Bahaushe yana da bukukuwan gargajiya tun kafin zuwan addinin Musulunci, daga ciki akwai na bauta, raya al’ada, aure, suna da mutuwa.
Daga cikin bukukuwan gargajiya akwai bikin buxin dawa, bikin shan kabewa, fashin ruwa, bikin noma, tuwon daji, tuwon qunshi, bikin sana’o’i (festival).
Bayan zuwan addinin Musuluci, Bahaushe ya qara da bukukuwan idin qarama salla (azumi) da babbar sallah (layya), maulidi, takutaha, daba (don tunawa da wani al’amari).
Domin karanta bayani akan Fasahar Bahaushe Danna nan
Bayan zuwan turarawa, party ko picnic (na tunawa da ranar haihuwa ko na bikin aure), qaddamar da ko buxe gini wallafa (launching/grand opening) da sauransu.
Wassani da Nishaxi
Bahaushe yana wasannin langa, iyon ruwa, tsiren gudu, kokawa, dambe, tauri, was an voyo, yara na ‘yar tsana, rawa, gaxa, carafke,. Bayan zuwan turawa aka sami karta da lido, sai kwallon qafa, da tseran babur, mota da keke.
Bayan zuwan addinin Musulunci kuma, Bahaushe ya qirqiri wasan tashe a lokacin azumi, domin tashin mutane sahur, hana albozaranci ko don nishaxantarwa (Ahmed, 1985).
Domin karanta cikekken littafin Danna nan