansu.

Daga nan kuma suka ce ya ƙara yin waƙar, za su ba shi ’yarsu. Zaki kuwa ya rera musu har ma ta fi waƙoƙin da ya yi a ba ya daɗi. Yana gamawa suka danƙa masa ’yar maƙwabtansu da ta biyo su dajin saboda taya su aikin nama. Can sai mutumin ya dubi Zaki ya ce: “Ƙara yin waƙar nan in ba ka matar nan tawa.”

Abu kamar wasa, Zaki ya yi waƙa, mai gida ya ba shi matarsa. Abu kamar wanda aka jefa, sai ya ce da shi: “Ka ƙara yi zan ba ka kaina.” Zaki sa’a ta samu; sai ya yi waƙar, mai gida kuma ya miƙa kansa ga Zaki. A taƙaice dai Zaki ya sami uwa da uba da ’ya’ya biyu da naman saniya; sai ya kai su gidansa ya ajiye, ya tafi neman itacen da zai dafa naman san nan.

Kafin ya dawo mai gida ya kwashi iyalinsa da naman sansa sun gudu. Bayan mai gida da iyalinsa sun yi ’yar tafiya, sai ya tsaya ya ce zai ƙirga su, don ya tabbatar ba a bar kowa a gidan Zaki ba. To, idan ya taɓa matarsa sai ya ce: “Ɗaya.” Ya taɓa ɗansa ya ce: “Biyu.” Da ya taɓa ’yarsa ya ce: “Uku.” Sai ya manta da kansa, saboda haka lissafi bai tashi daidai ba.

Haka ya dinga yin wannan shirme, har wani mutum ya zo, ya ga abin da ke faruwa, sai ya ce da mai gida: “Idan na samo maka cikon mutum na huɗu lissafi ya cika, me za ka ba ni?” Sai mai gida da matar baki ɗaya suka ce: “Duk abin da ka zaɓa daga cikin abubuwan da muke da su za a ba ka.” Sai ya ƙirga su lissafi ya cika daidai.

Daga nan sai ya dubi mai gida da matarsa ya ce: “To, ku cika alƙawari.” Sai mai gida da matarsa da ’ya’yansu suka tuɓe takalmansu suka rife; mai gida ya gyara hularsa, matar ta yi ɗamara, ’ya’yan kowa ya shirya. Baki ɗayansu sai suka zura da gudu, suka bar mutumin yana mamaki, amma cikin raha, saboda ya ga gwanayen wauta. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Mai hankali ba ya rama mugunta da sharri sai da alheri.
  • Son kai yakan jefa mai yin sa cikin haɗari.
  • Marowaci yana iya zama tamkar dabba har ma ya cuci kansa.
  • Karshen azzalumi da-na-sani.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Wani Mutum Da ‘Yarsa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Wani Mutum Da ‘Yarsa
Labarin na GabaTatsuniyar Nasiru Da Nisiru
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.